Chapter 10 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 14

27K to 30K   out of 40.2K words

Cikeda farin ciki yake sake makalesu ajikinsa yana tambayar ya suka tashi,tsayawa kawai husnah tayi tana kallonsu zuciyarta na kuna kadan kadan, "kaji ai matsalar yanzu duk sun wani zo sun yanyameshi kamar zasu cinyeshi..." Tafada acikin zuciyarta cikin takaici,

Bilkisu kam ko kadan bata san cewa tare da husnah suke ba shiyasa tabi yara suka yimasa oyoyo kamar yadda suka saba,yar rada fahad yayi mata cewa,

"Tare da kanwarki muke..."

Jin abinda yace yasata janyewa daga jikinshi cikeda kunya ta waiwaya dan ganin husnah wacce ke tsaye ta harde hannuwanta akirjinta tana kallon kirsa da kisisina wurin bilkisu acewarta..........


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/25, 2:21 PM] Nawartye&: 15***D'an b'ata rai kadan husnah tayi ta dauke kai tana kallon gefe aganinta wannan ma ai cin fuskane da rainin wayo yau dinma duk da kwananta ne baza abar mata mijinta ba,

"Amarya barka da fitowa,kin tashi lafiya.... Bismillah ga breakfast nan akan table"

Maganar da bilkisu tayine yasata dan kallonta tare da dan sakin fuska wadda bai kai zuci ba,

"Lafiya lau... alhamdulillah,to nagode"

Kan table din taje ta zauna tana karewa falon kallo kasa kasa cikin ranta tana yaba haduwa da tsarin falon kai dama gidan gaba daya lallai Fahad yazama young millionaire kamar yadda aka jima ana bata labari sai dai aganinta baiyi sa'ar mata ba gashi juyashi takeyi yadda taga dama sai abinda ta sashi yakeyi, harta bude warmers din abincin tafara zubawa tana ci bai taso daga wurin yaranshi ba yana can tsakiyar falo nanuke dasu sunata yimasa surutu,hakan yasake kular da ita amma bata tankaba taci gaba da cin abincinta tana kallon yaran wadanda kamar kara aka tsaga dashi dan tsananin kamarsu dashi,gaba daya yaran kamarsu daya sak,

Bilkisu na tsaye tana kallonsu yana tsugunne tsakiyarsu yana gyarawa awwab belt din wandonshi yana yimasa stocking,dan gyaran murya tayi sannan cikin sanyin murya tace,

"Hanfa kubar Daddy haka yaje yaci abinci kunji.... Maza kuzo muje muci gaba da kallo..... ka rabu dasu kaje ka karya.."

Dagowa yayi ya kalleta bai kai ga yin magana ba saiga mariya tashigo rikeda humaida yar yaya Abba da alama daga gidanshi take,

"Yaya Fahad ina kwana? Anty ina kwana?"

Murmushi bilkisu tayi tana amsa gaisuwar sannan tana kokarin karbar humaida wadda ke hannun mariya shikuma Fahad yana cewa su hanfa,

"Yawwa to ga yayarku nan ma mariya tazo maza kuje ta kaiku ku gaida ayiyah..."

"Dama ita ta turoni indaukesu wai duk jikokinta suna gida amma banda su..."

"To Allah kiyaye hanya gasu nan debesu kutafi" Bilkisu tafada tana kokarin barin wajen,gaba dayansu mariya tasa agaba suka tafi banda Mimi ita kam ta makalewa babanta dan ko wurin bilkisu ma kin zuwa tayi saida ita yanufi dining inda husnah ke zaune tana kurbar tea amma zuciyarta babu dadi aganinta ba haka yadace yayi mataba tunda ita amaryace,

Zama yayi yana dora Mimi kan cinyarsa cikin murmushi Yana cemata,

"To banda kiriniya dai sweetheart....."

Dauke kai husnah tayi tana jinsa yana cema mimin,

"Kinga anty...zakije ki gaidata ko?"

Ita haushin yaran nasa ma gaba daya takeji ko meyasa oho, ita kam bilkisu bama tasan wainar da suke toyawa ba tunda su hanfa suka bi mariya gidan ayiyah takoma falo tayi zamanta tana chaten da maama kanwarta wadda ke cemata may be next week zata kawo mata yaranta wato hudah,abrar da Nana saboda zata raka abban hudah chairo zaije asibiti kasancewar yana dauke da ciwon sugar,har su Fahad suka gama karyawa tana zaune inda take tana shan hirarta da maama wacce ke tsokanarta tana tambayar wai ya kwanan amarya jiya ta iya bacci kuwa?

