Chapter 13 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 14

36K to 39K   out of 40.2K words

tafara gajiya dashi ne?

Shiru sukayi baka jin bakin kowa sai aikin karar cokula zuwa can bilkisu ta nisa sannan sukaji tace,

"Amarya da ango me kuke so indafa mana da daddare amatsayin dinner? Ko zaku ci tuwo?"

Murmushi husnah tayi ta daga ido ta kalleta,

"Anty ai duk abinda kika dafa zamu ci....."

"Ai to ban saniba ko kuna da zabi...."

"Bamu da wani zabi duk abinda kikeso wallahi muma zai yimana..."

"To shikenan Allah yakaimu daren...."

Shi dai yana jinsu baice komai ba har suka gama sai su biyu ke dan taba hirarsu ahaka har bilkisu tagama tatashi tace bari tashiga ta duba mimi wacce ke cikin bedroom tana bacci. Da kallo yabita har saida ta kule masa yadaina hangota,sai a lokacin yasake da husnah,bayan sun gama cin abincin husnah tafita zuwa part dinta shi kuma yabi bayan Bilkisu zuwa cikin bedroom dinta,

Kwance ya isketa kusa da mimi da waya a hannunta,

"Ni zan fita....."

Kallonshi tayi fuskarta dauke da murmushi,

"Adawo lafiya ranka yadade...."

"Wannan bata tashi daga baccin ba?"

"Bata tashi ba ai gara tayi nima na huta"

"Zakiyi bayani idan taki yi da daddare...."

Daga haka yajuya yafita tabi bayansa da kallo, kwanciyarta taci gaba da yi acikin daki tana hutawa har saida su maama suka zo lokacin ne tafita dan rakasu part din husnah,ai kuwa cikin girmamawa da mutuntawa ta karbesu suka gaisa tareda yimata Allah yasanya alkhairi suka tafi. Part dinta takoma taci gaba da abinda yake gabanta lokacin dora girkin dare nayi tashiga kitchen bayan ta goya Mimi,sanye take da doguwar riga mai karamin hannu marar nauyi,tana tsaka da aikin tuwon da takeyi husnah tashigo cikin fara'a tace,

"Anty....ashe kina nan kinata aiki,kawo in tayaki"

"Ahhh haba amarya ai baza ayi hakaba daga zuwa sai kifara aiki? Dan Allah kibarshi karki damu wallahi..."

"A'a anty wallahi saina tayaki ai nima zama da kwanciyar wuri daya sun isheni....."

Dukda Bilkisu tana hanata amma bata yarda ba har saida ta karbi jajjagen kayan miya da yankan alayyahu ta tayata shiyasa tare suka yi girkin duk da bawata hira sukeyi sosai ba amma dai sunyi sun gama cikin armashi kuma anan itama husnah tasake ganin wasu abubuwan wadanda suka shafi girki duk da babu laifi itama tanada sani akai,tare suka kwashe tuwon shinkafar da suka girka miyar alayyahu wanda yaji isasshen nama sai kamshi ke tashi wanda idan ka shaka dolenka kaji yunwa na ratsaka koda kuwa akoshe kake,

Kasancewar lokacin anata kiraye kirayen sallar magrib yasa kowaccensu wucewa dakinta bayan sun gama shirya table, basu sake fitowa ba sai bayan da aka yi sallar ishah lokacin fahad yashigo shida su hanfa part din husnah yafara kai yaran yace suje su gaida anty sai yanzu ta tsaya tayiwa yaran kallon tsaf gaskiya tubarkalla kyawawa ne masu kama dashi sak dukkansu kamarshi sukayi,tare da ita suka shigo part din bilkisu itama fitowarta kenan daga dakin fahad tanufo falo tana rikeda mimi wacce ke tata rigimar amma ganin yan uwanta yasata fara karar murna tana bangala dariya,

Sosai husnah take kallon bilkisu afakaice wato idan Allah yabaka kishiya wayayyiya hawan jini tsaf zai iya kasheka mutukar baka kai zuciyarka nesa ba,yanzu ma wata arniyar shadda dark brown colour bilkisu tasaka sai maiko shaddar keyi dinkin ya kama jikinta kasancewar riga da skirt ne gashi taci dauri duk da bawani kalmashe kalmashe tayi masa ba simple style kawai tayi taci make up kamar mai shirin zuwa dinner Allah yasota itama tayi wanka ta sauya kayan jikinta daga na dazu zuwa doguwar riga yar kanti,kai ai dolema mutum ya koyi gayu ko dan bilkisu domin sam ita bata tsufa kullum cikin kuruciya zaka ganta,

