Chapter 2 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 14

3K to 6K   out of 40.2K words

na dan matsa mata, kallonshi tayi tasaki murmushi,

"Yaushe wai zamuje inda kace ne? Nifa wallahi zaman gidan nan ya isheni sabon gida nake so"

Mikewa tsaye yayi yana nannade hannun rigarshi yana murmushi idonshi fes akan fuskarta,

"Karki damu ai saura kiris akammala, nafiso sai angama komai sannan sai inkaiku kugani daga nan kuma sai muyi packing mu koma..."

"Masha Allah, Allah ya nuna mana..."

"Amin, bari nayi alwala"

Daga haka yajuya yayi ciki nan tabi bayanshi da kallo gaskiya sai yanzu tasan ta tafka kuskure babba abaya domin tana mutukar son Fahad wanda ada bata fahimci hakanba sai yanzu da zama yayi zama.

Kamar yadda suka saba bayan sallar ishah suka hadu suka ci abinci a faranti daya tare da yaran nasu shiyasa wani lokacin idan yaran basa nan shima fahad din baya nan sai takasa cin abincin ita daya saboda sabo da tayi naci tare dasu, adakin yaran suke tana zaune tana kallonsu suda abbansu yana shiryasu domin kwanciya bacci,duk wanda yashirya sai yaje kan karamin gadonsa ya kwanta, saida yagama shiryasu sannan yazo ya zauna yana yimusu tatsoniya dukkansu yaran dariya sukeyi bilkisu na tayasu saboda yadda yadage yana rera wakar da gizo keyi acikin tatsoniyar, daga karshe addu'a suka yiwa yaran suka fito daga dakin kowa yanufi nashi domin shirin bacci, wanka bilkisu tayi ta zauna ta bata lokaci wurin gyara jikinta da turaruka da mayuka masu kamshi sannan tasaka rigar bacci mai daukar hankali wannan itace dabi'arta da daddare bayan yara sunyi bacci takan sa kayan bacci na daukar hankali bayan sallar asubah kuma sai tasauya da wasu kayan masu dan dama dama, tana rikeda mimi akafadarta ta wuce dakin fahad yana kwance yana waya amma jin motsinta sai yakashe wayar ita dai batayi magana ba sannan bata kawo komai aranta ba tashi zaune yayi ya karbi mimi ya kwantarta gefe guda sannan yaja bilkisu jikinshi itama ya kwantar da ita yana fadin,

"Oyoyo baby nah.....bari inbaki wani labari..."

"Am all ears..." Tafada tana gyara kanta akan kirjinsa babu jimawa yajita shiru ashe tayi bacci abinta tabarshi yanata magana Shi kadai.

Cikin yan watannin da bazasu gaza huduba ginin da fahad ke yimusu ya kammala komai sabo yasaka musu acikin gidan ginine na zamani ga bedrooms din yaransu maza nasu daban suma matan hakan gaskiya yakashe kudi ba kadanba wurin gina gidan shiyasa bahaushe yace mahakurci mawadacine wata rana, walima sosai bilkisu ta shirya musu yan uwa da abokan arziki suka zo suka tayasu murna aranar suka tare, sun tare babu jimawa yabiya musu umarah ita dashi suka tafi suka bar yaran awurin ayiyah dama Mimi ce kadai ke shan mama, gaskiya fahad karshe ne domin kamar kada su dawo dan soyayyar da ya shayar da ita sunyi ibada kuma sun sha love dan zata iya cewa aduk tafiye tafiyen da suka taba yi tare dashi babu kamar wannan, wannan shine best moment din da yafi tsaya mata arai, gida suka dawo cikeda kaunar juna da kuma dokin ganin yaransu,dawowarsu babu jimawa ta samu canjin wurin aiki domin yanzu tana aikine tare da gwamnatin jaha duk inda gwamnati take tana nan shiyasa yanzu bata samun zama sai dai sam hakan bai shafi zamantakewarta da iyalanta ba tana basu lokutansu kamar yadda tasaba.