Maganar Fahad tajiyo daga bayanta yana cewa husnah tatashi suje wurin bilkisu akwai maganar da zasu tattauna,fasa fita husnah tayi tabi bayanshi tana harar mimi wacce ke ja masa kunne tana dariya shima yana tayata.

***

Tunda bahijja suka fita tare da faruk bata dawo cikin makaranta ba dama lokacin da suka fita wani wurin shakatawar batattun yara yakaita domin masu zama awurin duk bana kirki bane yaran masu kudine ke zama suna sheke ayarsu suyi shaye shayensu da zuke zukensu masu snooker nayi sannan masu karta nayi,

Shima saida yayi snooker din tana zaune kan kujera tana kallonshi gefe daya kuma tana dan kurbar bakin lemonta wanda yajefa mata wasu kananan kwayoyi guda biyu aciki,wayar da faruk din yakawo mata take dan dubawa gaskiya wayar mai tsadace ga kyau,

Zama yazo yayi akan kujerar dake kallonta yana kokarin kunna taba sigari,hannu tasa ta kade hayakin tana dan toshe hanci,

"Haba guy nafada maka fa bani son warin sigarin nan..."

"Am sorry baby..." Cire sigarin yayi yakashe yana kallonta,

"Baby nayi missing dinki.... Nima 2 days sai ahankaline, Dad ya rike komai Mom ta zugashi yadaina sakar min kudi....yanzu ma wannan sabuwar motar da Kika gani bai san na dauko ba kuma wallahi bazan koma da itaba sayar da shegiya zanyi..."

Saida ta dan ja numfashi sannan cikin sanyin murya tace,

"Guy akan me zaka siyar da ita? Tana da kyaufa"

"Tayi miki kyau?"

Daga kai tayi tana duba shafin Instagram akan wayarta,

"Shikenan nafasa siyarwa tunda kince tayi miki kyau zan barta muci gaba da dan basarwa da ita..."

Kafin tayi wata magana wayarta tasoma kida cikin sauri ta daga saboda ganin sunan yaya sagir dake jikin screen din wayar balo balo,

"Hello Yaya yanzu fa nake son kiranka inji ko ka sauka..."

"Na sauka yanzu bahijja,zuwana gida ma kenan... Dan Allah ki kula kinji...,ki dage kiyi karatu banda wasa da shashanci....ga antynki zaku gaisa"

"Insha Allah yaya zanyi yadda kace...toh bata"

Bayan sun gaisa da Marakisiyya sake karbar wayar yayi ya dan kara yimata nasiha sannan sukayi sallama,tagumi tayi ta zubawa wayar tata ido bayan sunyi sallama.

***

Gaba daya gidan cikin tashin hankali suke inka dauke baba kadai wanda yafisu tawakkali sannan kullum yake yimusu nasiha akan su kwatanta hakuri su rungumi k'addarar da ubangiji Allah ya saukar musu,tsakanin bahijja da shamsiyya kuwa ba asan waye yafi wani zubar da hawaye ba domin kullum ne sai kowaccensu tayi kuka sakamakon halin da ta tsinci kanta,gaba dayansu sun rame sun fita kamanninsu saboda tsabar tashin hankali,

Ita badiyya ma ko tsakar gida bata fitowa sai dai idan dole ce tasa amma rai da rai tana dakin gwaggo amarya ko na inna sabuwa.

Ayaune shamsiyya ta kudiri niyyar zuwa gidan abdurrahman debo kayanta tunda dai ta tabbata aure ya mutu,itada su zuhuriyya da gwaggo amarya suka tafi sukaje suka tattaro duk abinda yake natane sai magriba sannan suka gama suka dawo gida,daukar wayarta tayi ta tura masa text message kamar haka,

_Abban musaddiq naje na kwashe kayana kamar yadda ka bukata amma kasani har gobe kana nan makale cikin zuciya ta ina fatan ka maida ni dakina idan ka huce._

Tunda yaga sakon nata yayi biris da ita bai kulaba har sai lokacin da yazo kwanciya bacci sannan yatura mata sakon da ya daga mata hankali har ya hanata bacci a wannan dare,

Tana sakawa amrah Pampers domin kwanciya bacci text din nashi yashigo,daga wayar tayi daga kusa da ita tana addu'ar Allah yasa shine acikin zuciyarta,

Ai kuwa tana budawa taga shi dinne cikin sauri tafara karantawa kamar haka,

_Shamsiyya munyi rabuwa dake ta har abada saboda kinci amanata sannan kin ha'inceni....kisani ayanzu banda burin da yawuce na intaimaki baiwar Allahn nan da kikasa na batawa rayuwa nayi mata tabon da har abada duniya bazata daina kallonta dashiba,burina shine badiyya ta haihu lafiya bayan ta haihu zan aureta tunda shari'a tabani damar yin haka kuma cikin dake jikinta yanzu shi nake muradin gani domin ina mutukar sonshi....._

Ai bata kai ga karshen sakonba ta zabura ta mike har tana yarda amrah dake cinyarta saboda tashin hankali gaba daya jikinta rawa yake kamar mazari......