Table dukkaninsu suka hau fahad sai satar kallon mutuniyar tasa yakeyi wacce tafito kamar amarya kai wanda bai saniba bazai iya banbance tsakaninsu wacece amaryar ba cikin nishadi suka gama cin abincin domin su Muhammad nata basu labarin gidan ayiyah, husnah zama tayi tana kallonsu saboda yanda suka sake suna hira da yaransu da alama sun gina kyakkyawar rayuwa da mu'amalarsu da yaransu tun daga tushe kawai sai taji itama tana burin ta haihu ko dan irin haka,har wurin karfe 9 suna part din bilkisu fahad baida niyyar tafiya sai bilkisu ce ma tace,

"Baby to kuje mana amarya ta kwanta tahuta ko bacci take bukata...."

Dan harararta yayi kafin yamike,

"Tashi mutafi husnah tunda anfara korarmu...."

Dariya husnah tayi ta mike tayiwa bilkisu saida safe suka fita,tana ganin fitarsu tatashi tarufe ko ina ta tattara ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kan yaranta suka wuce ciki saboda tasan fahad na iya dawowa,ai kuwa sai gashi yadawo din ita lokacin ma ta kwanta,cizon yatsa yasoma yi saboda jin kofar falon nata arufe........



*_Ummi Shatu_*=?L? [2/1, 2:48 PM] Nawartye&: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


21***Kishingide yake bisa lallausar kujera wacce take sheki kamar gold kirar royal kan cinyarsa yar karamar laptop ce yana dan lallatsawa cikin kwarewa da kwanciyar hankali,sanye yake da kayan shan iska saboda yanayin zafi da garin na yola ke fama dashi,yar karamar rigace marar nauyi light blue sai wando iya gwiwarshi dukkaninsu shara shara ne marassa nauyi,

Wani matashin saurayine yafito daga cikin wani kayataccen daki yanufoshi fuskarsa dauke da murmushi,dukawa yayi ya durkusa sannan cikin sanyin murya yace,

"Nagama kammala komai ya shugaba na...zaka iya shiga ka watsa ruwa...na gyara maka dakin sannan kuma na wanke toilet din haka kuma na wanke maka dukkanin kananan kayan naka...yanzu abinda yarage shine kayi wanka sai ka karya domin tuni anjima da hada karin kumallon da yadace dakai wanda ko tantama banayi zakaji dadin sanyawa cikinsa shi....."

Shiru yayi kamar bai jishiba, kasancewar yasaba da halinsa idan har da sabo yasashi sake gyara zamansa sannan cikin sanyin muryar da tafi ta dazu yace,

"Ya shugaba na maina da alama yau kamanta ko wacce ranace yau agareka.....yaufa itace rana mafi muhimmanci da farin ciki atare dakai....Allah ya albarkaceka ya shugaba na, Allah yaci gaba da tsareka fari mai farar aniya...hadari sa gabanka inda kakeso...sukari bakai farin banza ba....."

Idanuwanshi na kan laptop din dake bisa cinyarsa ya dan buda baki kadan yace,

"Zaidu me kace anshirya min amatsayin abin karyawa?"

"Allah ya taimaki maina dan sarki jikan sarki....akwai gurasa da miya akwai da sugar sannan akwai da zuma,sai dankalin turawa da miyar kwai sannan anyi farfesun kayan cikin saniya sai soyayyen naman kaji masu romo romo da wainar shinkafa sannan anhada maka koren shayi kamar yadda aka Saba...."

Jijjiga kai yayi yaci gaba da abinda yakeyi zuwa wasu yan sakwanni yakalli wanda yakira da suna zaidu,

"Zaidu duk afitar dasu abar min iya kazar kadai da shayin...."

"Amma ranka yadade baka dan hadawa koda gurasar ne? Ka gafarceni ya shugaba na amma gaskiya wannan rashin cin abincin naka yafara yawa.... Kuma gwaggo kilishi har tafara korafi akai"

Dan murmushi yayi bayan yarufe laptop din dake kan cinyarshi sannan ya kalli zaidu dakyau,

"Zaidu halittar tawace ai haka ni bana son inta durawa cikina tarkace....ka kyale gwaggo kilishi gigin tsufa ke damunta...."

"Allah yaja zamaninka....." Zaidu yafada yana fadada murmushinsa,

"Kawo min abincin...."

