Chapter 5 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 14

12K to 15K   out of 40.2K words

ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 5:08 AM] Nawartye&: 8***Tamkar tajuya takoma da gudu haka takeji amma kuma tasan bata da mafita saboda yaya sagir yarigada ya ganta, jikinta na rawa ta nufi wurinsa sai jan mayafin dake kanta takeyi ko zata samu ya rufe mata jiki amma ina girmansa bai taka kara ya karya ba,

"Yaya sagir yaushe ka....."

Wani mugun kallon da ya jefeta dashine yasata kasa fadin abinda tayi niyya nan take tasake tsurewa cikinta yashiga kiran kululuu, takowa yayi zuwa kusa da ita,

"Wuce mu tafi gida..."

"Yaya sagir kabari na canja kaya dan...."

"Zaki wuce ko sai na farfashe miki baki? Wuce mutafi"

Tun daga nesa basira tahangosu lokacin da take tahowa amma kafin ta karaso har yasaka bahijja amota shima yashiga ya finciki motar da karfi yabar wurin shiyasa basira bata tarar da komai ba face kura,

Tunda suka dauki hanyar kano take faman rusa kuka gashi karar wayarta na ta sake kular dashi Wanda Karo na uku kenan ana kiranta amma bata dauka ba domin faruk ne idan tayi garajen dauka zata kara cikawa kwabarta ruwa,

"Kiyi min shiru ki hadiye kukan nan sannan ki kashe wannan mahaukaciyar wayar taki tun kafin na fasa shegiya....."

Hadiye kukanta tayi sai aikin hawaye da taketa malalarwa kamar anbude famfo, yau kam tasan kashinta yabushe domin yaya sagir akwai dacin rai sam baya wasa da yara bare har su samu sukunin kawo masa raini, tunda suka fara tafiya bata juya ta kalleshi ba dan tasan bazata ga da kyau ba akan fuskar tashi, baice mata uffan ba kuma bai tsaya ako inaba har saida sukaje cikin kano lokacin misalin karfe 1 da wurin rabi na rana, kai tsaye gidansu yawuce dasu tun kafin yakarasa parking ta balle murfin kofar ta fice da gudu shikam anutsensa yafito ya daka tsalle ya janyo rishe daga jikin bishiyar maina ya karyoshi sannan yabi bayanta zuwa cikin gidan.


***

Yau takama ranar daurin auren fahad da husnah tun bayan da bilkisu tayi sallar asubah bata samu ta koma bacci ba tanata kaiwa da kawowa shikuwa ango yana dakinshi kwance yanata shan bacci sakamakon jiya sun raba dare suna hira da bilkisu basu yi bacci da wuri ba, saida tagama hada masa breakfast da komai sannan ta nufi dakin nasa lokacin karfe 8 saura nasafe,

A bararraje ta ganshi ya makale pillow, sunkuyawa tayi ta dan bugi kafadarshi kadan,

"Ango atashi haka mana.... Yaunefa ko ka mantane.... Tashi pls karka makara"

Janyota taji yayi ya rungume bayan ya matsar da pillow din dake jikinsa ada,

"Dan Allah yau ba ranar fitina bace katashi kayi wanka kashirya 10 fa zaku tafi..."

"Karfe nawa yanzu?" Yatambayeta bayan yadan bude lumsasshun idanunshi yana kallonta,

"Karfe 8 takusa fa...."

"To ai dasauran lokaci baby love...har zaki bani breakfast..."

"Karka damu gashi nan nashirya maka dama... Tashi kayi wanka dan saurayi..."

Murmushi tasashi yi bai shirya ba,

"Idanma zolayata kikeyi babu wani abu...."

"A'a ni na isa? Nidai katashi pls"

"Wai dan Allah meyasa kike min rowane kwana biyun nan?"

Murmushi tayi ta shafi kansa,

"Yaufa nafara hutu.... Garama kasani...."

"Karya kikeyi.....ke ai bakya mensuration idan kina shayarwa ko kin zata namanta?"

"Naji dan Allah tashi... Kaji"

"Wai jiya ni kika yiwa wayo ko? Akomai dai sai kin nuna min kin rigani zuwa duniya...."

Dariya tayi ta tashi zaune tana fadin,

"Nidai bari naje nayi wanka.... Ina son yin hoto da ango kafin yafita kowa yaganshi"

Sake rungumota yayi,

"Let's do it together.... Please"

Makale kafada tayi tana kokarin zamewa,

"No kaje kayi kai daya..."