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/26, 10:47 AM] Nawartye&: 16***Cikin karaji wanda ke dauke da tashin hankali take furta,

"Wallahi bazai taba yuyuwa ba...kanwar tawa? Wallahi bazai yuyuba"

Zuhuriyya ce tashigo cikin dakin dan ganin meke faruwa saboda jiyo kukan amrah da sukayi wanda ya cika gidan,yashe zuhuriyya taganta akasa tana yin wani gigitaccen kuka yayinda itama shamsiyya ke nata kukan tana rikeda waya ta dora hannu daya aka,

"Wai anty shamsiyya meyake faruwa? Rasuwa akayi?" Zuhuriyya ta bukata,

"Zuhuriyya kinji abinda abban musaddiq yace? Nashiga uku wallahi sai na illata badiyya....meyasa zata munafurceni? Wai harni abdurrahman zai cewa yana son cikin dake jikin badiyya... Sannan wai ita zai aura idan ta haihu"

"Kawai fada fa yake anty amma taya hakan zai faru"

Jiyo kukan amrah wanda yaki tsagaitawa yasanya su Inna zuwa dan ganin abinda ke faruwa dan har lokacin yarinyar bata bar kukaba duk da tana hannun zuhuriyya tana faman jijjigata, zuhuriyya ce ta rattabo musu abinda ke faruwa kasancewar ita shamsiyya har lokacin kukanta yaki tsayawa,sakare dukkaninsu sukayi banda mahaifiyarsu wacce jin abinda zuhuriyya tafada yasata barin wurin takoma daki,

Shamsiyya kamar wata zautacciya tazama sai sumbatu take yi tana kiran sai ta balla badiyya,duk abinda akeyi badiyya na daki tanaji itama sai hawayen take fitarwa haba shiyasa ashe taga dazu yaturo mata da text message yana cemata Wai ta kwantar da hankalinta insha Allah shi zai zama gatanta sannan zai share mata hawayen da suke gudana a idanuwanta ahalin yanzu,

Wani kukan tasake fashewa dashi tana jin rayuwar duniya nafita daga ranta saboda wannan bala'in da take ciki ahalin yanzu gani take kamar duk duniya babu wanda yakaita shiga tsaka mai wuya,taya ma abdurrahman zaice wai zai aureta? Tayaya zata iya zaman aure dashi? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,

Tsabar tashin hankali tana daga zaunen da take jiri takeji yana daukarta,daren ranar bata samu bacciba,

Garin Allah na wayewa tafito zata shiga bandaki da buta ahannunta haka shamsiyya tafito ta shaketa tana kuka tana cewa,

"Wallahi baki Isa ki aurar min mijiba...ko mutuwa nayi balle ina raye, gara inkasheki kowa yahuta inyaso nima akasheni..."

Dakyar su mardiyya suka banbare badiyya daga hannunta,daki abasiyya ta mayar da ita wato dakin gwaggo amarya tana dafe da kirjinta suna shiga ta yanke jiki tafadi jini na fita daga jikinta cikin tsoro da fargaba abasiyya ta kwalla kara babu shiri kowa yanufo dakin ganin abinda ke faruwa yasa Inna sabuwa da gwaggo amarya fara neman agaji dan ahanzarta kaita asibiti dan jinine ke zuba bana wasaba.

Dakyar suka samu suka kaita asibiti mafi kusa nan aka karbeta aka bata gado,duk wasu yan bukatu da ake nema kama tun daga kan kudin magani da jini wanda za akara mata basuda shi saboda duk cikinsu babu wanda yakeda naira dari biyar tashi ta kansa,gashi baba yana wurin sana'arsa har lokacin ma shi baida masaniyar abinda yake faruwa,

Su shamsiyya na gida itada mahaifiyarsu da zuhuriyya da abasiyya dama da iya mardiyya kadai aka tafi asibitin,wayar badiyya ce keta faman kururuwa daga cikin dakin gwaggo amarya tun dazu wannan shine kusan karo na biyar da wayar keta faman kururuwar neman agaji,

Zuhuriyya ce takatse dinkin hular da takeyi ta mike tashiga dakin gwaggo amarya dan ta dauko,bakuwar number ce dan haka tayi azamar dagawa muryar abdurrahman taji yana cewa,

"Badiyya lafiya kuwa inata faman kira amma shiru ba adauka ba....hello kina jina?"

