Chapter 8 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 14

21K to 24K   out of 40.2K words

massage ta tura masa cewar itace sai gashi kuwa yakira,

"Hello guy... Nicefa yanzu banida wayane fa wannan ma ta sister inlaw dinace na dauka bata saniba..."

"Ayya baby ai inata nemanki but ban sameki ba what's happening? Meya faru da wayarki? Kina ina yanzu? Zan siyo miki waya sai inkawo miki ki fada min irin wacce kikeso?"

"Faruk kabari kawai sai nadawo school yanzu nafa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da maka ina gida kuma mamana ce mafa ta rasu...."

"Ohh my God.... What a great lost.... Allah yajikanta... Babu damuwa idan kin shigo zamu jone"

Sallama tayi masa ta kashe wayar sannan tagoge number dinsa tafita falo tayi sa'a kuwa dan har lokacin marakisiyya na kitchen tana aikinta. Daren ranar tayi niyyar yiwa yaya sagir maganar komawarta school amma atsorace take dashi dan gabanta inbanda faduwa babu abinda yakeyi, koda tayi masa maganar bayan yadawo da daddare shiru yayi yana nazari kawai wasiyyar umma yake tunawa nabar mishi amanar bahijja da tayi sannan tace yayi mata duk abinda takeso domin shine gatanta bayan babu ranta dan Allah kar yabarta tayi maraicin rashinsu,

"Shikenan naji kije zanyi shawara...."

Tunda taji yafadi haka tagane akwai alamun nasara washe gari da yafita ya iyo mata siyayya kaca kaca harda sabuwar waya amma yakarya sim dinta na da yace taje ta siyi wani Nasiha yayi mata sosai akan shaye shaye da lesbian din da take kokarin cusa kanta, washe gari da kanshi ya dauketa yakaita bauchi yamayar da ita makaranta,bayan sunje yakira azima amma tace itama tatafi gida kaninta ne yarasu, saida yasake ja mata kunne sannan yatafi yabarta, yana tafiya bayan takai kayanta hostel takira Faruk tace masa tadawo mintuna kadan sai gashi yashigo da sabuwar mota dal dan ko lamba ma babu ba adaurawa motar ba da sabuwar waya babba kirar kamfanin HTC daukarta yayi suka fita daga makarantar.

***

Abangaren abdurrahman da shamsiyya kuwa sai sam barka zamansu domin tun lokacin da yace mata yafasa aure zamansu yake dadi kullum cikin lallabata yakeyi saboda gudun kar yabata mata rai ciwonta ya tsananta kamar yadda dr bala yafada masa,

Tana zaune cikin kwanciyar hankali da yaranta guda biyar Musaddiq da muhibba sai shuraim da yusra da amra yar auta, su Kansu yaran yanzu sun san ana zaman lafiya agidansu dan shamsiyya rayuwarta takeyi gaba gadi sai abinda takeso take yi,

Yau da wuri ta tashi tayiwa abbansu muhibba karin kumallo domin tafiya zaiyi zaije garin abuja, kafin tagama hadawa har yayi wanka ya shirya yafito cikin suit bakake wadanda suka amsheshi sosai, sai kamshin turaren chronic men yakeyi, a dining yasameta tana karasa shirya kayan karyawar kiss yayi mata a kumatu kafin yaja kujera ya zauna yana murmushi jin dadi,

"Kin san fa 7 jirginmu zai tashi shiyasa naketa wannan gaggawar..."

"Ai baka makara ba..." Tafada tana murmushi,

Agurguje shikam yakarya yaje yaga yaranshi wadanda ke daki sunata bacci ya shafa kansu yafita tarakashi daga nan tadawo gida taci gaba da al'amuranta, aranar kanwarta badiyya tazo domin tayata zama itace kanwarta ta biyu kuma ahalin yanzu tana shekarar karshe a jami'ar sa'adatu rimi inda take yin NCE dinta a bangaren Islamic,

Suna zaune suna hira shamsiyya ta kalleta tana jan tsaki,

"Wallahi wasu matan ma shashashu ne inbanda shashanci tayaya mace dan mijinki zai kara aure ki wani saki jiki kina farin ciki harda tayashi murna a status? Kalli fa abinda sokuwar labour dinnan tarubuta...."