"Ni ban yarda ba, tare zamuyi"

Babu yadda ta iya haka dole ta biye masa suka shiga wankan tare wankan da ya daukesu tsawon lokaci dakyar ta samu ta banbarosu suka fito kowannensu daure da towel,

"Ina zuwa... Please ka shirya kafin nadawo"

Tafada tana saka babban hijab, fita tayi daga dakin ta nufi nata bedroom din,zama tayi ta shirya kanta cikin wani tsadadden leshi dark purple dinkin riga da skirt Wanda yayi mutukar amsarta, kwalliya tayi sosai tasha powder da janbaki harda jagira, kafa dauri tayi tasha turare tafita tana gyara sarkar Indian gold din da tasaka a wuyanta wacce take faffada domin ta cika mata wuya,dakin yara tashiga nan ta iske iyallo nata drama dasu hanfa wai ita sanyi takeji tagaji da wannan sanyin dake cikin dakin kamar ana zuba kankara shiyasa duk tabi ta kudunduna abargo sukuma su maryam suna shirya su Mimi da awwab ita Mariya tana bathroom tana yiwa Muhammad da hanfa wanka, gaida iyallo tayi suka gaisa iyallo nata fadan wannan sanyin da suke sakawa yara,

"Woww Anty wallahi kinyi kyau..." Maryam tafada tana dariya, jin haka yasa Mariya fitowa daga bathroom domin ganewa idonta,

"Woww Anty kamar ma kece amaryar....." Inji Mariya,

"Nagode maza ku gama shiryawa Ku fito Ku karya ga abinci can nashirya..."

Juyawa tayi ta kalli iyallo,

"Hajiya iyallo bari akawo miki naki nan ko?"

"A'a bar abincin nan yanzu sai zuwa anjima zan fito"

"To shikenan bari naje na sallami oga"

Juyawa tayi tafita takoma dakin fahad wanda ke zaune gefen gado yana sanye da blue din shadda sai kyalli takeyi yana ta kokarin balle links din hannun rigarshi, ganinta yasashi barin abinda yakeyi yazuba mata ido yana kallonta gaskiya yau tayi wata ta daban,

"Baby......wow.... Kinyi kyau"

Zama tayi gefenshi tana kallonshi,

"Bae kayi kyau kaima.... Yaushe akayi wannan askin ban ganiba sai yau?"

Wuyanta yakaiwa kiss yana cewa,

"Abinda nayishi tun jiya da yamma shine baki ganiba sai yanzu.... Gaskiya kin tafi dayawa..."

"Exactly.... And you look handsome this morning what's the secret? Ohhh namanta ashefa ango kake...."

Dariya yayi yana mai mika mata hannunshi dan ta balle masa links din dake jiki,

"Zan ramane bari nadawo baby... You will cry over and over and over again..."

Dariya tayi itama ta dauki agogonshi mai tsada na azurfa ta daura masa sannan ta dauko turare ta fesheshi dashi har saida ya kwace saboda kar ya hawar masa kai, hula ta saka masa wacce take kalar kayanshi amma akwai ratsin Fari ajiki,

"Wow.... Best ango eva.... Kayi kyau wallahi, duk wanda yaganka yau zaiyi expecting cewa yaune ranar aurenka nafarko, indeed you look very young & adorable...let me snap u...."

Kin yarda yayi ganin ta dauko expensive phone dinta, sai hannu yake sakawa yana karewa har yasamu nasarar janta jikinshi nan ta daddaukesu tare daga nan ta zauna ta hada musu breakfast tare suka karya gwanin ban sha'awa ayau dai babu wanda zai kalli fuskarta yace wai kishiya ake shirin auro mata saboda yadda tasake dashi sosai sunata zuba soyayyarsu, saida suka gama ciyar da juna sannan suka fita tamkar amarya da ango, afalo sukayi arba da su Mariya da yaransu suna karyawa cikin tsadaddiyar shiga ta alfarma matan kayansu iri daya haka suma mazan nasu irin daya su biyu, daukar mimi fahad yayi yajasu Muhammad da hanfa jikinsa yasake jan bilkisu gefen damanshi su maryama sunata haskasu ahaka salim yashigo ya samesu nan yafara tsokanar bilkisu yana cewa,

"Wai hajjaju bilkisu ke ko dan kishin nan ma bakya yi bare ki bata rai? Gaskiya fa kamata yayi ki tubure kice baki yarda ba...."

