Chapter 11 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 14

30K to 33K   out of 40.2K words

jeki part dinki ina zuwa bari naje dakina akwai abinda zan duba..."

Da to ta amsa masa tajuya tafita tana yiwa bilkisu sallama,tun kafin husnah tafita bilkisu tanufi hanyar da zata sadata da bedrooms dinta,saida yaga fitar husnah sannan yabi bayan Bilkisu yana faman yin kwafa tare da jan guntun tsaki bila adadin.....


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*

*_Ummi Shatu_*=?L? [1/27, 3:40 PM] Nawartye&: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*



17***Tana shiga cikin bedroom dinta ko zama bata kai gayiba sai gashi yashigo,ajiye mimi yayi wacce yake dauke da ita,

Juyowa bilkisu tayi ta kalleshi sakamakon karar rufe kofa da taji,

"Baby wai meye haka kike shirin aikatawa? Wannan wanne irin shirmeni kike kokarin yi? A ina kika taba jin anyi irin wannan shirmen?"

Tunda yafara magana kawai kallonsa takeyi har saida taji yayi shiru sai faman huci yakeyi alamar bacin rai yana rikeda da dukka kafadunta guda biyu,

"Shirme? Wanna irin shirme kuma?"

"Ohh tambayata ma kikeyi? Baby gaskiya idan kikayi haka bakiyi aiki da tunani ba sam....wacce matar kika taba jin ta sallama mijinta dan kawai yakara aure?"

"Idan babu matar da ta taba haka sai afara akaina....menene aciki? Ai kai godiya ma yakamata kayi,nagane kun jima bakwa tare da juna sannan abukace kuke kuma amatse da junanku shiyasa nabaku watanni kaga sai ku mori junanku sosai amma ai kwana uku yayi muku kadan...musamman ma ita da take yarinya nikuwa ai kaga na kwana biyu abunma yafara fice min arai.....kuje kawai Allah ya kaimu watanni biyu kamar yaune"

Jin abinda tafada yasake kular dashi barinma da yaga tanata wani murmushin da yakasa gane ma'anarshi,

"Ba wani fice miki arai da yayi....ai kinfi husnah bukatata ahalin yanzu,ke ai acikin jarababbun mata kina sahun farko...."

"To yanzu dai nace bana bukata kaje kaji da amaryarka ni abarni inhuta,hidimar yarana ma ta isheni"

"Wallahi baki isaba,idan ke kin barmata ni nikuma ban bariba... wannan wacce irin bakar mugunta ce? Tun wuri kifada mata dawasa kikeyi tunda dama ke kika fada tun farko tom....."

Daga haka yajuya zai fita ransa adan bace karo sukaci da mimi wacce ke bayansa atsaye,cikin sauri ya dagata ya dora kan gado yafice yana hararar Bilkisu,

"Zaki wani ce kin bamu wata biyu to me kike nufi da hakan? So kike Allah ya kamani da hakkinki ko me......"

Garam taji yarufe kofar bayan yafita yana ta mita,zama tayi gefen gadon tana lallaba mimi ko wai zata samu tayi bacci amma taki dole daga karshe sai goyata tayi saboda girkin rana take son dorawa,

Kitchen tashiga ta fara shirya abubuwan da yadace ta girka, lemon rice da miyar kayan lambu ta dora sannan ta dauko carrot domin hada juice,sai farfesun kaji,

Tana cikin kitchen tajiyo sallamar husnah da baki, yan uwanta ne dake nan kano sukazo kamar yadda aka saba sannan kuma wadanda zasu koma kaduna suma zasuyi mata sallama,da fara'a Bilkisu ta taresu suka gaisa sannan suka tafi,har part din husnah ta rakasu sai lokacin taga yanda aka shirya mata bangaren nata, komawa nata bangaren tayi taci gaba da girkinta tana dab da kammalawa yashigo yana rikeda ledoji a hannunsa,

Zuwa tayi ta karbi kayan hannun nashi tana kallon fuskarsa yayinda shi Kuma yake kokarin ciro wayarshi daga aljihun gaban rigarshi saboda neman agajin da ta fara yi,

"Hello ya Abba sakona yashigo kenan?"

