Chapter 6 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 14

15K to 18K   out of 40.2K words

su Lady suna bata kulawa duk abinda takeso shi suke yimata, suttura abinci da komai da take bukata sai wanda ta zaba ita kanta tana mamakin wai a ina su lady ke samo kudade har haka? Sai ahankali tafara fuskantar tayadda suke samo kudin domin wasu alhazawa garesu wadanda ke basu kudi kamar basu san ciwon nemosu ba, sam ita yanzu babu ruwanta da basira domin kayanta ma dake can wurin basirar sannu ahankali taje ta sadada ta kwaso abunta tadawo dasu dakinsu Lady, sune zuwa clubs sune shaye shayen kayan maye sune shigar banza gaba daya makarantar nan duk wasu tantirai su biyo bayansu shiyasa cikin watanni biyu kacal bahijja ta goge acikinsu tazama tantiriyar yar duniya dan harma taso tafisu iya bariki kawai ita abu dayane bata yi bin maza wannan kam tayiwa kanta alkawarin bazata taba bin mazaba saboda ta tsani maza ayanzu bata ko kaunar hada hanya dasu sakamakon sune suka jefata halin da take ciki, cikin yawace yawacensu na zuwa party da picnic ta hadu da wani yaro tacacce irinsu waishi faruk tare suke haduwa suyi shaye shayensu yasake budar mata da ido,dayake shi bai nuna mata jikinta yakeso ba shiyasa ta yarda suke mu'amula dan bai taba ko gwada rike hannunta ba. Har aka kafe musu time table din exams bata fara karatu ba,cikin wannan hali Yaya sagir yakawo mata ziyara kamar yadda yasaba saida yakira basira kawarta saboda ita wayarta akashe take tun jiya.

Yana sanye cikin shiga ta manyan kaya matashine wanda bazai wuce shekaru 34 ba, asanyaye basira tazo suka gaisa sai dai harga Allah bata da niyar boye masa gaskiya gara ta fada masa ko zai samu nasarar samo bakin zaren,

"Kanwata ya naganki ke daya? Ina yan biyun taki?"

Murmushin yake tayi ta sunkuyar dakai,

"Yaya sagir ai yanzu bama tare da bahijja domin tabar dakinmu takoma na wasu...."

"Bakwa tare? Fada kukayi ko me?"

"Sam ba fada mukayi ba yaya sagir, bahijja yanzu ta gujeni ta koma ta hada kai da wasu marassa tarbiya, yan shaye shaye, yan lesbian, marassa son karatu inbanda kule kulen maza da yawon zuwa clubs babu abinda sukeyi... Bahijja gaba daya ta sauya hali tatashi daga bahijjan da kasani ada tadawo wata sabuwa ta daban.... Ko sutturar mutunci yanzu bata sakawa,duk wanda yasanta ada ayanzu ta sane masa sakamakon muyagun dabi'un da ta dorawa kanta, ni yanzu ko ahanya muka hadu bata yimin magana saboda bata son infada mata gaskiya... Dama naki fada makane tun farko saboda gudun kada taga laifina na shiga tsakaninta daku amma dama araina nayi alkawarin muddin ka tambayeni to babu abinda zan boye maka...."

Dafe kansa yayi yakoma cikin mota ya zauna yana karanta Kalmar,

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..."

"Yaya sagir kayi hakuri yanzu dai kawai mafita ya kamata anema domin agaskiya ko karatu bana jin tana zama tanayi gashi karatunta yana bukatar cikakkiyar nutsuwa..."

"Na kikkira wayarta akashe tun jiya amma shekaran jiya munyi waya da ita dama ban fada mata zanzo ba unexpected visit naso yimata... Ko zaki je ki nemo min ita? Yafada idanuwansa jajur sakamakon bacin ran da yake ciki,