Ta karasa maganar tana mikawa badiyya wayar tata, nan takarba tana dubawa kyakkyawar mata tagani da wani handsome din mijinta harda yaransu tare dasu sunyi masifar kyau akasan hoton ta rubuta _I congratulate you on your wedding and wish you half of the most beautiful things in the world. The other half I ll leave for me._

Murmushi badiyya tayi aranta tana fadin woww, afili kuwa tace,

"Anty shamsiyya wannan din kawarki ce? Gaskiya sun burgeni"

"Class mate dinace... Tare mukayi secondary da ita, wai dan tsabar dorawa kai wahala shine harda wani hada walima.... Mtswww nonsense...."

Dariya badiyya tayi bata kai ga yin wata maganar ba su muhibba suka shigo aguje daga makota ganin badiyya duk suka rufu akanta suka rungumeta suna murnar ganinta,

Daki guda shamsiyya ta ware ma badiyya kamar yadda tasaba duk lokacin da daya daga cikin kannenta sukazo bata hadasu da yara dakinsu daban take basu,

Duk aikace aikacen gidan badiyyan ce keyi tayiwa yara wanka da sauran hidindimu, kwananta biyar agidan abdurrahman yadawo daga abuja,

Kullum ita dai badiyya tana daki idan tafito to aiki zatayi kasancewar acikin dakin da takema akwai kayan kallo, kwananta goma sha biyu agidan da wata safiyar
alhamis shamsiyya na bedroom dinta tana sakawa amrah pampers bayan ta yimata wanka, ganin badiyya tayi tashigo idanuwanta jajur kuma shabe shabe da hawaye tana rikeda jakar kayanta,

"Anty natafi gida...." Shine abinda badiyya tafada kuma bata ko jira amsar shamsiyya ba tayi waje abinta da sauri duk da cewa shamsiyya nata kwalla mata kira amma bata tsaya ba,hankalinta ne taji yatashi saboda atunaninta agidane wani abu yafaru shiyasa tayi azamar bin bayanta amma kafin ta karasa tuni badiyya har tafice daga gidan duk da tanata faman kwala mata kira bata saurareta ba tayi tafiyarta akan idonta ta tare napep tashiga har lokacin tanata faman share kwallar dake zuba a idanuwanta, cikin sauri takoma cikin gida taje ta dauki wayarta takira Abasiyya wato kanwarta dake bi mata,

"Hello anty..."

Cikin tashin hankali tace,

"Abasiyya meke faruwa ne agidan? Waye ya mutu?"

"Wai wanne gidan? Mutuwa kuma?"

"Dan Allah ki sanar dani gaskiya, gidanmu mana"

"Mu nan lafiya lau muke wallahi, mafarki kikayine?"

"A'a badiyya ce naga tafita tana kuka inata kiranta amma taki saurarata"

"Rabu da ita da shirmenta kila haukan natane ya motsa... Ni wallahi kinma katse min baccina da nakeyi haka kawai"

"Shikenan sai kije kiyi tayi nidai tunda lafiya kalau shikenan"

Daga haka ta katse wayar ta ajiye taci gaba da abinda takeyi wato shirya amrah tana ta taba baki aranta tana tunanin to me tayiwa badiyya da ta tafi da duku dukun nan kuma tana kuka? Bata da amsar wannan tambayar shiyasa ta watsar taci gaba da abinda takeyi.....


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 2:04 PM] Nawartye&: 12***Yana nan tsaye inda tatafi tabarshi yajingina da jikin bango rungume da hannayensa sai turo baki yake kamar tana wurin, yasan bilkisu kawai jarumta da dauriya take nunawa amma tana da mutukar kishi akansa ko ada da bata sonsa bare yanzu da yazame mata wani sashe na rayuwarta,

Hannunshi ya cusa cikin sumar kanshi yana shafawa ahankali Allah sarki yasan yanzu watakila tana can tana kuka ko kuma tana tunane tunane dakyar ma daren yau idan zata iya bacci,

Fasa zuwa part din amarya husnah yayi yanufi wurin bilkisu domin yanada bukatar ganin halin da take ciki sam baya son damuwarta baya kaunar yaga tana cikin damuwa wannan ajininsa ne,

Bilkisu kuwa lokacin da tabar dakin fahad dakinta taje takai kayanta da ta debo kamar su inner wears, turare, hijabai da zannuwa sai kayan bacci dama su tafi ajiyewa adakin nashi, tana son ta kwanta amma kuma tana jin kamar bazata iya wannan baccinba sakamakon abinda ke sokar zuciyarta, bata kwana da yaranta amma yau yazama dole ta kwanta tare dasu ko hakan zai debe mata kewar mijinta,

Dakinsu hanfa taje ta rinka daukosu daya bayan daya tana dawo dasu dakinta tana kwantarwa kan gadonta bayan tagama tashiga bathroom ta dauro alwala kamar yadda tasaba domin hakan yana da mutukar muhimmanci kuma kariyace tsakiyar yaran tashiga ta kwanta tana kokarin yimusu addu'a taji yabude kofa yashigo, wuta ya kunna ganin kan gadon acike dasu hanfa yasashi waro manyan idanuwansa yana gimtse fuska,

"Baby daga tafiyata yau shine har an kawo masu maye gurbina...?"

