Chapter 4 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 14

9K to 12K   out of 40.2K words

ita tanata numfarfashi tana tartsatsin jini yara sai kuka sukeyi cikin tashin hankali ya kinkimeta yayi mota da ita, agigice hankali atashe ya tura yaran makota yanufi asibitin da suke zuwa da ita danma babu wata yar tazara sosai. Sosai hankalinsa yatashi lokacin da yaga annufi ICU da ita dakyar ya iya zuwa yayi salla yadawo, yana zuwa Dr bala yakirashi zuwa office dinshi,

"Manager meya faru haka? Garin yaya kayi sakaci wife dinka takamu da wannan cutar har tayi worst haka? How comes?"

"Dr meke faruwa? Meke damunta?" Ya tambaya hankali atashe,

"Maganar gaskiya har yanzu bamu gama gano damuwarta ba amma dai abinda mukayi nasarar fahimta shine tanada ciwon zuciya wanda yajima yana addabarta amma ba agane hakanba sai yanzu.... And abinda kuma muka kasa fahimta shine shin menene musabbabin wannan tsartuwar jinin da take yi... Gaskiya sai anyi dagaske idan bahaka ba komai na iya faruwa... Yanzu gashi kaje pharmacy ka samo wadanda magungunan kuma cikin hukuncin Allah mun samu nasarar tsayar da jinin da take tsartarwa...."

Hankalinsa atashe yakarbi takardar da Dr bala ke bashi yafita da sauri zuwa pharmacy. A asibitin ya kwana yanzu abubuwa biyune sukafi damunsa tunanin yaransu da suka baro a makota sai kuma tunanin halin da shamsiyya take ciki na halin rai kwakwai mutu kwakwai.

***

Bilkisu daga gidan shamsiyya gidansu tanufa, Ammah na ganinsu tasoma yiwa Mimi waka,

"Ga samodara mai cinye tuwo ga samodara mai shanye kunu... Kishiya ta biyoni har gida... Akoma bana maraba lale da ita"

Dariya bilkisu tayi ta sauke mimi tana cewa,

"Kinji abinda ammah ke cewa ko?,wai bata maraba dake kinzo cinye mata tuwo da kunu..."

"Kunu ansha... Momy"

Daga ammah har bilkisu dariya sukayi sakamakon jin abinda Mimi tafada cikin gwarancinta, zama bilkisu tayi suka gaisa da ammah sannan ta tashi ta hadowa Mimi kunu irin wanda ammah tasaba hada mata kullum shiyasa gata nan bul bul da ita,

"Mai gado dan Allah ki sake kwantar da hankalinki kinji... Komai mai wucewane wata rana sai labari, shi kara aure zuwa yakeyi kuma dan mutum yace zai kara aure bawai yana nufin cewa kai da yake tare dakai baka da amfani awurinshi yanzu ba, ko ni dinnan ban wuce akaro min kishiya yanzuba saboda wani karin auren sai agirma ake yinsa sai ku shafe shekara 30 ko fiyeda haka da mutum daga karshe yakaro maka wata.... Duk wannan tana cikin jarrabawar rayuwa...."

Wadannan sune ire iren nasihar da ammah ke ta yimata kullum shiyasa taji tasamu nutsuwa sannan hankalinta ya kwanta, wurin karfe 2:30 tabar gidansu takoma gida, sai da tayi wanka tasha kwalliya sannan tashiga kitchen domin dora girki,

Bayan ta gama tana shirya table fahad yashigo yasha kananan kaya, kallonsa ta danyi tasaki murmushi dan sai yanzune a wadannan shekarun yafito tsaf a prince dinshi, ko wanne irin kaya yasaka karbarsa yakeyi yayi masa kyau sannan babu mai ganinsa ya yarda akan yanada iyali,

Hancinta taji yaja hakan yasata saurin dawowa cikin nutsuwarta,

"Wannan kallon hajjaju kamar yau kika fara ganina... Dan Allah karki cinyeni mana" yafada cikin tsokana fuskarshi dauke da murmushi,

"Dan saurayi daga ina haka?" Tafada bayan ta rike kugunta tana kallonsa, shima kugun nata ya riko yahadata da jikinsa,

"Yanmata kin manta inda nafada miki zanje? Wurin aikin ginin nan mana yaufa aka fara..."

"Ohh haka... Mantawa nayine, kai dinne kayi kyau shiyasa duk na rude..."

Dariya yayi yasake matseta,

"Karki zugani mana infara daukar kaina wani handsome guy..."