"To bari naje na nemota.." Daga haka tajuya tatafi tabarshi cikin kunar rai, da dakinsu lady tafara amma basa nan dakin nasu arufema yake da wani garkamemen kwado daga can tawuce duk inda tasan zata iya samun bahijja amma bata sameta ba tafi awa daya da rabi tana yawon nemanta amma babu ita babu alamunta kai ko mai kama da itama bata ganiba su kansu kawayen nata su lady ko daya acikinsu bata ganiba haka ta dawo wurin yaya sagir jiki asanyaye gwiwa asace ta sanar dashi nemar wuri yayi yasake gyara parcking din motarshi dan ya daukarwa kansa alwashin cewa ko zai shekara a bauchi bazai tafiba sai yajira bahijja tadawo daga duk gidan uban da taje gashi wayarta har lokacin akashe take wuni guda har magrib yakai aciki makarantarsu amma shiru bata dawo ba duk da baizo da niyyar kwana ba amma yazam??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a dole ya kwana. Ita kuwa bahijja tana can Kaduna itada Faruk sun kama hotel suna hutawarsu domin Faruk dan gatane sosai babansa babban mutum ne mai tarin arziki shiyasa yake yin abinda ya gadama, tunda sukaje hotel dinnan babu abinda suke yi sai shaye shayen kwayoyi da syrup kwanansu hudu kenan yau daga shi har ita duk sun kashe wayoyinsu, washe gari suka koma bauchi saida suka biya restaurant suka ci abinci sannan suka wuce school zai mayar da ita, awurin da aka tanada domin ajiye motoci yayi parking gaba daya motar tin tac ce baka ganin na ciki,

"Beb sai zuwa gobe ko zanzo muje wani casu na friend dina....."

Murmushi tayi ta dauki red din gyalenta ta dora akanta wanda yake atsefe ta tufkeshi dan hadiyar yawu faruk yayi yana kallon jikinta kasa kasa ita kanta na aduke tana lalubo wayarta zata kunna sam bata kula da irin kallon da yake yimata ba, bakar t shirt ce ajikinta mai gajeren hannu da jan wando pencil wanda ya kamata takalmin kafarta shima jane high hill,

"Babu damuwa guy sai kashigo..."

Daga haka tabude kofar motar tafita tana gyara rigar jikinta, Yaya sagir na zaune karkashin bishiya yana jiran karasowar basira kamar amafarki yaga bahijja tafito daga cikin motar da yaga tsayuwarta da jimawa atsakanin jerin rukunin motocin dake ajiye awurin, tun daga nesa yamike yake binta da kallo daga sama har kasa yana mai sake murza idonsa sosai dan ya tabbatar cewar ita dince yake gani ko kuma idanuwanshi ke yimasa gizo yana fada masa karya? Kamar yadda yake kallonta kamar bai taba ganinta ba sai yau haka itama ta tsinkayoshi daga nesa, dagaske yaya sagir take gani ko kuwa mafarki takeyi? Wani irin kadawa yan hancin cikinta sukayi kamar zata saki fitsari haka takeji dan tsananin gigita da razani.......


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 5:08 AM] Nawartye&: 11***Har tagama shirya amrah bata bar mamakin abinda badiyya tayi ba to menene ma'anar hakan? Wannan tambayar take ta yiwa kanta daga karshe tamike ta fita kai tsaye kitchen tashiga domin shirya breakfast tunda ita wacce tasaba shirya musu yau tayi kaura tabar gidan, saida tagama yan soye soyenta sannan ta fito tashiga dakin abbansu muhibba amma ga mamakinta baya cikin dakin, har toilet taduba amma baya ciki daga karshe tafita har compound din gidan amma babu shi babu alamunsa kuma motarshi ma bata gidan wanda hakan ya tabbatar mata da cewa yafita to ko aiki gareshi a office haka shiyasa yayi wannan uban sammakon?

Ganin bata da amsar wannan tambayar yasata komawa ciki domin gyara gidanta, bayan tagama shirya yara sun tafi makaranta tayi bakuwa matar abokin abdurrahman wadda itama suke dan kawance da ita sakamakon mazajensu abokanai ne, munubiya sunanta yar asalin garin katsina da murnarta da komai ta tarbi munubiya suna gaisawa munubiya tafara shafa mata labarin da yakawo ta,

"Maman muhibba basai ga kabir da neman aureba... Wai har yakai angani ana so....ni kuwa na bude masa fefen rashin mutunci dan dole yayi collapse..."

"Ai ni ban san meyake damun mazajenmu ba wallahi... Basu da wata magana saita kara aure idan kayi musu magana suce wai taimako zasuyi idan aikin lada suke so ai akwai hanyoyi dayawa na samun lada bawai dole saita hanyar aure ba...."