Bata san me yaya Abba yace ba tajishi ya danyi dariya kadan sannan yace,

"Ai ni ba aminin gwauro bane biyu gareni...shikenan karka damu anjima sai nakawo maka"

Daga haka yakatse wayar yabita cikin kitchen din ta bayanta ya tsaya yana kokarin karbar mimi daga bayanta wacce tuni ta jima da yin bacci,

"Ji yadda kika langabarwa da yarinya kai sai wuyanta yayi ciwo....saukota inkaita inkwantar da ita"

Kunce goyon tayi batare da ta tankaba saboda tasan neman hanyar da zaiyi mata fada yakeyi tunda awuya yake da ita,

Ta can yawuce part din husnah bayan ya kwantar da mimi adakin bilkisu,kwance yasameta tana bacci sakamakon gajiyar dake tattare da ita ga tarin bacci dake idonta,bai tasheta ba yabi gefenta shima ya kwanta domin baccin yake ji shima sosai.

Bilkisu kuwa tana gama girke girkenta ta wuce bedroom ta sheka wanka sannan ta zauna ta dan yi kwalliya sannan ta saka maroon din atamfa mai adon flower ajiki,dan kwali ta daura ta feshe jikinta da turare sannan taturawa Fahad da text massage kamar haka,

_Ranka yadade lunch yazama ready,ko nan za akawo muku? Tunda ango kake._

Jin shigowar text massage din yasashi mika hannu ya dauko wayar yana rikeda husnah a kirjinshi ganin abinda bilkisu tace yasashi yin murmushi sannan ya mayar mata da reply kamar haka,

_Duk da ni angone ai dole nazo naga kyakkyawar fuska baby na duk da dai tana yimin rowar kayana amma wallahi kishirya karbata jibi..._

Kallon husnah yayi yace tatashi ta kintsa zasuje suci abinci bilkisu tace ta gama, tashi tayi idonta cikeda bacci tanufi toilet,

Bilkisu na falo tana zaune ta dora daya akan daya tana kallon tashar zee world suka shigo,ba Fahad ba ita kanta husnah saida bilkisu ta burgeta woww irin wannan kishiyar akeso wacce take jan ajinta yanda ya kamata yanzu gashi taci adonta sai zuba kamshi take sannan fuskarta awashe taboye kishinta acikin ranta,murmushi tayi ta mike tana cewa,

"Barkanku da fitowa amarya da ango.... Bismillah mu karasa kan table"

Binta sukayi abaya kowannensu yana kare mata kallo musamman ma fahad wanda kamar yaune yafara ganinta.

***

A farfajiyar club din suke zaune itada shi gaba daya wurin ya kaure da warin hayakin wiwi da na sigari,basu damu da kusancin dake tsakaninsu ba domin amanne suke da juna shi yana aikin shakar wata farar hoda ita kuma tana yin game awayarta,

"Guy yakamata inkoma hostel fa haka saboda nafada maka ranar Tuesday inada exam......"

"Babu matsala baby....yanzu abinda zai faru shine bari nakarasa wannan hawa network din sai mu wuce kawai...."

Cigaba yayi da shakar hodar ita kuma tana yin game dinta lokacin misalin karfe 12 saura na dare,kamar daga sama taji dirar mutane nan wasu suka zabura da niyyar guduwa amma kafin sukai ga hakan jami'an hisbah duk sun yimusu kofar rago sun cafkesu,har wadanda ke cikin club dinma suna cin karensu babu babbaka duk ankamosu anfito dasu kai tsaye office dinsu suka wuce dasu nan suka turasu cikin cell maza nasu daban haka suma matan nasu daban,duk hankalinta yatashi kasancewar wannan shine karo nafarko data tsinci kanta acikin cell,

"Nashiga uku ni bahijja gashi ranar Tuesday inada exam......innalillahi" tafada tana dora hannunta aka,gashi duk ankwace wayoyinsu an ajiye,kasa bacci tayi sakamakon cizon sauro da kukansa ga duhu,ahaka suka wayi gari nan akace kowa yabada number din iyayensa za akirasu,

Harga Allah ita kam bata son yaya sagir yasan da wannan al'amari amma yazata yi yazama dolenta tabada number shi kamar yadda suka bukata dan sunce idan mutum zai shekara anan bazasu sakeshi ba dole har sai wani nasa yazo yayi belinsa,

Aranar aka kira ya sagir aka fada masa shi kuwa faruk tuni har Dad dinsa ya aiko anfitar dashi bayan anja masa kunne,

Wurin lokacin sallar azahar Yaya sagir yazo,bata dai san yanda sukayi ba taga anzo anfitar da ita sai lokacin taji kunyar shigar dake jikinta wacce yaya sagir yahanata tunba yauba,baice mata komai ba yafita tana biye dashi bayan anbata wayoyinta da komai nata da suka karba.