"Da menene? Shine ai, dagaske kanada kyau fa... Muje kayi wanka kazo kaci abinci, idan kuma abincin zaka fara ci to"

"No, dake zan dai fara sannan wanka sai kuma inci abinci"

Harararshi tayi ta fara kokarin kwacewa daga hannunshi,

"Kai wai wanne irin mutunne.... Baka gajiyane wai"

"Yaro fa kika aura, ni wallahi ban gajiba..."

Da kyar tasamu ta lallabeshi ya zauna suka fara cin abinci,

"Yawwa baby.... Dama inaso in tambayeki, wai yanayin kayan lefe da zan hadawa husnah ya yakamata ayi?"

Sake gyara zamanta tayi akan cinyarshi ta dan kalleshi,

"Ka tambayeta ne?"

Girgiza mata kai yayi,

"No, dama inasone mufara maganar dake first kafin in tambayeta..."

"To ai gara ka tambayeta, kaga me yuyuwa ita ba kayan take bukata ba sai kabata kudi,kasan wasu matan akwai stage din da basu bukatar akawo musu kaya saboda sunada komai sunfi son abasu kudin may be sunada wani abu da zasuyi, wasu kuma basu bukatar kudi kayan suke so, kawai gara ka shawarceta kaji ita me take bukata? Inyaso sai asan abunyi..."

"Angama ranki yadade.... Ubangiji Allah yayi miki albarka"

"Amin, kayi kokari dai kagama komai kaga lokaci na karatowa..."

"Ai ko yazo babu damuwa tunda inada ke nasan zaki taimaka min tunda ke hajiya ce..."

Dariya tayi taja hancinsa,

"Baka da matsala, da kudina zan hada maka lefe amma sai zaka kara wani auren..."

Waro ido yayi ya kalleta tareda buda baki,

"Mekike nufi? Mata uku fa... Sai kace wani namamajo...."

Dariya tayi ta hade fuskarsu wuri daya,

"Maida idon guy.... Ba namamajo bane but...."

Dan ja baya tayi ta tashi tayi ready din guduwa sannan ta kalleshi,

"Ba na mamajo bane amma ai naga kai din harijine...."

Kafin yamike ta gudu tayi hanyar bedroom dinshi, tana shiga kafin tarufe ya cimmata,matseta yayi yana haki sakamakon gudun da sukayi,

"Wa kika cewa hariji?"

Cikin numfarfashi ta lumshe idonta,

"Ba kaiba.... Da kaina nake"

Daga shi har ita dariya sukayi ya lakuce mata hanci,

"Matsoraciya.... Ashe dai ana tsorona..."

"Sosai ma kuwa.... Dan sassauta min rikon kar na balle"

Dariya yayi yakarasa dasu saman gadonshi suka zauna suna ajiye numfashi.

Sun samu kyakkyawar fahimta atsakaninsu ita gaba dayama wani lokacin mantawa takeyi da wai zai kara aure domin tacire abin aranta ta rungumi mijinta da yaranta, kowa yaji dadin ganin bata tashi hankalinta ba musamman ma shi uban gayyar shiyasa yadda yabawa husnah zunzurutun kudade amadadin kayan lefe da sauran kayan al'ada haka ya lale yabaiwa Bilkisu baiyi ko ragin ficika ba kuma bikin yarage saura sati hudu yabiya musu umarah gaba dayansu har yaransu sosai kuwa Bilkisu taji dadin wannan tafiyar domin lokacin da taje dakin Allah addu'a tayita kwararawa mijinta da yaranta da kuma ita kanta satinsu biyu suka dawo gida bayan ta lodo kayan bacci na garari da sauran kayan shan iska, suna dawowa kuma suka fada shirye shiryen biki domin saura sati biyu ba wasu yan kwanaki yanda ake yiwa amare gyaran jiki haka itama su maama suka matsa mata akazo ana yimata sai lokacin ta fahimci ashe gyara na kowacce mace ne bawai sai iya amarya ba kema amatsayinki na uwar gida idan kikayi hakan na kara daga darajarki a idon mai gida, gyara kam itama tasha shi sosai sannan tayi kunshinta da gyaran kai, wannan karonma yan uwan husnah yarage saura kwana biyu daurin aure sukazo sukayi jere, yanzu kusan kullum gidan baya rasa jama'a dama su hindu kam kullum sai sunzo tunda yanzu dukansu sunyi kafa dan lokaci guda Abba yasiya musu motoci su hudun gaba daya iri daya sai banbancin kala shiyasa fita bata yimusu wahala shikuwa fahad kullum cewa Bilkisu yake ya yarda idan mace tayi mota tafi yawo saboda itama yanzu kullum fita bata yimata wahala dan wani lokacin ma sai dai takirashi ko tayi masa text taje wuri kaza.