"Ai ban yarda na amince ba har saida nayi iya iyawata naga na hana wannan auren... Akan me nikuwa zan yarda akawo min jangwam? Kishiya ai bala'i ce... Tab wallahi bada ni ba"

"Kin yimin daidai wallahi.... Sai mutum yayi magana ace wani wai kishiya dole ce to wallahi ba dole bace su yanmatan dazawaran wani shegen yahanasu su samu mijinsu su kadai su aura? Ko dole sai mijin wata zasu aura... Ai ni bana tolerating wannan nonsense din"

"Ai ni kasa hakuri nayi har saida nakirata nayi mata tass nace ta rabu da mijina wai wani nan wai mijinta ne ya mutu yabarta da yara biyu.. To ni na kasheshi"

"Gara da kika yimata haka ai nima lokacin da abban su musaddiq yana neman aure sai da naci mutuncin yarinyar nan sosai infada miki.... Kaca kaca nayi mata"

"Banga laifinki ba wallahi..."

Ahaka hirar tasu ta kare a ire iren wadannan maganganun har wurin la'asar suna tare da munubiya sannan ta tafi, haka taci gaba da zuba idon abdurrahman amma shiru bai dawo ba dama tasan yanayin aikinsu basa tashi sai 6 wani lokacin kuma bama ya dawowa gida sai 8 amma yau kamar lamarin yafi na kullum dan har tayi bacci bayan tagaji da jiransa bai dawo ba kuma washe gari yafice duku duku kamar yadda yayi jiya nan abin yafara tsaya mata arai gashi idan ta kirashi awaya baya dauka ranar ma har tayi bacci bai dawoba amma washe gari tayi nasarar tarar dashi lokacin yafito daga wanka yana shirin tafiya office amma yana ganinta yahade rai yadaure fuska abinda yayi mutukar bata mamaki domin a iya saninta babu abinda yashiga tsakaninsu na sabani,

Zama tayi gefensa tana kallonshi yana kokarin saka safa akafarshi,

"Abban muhibba lafiya kuwa?"

"Me kika gani fa?"

"A'a babu komai kawai dai gani nayi kwana biyu baka samun dawowa gida da wuri sannan kuma da wuwwuri kake fita..."

"Yanayin aikinane ya canja" yafada fuskarshi adaure daga haka kuma bai kara cewa komai ba yakaras shiryawa ya dauki jakarshi yafita sosai abin yabata mamaki to wannan Fushun da yaketa yi na menene? Ganin tana batawa kanta lokaci abanza kawai yasata yin watsi da tunanin, falo takoma tana tunanin badiyya wato yarinyar nanfa tun ranar da ta tafi taketa kiranta amma taki dauka har yau dinnan ko me tayi mata har haka oho.

Gaba daya takasa gane kan abdurrahman kuma idan ta tambayeshi ko laifi tayi masa sai yace a'a amma haka kawai yaki zaman gidan, ranar lahadi da yamma yashigo gidan tana kitchen tana dafa tuwon dare yara kuma suna islamiyya yauma kamar kullum fuskarshi babu annuri,

"Shamsiyya..." Yakirata,fitowa tayi ta sameshi zaune kan kujera,

"Kibar girkin nan da kikeyi kitafi gidanku na sakeki saki daya...."

A razane ta kalleshi hankalinta amutukar tashe cikin rawar baki tace,

"Abdurrahman.... Ka..sa..ke..ni fa kace... Anya kuwa lafiyarka kalau? Laifin me nayi maka? Muyi ya da yaranmu?"

"Lafiya lau nake.... Karki kara koda mintuna 10 acikin gidannan ki tattara kayanki kibar min gidana, yara kuma bance ki tafi da ko guda daya ba saboda inada inda za arike min su...."

Bai jira tadawo daga sabuwar duniyar da ta tafiba mai cikeda mamaki da al'ajabi yamike yahau sama yana taka step kamar wanda kwai yafashewa aciki,Da saurinta tabi bayanshi amma kafin taje har yashiga daki ya turo kofa, buga kofar tashiga yi da dukkan karfinta amma yayi mata biris kamar ba yaji,

"Abban amrah kabude kaji.... Ka bude kasanar dani laifin da nayi maka"

Shiru yayi mata kuma da alamar bashida niyyar bude kofar wannan dalilinne yasa ta juya ta dawo kasa ta nufi dakinta tana kuka wannan ko shakka babu aikin sihirine, duk yanda akayi tsohuwar budurwarsa wacce ada zai aura yafasa bai aureta ba itace tayi kutun kutun tashiga tafita tayi tsafinta zata rabasu,

Haka zuciyarta taketa raya mata, cikin hawaye tagama zuba duk abinda zata bukata da na amrah yar karamar yarta tajanyo akwatin tafito sai lokacin taji kauri a kitchen cikin sauri taje ta kakkashe komai tafito tana goye da amrah yarta abaya, da kuka tafita daga gidan ta tsaya ta tare napep tahau tana hawaye tana fada masa inda zai kaita.