Murmushi tayi tamike zaune sannan itama tayi kasa da murya gudun kada su tayar da yaran,

"Dan Allah ango kaje katafi kabarmu muyi bacci muma... Ni wallahi bacci nake son inyi"

"Au korata ma kikeyi?" Yafada yana sake bata rai, sauka tayi daga kan gadon ta nufeshi tana zuwa takama hannunshi tajashi waje,.

"Dan Allah karka tada min da yara suna bacci... Jeka tafi wurin amaryarka saida safe"

Hannun nata yaja yahadata da jikinsa yana laluben bakinta har yayi nasara, tureshi tayi bayan yan mintuna tana harararshi,

"Haka kawai ka bata min alwala ta..."

"Alwalar kwanciya bacci ai bata karyewa koda kuwa mutum yasake kama ruwane so karki damu da wannan.... Muje ki rakani"

"Anki din..." Daga haka tashige cikin daki tana jinshi yana cewa,

"To kin manta hular baccinki..."

Dakin yasake binta yakai mata hular ya isketa tana cikin toilet ajiye mata yayi yafita zuwa part din husnah wanda shima yahadu ajin karshe komai nata coffee and milki inbanda kamshi babu abinda yake tashi, komai dake cikin part din iri dayane dana Bilkisu har da dakin yara itama gashi nan gefe daya. Da murmushi dauke akan fuskarsa yabude dakin nata yashiga tana kwance saman gado ta lulluba da mayafinta dan harma tafara dan bacci zama yayi daf da ita yana kallonta tasha gyaran jiki itama tayi wani kal da ita ga yiri yirin kitson dake kanta wadanda akayi mata kitson gaba kai gaskiya husnah fa ta canja sosai,

Hannunta yakamo wanda ke cikin mayafi atukunkune babu shiri tabude idanuwanta ta kalleshi,

"Ashe kana tafe sai yanzu tabarka kataho?" Tafada tana dan bata rai kadan,

Hannun nata yasake makalewa cikin nashi yana murmushi,

"Ita wa?"

"Uwar gida mana sarautar mata"

Kawar da zancen yayi tahanyar cewa,

"Nidai fatana wannan karon ba irin zuwan baya kika yimun ba...., kar naji kince kina wannan abun naki mai yawan kwanaki"

Dariya tayi masa ta lumshe idanuwanta,

"Duk matsuwarka dai kabari yatafi"

Ido yazuba Mata wanda har saida taji dan kunya wai meyasa fahad baida kunyane ita lokacin suna saurayi da budurwa wallahi kallon salihi take yimasa ashe silent killer ne duk yabi yagama batata da maganar rashin kunya,

"Bafa bacci zakiyi ba Asma'u.... Tashi dan Allah.... Kema ai amatsen kike..... Tashi muje falo kici wani abu sai muzo muyi bacci, tashi tayi tabi bayanshi yana rikeda hannunta suka fita.

***

Da kuka shamsiyya takarasa gidansu dake tudun mun tsira anan cikin kwaryar kano, tana shiga ta iske duk yan gidan na tsakar gida kamar yadda suka saba zama Gwaggo amarya tana gaban murhu sai fama da hayaki take tana ta hura wutar amma taki kamawa da alama itacen danye ne kokuma wani abu mai kama da haka, kasancewar tsakar gidan irin dan kut dinnanne baida girma yasa duk tsakar gidan turnikewa da hayaki sai inna sabuwa da babarsu wacce suke kira da baba suna zaune suna tankade da dakan garin kuka wanda za akada miya dashi ganinta tashigo tana kuka yasa duk hankulan mutanen gidan yakoma kanta, wuri tasamu ta zauna bayan ta dangwarar da akwatin da tazo dashi, daidai lokacin Gwaggo amarya tazo inda take domin tayi sa'a wutar takama,

"Ke shamsiyya menene haka? Ya zaki shigo gida da kuka? Lafiya?"