Kai idan kaga Bilkisu tabbas sai ta burgeka domin babu damuwa da tashin hankali atattare da ita tayi kyau abinta kuma abinka da mai shayarwa acike take dam babu batun rama bare komadewa, daga ita har yaranta tsaf suke suma matan anyi musu kunshinsu da kitso, ango kuwa ba zama saboda wani aiki da ya tago na gina babban boutique kamar yadda Bilkisu tabashi shawara abaya, har ana igobe daurin aure bai samu zamaba dan sai dare yadawo lokacin kowa yatafi sai hajiya iyallo da tazo daga garko su maama suka roki ta zauna ta kwana dan ta debewa Bilkisu kewa, Bilkisu najinsu sunata jan juna da fada itada fahad daga bisani tatashi tashiga dakin yara tana cewa,

"Ni kaga tafiyata wannan kallon abun nasarar taku mesaka hawaye ya isheni"

"Bazaki jira muyi hiraba.... Koda yake jekima da kayan tsufanki ni ga matata saita tayani hirar..."

"Ku kwana anan karewar so..."

Daga bilkisu har fahad dariya suka yi bata sake saurararsu ba tashige daki, tashi bilkisu tayi takoma kusa da fahad ta bigeshi da kafadarta sannan tasaka hannunta ta sakalo kafadarshi,

"Baby albishirinki....."

"Goro...." Tafada tana lumshe masa idanuwa,hannunta yakama tiryan tiryan tana biye dashi har zuwa yal???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wataccen compound din gidansu wanda yake tarwal da hasken wutar lantarki tamkar rana, wata arniyar mota tagani hamshakiya sai uban sheki takeyi ash colour kirar kamfanin Toyota amma wannan latest one ce,key din taji yasaka mata aciki sannan ya rungumeta ta baya,

"Ohh my God.... Woww.... Bae me zan gani?" Tafada cikin rudewa saboda tsabar murna,

"Baby takice... Ke na siyawa"

Rufe bakinta tayi da dukkanin hannayenta tana murna cikeda farin ciki tace,

"Baby I don't know what to say.... Ohh my God"

"But u have to say baby..."

Hannayenshi tarike wadanda ke zagaye da cikinta,

"Yes... I have to say but don't know what to say..... Thank u bae..... thank u for being part of my life......"

Har gaban motar suka karasa takare mata kallo suna rungume da juna, sai wurin 11 saura suka shiga ciki,wanka sukayi cikeda farin ciki sukayi shirin bacci. Tana kwance jikinsa shikuma yana dan yin chaten wanda tasan kila da amaryar ne yadan kai kamar mintuna biyar sannan yakashe wayar ya kalleta,

"Bani labari...."

"Wanne labari kuma? Dan Allah kawai yi barci gobe ne fa..."

Dariya yayi yariko hannunta yana gani,

"Lokacin da kina karama me kikayi wanda har gobe idan kika tuna kina jin kunya....?"

"Tabdijam naki wayon, infada kayi min dariya?"

"Allah bazan yiba, nimafa zan fada miki nawa"

"Ok kai kafara fada to...."

Dariya taga yayi sannan ya shafo gemunsa,

"Wata tambaya na taba yiwa su mamuh lokacin fa harda su ya auwal awurin wallahi kawai nayi subutar baki.... Ni kullum idan ayiyah ta kunna radio ko mamuh sai inji ana cewa saduwa to kawai ranar sai cewa mamuh nayi wai mamuh menene saduwar nanne....?"

Bude baki bilkisu tayi alamun mamaki sannan tafashe da dariya,

"Wacce amsa suka baka?"

"Wata harara mai kada yan hanji ayiyah tayi min ita kuma mamuh tace inbari zata fada min idan nagirma lokacin i was in jss 3,amma kin san bayan nan saida nasake wata tambayar bayan wannan.... Nacewa mamuh menene wankan janaba shima tace inbari idan nagirma zata fada min....."

Dariya bilkisu keyi sosai harda neman kwarewa,

"Gaskiya ka iya tambaya..."

"Shiyasa ai lokacin da zan kai maganar aurenki gida nayita jin kunya saboda nasan ina cemusu zanyi aure zasu tuno da tambayar da nataba yimusu kinga kenan nasan amsar yanzu shiyasa zanyi aure...."

"Kai gaskiya kanada fitina tun baka tafasa ba kafara konewa"

Dariya yayi ya rungumeta tsam ajikinsa yana sinsinarta. Asubah tagari.