Daga haka ya maida hankali kan wayarshi wacce ke ajiye kusa dashi bai kara bi takan zaidu ba wanda yadage yanata zuba masa kirari kamar babu gobe,

Tea din ya karba bayan zaidu ya tsiyaya masa cikin cup nan yafara kurbarshi sannu sannu yana yi yana duba jaridar daily trust da ya dauka bayan ya ajiye wayarshi,

Suna nan zaune zaman kurame yana cigaba da karatun jaridar da yakeyi aka kwankwasa kofa da sauri zaidu yatashi yafita mintuna biyu yasake dawowa cikin girmamawa ya tsugunna gabanshi yana yimasa alamar girmamawa da hannunshi,

"Maina mai wanke maka kafane yazo....ashigo dashi yanzu ko sai ka kammala karyawa?"

Agogo ya dan kalla 12 daidai na rana dan rausayar da kanshi yayi,

"Ai kawai kashigo dashi zaidu kaga yau juma'a banida isasshen lokaci sosai"

"Angama ranka yadade...." Zaidu yafada yana barin wurin cikin hanzari,

Sake kishingida yayi yana cigaba da karyawa har su zaidu suka karaso cikin girmamawa mai wankin kafa yafara aikinsa yayinda shi kuma zaidu ya zauna yana dan bawa maina labari lokaci zuwa lokaci ahaka har aka kammala wanke masa kafafun nasa,

Ciki yatashi yashiga batare da yadauki komai wanda yake wurin ba duk sai zaidu ne ya tattare su yamayar ciki bayan ya sallami mai wanke kafar,

Wankan juma'a yayi sannan yayi shirin masallaci cikin manyan kaya brown din shadda yar gaske da hula yar bama mai mutukar tsada kalar kayanshi sai agogon Rolex na azurfa turaren oud khasusi yafesa sannan yafito kafarshi sanye da takalmi silifas,zama yayi a falonshi ya dora kafa daya akan daya kamar yadda yasaba wannan shine zaman da ya iya, baiyi ko minti biyu da zamaba zaidu ya bude kofa yashigo shima cikin tashi shigar ta zuwa masallaci,

Bakaken takalma half cover irin na sarauta yaje ya dauko masa yakawo gabansa ya ajiye nan yasaka baice komai ba yatashi yayi gaba zaidu yatake masa baya har zuwa gaban motarshi wacce ke ajiye agaban sashen,bude masa gefen mai zaman banza yayi yashiga ya zauna sannan shima yashiga mazaunin driver yaja suka tafi.

Misalin karfe 2:30 zaidu yayi parking aharabar gaban sashen umma jidda nan yafita cikin sauri ya budewa maina kofa yafito yana yiwa iska wata irin shaka wacce bazaka taba gane abinda yake nufiba shin isace ko kuma sarauta?

Dai dai yake taku har zuwa cikin sashen nata wanda ke kawace da ababen more rayuwa,babu motsin kowa sai kukan tsintsaye wanda har hakan yaso bashi mamaki domin yasaba ganin jama'a dankam asashen nata,anutse yabude kofa yashiga,yana shiga yasake shiga cikin wani mamakin domin wani hadadden decoration akayi kamar hall din biki ko ina balam balam ne different colours anyi ado dasu ganin wurin ya gauraye da duhu ya dan ji rass amma sai ga wasu kaloli sun fara kawo rubutu mai dauke da _Happy birthday maina_, kafin yayi wani motsi yajiyo ihun mutane suna ihun "Happy birthday to you...... happy birthday to you......"

Ajiyar zuciya yasaki ya dan fadada murmushinsa yajuya yana kallonsu,dukansu jere suke cikin kwalliya ta alfarma sunyi mutukar kyau,jinin sarauta kenan,sun doshi su goma mata da maza dukkaninsu kannenshi ne da cousins dinshi,kan kujerar da aka tanada dominsa yaje ya zauna yana kallonsu daya bayan daya cikeda nishadi,wani gingimemen cake ne girke gabansa ummussalma ta mika masa wuka wai ya taimaka ya yanka tashi yayi ya yanka yabisu daya bayan daya yana saka musu abaki,sai da yagama dasu sannan yanufi dakin umma jidda wacce yasan koda za ashekara ana wannan shagali tofa bazata fito ba shiyasa shima baya iya sakewa da ita,

Yana shiga ya isketa Kishingide kan carpet tana fuskantar kofa amma ganinsa sai ta juya baya shima asanyaye yakarasa gefenta ya durkusa ya gaisheta gaisuwar dai bata wuce uku kamar yadda aka saba daga nan suka cigaba da zaman kurame har na tsawon wasu mintuna kafin yamike yana fadin,

"Nabarki lafiya ranki yadade...."