Kafin tayi magana abasiyya,zuhuriyya da mardiyya sun fito daga cikin dakinsu sunzo wurin amma banda badiyya duk yadda akayi ita bata nan watakila,

"Wai badake nakeba shamsiyya ki fada mana abinda yake faruwa" Gwaggo amarya tasake fada cikin daga murya,

"Gwaggo abdurrahman yasakeni.... Haka kawai banyi masa komai ba"

Salati suka fara yi da sallallami jin abinda tace,

"Kuma kikace bakiyi masa komai ba? Anya kuwa shamsiyya ayi saki batare da laifin komai ba?" Inna sabuwa tafada tana jimamim abun ita dai baba wato mahaifiyarsu batace komai ba saima tankaden kukarta da take tayi kamar bata wurin,

"Wallahi babu abinda nayi masa innah.....girki ma nakeyi yace inbari intaho gida yasakeni"

"To wannan abu dai akwai alamar tambaya domin yazo da salo na daure kai... Allah yasawwake"

Gwaggo amarya ce tafadi hakan tana komawa gaban murhu domin har wutar tasake mutuwa, Jakarta ta bude ta kalli khamisu kaninta Wanda shigowarshi kenan da allo ahannunsa da alama daga makarantar yamma yake tace yaje yasiyo kalanzir yakawo azuba awutar ko za asamu takama.

Sai lokacin ta mayar da kallonta gasu abasiyya wadanda ke tsaye kikam fuskokinsu dauke da damuwar jin bakin labarin da tazo dashi,

"Abasiyya kuna ciki kenan...."

"Ehh wallahi anty, miko amrah din ingoya ta..."

Abasiyya tafada tana mika hannu domin karbar amrah yayinda sukuma su zuhuriyya ke tsaye basu ce komai ba saboda sosai abinda shamsiyya tazo dashi ya gigita tunaninsu,

Suna nan zaune atsakar gidan har badiyya tashigo lokacin an kusa sallar magrib, ganin shamsiyya harda akwatin kaya itama yasata yin turus tana jimami nan ta zauna suka gaisa shamsiyya nakara basu labarin irin sakin wulakancin da abdurrahman yayi mata tunda ita dai tasan bata yimasa laifin komai ba, ahaka har lokacin dawowar mahaifinsu yayi wanda suke kira da baba yana rikeda bakar leda wacce yasiyo yan kayayyakin kusa da baki kamar yadda yasaba duk lokacin da zai dawo daga wurin sana'arsa ta k'ira ganin shamsiyya shima abin yasashi cikin yanayi marar dadi dama ranar adakin baba yake wato mahaifiyar su shamsiyya yana shiga yar turakarsa yakira shamsiyya domin jin abinda ke faruwa,kamar yadda ta fadawa su gwaggo amarya haka shima ta fada masa amma takare maganar da kuka tana cewa,

"Ko shakka banayi nasan budurwarsa wacce da zai aura amma yafasa itace taje ta shiryo asirinta dan ta rabamu"

"Ya isa ki daina kuka sannan kar na kara jin kin fadi wannan maganar.... Yanzu dare yayi amma insha Allah gobe da safe zanje gidan waliyyinsa inji abinda yake kwakwai.... Allah yarufa asiri, tashi kije."

Tashi tayi tafita tana jin kwalla na taruwa a idonta wannan wacce irin muguntace abdurrahman yashiryo mata haka kawai yazabi ya rabata da yaranta dan kawai ya kuntata mata? Dakinsu abasiyya tashiga wanda ke dauke da wasu tsoffin katifa guda biyu sai ko yan kayayyakinsu daga gefe kuma dakinma ba wani girma gareshi ba dan ko su hudunma atakure suke acikinsa, zama tayi gefen daya daga cikin katifun dake dakin tana kokarin lallaba amrah wacce ke motsi tana son tashi,

Gwaggo amarya ce ta bankado labule tashigo tana dauke da kwanukan abinci dan sai yanzune tasamu nasarar gama tuwon da take girkawa tun la'asar,

"To ga abincin naki shamsiyya"

"Tom gwaggo amarya sannu da kokari...."

Saida ta tabbatar da cewa amrah takoma bacci sannan tajawo kwanon abincin ta bude, tuwon dawane miyar kuka gashi nan bakikkirin dashi haka dai ta dan runtse ido ta daure ta caccakula taci kadan ta kwashi kayan tafita dasu,

