Chapter 3 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 40.2K words

yana budewa yaga ta rubuta,

_Salam, dafatan katashi lafiya, nafita aiki ga breakfast dinka nan idan katashi._

Tsaki yayi yasoma kiran layin nata amma baya tafiya, hakura yayi ya ajiye wayar yasoma tunanin abinyi cikin haka wayar tashi tasoma ruri yana dubawa yaga husnah ce bai dauka ba yasake jan wani guntun tsaki, itama husban bacin ran da bilkisu ta jaza masa ya shafeta. Toilet yawuce duk ransa abace yasaba kowacce safiya bilkisu keyi masa komai ta shiryashi ta bashi abinci abaki yana yi yana zuba mata shagwaba, babu abinda yake yi da kansa indai tana gidan sai dai idan bata nan.

Koda yafito daga wanka bai wani bata lokaci ba kawai yazira kaya yabar gidan ko abincin da ta ajiye masa bai ciba. Kamar yadda tasaba around 1 narana tadawo gida domin shirya lunch, batayi mamakin ganin gidan shiru ba domin su hanfa na makaranta shikuma uban gayyar tasan yana office, agurguje tayi wanka tashiga kitchen tayi girkinta ta kammala lokacin karfe uku na yamma, tana shirya table yashigo sanye da blue din shadda, batare da ta kalleshiba ta dauke kai tace,

"Sannu da zuwa..."

Daga haka bata kara cemasa komai ba tazo zata wuceshi, rikota yayi yana kallon fuskarta,

"Wai dan Allah laifin me nayi da ake yimin wannan azabtarwar?"

Batare da ta kalleshiba tace,

"Meyasa baka ci breakfast din da na ajiye maka ba?"

"Kin damu da inci ne? Ba fushi kikeyi dani ba?"

"Fushi? Kayi min wani abune?"

Daga haka ta fincike tawuce bedroom dinta, duk yadda yaso yashawo kanta ta saurareshi suyi magana ki tayi har dare babu wani cigaba, lokacin da yakammala shirin bacci kamar jiya arufe yaji kofar tata yauma haka yayi kwanan takaici shiyasa tun jikin asubah wani zazzabi yafara hawa kansa kafin gari yawaye zazzabin yagama rufeshi ruf....


*Anan nakawo karshen d'andanon kumallon mata ga mai bukatar siyar wannan labari.... wato mulki ko sarauta Kashi na biyu na marubuciya phertymah xarah da kuma takwaransa kumallon Mata wanda ke dauke da cigaban labarin kamar da wasa wanda marubuciya ummi Aisha ta rubuta... Wanda ke bukatar wadannan dadadan littattafan guda biyu zai biya 500 mai son guda daya kuma zai biya 300 ta wadannan lambobi kamar haka.*=?G?

2083371244
Aisha M.Salis.
Zenith Bank

Sai atura shaidar biya ta wannan no=?G?
+447894142004

Ko kuma recharge card ta wannan no=?G?
08169334980

*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 5:06 AM] Nawartye&: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


4***Yanda ya kwana da zazzafan zazzabinsa haka yatashi dashi shiyasa ma yakasa tashi bare yakai ga fitowa, bilkisu kwata kwata bata da masaniyar abinda ke faruwa shiyasa ko lekashi ba tayiba lokacin da ta tashi, saida ta kammala hadawa yara breakfast da wanda zasu tafi dashi school ta sallamesu suka tafi sannan ta gyara gidan, breakfast din fahad daban ta hada masa kamar yadda tasaba, tana kammalawa taje tayi wanka sannan tayiwa mimi ta shiryata ta dauko duk abinda take bukata tafito tana rikeda mimi, ruwan tea kadai tasha saboda daga shekaran jiya zuwa yau bata iya cin abinci. Bata yi tunanin ta duba fahad ba ta sabi yarta suka tafi, gidan ammah tafara zuwa takai mimi kamar yadda ta saba sannan tawuce office, wayarta gaba daya kwana biyun nan akashe take saboda bata son damuwa,

"Allah sarki khulsum kawata, nayi missing dinki over, da kina nan na tabbata tare zamuyi shearing din wannan damuwar tawa..."

Ta furta ahankali sannan ta kwantar da kanta jikin kujerar da take zaune, tana aikinne dai kawai cikin karfin hali amma azahiri bata cikin nutsuwarta gaba daya bata da walwala, damuwace fal zuciyarta.