Acikin mota ta sameshi zaune idanuwanshi jajur kamar garwashin wuta,hakanne yasata jin faduwar gabanta ta karu shiyasa adarare tashiga cikin motar ta zauna tana sussunkwi da kai ita kanta ta kasa gano irin hukuncin da yaya sagir zai dauka akanta,

Ji tayi ya finciki motar a tamanin,babu shiri ta sake tsintar kanta cikin matsanancin tsoro duk da cewa ba yaune karo nafarko da ta fara ganinshi cikin damuwa ba amma wannan yafi kowanne rikitata,

Saida suka yi nisa da hisbah office din suka kama hanyar makarantarsu sunje dan wurin da yake da karancin jama'a taji ya taka burki kuuuuuuuuu wanda yabada sautin wata kara mai firgitarwa,gangarawa yayi gefen titi yayi parking nan da nan tsoronta yasake ninkuwa domin bata da masaniyar hukuncin da zai dauka akanta gashi ransa daga gani yakai makura wurin baci.........


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/28, 2:49 PM] Nawartye&: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


18***Tunda yayi parking taga yafara kici kicin ciro belt daga jikinshi dama kuma kananan kayane sanye ajikinshi jeans da t shirt,

Tana son tagudu amma babu dama domin yarufe duka kofofin motar,juyawa tayi tafara kokarin budewa amma kafin ta bude tasoma jin saukar belt ajikinta babu kakkautawa dan dukanta yakeyi tako ina duk inda yasamu,kuka tacika motar dashi tana rokonsa,

"Yaya dan Allah kayi hakuri wallahi bazan sakeba....... Dan Allah yaya kayi hakuri..."

Baiko saurareta ba yaci gaba da laftarta duk ihun neman agajin da takeyi babu wanda ya kulasu bare har ace za azo cetanta saida yayi mata shegen duka duk ya farfasa mata jiki sannan yabarta,kuka take kamar zata mutu tana takure kasan kujera sai murkususu take yi,

"Daga kawoki shekaran jiya shine har kin fita dauko magana ko? Dama ba karatun kika dawo yiba yawon neman magana kika zo kenan? Ke yanzu har kinyi wayewar da Zaki rinka zuwa club?.......badake nake magana ba?" Ya karasa maganar da daka mata tsawa,cikin matsanancin kuka ta girgiza kai,

"Yaya sagir bafa club najeba wucewa nazo yi shine......"

Wani dukan yakai mata afusace babu shiri ta kankame jikinta tana sake sakin kuka,

"Yimin shiru ko nasake nada miki na jaki yanzunnan....shashasha kawai wacce bata san ciwon kantaba....anfada miki ban san duk abunda yafaru bane? Ai su wadanda suka kamaki din ba mahaukata bane da kawai zasu kamaki batare da laifin komai ba....duk abinda yafaru sun sanar dani komai,to wallahi wannan yazama shine first and last da zakije club....idan har hakan tasake faruwa babu inda zanje inyi belinki sai dai kiyita zama hannunsu har kimutu ko yunwa da sauro su kasheki...."

Sake fincikar motar yayi zuwa cikin University dinsu tana kuka tana komai ko kallonta bai sake yiba ya daka mata tsawa,

"Kwashi kayanki kibar min cikin motata..... stupid kawai"

Daukar komai nata tayi tafita tana kuka bai sake ko minti daya awurinba ya buleta da kura yakara gaba zuciyarshi na tafarfasa kamar zata kone domin babu wanda yake son yaga nasa acikin mummunan hali kowa so yake ace nashi shine yafi kowa afannin halin kwarai,

Takalmanta tasaka tana kuka ta nufi hostel batare da ta damu da kallon da sauran daliban dake harabar cikin makarantar ke binta dashi ba,

Da kuka ta bude cikin dakinsu ta shiga,lady na zaune daga ita sai half vest ajikinta da gajeren wando tana cin indomie da kwai ita kuma zeetah na kwance tana ta shakar bacci da gani syrup ta narka yayi mata mankas,

Ganin tashigo tana kuka yasa lady kamota ta zaunar da ita kusa da ita tana rarrashinta,

"Beauty.....meke faruwa? Yi shiru princess......waye ya taba ki?"