Har lokacin baba wato mahaifiyarta ba aji kalma ko guda daya daga bakinta ba har sai da lokacin kwanciya yayi ana maganar ta yadda zasu kwanta adakin tunda yayi musu kadan shine tace wata acikinsu tazo dakinta ta kwana sai gwaggo amarya tace a'a badiyya da zuhuriyya suzo dakinta su kwana tare, sai lokacin tayarda tabbas bahaushe yayi gaskiya dan duk wanda yabar gida to gida yabarshi, ahaka dai ta kwana batare da tayi cikakken bacci ba, gari da yawaye gwaggo amarya takawo mata koko da kosai da dumame duk dai sama sama taci su sannan tatashi taje tagaida baba anan yake sake bata hakuri sannan yace yanzu gidan walin abdurrahman zaije wanda ke unguwar sharada, daga nan dakunan iyayensu mata duk tabi tagaidasu daga karshe tayi zamanta adakin innah sabuwa. Tunda baba yafita take zuba idon dawowarshi amma shiru har la'asar atakaice dai saida lokacin dawowarsa daga makera yayi sannan sai gashi yadawo bayan yahuta yakirata kamar jiya,

"Shamsiyya naje gidan Alhaji mai kwano kuma mun tattauna dashi.... Ashe ma yaran naki suna gidansa can abdurrahman din yakaisu, to abinda yake faruwa yanzu ma shi mijin naki baya nan wai ayau dinnan yabar kasar yatafi kasa mai tsarki sai nan da makwanni uku zai dawo... To yabani hakuri akan mujira yadawo din domin shi koda wasa bai sanar dashi cewa yasakeki ba...."

"To shikenan baba dama shima bayin kansa bane wallahi budurwarsa ce ta shirya wannan abun"

"Koma dai menene shamaiyya kiyi hakuri insha Allahu Allah yana tare dake" inji innah sabuwa kasancewar tana cikin dakin.

Haka taci gaba da zama agida har tsawon sati uku babu yan kwanaki cikin wannan hali badiyya tafara wani matsanancin zazzabi da amai mai ban tsoro duk ta dashe tayi wani fari fauuu wanda hakan yatashi hankulan jama'ar gidan nan gwaggo amarya ta tisata agaba takaita asibiti kasancewar akwai layi tunda asibitin gwamnatine yasa suka wuni curr acan basu dawoba sai la'asar liss,

Lokacin da suka dawo duk su shamsiyya na tsakar gida banda zuhuriyya wacce ke can dakinsu tana karanta littafin Hausa,

Zama gwaggo amarya tayi jikinta duk asanyaye kuma babu kuzarin kirki,

"Lafiya dai ko? Allah yasa dai ba malaria dinnan bace ko typhoid dan yanzu su sukafi addabar al'ummarmu zazzabi kadan sai ace malaria ko typhoid" inji inna sabuwa, ita kuwa baba dake gefe cewa tayi,

"Nikuma ulcer nafi kawo mata tunda tace kirjinta har rikewa yakeyi"

Ajiyar zuciya gwaggo amarya tasauke sannan cikin sanyin murya tace,

"Kaddara ce dai Allah yarigada ya aiko mana, badiyya tajawo mana magana ta iyo cikin shege....."

"Innalillahi wa innah ilaihir raji'un" shine abinda kowannensu ke furtawa, abasiyya kuwa tsaye ta mike tana rikeda amrah amma bata san tamike dinba saboda tsananin rudewar da tayi, kowa arazane yake mutuka ita kuwa mahaifiyarsu tamkar wacce aka kafa takasa koda motsi, wani irin kuka mai ban tausayi badiyya tafashe dashi jin irin cagwadar da ake ta yimata kowa na tofa albarkacin bakinsa ana cewa tayi asara ta daukowa gidansu abun kunya, har baba yadawo tana kuka kuma taki tayi magana tambayar duniya su innah sabuwa sunyi akan tafadi wanda yayi mata cikin amma taki tace komai daga karshe saida baba yadawo shima ya iske wannan bakin labarin karshen tashin hankali shima yashiga dan da ace yanada cutar hawan jini to da tabbas babu abinda zai hanashi tashi, shima dai maganar guda dayace akan waye yayi mata ciki amma shi dinma bata fada masa ba, ai tun a wannan rana tafara ganin tsangwama da kyara da tsana domin babu ruwan kowa da sabgarta iya gwaggo amarya ce kadai ke dan sakar mata fuska tana lallabata tana yimata nasiha cewar tabata wayonta tunda ta iyo cikin shege amma ta daure tafada musu wanda yayi mata. Da wayo da dabara gwaggo amarya tasamo kanta tace zata fada aranar da daddare bayan baba yadawo daga wurin sana'arsa dauke da tsarabar su yalo, goba, rake da sauransu gwaggo amarya ke sanar dashi tashawo kan badiyya zata fadi ko waye yayi mata wannan cikin, gaba dayansu duk sun taru atsakar gidan suna

8 / 14