Jin muryar abdurrahman yasata saurin fita daga cikin dakin tana amsa masa da,

"Ba ita bace ita suna asibiti bata da lafiya....rikicine keta faman barkewa tsakaninsu da anty shamsiyya...dan Allah yaya abdurrahman kayi wani abu akai"

Kafin yabata amsa shamsiyya tafito ta warce wayar cikin kaushin murya tafara magana,

"Munafuki annamimi macuci...me kuma yahadaka da wayarta? Ko yanzunma laifinane? To cikin shege dai na barar dashi sai kasake zuwa kayi mata wani"

Cikin kaushin murya shima taji yace,

"Shamsiyya ina mai gargadinki akaro na biyu akan cikin nan mutukar yazube sai nayi shari'a dake dan ayanzu babu abinda nakeso sama dashi...."

Bai bari ta sake magana ba yakatse wayar mintuna ishirin tsakani sai gashi agidan lokacin baba mahaifiyarsu tasa shamsiyya agaba sai fada take yimata akan abubuwan dake faruwa,bai shiga gidanba yatura yaro yayi masa sallama da mardiyya ko abasiyya, abasiyya ce tafito domin ita mardiyya tana bayi,ganinshi yasata dan fadada murmushinta bai jira dogon bayani ba kawai yadauketa amotarshi suka tafi asibitin da aka kwantar da badiyya,

Shine yabiya komai da ake bukata na magunguna da kuma jinin da za akara mata daga karshe dai likita yasanar dasu cewa cikin dake jikinta yafita,

Duk da cewa cikin ba na halak bane saida yaji ciwon rasashi amma ita badiyya dadin jin hakan taji koba komai tarabu da kwallon mangwaro tahuta da kuda, lokacin data farfado zuhuriyya ce kadai acikin dakin ga kayan ciye ciye nan Kala Kala wanda abdurrahman yakawo wasu sabbin hawayen take sake zubarwa zuhuriyya nabata hakuri ahaka har iyayen nasu suka shigo,

Tun a asibitin lokacin da ta fara samun lafiya abdurrahman yafara nuna mata bukatarsa shiyasa take daure fuska da zarar taganshi tunda kullum yana asibitin, aganinta ko giyar wake takesha mezai kaita auren mijin yayarta uwa daya uba daya alhalin kuma tana raye? Kai ai koma mutuwa tayi bata jin zata iya auren mijinta,

Kwananta hudu a asibitin amma dai cikin hukuncin ubangi ba ayi mata wankin cikiba likita yace babu matsala dan harma ta dan warware kuma aranar ake son ma a sallameta dan harsu gwaggo amarya ma sun tafi yanzu daga ita sai mardiyya wacce itace ke bi mata,suna zaune kan gadon asibitin suna dan tattauna matsalar da tafi addabar gidansu ayanzu yashigo dauke da bakar leda a hannunsa na dama dayan hannun kuma wata blue din leda ce mai kyalkyali a rubuta kamore communication,daure fuska tamau badiyya tayi tana sake gyara zamanta yayinda ita kuma mardiyya cikin fara'a da sakin fuska tasoma gaidashi cikin sakin fuskar shima ya amsa mata sannan yaja farar kujerar roba wadda ke ajiye gaban gadon ya zauna yana kallon badiyya wacce ta tattaro girar sama da k'asa duk tahada ta daure tamau,

"Sannu yajikin?" Shiru tayi kamar bata jiba sai da ta dan ja lokaci sannan ta amsa cikin daurewar fuska,

"Dasauki..."

Ledar hannunsa yamika ya ajiye kusa da ita sannan cikin sanyin murya yace,

"Ga wannan..wayace na siyo miki sannan dan Allah inaso kibani koda mintuna biyune muyi magana..."

Sunkuyar da kanta tayi batare da tace komai ba hakan yabawa mardiyya damar tashi tafice daga cikin dakin,

"Badiyya kamar yadda na sanar dake abaya ayanzu banida matar da nake burin aura wacce ta wuceki....kiyi hakuri kibani dama domin nine na cancanci zama mijinki tunda nasan abunda yafaru....abunda yafaru wallahi k'addara ce tunda ba ason raina yafaru ba kema ba ason ranki yafaru ba sannan dukkanmu ba halinmu bane....yayarki ce ta zalunceni har nakai ga aikata haka dan Allah ki amince kibani dama..."