Bata amsaba har yafita daga cikin dakin,har lokacin masu shagalin birthday na nan kamar yadda yabarsu sunata faman shan rawa,dakyar shikam ya yarda yatsaya sukayi hotuna dasu sannan yafita yanufi sashen gwaggo kilishi.

Tun daga bakin kofa yake karaskiya da bayi amma babu wata gaisuwa tsakaninsu musamman ma matan saboda kasancewarshi ustaz kowa yasan halinsa a masarautar da iya maza kadai yake mu'a amalarshi banda mata tsakaninsa da mata sallama ce itama ba koda yaushe ba,

Lokacin da ya isa sashen kilishi ya iske sai drama ake yi da ita akan cin abinci ita alallai sai taci abinda likita ya hanata ci kasancewar tanada lalura,mabruka na gefenta sai lallabata takeyi shigarsa yasanya mabrukan fita zuwa cikin daki sukuma sauran bayin dake zagaye da ita suka fita izuwa sashensu,

Zama yayi yana kallonta irin kallon tuhuma,

"Ke wai meyasa kike da taurin kai da kakkafiya ne? Ga abunda likita yace kici amma baza kici ba......kiduba fa kiga irin halin da kika shiga last month kika samu muka rinka wahala da dawainiya.....kece India kece chairo kece saudiyya duk dan kisamu lafiya amma shine yanzu saboda kin samu sauki zaki kara zuwa ki jangalo mana wata wahalar....."

Tunda yafara maganar take harararshi har lokacin da yagama saida ta kare masa harara sannan tace,

"Umhummm ai dama maganar kenan....fitinanne mai jarabar sa idon tsiya....idan mutum yayi magana kuma kaje ka kaishi gaba har wurin mai martaba....."

Dariya yayi ya jingina da jikin kujera bayan ya cire hular dake kanshi,

"Dan Allah dan saka akawo min wannan dambun naman kinji amaryas...."

Harara ta sake jifanshi dashi sannan ta ja dambun accha din dake gabanta wanda dazu su mabruka keta lallabata akan taci amma taki,

"Bani dashi.....kaima kayi zuciya ka auro mata tarinka yimaka mana"

Dariya yayi yamike yanufi hanyar bedroom dinta yana cewa,

"Maganar dai kenan kwaya daya kullum itace....bakida wata magana saita aure"

Yana jiyota tana fadin,

"Haisam karka yarda inshigo dakin nan insameka....kafito min daga cikin daki na fada maka"

Bai fito dinba har saida yadebo dambun naman cikin flate sannan yazo yasake zama kusa da ita,

"Maina kasan me nake so dakai? Kasamu yarinyar can ku daidaita kanku daga nan zuwa watanni biyu domin ni ayanzu banida burin da yawuce naga na aurar daku gabaki daya...." Tafada tana nuna masa dakin da mabruka take ciki,

"Meyasa kika damu da wai lallai sai kin aurar damu ne? Me muka tare miki?"

"Baku tare min komai ba maina amma lokaci yayi wanda yadace ace kasamu iyali....ka duba kaga duk kannenka kowa da iyalinshi daga matan har mazan kai kadai yarage yanzu kuma kaine babba....kaduba kaga duk kannenka mai martaba yabawa kowa sarauta mai daraja amma kai ya hanaka saboda bakada aure ko hakan bazai saka kayi aureba?"

Murmushi yayi yana taunar dambun naman dake bakinsa tabbas kam shi yasan wannan shine dalilin da yasa mai martaba bai bashi sarauta ba amma sauran kannenshi kowa yanada ita tunda ranar shagalin aurensu ake hadawa da na sarautar ayi amma dayake masarauta ba arabata da gutsuri tsoma da jita jita mutane sai suka juya maganar suka ce wai dan sarki yafi son haisam ne shiyasa bai bashi sarauta ba saboda shi yake son ya gajeshi kowa a cikin masarautar akan wannan tunanin yake sannan kuma dashi din ya yarda,

"Nidai dan Allah maina badan na isaba ku daidaita kanku kaida mabruka kaga ai yar uwarka ce cikinku daya...."

Sai lokacin ya dakata da taunar da yakeyi ya zuba mata dara daran idanuwanshi masu haifar da kasala,

"Wai gwaggo kilishi ana so dole ne? Tace bata sona nima bana sonta to ba shikenan ba?"

"Shikenan kam to amma duk da haka bazaka zauna ahaka kaki aureba......munyi magana da mai martaba akwai yar amininsa zakaje kaganta tunda kai kowacce mace aka hadaka da ita sai kace bata yimaka ba...."