Shikam fahad yana can kwance cikin zazzabi gashi yanata kiran wayar bilkisu amma baya samunta wayar akashe hakura yayi ya zubawa sarautar Allah ido, zuwa can sai ga kiran husnah, tun daga yanayin yanda taji yana magana da kyar ta fahimci baida lafiya nan ta tambayeshi abinda ke damunshi ya sanar da ita, text massage ta turo masa na magungunan da za asiyo masa harda drip guda biyu dan yafi jin karfin jikinsa, salim ya turawa massage din da husnah ta turo, ba afi mintuna ishirin ba sai ga kiran salim, awahalce ya daga yacewa salim kawai yashigo master bedroom dinshi, babu bata lokaci yaji alamun bude kofa alamar salim yashigo kenan gaban gadon yakaraso ganin yanayin da fahad din ke ciki yasa salim komawa bakin kofar yacewa Rabi'u yashigo dama tare suka taho dashi makocinsu ne kuma yanada chemist dinshi da yabude nan jikin gidansu salim din,

Duk wata kulawa da yake bukatar abashi cikin gaggawa Rabi'u yabashi da taimakon salim daga karshe aka daura masa drip, kallon fahad salim yayi sannan yace,

"Ina ita Maman hanfa dinne?"

"Taje office" yabashi amsa atakaice,

"To akirata mana... Ai yakamata tadawo ta zauna tare dakai..."

Shi dai baiyi magana ba saima lumshe idanuwansa da yayi. Koda rabiu yatafi salim na nan tare dashi, breakfast din da bilkisu ta shirya shi yadauko yazuba yaci,duk inda take yasan karfe 1 nayi zata dawo saboda yin abincin rana, ai kuwa daya nayi sukaji dirin shigowar motarta,

Tana shigowa babban falo ta hango salim na fitowa daga dakin fahad,

"A'a abba salim kuna ciki dama?"

"Wallahi kuwa hajjaju, mijinki ashe babu lafiya shine nazo da likita yaduba shi yanzu gashi can ansaka masa karin ruwa... Ni garama da Allah yakawoki dama inada uzuri"

"Subhanallahi, amma sai bayan da natafi ko? Bari naganshi..."

Tare suka shiga dakin fahad, idanuwanshi alumshe alamar bacci yakeyi, sallama salim yayi mata yafita, cikin sauke ajiyar zuciya ta zauna gefenshi tana kallonshi sai taga ya fada gashi jikinsa akwai dan zafi kadan alamun zazzabi, goshinsa ta dafa sannan ta rike hannunshi wanda ba ashi ake kara masa ruwanba,

"Am sorry bae... Sannu Allah yabaka lafiya....."

Tana nan tare dashi tun dazu aketa kiran wayarshi amma ita dai bata duba ba jin kiran yaki karewa yasata dauko wayar wacce ke can gefen pillownshi ta duba, husnah love taga anrubuta ajiki, tabe baki tayi ta ajiye masa wayar agefenshi daga karshe tasaki hannunsa bayan tayi masa kiss tamike tafita, girki mai sauki ta shirya tana yi tana zuwa tana lekashi amma har lokacin bai tashi ba,wanka tayi tasaka English wears riga da skirt tasake komawa wurin fahad lokacin yafarka,zama tayi gefensa,

"Sannu bae.... Yajikin?"

"Da sauki..."

"Allah yabaka lafiya.... Akira salim suzo su cire maka wannan ruwan ko? Tunda naga yakare saura kadan"

Kai yadaga mata yamika mata wayarshi, karba tayi sannan ta nuna masa screen din wayar,

"Ankiraka...."

Kalla kawai yayi baice komai ba, ita dinma bata kara cewa komai ba ta kira salim ta sanar dashi sakon fahad,

Rigar jikinshi yayi mata nuni da ta dan cire masa botiran dake jiki saboda zazzabin jikinsa yasakeshi nan ta babballe masa sannan ta mike tafita zuwa bedroom dinta, hijabi tasako tadawo wurinshi ko zama bata yiba taji knocking sake juyawa tayi taje ta bude, salim ne da rabi'u suka shigo ganin yanda fahad yayi laushi yasa salim fara tsokanarshi,

"Haba ango yakuma zaka kwanta jinya tun amaryar batazo ba..."

Ita dai bilkisu tana jinsu dariya kawai take danyi har zuwa lokacin da rabi'u ya kammala komai sannan yakara jaddada mata lallai lallai yaci abinci yasha magungunanshi gasu nan, godiya tayi musu suka yi sallama dasu suka fita, bata fuska yayi yana kallonta,

"Me kuma kakeso?" Ta tambaya tana zama kusa dashi, hannunta yakama sannan yanunata da hannu,

"To menene na bata ran? Saki fuskarka mana... Dan yi murmushi nagani please...."