Dariya tayi tace,

"A'a Abba salim ko kaima kana cikin yan bakin cikin zamu samu karuwa ne? Ai duk macen da take ita daya babu kishiya to bata sanin level din son da ake yimata....."

Dariya salim yayi yana gyara zaman hularsa shi dai fahad jinsu yakeyi baice komai ba,bin bayansu tayi domin rakiya tana yiwa fahad addu'ar Allah yatsare ya kiyaye hanya,

"Wai.... Lallai hajjaju harda su rakiya? Auren kishiyarki fa zamu je mu dauro"

"Ohh Abba salim, adawo dai lafiya"

Daga haka takoma ciki tana dariya shikuma fahad ya daki salim akafada yana cewa,

"Fuck you malam kana neman ka ballo min ruwa... Kabarni da rigima"

Tunda suka tafi take hidimar gabanta domin ta shirya walima inda zata gayyato malamar addini wacce zata tunatar da yan uwa mata,

Gidan fal yake da mutane musamman ma danginta da na fahad duk matan yayunshi na gidan amma banda Anty juwairiyya matar ya sunusi, duk wannan uban cikowar bata dauke mata hankali ta manta da fahad ba ana gama girki ta dibar masa nasa takai dakinsa sannan ta kirashi domin taga miss calls dinsa har guda uku, tana daf da katsewa taji ya daga,

"Soul mate... Ina kika shiga ne haka?"

Murmushi tayi ta zauna gefen gadonshi,

"Sorry bae wallahi hayaniyace tayi yawa..."

"Sannu da kokari Allah yayi miki albarka nima yanzu zan taho gareki..."

"Allah yadawo dakai lafiya..."

"Amin I love you..."

"I love u too..." Tafada tana kissing din wayar sannan takatse tafita ta nufi bedroom dinta, wata kwalliyar tasake sha cikin golden colour din material doguwar riga taci dauri mai kamada gwaggwaro sannan tafita nan gida ya gauraye da guda kowa sai tayata murna yakeyi sakamakon ga motar da fahad yasiya mata nan kowa yana gani,anan compound din gidan aka gudanar da walima kamar yadda tashirya inda malama Hajara ta gabatar da lecture mai taken kishiya abokiyar rayuwa, kowacce mace dake wurin taji dadin wannan lecture din saboda malama hajara tabayar da wasu sirrika na mussaman,
saida aka kusa tashi daga walimar sannan anty Juwairiyya tazo tanata tabe taben baki gamida harare harare sai kallon bilkisu take tayi wacce ke cikin kyakkyawar shiga itada yaranta cikeda walwala, itafa saima yau ta taba zuwa gidan ashe haka fahad ya tara kudi? Ashe haka ya kashewa bilkisu da yaranta kudi? Hararar bilkisu tayi aranta tana cewa,

"Munafuka jibi yadda taketa fara'a tana walwala kamar ba kishiya ake yimataba... Ni banma taba ganin matar da tashirya walima dan ana yimata kishiyaba sai ita.... Kai gaskiya ban yarda da itaba duk yadda akayi akwai wani mugun nufi aranta"

Maganar Anty Kubra faccalarta ne yadawo da ita hayyacinta,

"Gaskiya bilkisu ta burgeni... Kiga yadda tasaki ranta shiyasa shima fahad din yaketa daga darajarta a idon duniya.. Kalli dalleliyar motar da yasiyo mata can fa..."

Ai tunda Anty juwairiyya taga wannan motar hankalinta yasake tashi nan ta sulale takoma gefe tana kiran layin husnah dan yazama dole tashafawa husnah wannan labarin tunda duminsa dan idan tazo itama ta san irin takunta sannan karta yarda da bilkisu dan duk abinda takeyi yanzu makircine da kaidi irin na mata.....


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 5:08 AM] Nawartye&: 7***Ahankali take bude idanuwanta wadanda suka yimata nauyi sannan shima kanta yayi mata wani irin dummmm babu dadi, dakin take bi da kallo tana son tunano shin meya kawota nan?