***

Kwanan shamsiyya daya a asibiti aka sallameta bayan Dr bala ya korawa abdurrahman jawabi kamar haka,

"Matarka tana bukatar kulawa da bata farin ciki, aguji bata mata rai domin hakan na iya sakawa zuciyarta ta buga har takaita ga rasa ranta.... Dan haka akiyaye aguji sakata cikin damuwa domin lalurar dake tare da ita ta tsananta"

Shiyasa tunda suka dawo gida abdurrahman yarasa abinda keyi masa dadi, indai hakane kuwa to yazama dole ya hakura da wannan auren da ya daura aniyar yi ko dan lafiyar matarsa, zama yayi ya fuskanceta tana tsaka da cin ayaba,

"Shamsiyya ki kwantar da hankalinki, maganar auren da nake shirin yi nafasa....."

Wata irin ajiyar zuciya ta ajiye tana jin sanyi acikin ranta tamkar an tsomata a kankara......


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Aisha_*=?L? [1/21, 5:06 AM] Nawartye&: 6***Yamutsa fuska taci gaba dayi tana cin kayan marmarinta tamkar bata farin ciki da abinda yafada amma acan kasan ranta jinta take yi tamkar ta tashi tayi tsalle akan kaya kokuma ta zuba ruwa akasa tasha dan tsabar farin ciki da murnar da take ciki,

"Shamsiyya dan Allah kiyi kokari kicire damuwa daga ranki, idan har auren da zanyi shine ke yunkurin sakawa ki rasa ranki to ki sanyawa zuciyarki salama domin nahakura kuma nafasa.... Sauran bayani kuma ni nasan yanda zanyi dan shawo kan matsalar... yanzu ga magungunanki nan da Dr bala yace kar kiyi sakaci dashi kina gama cin abincin nan ki dauka kisha.... Ni inasone zanje office saboda akwai muhimman aikin da nabari inaso naje naduba sannan dan Allah da zarar kinji wata matsala ki sanar dani, kuma kamar yadda kika bukata na kar na fadawa gidanku saboda gudun tashin hankalinsu to ban sanar dasu dinba.... Bari naje, ko akwai abinda kike bukata?"

Girgiza kai tayi alamun a'a ganin haka yasashi tashi yafita yabarta tana mai cigaba da ciye ciyenta tana yamutsa fuska, tana nan zaune yasake shigowa bayan wasu mintuna yana sanye da manyan kaya yasha farar shadda da hula,

"To ranki yadade ni zan fita..."

"Adawo lafiya"

Juyawa yayi yafita tana ganin haka tamike tsaye ta fashe da wata gigitacciyar dariya sannan ta hau taka rawa tana juyawa saida tagama sannan ta babbali magungunan dake cikin leda da sunan nata tawuce toilet taje ta watsasu cikin toilet tayi flushing dinsa sannan ta sheka wanka tasha kwalliya ta dauki wayarta tafita falo ta zauna tahau network, duk wadanda ada suka san mijinta zaiyi aure ayau tana mai farin cikin sanar dasu ai anfasa,

"Aikin banza.... Hauka nakeyi da zan bari ayi min kishiya? Ai wallahi nida kishiya sai dai inji anayi badai ni ayi min ba,haka kawai matan nan nayanzu masu budadden ido akawo maka su ko akawo maka kajaga.... Ko kuma kwarkwasa" Tafada cikin fada tamkar ba ita kadaice acikin gidanba, group din yan class mate dinsu na secondary tashiga tana bin chat dinsu daya bayan daya tana dubawa tamkar a mafarki ta ga bilkisu ta tura invitation card din bikin mijinta fahad da husnah,

"Kan ubancan.... Gaskiya labour bazata taba canjawa daga sakaliya ba... yanzu dan kawai mijinta zaiyi aure shine zatabi ta kanainaye tarinka farin ciki tana nunawa duniya tana murna da auren? Wai ita ga matar mamman ko, to ai ko matar mamman din agaske bazata yi abinda tayi ba.... Mtswwww wallahi dai Allah wadaran halin wasu matan..."

Khulsum tabi private chat tana sake balbala masifa akan abinda bilkisu tayi domin taga ita bilkisun bata online.