Makale kafada yayi hakan yasata dan murmusawa sannan ta mike tawuce bathroom tana fadin,

"Bari inhada maka ruwa kayi wanka sai kaci abinci kasha maganin..."

Da taimakonta yayi wankan yayi salla sannan yasake kwanciya, shi dama jinyarshi haka take sam baya kaunar shan magani da cin abinci, macaronin da ta dafa jalop wanda yaji kifi sukumbiya ta zubo masa saida tayita lallabashi kamar wani jariri sannan yayarda ya dan ci yasha magani yasake kwanciya,

"Wai tun yaushe ne kafara rashin lafiyar....?" Ta tambayeshi bayan ta ajiye cup din dake hannunta wanda tabashi ruwa yasha,

"Tun ranar da kika fara fushi dani...." Yafada yana maida kanshi kan cinyarta,

"Ayya bae kuma shine baka fada min ba?"

"Tayaya zan fada miki bayan kin ki kulani.... Ni wannan fushin naki yafi komai zafi agareni... Da kiyi min irin wannan fushin gara ki hanani auren gaba daya...."

Yatsanta ta dora kan bakinshi,

"Yawuce please.... Idan nahaka aure zina nake son kaje kafara? Karka damu Allah yabaka ikon yin adalci..."

"Allah idan kikace kar nayi hakura zanyi baby, bana son wannan fushin da kikeyi"

"Insha Allah bazan karaba, katashi daga zazzabin nan haka please ko dan ni da yaranmu"

"Nasamu sauki ai dama kin kulanin da bakya yine yajawo min shi...."

Dariya tayi ta sumbaci kumatunshi tana dagowa suka hada ido yayi dariya,

"Ina mimi na ne wai?"

"Ohh my God... Ko kasan na manta da yarinyar nan..."

Murmushi yayi yamatsa hannunta dake cikin nashi,

"Ashe dai har yanzu ana sona tunda gashi ana mantawa da auta saboda lalurata..."

"Ai idan ina tare dakai bana tunawa da kowa bae... U are my world...."

Murmushin jin dadi yayi yakafeta da ido yana motsa baki, harararshi tayi tafara kokarin mikewa,

"Kaida baka da lafiya amma shine zaka fara jan fada ko? Dagani naje na kira ammah infada mata tasa akawo min baby nah"

Sake kankameta yayi dakyar ta banbareshi tafita, tana kunna wayarta bata kai ga kiran ammah ba kiran khulsum yashigo,

"Besty tun safe fa nake son kiranki..." Inji bilkisu,

"Allah sarki kawata, yagida ya yaran? Kin san me? Kiranki nayi infesa miki Dazu na haduda kawarki awani group anata fada da ita akan wai anturo wani topic wanda yashafi kishiya shikenan fa infada miki mutuniyarki ta rude taketa maganganu daga karshe har ta mayar da abun fada... Daga fa cewa wai ai tunda masoyin masoyinka shima masoyinka ne dan haka ashe kishiya itace babbar masoyiyarka tunda masoyiyar mijinka ce shikenan tahau sababi...."

"Wai wa kike magana ne khulsum...?"

"Shamsiyya Abbas makaho fa, ai saida nabita private ina bata hakuri nagane ma ashe mun san juna, shamsiyya yar bencinku dai kuma yar hostel dinku..."

Dariya bilkisu tayi kafin tace,

"Assistant house captain fa? Dan Allah tana ina yanzu? Tayi aure ko?"

"Tun wanne zamani, yaranta biyar nabata number dinki zata kiraki, nima nace mata insha Allah idan nashigo kano zan nemeta"

"Ohh Allah sarki, to shikenan kawata insha Allah cikin week dinnan zanje mata kuwa ko a ina take, Allah sarki shams makaho..."

Dariya khulsum tayi tana cewa, "ai yanzu andaina fada mata wannan sunan, kigaida oga sai munyi waya"

Daga haka takatse wayar tana dariya saboda jiyo hayaniyarsu hanfa alamun sun dawo, bata kai ga tashiba taji wani kiran yasake shigowa ganin ammah ce yasata sake komawa ta zauna,

"Nace ni yau ko anbar min wannan cakwaikwaiwar ne inrike?"

Dariya tayi tana jiyo gwarancin Mimi ta cikin wayar,

"Ai karfi da yaji yarinyar nan so take sai ta koyi magana ammah, surutu ne da ita, yanzu dama nake shirin kiranki ince ko zaki sa akawota, abban nasune baida lafiya shiyasa banzo na dauketa ba...."