Idonta ne yakai kan zeetah wacce ke kwance da waya a hannunta daga ita sai half vest da gajeren wando iya cinya kanta yasha kitson attachment wanda yake tuli guda, fashewa tayi da kuka sakamakon tuno abunda ke damunta,

Daidai lokacin azima tashigo ita da Lady hannunsu sakale cikin na juna,

"Beauty kin tashi..... Sannu" lady tafada tana zama gefen ta tare da kamo hannunta,

"Pls kidaina kuka mana bahijja.... Kiyi hakuri, tashi kiyi wanka kici abinci gashi"

Har lokacin bata bar kuka ba sakamakon tuno rayuwarta da ko ita wacece amma yau wai itace cikin wannan halin,

"Kitashi kiyi wanka kici abinci...." Lady tace da ita tana dagota, bata da zabin da yawuce tabi abinda suka fada amma kanta wani irin azababben ciwo yake yimata kamar zai rabe gida biyu,

Da taimakon azima taje tayi wanka tafito domin jikinta babu wani karfin kirki har yanzu sakamakon abinda tasha,

Kayan sawa suka fito mata dashi acikin kayansu sannan suka ajiye mata take away wanda suka shigo mata dashi, muryar lady taji tana cewa,

"Wannan nakine beauty... Ke na kawowa"

Bata ce uffanba ta dauki kayan tasaka sai lokacin idonta yakai kan agogo karfe 9 da wasu mintuna,

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un...."

Tafada tana dafe goshinta sakamakon tunowar da tayi cewa batayi sallar magrib ba jiya haka ta ishah, gashi yau ta makara sallar asubah har karfe 9,

"Ki daure kici abincin nan beauty... Pls"

Kallon lady tayi sannan ta dauki hijabinta,

"Bari nayi salla tukunna...."

"Is ok"

Tashi tayi tai salla sannan suka bata abincin takarba ta bude, soyayyen dankaline da kwai sai yar sos agefe sannan ga lemo wanda taga lady ta watsa wasu kananan kwayoyi aciki sama da guda biyar sannan ta tsiyaya tasha ta ajiye mata rabi agabanta,

"Beauty kisha saboda kisamu ki manta da damuwarki... Mu masoyanki ne muna sonki bama so ki kasance cikin damuwa..."

Duk wadannan maganganun da Lady keyi bata tanka ba har tagama cin abincin ta dauki robar lemon ta dan kurba, da dadin baki da komai su lady suka sakata ta shanye lemon sannan ta mike dakyar tana faman hada hanya tanufi saman gado ta kwanta ko minti biyar batayi ba bacci ya dauketa baccin da yakaita har yammaci domin lokacin da ta farka karfe 4 da kusan rabi babu kowa cikin dakin sai zeetah tana gaban gas tana juya naman kajin da take dafawa cikin babbar tukunya,

Duk jikinta amace take jinsa tamkar babu jini ko kuma babu bargo, idanuwanta kuwa dakyar take budesu saboda dakansu suke rufewa wani irin bacci ne dankare cikinsu kamar ta shekara bata runtsa ba,

Tana so tabude baki tayiwa zeetah magana amma takasa haka so take ta tashi tayi salla nanma jitake bazata iyaba sakamakon daukar da jiri tareda hajijiya kemata, dole taci gaba da kwanciyarta har zeetah ta farga da ita lokacin ta sauke farfesun da take dafawa, wani babban flate ta dauka ta cikowa bahijja ta kawo mata kan gadon da take kwance,

"Gashi tashi kici...."

Dan bude idonta tayi tana kallon zeetah,

"Daina mamaki bahijja... Mu nan haka muke sai abinda mukeso muke ci koda kuwa namane....bama dora tukunya adakin nan sai dai idan nama zamu dafa ko ruwan zafi"

Yunkurawa tayi dakyar ta tashi zaune ta dauki farfesun tafara ci, idanuwanta nasake yimata nauyi saida ta koshi dam sannan ta ture flate din tasake kwanciya babu jimawa Lady tashigo cikin riga da skirt yan kanti ta dan yane kanta da wani guntun vail baki fuskarta taci bakin glass kafcece hannayenta rikeda manya manyan ledoji, zama tayi tana shafa kumatun bahijja,

"Sannu beauty.... Har yanzu ciwon kanne?"

Daga mata kai bahijja tayi alamar ehh hakan yasata bude ledojin da tashigo dasu ta ciro mata apple guda daya ta mika mata, girgiza kai tayi alamun ta koshi, dishi dishi tafara kallon kowa zuwa dan lokaci kankani bacci yayi gaba da ita.