Tun daga wannan rana da ta tabbatar da cewa abdurrahman yafasa auren da yake da niyyar yi ada kamar yadda yafada tasaki ranta komai yakoma normal kamar da domin hatta danginshi da sauran yan uwansa sun san da maganar fasa auren duk da har gobe babu wani kwakkwaran dalili wanda yasanar musu cewa shine musabbabin faruwar hakan, amma komai wanda yakai gidansu yarinyar yace yayafe yabar mata kar akarba, da tambaya kawu musa mai kwano yatisashi agaba kan yafadi dalilinsa nafasa wannan auren saboda yana nema ya mayar dasu kananan mutane amma yace babu dalilin komai kawai dai shi ya canja ra'ayine, babu yadda suka iya haka sukaje gidansu yarinyar da yake neman aurenta ada suka sanarwa da iyayenta wannan bakin labarin,nan suka karbo kayan lefensu duk da shi abdurrahman din yace ya yafe kayan,

Shi kansa abdurrahman din yana cikin damuwa amma babu yadda ya iya dole yahakura bawai dan yanaso ba saboda idan bai bi wannan matakin ba wurin samarwa kansa mafita yana iya rasa matarsa to kuma wacce amsa zai bawa yaransu da iyayenta a lokacin da sukaji cewar shine yayi sanadiyyar mutuwarta dan kawai son kai irin nashi? Wannan dalilinne yasashi yin watsi da komai ya rungumi matarsa suka cigaba da zamansu cikin kaunar juna kamar da domin yanzu babu bakar magana bare harara sai zaman lafiya.

***

Zaune take kan wata kujera wacce aka yi da siminti acikin wani jeji mai cikeda bishiyoyi da sauran shuke shuke tana sanye da dogon hijabi har kasa fuskarta sharkaf da hawaye sai faman kuka takeyi tana shessheka,

Ahankali ta zauna kusa da ita ta dafa kafadarta,

"Bahijja wai meyasa kike son ki mayar da bacin rai da bakin ciki abokin rayuwarki ne? Duniyar nan fa dole sai kana mantawa da wasu abuwan idan bahaka ba bakin ciki ya jaza maka hawan jini yazama ajalinka..... Nafada miki inada hanyar taimakonki amma kin ki sanar dani damuwarki.. Ki fada min dan Allah"

Idanuwanta jajur fal da hawaye ta kalleta,

"Azima bazaki taba fahimta ba amma abinda nasani kawai shine zan cigaba da rayuwa cikin bakin ciki domin narasa farin cikina na har abada..."

"A'a bahijja daina fadar haka... Akwai solution mutukar kin sanar dani damuwarki... Zan taimaka miki da maganin bakin ciki da damuwa"

"Azima ina mutuwar sonshi kamar raina sai dai kash..... Ya rabu dani adaidai lokacin da nake bukatar kasancewa tare dashi... Ya barni batare da nasan laifin da nayi masa ba..."

"Bahijja waye? Waye shi?"

"Abu Arqaam...." Tafada idanuwanta nasake tsiyayar da hawaye,

"Karki damu bahijja akan namiji bai kamata ki rayu batare da farin cikinki ba... Ungo kisha... Karbi tun ranar nan da na fahimci kina cikin damuwa nabaki kika ki karba..."

Wata robar lemo ta dauko mai dauke da bakin abu aciki ta mika mata, runtse ido bahijja tayi takarba tabude amma har takai robar bakinta sai kuma ta tsaya cak nan azima tashiga karfafa mata gwiwa,

"Kisha kawai bahijja idan fa baki shaba wallahi wannan damuwar bazata taba sakinki ba... Bana son ki rayu cikin bakin ciki"

Jin irin maganganun da azima ke fada yasata kai robar bakinta ta daga ta shanye tas duk azima na kallonta tana sakin murmushi mintuna kadan wadanda basu gaza biyuba zuwa uku tafara layi tana surutai,

"Wallahi ina sonshi.....daukeni ki kaini wurinsa..."

"To shikenan muje na kaiki.." Azima tafada tana murmushi tareda tarairayar bahijja akafadarta ta daukar mata handbag dinta, tsakanin inda suke da hostel akwai yar tazara amma haka ta daure suka shiga cikin hostel. Direct daki mai number 29 tawuce da ita tana ta murmushin jin dadi, wasu yan matane guda biyu kowacce akusan rabin tsirara domin dagasu sai pant da bra, bisa gadon kasa ta kwantarta sharaff sannan tajuya ta kalli daya daga cikin yanmatan wacce ta kasance fara katuwa tace,

"Lady nagama aikina.... Yau ga bahijja kuma sai yanda mukayi da ita"

"Weldon azima.... Zeetah gafa haja da duminta...."

Wacce aka kira da suna zeetah itace ta taso tazo tafara zare hijabin dake jikin bahijja.....

*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa

4 / 14