"Allah sawwake, ayi masa sannu, ita kuma wannan nariketa"

"To shikenan ammah mun baki"

Sallama sukayi ta katse wayar ta tashi tafita, adakin fahad ta iske su hanfa duk suna kwance ajikinshi su ukun saboda ganin bashida lafiya suma duk yaran sai suka zama kamar marassa lafiya domin idan lafiyarsa kalau yarinka wasa dasu kenan suna kokaye kokaye, zama tayi tana dago Muhammad da hanfa daga jikin fahad,

"Ku daga Daddy ai kunga bashida lafiya...."

"Ki kyalesu..." Yafada yana sake rungume yaran, barinsu tayi dama har Muhammad yabude baki zai saka mata kuka,

"Ammah tace tarike Mimi...."

Murmushi yayi baice komai ba, wayarshi ce tafara vibrating amma bai daga ba tasan duk yadda akayi husnah ce shiyasa ta mike ta kwashi yaran suka fita domin lokacin salla ma yayi. Bayan sallar ishah saiga ammah takawo mimi sannan tazo duba fahad, tafiyarta babu jimawa suma su ayiyah suka zo kowa sai tsokanar mimi yake saboda gwaracinta ita adole saita fadi sunan kowa na gidan ko kuma duk abinda aka fada saita maimaita,tun adaren ranar ta fahimci sauki yasamu saboda irin yadda ya dameta ya hanata bacci. Cikin kwanaki biyu fahad yawarke ras sannan kuma suka koma normal shida bilkisu wannan fishin da ta fara tuni tayi fatali dashi musamman ma da ammah ta zaunarta tayi mata Nasiha sosai akan ta kwantar da hankalinta haka suma su khulsum kowa shawarar da yake bata kenan, tsakaninta da fahad kuwa yanzu yar tsokanace sai tayita cemasa ango da yagaji ranar bata rai yayi yace yaga ita kamarma murna takeyi saboda zai kara aure kenan tadaina sonshi? Dariya ita abinma yabata wato dai su maza ba afita awurinsu, aranar tace masa tanaso zata biya ta gidan kawarsu wato shamsiyya Abbas dan tun washe garin ranar da khulsum tafada mata takirata bai hanata ba yace adawo lafiya bayan canma idan akwai wurinda zata je duk yayafe taje. Daga ita sai mimi suka tafi zuwa gidan shamsiyya sosai itama gidanta ya shiryu kuma ya kawatu daga gani kasan suna cikin daula amma kallo daya zaka yiwa gidan kagane akwai matsala shiyasa bayan sun gama gaishe gaishe da hirar yaushe gamo bilkisu tafara tambayarta meke faruwa?

"Labour aure mijina wai zaiyi kuma wallahi tallahi bai isaba... Akan wanne dalili zaije yakwaso min yanmatan nan nazamani marassa mutunci masu aurar maka miji su nuna sun fika sonshi..."

"Haba Shamsiyya ai wannan ba wani abu bane, kishiya bafa abokiyar gaba bace, to nima da kika ganni yanzu ahaka mijina aure zaiyi... Har an saka date anyi komai, ni dama nataba zama da ita tun ban haihuba kuma gida daya falo daya, kitchen daya bare ke kowa da part dinsa, nima yanzun kowa da part dinsa to kinga banda case da ita..."

"Tabdijam lallai labour anyi sakarya anan, ke yanzu yarda zakiyi yayi auren?"

"Shamsiyya to zan hanashi ne? Wallahi babu abinda yasha min kai yaje yayi abinshi bafa akaina zata zauna ba, ada shaidan yafara zugani nafara hawa dokin zuciya amma yanzu tuni nayi watsi da wannan shirmen na rungumi mijina tunda yana sona badan yagaji dani zai kara aureba"

"Lallai kam, to ni bazan iyaba wallahi, kishi gareni na tashin hankali bazan iya shearing mijina da wata ba wallahi..."

"Karki ce haka shamsiyya, ki daure kimaida komai ba komai ba insha Allah zakiga alfanun hakan dan ni wallahi gani nake kishinki baifi nawaba kawai ni na danneshi ne...."

"Ai labour bazaki ganeba, kishiya fa masifa ce... Kai ina... Bada niba wallahi"

"Shikenan to Allah ya kyauta, mun gaisheki bari mu wuce sai gani na biyu..."

