Author : MINAL SAEED Category : Romantic Hausa Novels
ta na ma sa salon shagwaba ji ya ke kamar ya sace ta ya gudu, a ban garen Iklima da nata gwarzon Aliyu jan zaki, suma sun yi zurfi a tasu soyayyar.
Bayan wata shida
Aisha na hango hannun ta ɗauke da yarinya yar wata biyar, cikin wata haɗaɗiyar doguwa riga tabi jikinta ta kwanta luf, kamar a nan aka halicceta, sai zuba ƙamshi take yi tana sakin murmushi, can na hango wasu kyakyawawan yara suna ƙwallo daga gyefen ta, dana kalle su da kyau sai naga ashe yan biyu ne, dana sake waiga wa sai na ga Zainab ƴar gidan Hajiya ana ta fama karatu domin dai yanzu haka suna shirye shiryen fita daga primary.
Wani tattausan kiɗa na ji yana tashi daga gyafe, ta miƙa zara zaran yatsunta ta ɗako wayar da kara a kunne, shagwaɓe fuska na ga tayi kamar zatayi kuka, can na ji ta ce “haba Yaya tun ɗazu na ke jiranka amma kaƙi dawowa, kasan fa lokaci na kurewa, ga shi Khairat sai kirana ta ke yi har ta gaji ta wuce,” “ki yi haƙuri. Quratul aini wallahi hold on ne ya riƙe ni amma ki bani minti biyar ga ni nan ƙara so wa.”
Yaya Sulaiman ke nan mai faɗa da cikawa, kamar yadda ya ambata a cikin mintuna biyar, sai ga hon din shi me gadi ya buɗe ma sa ƙofar ko fitowa bai yi, ba ta yafa mayafi ta ɗauki jaka suka fita ita da yara, suka ɗauki hanya suna tafe suna hira cikin wani holl naga ya na shigar da motar a hankali, ya nemi guri ya yi parking, tar na ga haske ya karaɗe gurin kamar ba dare ba, can na hango su Yaya Abubakar da amaryar sa Hanifa yana mata raɗa a kunne sai murmushi take yi.
Ina waiga wa na hango su Jamal da Haidar tare da amaren su, sai sakar ma juna murmushi suke yi, na ce lallai yau akwai shagali, biki uku a haɗe abun na manya ne, cewa na yi ba za'a yi shagalin nan babu yan the noble team ba, waya na ɗauko na fara kiran su ɗaya bayan ɗaya, aiko basu bani kunya ba, can na hango su suna shigowa, daya bayan ɗaya.
Mawaƙa kala kala suka ƙayatar da gurin diner da ake yi, Sulaiman ya na ta dama dama da matarsa, a zuciya ta na ce su Yaya Sulaiman an ƙi girma da soyayya a barma ƴan baya, washe gari ranar Juma'a haka na ga dan dazon jama'a kamar ana hawan idi, auren su Yaya Abubakar aka fara ɗaurawa, sai na su Jamal ya biyo baya, na su Iklima ne ƙarshe, Alhamdulillah naji angwaye na furtawa, ba su yi wata bidi'a ba walima kaɗai Sukayi bayan an ɗaura auren amare sun tare gidan su lafiya.
Bayan shekara biyu hayaniya na ji na tashi dana duba da kyau sai na ga ashe taron suna ake yi na Khadija Allah ya azurtasu da samu ƙaruwar ƴa mace kyakkyawa kamar Babanta ya yi kaƙi ya to far, can ha hango su Hanifa da Baby boy yayin da Iklima ke ɗauke da tsohon ciki, nace ma sha Allah da alamun dai ansamu ƙaruwar aure, Yarinya taci sunan Habiba sunan mahaifiyarsu Jamal ke nan zasu rinƙa kiran ta da Hibba.
Raziƙa
“Raziƙa wai ke ba za ki ta shi kije asibiti a duba ki ba ko, sai zama kike da ciwo a gida,” “Umma kenan zuwan me zan yi bayan na san abun da ke damuna, cuta ce kin riga da kin cuce ni, dan da baki nufi marayun Allah da mugun nufi ba da bai faɗa kai na ba, gashi nan ke ba a auren ba ba lafiya ba, nima na rasa lafiyata to yanzu wa gari ya waya Umma, arauwar nan in dai zaka ki bin abun da Allah da manzonsa suka ce wallahi ba zaka ga dai dai ba.”
“Hakane Raziƙa ni yanzu ga shi nan na rasa ƙafa ɗaya garin bin bokaye da malaman tsubbu, Allah ka yafe min laifukana a gareka suna da girma,” ta faɗi tana share hawaye da gyafen zani.
Abun da ya faru da Umman Raziƙa, bayan barinta gidansu Jamal, bata haƙura da bin bokaye da malamai ba, haka ta shirya dan zuwa gun wani boka da taji labari yana aiki kamar yankan wuƙa, ta samu nasarar zuwa ta amso magani da bokan ya bata, a hanyar ta ta dawowa tayi hatsari inda ta rasa ƙafarta ta hagu, aka kaita asibiti a nan ne aka rasa mai bata jini, Raziƙa tace a dibi nata ana aunawa aka sameta da cutar ƙanjamau, tayi kuka tayi nadama, Kuma ta ƙara komawa ga Allah.
Anyi anyi da ita taje asibiti amsar magani, da gwamnati ke ba masu cutar ta ƙi, a yanzu haka ciwon ya fara cin ƙafinta tana kwance a halin jinya gashi Umma ba ƙafa, “Raziƙa in dai har da gaske kin tuba, to umarni nake baki ba shawara ba, gobe ki shirya kije ki amso magani a asibiti,” “to Umma in sha Allah zan je,” “Allah ya yi miki albarka ya yafe mana zunubanmu,” “ameen.*
Zainab bayan komawarta gida, gidan Innatar ta koma amma tasha faɗa akan hukuncin data yanke, na tafiya bariki ta bar gida, ta bata haƙuri kuma tayi tuba na gaskiya, a haka Allah ya fito mata da miji me mata ɗaya da yara biyu ta aura dan ita Allah ya kare ta.
Nasiru ko sanadin kama matarsa da ya yi, da tsohon saurayinta yasa ya yanke jiki ya faɗi, ya kamu da cutar shanyewar barin jiki, a yanzu haka sai an kwantar sai an tayar Hajiya Uwa ana nan tsufa ya kara kamata, sai dai babu me kula da ita abun da zata ci ma, wani lokacin gagararta yake, sai ta yi bara.
“Qalbina” “na’am Yayana” “wallahi Aisha ina matukar ƙaunar ƙi, ƙi so ni Ishat kece silar kasancewata a rayuwa, kece silar dauwamar farin ciki a duniyata, kece silar dariyata”
“Kaine silar farin cikina, Yaya rai da zuciyata duk mallakinka ne, ina matuƙar alfahari da samunka a matsayin miji, Ina fatan rayuwa da kai har a aljanna ina son ka Sulaima”
“Na gode Aishan sulaiman” faɗawa jikinsa tayi suna dariya.
Tammat bi hamdalah duka duka a nan na kawo ƙarshen wannan littafi mai suna “KECE SILA” abun da na rubuta dai dai Allah ya hadamu a ladan wanda kuma na yi kuskure Allah ya gafarta mana.