Baice komai ba ya ajiye flate din dambun naman dake hannunshi yatashi zai fita,

"Kafi ruwa gudu sarkin zuciya"

Yana jinta bai tanka ba yadauki hularshi yafita yana zancen zuci,shi wai meyasa aketa tallenshi ne kamar wani wanda ya shekara sittin baiyi aure ba? Kullum su kenan cikin kai tallenshi wurin kananan yara bayan kuma idan yaje ba daidaitawa sukeyi ba, wannan karon kam babu inda zaije.......



*_Ummi Shatu_*=?L? [2/2, 2:06 PM] Nawartye&: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


22***A zuciye yafita daga sashen gwaggo kilishi yana jin wayarshi na kara amma bai kulaba har saida ya isa wurinda zaidu ya ajiye motarshi shikuma yana can zaune shida sarkin gida da mabudi suna cin rogo da gyada wanda mabudi yasiyo a bakin kasuwa bayan yadawo daga sallar juma'ah,

Hango haisam da zaidu yayi yasashi azamar tasowa bama shi kadaiba hatta su mabudi da hanzarinsu suka taso suna kirari,

"Ran maigida yadade....barka da fitowa baya goya marayu....aljannah mai masoya da yawa...."

Shi ba ma'abocin dariyane satataaa ba shiyasa kawai yadan murmusa yadaga musu hannu cikin sanyin murya yace,

"Assalamu alaikum....kuna lafiya?"

Daga haka yashiga cikin gaban mota bayan zaidu ya bude masa,babu bata lokaci shima zaidun yazagaya yashiga yaja motar sukayi gaba,karar wayarshi da ta dameshi yasashi cirota daga aljihun rigarshi,

"Hello David......kasamo wani bayani ne?.....ok bari zan kiraka zuwa anjima"

Daga haka yakatse wayar yana mai yiwa baura nuni da yatsanshi alamar yakaishi bangarensa bawai fada ba kamar yadda yaga yana kokarin yi. Sauya akalar sitiyarin motar baura yayi daga hanyar fada zuwa sashen maina wanda da akwai yar tazara tsakani,

Baura na yin parking maina haisam yafito rikeda hularshi yabude falonshi ya shiga bai tsaye anan ba yawuce bedroom dinshi yana shiga yafara kokarin cire rigar dake jikinshi yarage daga shi sai farar vest irinta maza sai dogon wandon shaddar dake jikinshi,jin ana kwankwasa kofa yasashi zama gefen Royal bed dinshi yana tankware kafarshi guda daya,

"Yes...." Yafada muryarsa akasa amma kasancewar baura yagama saninsa ciki da waje har yajiyo daga inda yake tsaye,shigowa dakin yayi yana dan russunawa,

"Ranka yadade akwai abinda kake bukata ne....? Zan dan leka gidane"

"Bana bukatar komai baura...." Yace da zaidu wanda suke kira da baura,

"To amma ai ranka yadade baka ci abincin rana ba yakamata inje infara karbo maka tukunna...."

"Duba fridge afalo akwai fura da nono ka kawo min ita kadai ma ta isheni....."

Murmushi zaidu yayi sannan cikin wasa yace,

"Yallabai kai dai kam soyayyarka da fura ta musamman ce zaka iya rayuwa da ita ko babu abinci...."

Dan murmushi shima haisam din yayi yana matsa wayarshi,

"Ai ni indai da fura da tea da nama to zan iya rayuwa...."

"Ai nasani yallabai.....bari nakawo maka"

Ganin zaidu yabude kofa yafita yasashi tashi ya dauko laptop dinshi yahaye saman gadonshi yana kokarin kunnata,har lokacin da zaidu yakawo masa furar ya ajiye hankalinsa naga laptop dinshi saboda akwai muhimmin abun da yake dubawa,

Sallama zaidu yayi masa yafita zaije gida yadawo zuwa la'asar,saida ya dan jima idanuwanshi akan laptop din ko kifatawa bayayi sannan yadago ya janyo wayarshi yayi dialing number din David bayan ya dan tsiyayi furarshi kadan wacce tasoma hucewa sabanin da wanda harda kankara aciki,

"Hello David naga komai....yanzu kasan me zai faru? Bani number din yellow inkirashi...."

Ba ajiyo abinda na kan wayar ke fada wato David,sake gyara zamansa yayi akan gadon ya bude bedside drewar dinshi yadauko wata waya kirar LG,

"Ok fadi muji....."

Saida yagama saka number din sannan yakatse wayar David yasoma kiran ta

13 / 14