Mikewa sukayi gaba daya shamsiyya tabi bayanta domin rakata lokacin da suka fito bilkisu ta kula da irin hadadden gyaran da gidan yasha gaba daya nan ta dan girgiza kai tasan kishi yafi wuta zafi awurin wasu matan shiyasa ta zabi da tayi shiru dan ko ta fadawa shamsiyya abinda ke ranta nagaskiya ba lalle ta fahimceta ba,

A bakin gate suka tsaya suna sallama daidai lokacin abdurrahman yadawo wato mijin shamsiyya, da bilkisu kadai suka gaisa har yana tambayar sunan mimi yana cewa wannan wacece? Daga haka yawuce ciki ita kuma bilkisu tayiwa shamsiyya sallama ta tafi, bilkisu na tafiya shamsiyya takoma ciki direct dakin abdurrahman tawuce domin dama yau ko sanda yafita bata saniba tunda yanzu babu abinda ke hadasu, cikin sa'a taga baya cikin dakin amma ga wayoyinshi nan da key din mota da na office yazube su bisa gado, cikin sanda kamar wata barauniya takarasa ta dauki daya daga cikin wayoyin, cikin sauri tafara binciken calls dinshi na wannan rana wadanda yakira da wanda suka kirashi kai harma da miss calls din dake cikin wayar, cikin azama ta kwafe number din yarinyar da zai auro dama wannan shine shirinta, bata ajiye wayar tashi ba tafice da ita tana dialing din number din yarinyar wacce yayi saving da Bhj.......



*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 5:06 AM] Nawartye&: 5***Har tayi ta katse ba adaga ba bata hakura ba tasake dialing akaro na biyu tana daf da katsewa taji andaga cikin siririyar muryarta tayi sallama da,

"Assalamu alaikum abin kaunat....."

Tun kafin ta karasa shamsiyya tayi azamar katseta,

"To karamar karuwa..... Marar aji marar tarbiyya nafada miki kifita daga harkar mijina kinki yarda ko? To wallahi tallahi....."

Kit taji ankatse wayar kafin ta karasa fadar abinda tayi niyya nan tasake kira amma aka ki dagawa tana huci zuciyarta sai tafarfasa takeyi abdurrahman yashigo dakin yana rikeda wayarshi guda daya,

"Meya hadaki da wayata?"

Harara ta watsa masa sannan ta kalleshi awulakance,

"Ga wayarka ba wani abun nayi da itaba..."

"Kin dai yi halin naki da kika saba... Baki da aiki sai binciken wayata kiyita kiran abokan arzikina kina kare musu zagi sai kace ke kadaice macen da aka halitta da kishi.... Yanzu dan Allah ina girma anan koda yaushe kina kiran yarinya kina zaginta da sunan kishi? Wannan abun da kikeyi haukane da jahilci yake damunki"

"Ehh dole dama ka kirani da jahila mahaukaciya tunda ka shirya auro mai degree, degree din banza degree din wofi... Da can baka san ni jahilar bace ka aureni?,ai ni baka burgeni ba wallahi sai kaje ka dauko mai PHD...."

Bai kulataba yasaka kai yafice domin office zai koma haka yatafi yabarta tanata bambami kamar zata saka duka, zama tayi ta tsara text massage na wulakanci ta turawa budurwar tasa wacce yake shirin aurowa sai lokacin taji tasamu dan sassauci domin tasan aduk inda take yanzu tana can hankalinta atashe ranta abace saboda irin cin zarafin da ta tura mata. Abdurrahman yana office yarinyar ta kirashi tana kuka tana fada masa abinda matarsa ta turo mata shi yarasa ya zaiyi da halin shamsiyya gaba daya ta shiga rayuwarsa tahanashi farin ciki gashi ko yakai kararta gidansu anyi mata magana baji zatayi ba tunda yasha zuwa gidansu yasamu mahaifinta yafada masa amma ko ya kirata yayi mata nasiha ko fada bata gyara halinta akanta saida ya sakewa budurwarsa layin waya fiyeda sau uku saboda agujewa fitunar shamsiyya amma dan jarabar kishi kullum ita kenan cikin binciken wayarshi ahaka take lalubo number din yarinyar ta kirata taci mata mutunci,

Da bacin rai yakoma gida kuma yakoma da niyyar ya ciwa shamsiyya mutunci akan abinda tayi masa saboda yagaji da lallabatan nan da yake tayi amma bata gani, ya nuna mata karshen kawaici saboda baya so ya biye mata suyita bakanta ran juna sai ta dauka saboda auran da zai karane yasa yake wulakantata, da fushinsa yashiga gidan amma koda yashiga dakinta sai ya isketa ita da yara kewaye da

3 / 14