***

Ayaune amarya husnah zata tare shiyasa tun safe yan uwanta na nan kano sukazo gidan domin sake tsaftace sashen amarya sannan kuma sune zasu taryi amarya,

Abangaren uwar gida bilkisu itama ba abarta abaya ba dan tunda garin Allah yawaye take kaiwa da kawowa saida ta hadawa fahad breakfast takai masa daki sannan tafara tashinsa daga baccin da yake tayi mai cikeda gajiya da kasala sosai,

"Baby... Baby tashi kayi wanka ga breakfast kaci"

Dan idonshi yabude guda daya mai cikeda alamun bacci sannan yamayar ya rufe yana sake jan bargo, rike bargon tayi tana cewa,

"To ga dangin amaryarka can sunzo suna jiranka garama ka tashi"

Shiru yayi yabude idonshi daya amma kuma bai tashi dinba,

"Baby wallahi baccin bai isheni ba...."

"To ya za ayi haka zaka tashi kawai, anjima sai kasake yi"

Tashi zaune yayi yana cuno baki sai mutsuttsuka ido yaketa faman yi,

"Bae wai katashi mana... Nidai ga breakfast dinka nan idan kashirya... Bari inhada maka ruwa"

Daga haka tawuce toilet tana shiga yabita, rungumeta taji yayi tabaya yana sakin ajiyar zuciya, da taimakonta yayi wankan yafito ta tayashi yashirya cikin sky blue din yadi marar nauyi dan har farar singiletin da yasaka ta dan bayyana kadan ta cikin rigar,

Tare suka karya sannan suka fito tare, hajiya iyallo yafara zuwa yagaisar sunata halin nasu na tsokanar juna sannan ya dauki Mimi yafita, part din amarya yanufa ita dai bilkisu bata bishi ba takoma ciki taci gaba da aikace aikacenta, bai wani jimaba sai gashi yadawo da Mimi dan fita yakeson yi dakyar Mimi ta yarda taje wurin bilkisu sai kuka take yi lokacin da yana bata ita, kumatunta yashafa yana fadin,

"Haba mai kamada Darling.... Sorry daina kuka zan taho miki da ice cream"

Harararsa bilkisu tayi jin abinda yafada,

"Mai kama dakai dai... Kai ai duk yaranka kamarku daya"

"A'a baby wannan dai dake take dan kama, kallifa idonta"


Goya Mimi tayi abayanta batare da zani ba tana cemasa,

"Wannan large eyes din ai kowa yasan maisu... Ni bahaka idanuwana sukeba"

Dariya yayi yajuya zai fita,

"Kibari zamu hade a bed anjima"

"Sai dai ku hade da amarya, amma bada ni ba nima yau Allah yahutar dani"

Da dariya yafita bai sake cewa komai ba, ita kuma tanufi dakinta dan ta dauko zani ta goya mimi.

Yauma kamar jiya gidanta cike yake da yan uwa hajiya iyallo sai drama suke tayi da yan jikokinta suna bawa mutane dariya, bayan sallar magrib yan kawo amarya suka iso part din bilkisu aka fara kawota akace ga amana nan sannan suka mika ta part dinta Wanda shine na farko domin part din fahad na tsakiyane babban falonshi yana center kowacce akwai kofar da zata kaika part dinta ta ciki,

Har bayan ishah su maama na nan sai wurin 8 sannan suka baje suna sake bawa bilkisu hakuri wacce sai yanzune take dan jin damuwa sama sama amma ada harkar gabanta takeyi,

Tajima zaune gefen gado bata ma san me zatayi ba dan gaba daya zuciyarta babu dadi daga karshe dai tatashi tashiga wanka tafito ta zauna kan stol domin shiryawa gaba daya komai tana yinshine asanyaye kuma sukuku,

"Ko inzo intayaki shafa mai dinne?"