"Brother nane ya dakeni...."

Sai lokacin Lady ta lura da shatin dukan dake jikinta rado rado danma ba fara bace da sai yafi haka fitowa,cikin zaro ido lady ta daga body hug din jikinta gaba daya tun daga wuyanta zuwa cikinta dasu bayanta shatin belt ne sannan ga hannunta nanma harda gefen fuskarta,

"Ya salam....gaskiya brother bai kyauta ba,yi hakuri Queen..."

Bata kai ga yin magana ba taji wayarta na rero wakar p square,sam batayi niyyar daukar wayarba amma sai lady ta dauka ta miko mata tana cewa,

"Ki dauka boyfriend dinnan nakine faruk"

Karba tayi cikin kuka ta daga,jin tana kuka taji yarikice yana tambayarta meya faru? Babu amsa sai kuka hakane yasashi cewa gashi nan zuwa babu shiri,

Lady nata rarrashinta tana bata indomie din da tasameta tana ci faruk yazo,kayan jikinta kawai ta sauya da riga gown tafita,yana zaune cikin motarshi yar zamani sai sautin kida ke tashi tabude tashiga idanuwanta jajur,

"Am very sorry baby.....daina kuka, brother bai kyauta ba,waye yace masa ana dukan mace irin haka?"

Hannunta yakamo yana dubawa zuwa gefen wuyanta da fuskarta wanda duk wurin ya farfashe,

"Am very sorry baby......muje inkaiki clinic adubaki"

Bai jira cewarta ba yayi reverse suka fita daga makarantar har lokacin hawaye bai bar gudana daga idanuwanta ba,

Kamar yadda yace wani private clinic ya kaita can aka dubata aka bata drugs yadauketa zuwa cikin gari, fruits ya siya mata da drinks masu sanyi sannan suka juya dan komawa makaranta sai buga sitiyarin motar yake yana kiran,

"Gaskiya wannan brother din naki dan dai kawai shine ya dakeki amma wallahi da wanine sai ya kwana a cell...."

Ita dai tana jinsa batace komai ba hawayen da takeyi ma tasamu sun tsaya,tana jinsa sai faman lallashinta yakeyi yana yimata sannu da haka sukaje cikin makarantar,

Hannunta yakamo yayi mata kiss sannan cikin sanyin murya yace,

"Baby ki kula da kanki kinji.....sai zuwa anjima zan kiraki idan ban dawo ba"

Fita daga cikin motar tayi tana dan yatsine fuska kadan jin jikinta na amsawa tako ina sakamakon dukan da tasha hannun yaya sagir,

Tana daf da shiga hostel dinsu taji magana daga bayanta,

"Bahijja.... bahijja"

Waiwayawa tayi nan taga basira wato babbar kawarta ada,

"Bahijja lafiya kuwa kike?"

"Lafiya lau....."

Daga haka tashige hostel tabar basira atsaye tana faman kallonta,tana zuwa daki wanka tayi da ruwan dumi sannan ta kwanta sai lokacin taji tana bukatar kiran yaya sagir domin neman afuwar abinda ta aikata,

Har wayar tayi ta gama bai dauka ba nan tasake kira amma shiru bai daga ba tasan fushi yake yi da ita bana wasaba,shikuwa lokacin ma yana gida shigarsa kenan zuciyarsa duk babu dadi amma ya boyewa marakisiyya damuwarsa duk da faman tambayarsa da take tayi domin ranshi abace yashigo cikin gidan amma yaki sanar da ita duk da yafada mata cewar daga bauchi yake amma koda ta tambayeshi bahijja sai yace bai hadu da itaba domin wani uzurinne daban yakaishi garin shi ko nemanta ma baiyi ba, Allah sarki dan uwa rabin jiki duk da abunda tayi kokarin rufa mata asiri yakeyi,yana jin wayar da take yimasa yaki dauka daga karshe ma sai yakashe wayar tasa gaba daya.