Cikin damuwa da bacin rai ta kalleshi,

"Allah ya sawwake in aureka wallahi"

"Badiyya....kalleni...kalli idona nace..."

Dagowa tayi ta kalleshi na tsawon 5 seconds sannan tajanye idonta,

"Kikace bazaki aureni ba? Saboda me?"

Maimakon tabashi amsa sai kawai yaga ta fashe da kuka nan taki cemasa komai sai kuka da taketa yi har yagaji yafita cikeda damuwa ahaka mardiyya tashigo ta sameta tana wannan kukan mai cin rai ita abu dayane yanzu ke sakata kuka zamanta a asibitin nan ya yi sanadiyyar da zazzafar kaunar abdurrahman ta shigeta batare da ta shiryaba tabbas wannan kaddarar biye take dasu tunda gashi tana jin abdurrahman acikin zuciyarta kamar jinin jikinta,yanzu menene mafita agareta?.

***
Zama dukkansu sukayi kan 3 sitter husnah na katarin Fahad wanda hakan yaso baiwa bilkisu dariya amma ta maze tana mikawa mimi hannu alamar tazo ta dauketa amma taki tasake makale fahad,

"Alhamdulillah.... husnah... bilkisu yau dai gaku kun sake haduwa amatsayin matana akaro na biyu.... Ina fata dukkaninku zakuyi hakuri ku hada kanku dan mugudu tare mu tsira tare....zaman lafiyarku shine zai zamemin jagora wurin yin adalci atsakaninku dan Allah kuzama masu hakuri acikin zamanmu sannan ku gujewa yan bani na iya wadanda ke yada maganganu na rikici tsakanin mutane.....ke husnah kece karama dan haka ina umartarki da kizama mai biyayya agareta, bilkisu kekuma ki daure ki rike girmanki dan Allah.... husnah kanwa take agareki kekuma husnah ki dauki bilkisu amatsayin yayarki.....insha Allah bayan nagama kwanaki uku adakin husnah zaku fara rabon kwana kamar yadda shari'a ta tanadar amma sai abinda muka shawarta yanzu atsakaninmu tukunna.... sannan maganar hada girki ko rabawa sai yanda kuka zaba tunda kune masu yi....... Bilkisu me zakice?"

Murmushi bilkisu tayi saboda yadda husnah ke sake matsar fahad abin nata sakata dariya acikin zuciyarta,

"Ranka yadade ai kagama magana sai dai ni in danyi tambishi kadan.... maganar rabon kwana ai ba yanzuba saboda idan kagama kwanaki uku adakin amarya ni nakara muku watanni biyu ciss yadda zakuji dadin kulawa da junanku.....sai maganar girki shima karku damu insha Allah kullum zan rinka girki daku ai anzama daya kuma husnah kanwata ce kamar yadda kafada....ko ba hakaba husnah?"

Cikin fara'a da sakin fuska husnah ta daga kai tana cewa,

"Hakane anty...nagode madallah Allah yasaka da alkhairi amma girkin ai da kin raba sai nima inrinka yi bazai yuyu kita shan wahala ke kadai ba"

Murmushi bilkisu takuma yi sannan tace,

"Babu komai amarya ai bazai yuyu inbarki kishiga kitchen tun daga yanzu ba kedai kawai ki kula da oga...."

"Insha Allah anty...." Husnah tafada tana yin kasa da kanta,duk hidimar nan da sukeyi Fahad najinsu sai watsawa bilkisu harara yakeyi afakaice amma taki yarda su hada ido, gaskiya bilkisu kishinta dabanne wato ita kuma da wannan damar zatayi amfani ta hukuntashi akan yimata kishiyar da yayi? Shi da wannan matakin da take shirin dauka akansa ai gara da tun farko hanashi auren tayi,yasan da biyu tafadi haka dan kawai ta hanashi kwanciyar hankaline tunda duk da cewa yayi sabuwar amarya ai kowacce mace daban take da yar uwarta,

Yana ji husnah sai faman zuba godiya takeyi tanata murna ita alallai wacce aka bawa kyautar miji har na tsawon wata biyu,tab ina ai wallahi hakan bazata taba faruwa ba inbanda shirmensu a ina suka taba jin anyi haka,

"To idan angama shikenan ni zan shiga ciki lokacin dora girki ma yakusa.... ango miko min Mimi muje ciki"

Wata lafiyayyar harara ya watsa mata sannan yamike yana rike da Mimi ahannunsa batare da yamika mata itaba yakalli husnah,

"Asma'u

10 / 14