Taji maganarshi daga bayanta wanda ita razana ma taso yi dan kwata kwata bata san yana cikin dakinba batama San lokacin da yashigo ba,

"Har ka tsoratani wallahi... Yaushe ka shigo?"

"Tun kina wanka ranki yadade... Agama nima azo ayi min"

Murmushi tayi tana cewa,

"Ai yau wankan na musamman ne tunda wurin amarya za aje..."

"Nifa harma namanta da ita badan kin fada ba.... Nidai azo ashiryani dan gaskiya a gajiye nake"

"Zama ka wartsake ne.... Ko sai na dafa maka tsumine?"

Dariya yayi yasake kwanciya kan gadonta,

"Me kikeson cewane?, banda karfi ko?"

"A'a ni ai kaga tsohuwa ce ita kuma amarya yarinyace kamarka gara kaje da karfinka"

"Nine yaron ko? Mark my word sai kinyi kuka duk ranar da muka hadu.."

"Bayan wanda kasani lokacin amarci?"

Dariya yayi ya lumshe idanuwansa yana tuno lokacin,

"Ai kin zuba raki yarinyar nan.."

"Kai kuma ka zuba mugunta ko?"

Dariya yayi yatashi ya riketa tana kokarin saka rigar baccinta,

"Yaya Abba yana gaisuwa fa.... Nusaiba kuwa tazo gidan nan?"

"Ina amsawa, ehh tazo ranar walima amma bayan nan bata sake dawowa ba"

"Nusaiba kenan karfi da yaji dai tazama yayata bayan kanwarmu ce"

"Kanwarku a ina? Yayarku dai Malam"

"Haka akayi.... Lokacin da aka haifeta to da wayona aka tafi barkarta da yaya Abba a lokacin maman su salim take tsokanarshi tana cewa tabashi ita ga mata ta haifa masa kinga kuwa ashe tafada da bakin mala'iku"

"Thank God da bakai kayi rakiyarba bare abaka ita"

Dariya yayi zai sake magana taja hannunsa tana cewa,

"Ya isa muje kayi wanka kabar amarya nata jiranka gashi dare yafara yi"

Tana nan yayi wanka yashirya yasaka kayan bacci ita kuma tana faman tattare kayanta dake cikin dakin, rike hannunta yayi,

"Meye haka?"

Kallonsa tayi,

"To ai yanzu bani kadai bace ko? Turakar mai gida ai takowa ce kaga gara na kwashe abubuwane ma suka yimin yawa amma da tun tuni ya kamata na kwashe...."

"Kai baby wallahi kema dai"

"Baby ko gaskiya"

Komai nata saida ta dauke sannan ta yaye bedsheet din dake kai ta shimfida wani sabo kar daga nan tayi masa sallama tafita yanata shagwabe fuska wai bazata rakashiba dakin amaryar? Uhmm tace sannan ta tafi saboda wasu amaren basa son wannan rakiyar da uwar gida keyi kallon hakan suke yi a matsayin tozarci da nuna isa gamida makirci shiyasa gara ta kama kanta......


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 5:08 AM] Nawartye&: 9***Bilkisu hidimar gabanta kawai takeyi jama'a sunsha kanta domin sosai gidan nata yacika wasuma bata sansu ba kawai ance dai anayin wa'azine shine sukazo saboda malama Hajara tayi suna sosai wurin wayarwa da mata kai,

Har bayan sallar magrib gidanta dam yake da mutane dangin su fahad da danginta,anty juwairiyya kuwa takasa zaune takasa tsaye sai faman bin kowanne lungu da sako takeyi da kallon kurulla domin ba kadanba gidan ya tafi da ita bata taba sanin cewa haka fahad ya gatale bilkisu ba amma kuma kamar ma part din nata yafi na husnah girma da yawan bedrooms, bilkisu bata samu kanta ba sai bayan sallar ishah lokacin su maama suma sukayi mata sallama suka tafi suna cemata sai gobe zasuzo tarbar amarya, har lokacin fahad bai shigo gidanba sai misalin karfe 9 saura na dare,

Zama yayi kan gadonshi yana kiran layin bilkisu domin bai ci komai ba tun abincin safen da suka ci tare, gashi kuma yagaji mutuka, lokacin ita kuma tana daki fitowarta daga wanka kenan, ganin kiransa

6 / 14