***

Tunda aka sallami badiyya takoma gida al'amari yaki dadi domin fada yaki ci yaki cinyewa tsakaninta da yayarta shamsiyya saboda abdurrahman yace ahalin yanzu baida wadda yake mutukar so kamar badiyya,

Wani tashin hankali ita ma kuma yanzu jin sonsa take kamar zatayi hauka kai kamar bazata iya rayuwa ba ma idan batare da shi ba shiyasa zaman lafiya yagagara acikin gidan ko haduwa sukayi atsakar gida masiface zata tashi wannan dalilinne ma yasa badiyya tabar dakinsu takoma dakin gwaggo amarya rai da rai tana can shi kuwa abdurrahman bai daina nado kayan arziki yana kawowa ba gaskiya sai yanzu suka gane namiji baida ta ido domin shi harga Allah yanzu burinshi shine ya auri badiyya domin acewarshi shine yafi cancanta da ita,

Zaune take dakin gwaggo amarya ta bararraje bisa gadonta mai runfa tana yin waya, murmushi tayi mai dan sauti sannan cikin kasa kasa da murya tace,

"Nifa gaskiya yau sai ka sanar dani dalilin da yasa ka dage ka makale wai sai ka aureni.......ka fada min inaji"

Kwantar da murya yayi daga daya bangaren sannan cikin taushin murya yace,

"Saboda ina sonki...... sannan asahun mata kina gaba gaba...... badiyya wallahi duk namijin da ya aureki ya huta kuma yasamu rabin farin cikin duniya.....kinada wata baiwa ta daban wacce baduk mace keda ita ba ciki kuwa harda yayarki shamsiyya"

Sai yanzu ta fahimci inda maganar tashi ta dosa wato dai a fakaice yana yaba baiwarta ta 'ya mace,cikin damuwa da jin kunya tace,

"Ai ni wallahi ya abdurrahman kagama dani.......yanzu fanko kake kallona nasani"

Bataji abunda yafada ba sakamakon maganar shamsiyya da taji cikin kausasshiyar murya,

"Kan ubancan......yau za ayi bala'i agidan nan munafuka da mijina kike yin waya? Na rantse da Allah sai na koya miki hankali....." Ta kare maganar tana cukumo badiyya wacce ke zaune tana kallonta amma ta cire wayar daga kunnenta,

Duka takai mata tana cewa "wallahi ko ani ko ake"

Nanfa itama badiyya ta mike saboda tagama gajiya da wannan halin na shamsiyya nan suka fara dambatawa babu kowa agidan sai iyayensu mata domin su zuhuriyya duk suna makaranta,

Dakyar su gwaggo amarya suka rabasu tsayawa sukayi cirko cirko kamar wasu zakaru,

"Wallahi ku fada mata tafita daga hanyar mijina"

"Baza afita ba kuma son mijinki yanzu nafara.......aurenshi kuwa kamar anyi angama sai na aureshin inyaso ki mutu....."

Sake kokarin fusgewa shamsiyya take faman yi ahaka iya mai koko tayi sallama tashigo dauke da dan kullin kayanta ahannu wanda ta taho dashi daga kauye,

"Me kuma yake faruwa agidanne ni fatsima? Lafiya naganku cirko cirko kamar zakaru? Ke shamsiyya meya kawoki gida?"

"Alhamdulillahi iya mai Koko gwara da Allah yakawoki....." Inna tabawa tafada tana komawa gefe, dukkansu gefe suka kokkoma suka bata wuri tashiga dakin ta zauna,kowa zama yayi bayan ta zauna kasancewarta mahaifiyar baba wato kakarsu shamsiyya atakaice,

Babu abunda ska boye mata na daga abubuwan dake faruwa acikin gidan nan ta rike baki tana salati,

"Yanzu shine zaku maida gidanku gidan kokawa ko dambe? Tirkashi...... shamsiyya hali dai yana nan bai sauya ba ko? Kina nan da wannan bakin kishin naki.....to ai shikenan bari uban naku yazo ita badiyya tagama zama a wannan gida....kauye zan tafi da ita,kuna zaune garsama garsama daku agida amma babu hankali da tunani? Ubanku na can yatafi yana yimuku fafutukar abinda zai kawo muku kuci kukuma kuna nan kuna bawa hammata iska? Wadannan iyayen naku basu baku tausayi ba? Bakwa tunanin wata ta yanke jiki cikinsu ta fadi saboda bacin rai....."

Ta inda iya take shiga bata nan take fitaba har baba yadawo nan take sanar dashi kudurinta na tafiya da badiyya gano ko hakan zai kawo zaman lafiya agidan,

Badiyya tattara nata ya nata tayi shamsiyya sai faman yanka mata harara take kamar idonta zai fado itama tana ramawa,iya mai koko da niyyarta tayi kwanaki biyu agidan amma yanda taga lamarin yasa kawai

11 / 14