Misalin karfe 11 nadare tafarka ganinsu tayi dukansu zaune tsakar dakin suna kallo a system din da bata da masaniyar ko tawaye, kallonsu takeyi daya bayan daya saboda a lokacin jinta take cikin nutsuwarta sosai sai dai rashin kuzari dake addabar gangar jikinta,

"Beauty kinsha bacci.... Barka da tashi"

Dan murmushin yake tayi sannan tajuya ta kalli lady,

"Dan Allah kubani komai nawa intafi.... Zan koma hostel dinmu"

Tashi azima tayi takoma kusa da ita,

"Haba bahijja wai antayin magana daya kenan? Nafada miki so muke kishigo cikinmu mu zauna tare.... Duk fa nan da kika ganmu matsalarmu iri dayace kamar taki sai dan banbancin da baza arasa ba, ki kara hakuri akwai wani lokaci wanda zamu fito fili mu sanar dake ko mu suwaye....ki saki jikinki domin mun zama daya"

Tabbas a lokacin kalaman azima sunyi mutukar tasiri agareta wannan dalilinne ma yasata sakin jiki kamar yadda aziman ta bukata. Tsawon kwanaki uku ta dauka tare dasu babu abinda takeyi sai dai taci tasha kayan maye ta tiki baccinta, rabonta da taje lectures har tafara mantawa, saida tayi sati daya adakin su lady sannan tafara fita ranar da ta fita ba yan department dinsu kadai ba kusan kowa dake makarantar indai yasanta kallon mamaki zai tsaya yana yimata, taci riga da wando matsattsu sai karamin mayafi data yafa akanta irin shigarsu Lady sak,

Bayan anfito daga lecture tana zaune ita daya tana duba wayarta taji anzauna kusa da ita, dan bata rai tayi ta kawar da kanta gefe, cikin fada budurwar da ta zauna kusa da ita tafara magana,

"Bahijja ashe da gaskene maganganun dake yawo cikin school dinnan.... Bahijja kanki daya kuwa? Yanzu idan yaya sagir ko Umma suka zo suka ganki cikin wannan mummunar sabuwar rayuwar da kika fara gudanarwa me kike tsammani?"

Kallon up and down tayi mata sannan tace,

"Ya isa malama, ina ruwanki da rayuwar da na zaba? Tare muka zo school dinnan ne ko tare aka turo mu daga gida? Kiyi rayuwarki kawai inyi tawa..."

"Lallai sai yanzu nayarda da maganar bahaushe da yake cewa zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai, yanzu bahijja acikin yan kwanakin nan har kin dauki dabi'ar da ba takiba? Bahijja nice fa? Ki tuna tsawon lokacin da muka dauka muna tare, tun level one... Bahijja idan kika cigaba da wannan rayuwar wallahi baki yiwa mahaifiyarki da dan uwanki adalciba sannan baki rike maraicinki ba, lokacin da yaya sagir yakawo ki makarantar nan sanye kike da hijabi har kasa harda safa akafarki kuma irin wannan shigar kika cigaba dayi har kawo lokacin da shaidan ke yunkurin sauya miki rayuwa..."

"Basira kinfa dameni... Nafada miki kifita daga rayuwata, kin san irin halin da nake ciki kuwa? Ko kin san irin damuwar dake cunkushe cikin raina? Soo is better kawai kiyi rayuwarki nima inyi tawa..."

"Naji bahijja, naji ban san damuwar da ruhinki ke cikiba amma kisani ba kece mace tafarko da aka fara saka ranar aurenta aka fasa ba, wadanda irin haka tafaru dasu suna nan dayawa bazasu lissafu ba kuma hakan bai hanasu cigaba da gudanar da rayuwarsu ba... Nidai shawarar da zan baki itace yakamata ki zauna kiyiwa kanki karatun ta nutsu tun kafin lokaci yakure miki kuma kinga yanayin karatunki yana bukatar kulawa da bada himma idan har kika cigaba da irin haka to wallahi zaki bata shekarun da kikayi abaya abanza.... Sannan abu nakarshe da zan fada miki shine idan har yaya sagir ko umma suka bukaci jin wani abu daga gareni wallahi tallahi bazan rufa miki asiri ba zan sanar dasu gaskiyar abinda nasani..."

"Kanki akeji basira...."

Basira bata tanka mataba ta dauki handbag dinta takara gaba jitake kamar ta zubarwa da bahijja hawaye yarinyar da take kamammiya kuma kamilalliya mai ibada da nutsuwa wacce ake buga misali da ita wurin kyakkyawar tarbiya amma yau itace cikin wannan rayuwar? Gaskiya yazama dole tayi wani abu ko dan ganin ta cetota daga halin halakar da take kokarin fadawa.

Abangaren bahijja kuwa ita saima yanzune take jin dadin rayuwarta domin tana shanawa son ranta kuma bata da damuwar komai

5 / 14