Zaune take kan gadonta tana sanye da kayan baccinta purple colour masu mutukar santsi idonta sanye cikin farin glass din dake kara karfin ido, aiki takeyi acikin system dinta Mimi kuma na kwance gefenta tana bacci dakin duk ya gauraye da daddadan kamshi na night spray dinta, ahankali yabude kofa yashigo jikinsa asanyaye,zama yayi gefenta ya kwantar da kansa kan kafadarta,

"Bae ya akayi?" Tafada tana cigaba da latsa system dinta, dagowa yayi ya kalleta yana jin faduwar gaba,

"Baby magana zamuyi....."

Barin abinda takeyi tayi tarufe system din ta tureta gefe daya sannan ta maida hankalinta gareshi ta rungumeshi ajikinta kamar wani jariri, lukus yayi yana shakar kamshin jikinta,

"Bae meke damunka? Uhmm?"

"Kaina ke ciwo...."

"Ayya sorry.... Kasha magani?"

Kai yadaga mata sannan ya kalli Mimi wacce ke kwance tana bacci, mayar da kallonshi gareta yayi ya dan saki murmushi,

"Bari naje dakina please kizo yanzu..."

Kai ta daga masa tana cire medical glasses din dake idonta, a wani sukurkuce yafita daga dakin nata har lokacin fa gabanshi bai bar faduwa ba kai anya kuwa zai iya sanar da ita? Tayaya? Kasa zaune kasa tsaye yayi adakinshi sai kaiwa da kawowa yake tayi ahaka tashigo ta iskeshi tasake bulbulo wani turaren mai rikita tunani, hannunshi takama har bakin gadonshi suka zauna,

"Kamar da akwai abinda kake son fada min ko bae?"

Lumshe idanuwansa yayi shi dama yasan bilkisu tasan shi ciki da waje takan gane damuwarsa tun kafin ya fada mata. Girgiza mata kai yayi sannan ahankali ya kwanta ajikinta yadora kanshi akan cinyarta,

"Bana jin dadine...."

"Ayya sorry baby ai kafada min..... Zo kayi bacci you will feel better insha Allah..."

Kafada yamakale mata nan tayi murmushi ta hade tafin hannunta da nashi tana murmushi,

"To mekake bukata da baza kayi bacci ba?"

Da hannu ya nuna ta idanuwanshi alumshe,

"Ni....?"

Kai ya daga mata, sumarshi ta shafa sannan ahankali tasoma yimasa magana kasa kasa bayan takai bakinta kusa da kunnenshi,

"Karka damu dama ni ai takace akoda yaushe but yanzu ka dan yi bacci zakaji dadin jikinka please.... da asubah sai inbiya bashi"

Kai ya daga mata, gyara musu kwanciyar tayi suka kwanta tare sai shagwaba yake zuba mata ahaka yasamu bacci. Washe gari da safe ta rigashi fita aiki shikam bayan tafita zama yayi yanata tunanin tahanyar da yadace yabi wurin fada mata abinda ke ranshi daga karshe salim yakira yana dauka yafara fada masa shifa yakasa sanar da bilkisu, dariya salim yayi yace,

"Shiyasa idan ance kai matsoracine ka musa, kai wallahi mijin hajiyane tsoronta kakeji, simple abu ka kasa fada mata.... To me kake nufi?"

"Salim dan Allah kazo ka fada mata, yanzu tafita aiki amma nasan around 1 zata dawo saboda girka lunch..."

"Shikenan may be zan shigo.... Matsoraci kawai"

Murmushi fahad yayi yakatse wayar duk da haka fa gabanshi bai bar faduwaba dan koda yafita yaje wurin aiki ma kasa zama yayi, 2 da yan mintuna yakoma gida, yara duk sun dawo daga makaranta suna babban falo suna kallon cartoon ita kuma bilkisu taci uwar kwalliya cikin coffee din shadda ta kafa dauri sai kamshi takeyi, gaba dayansu daga ita har yaran sukaje suka taroshi suna yimasa oyoyo, hadasu duk yayi ya rungume yana kashewa bilkisu ido daya alamun tayi kyau, tanata jera masa abincin da tayi akan center table din dake tsakiyar falon salim yakirashi yace ya karaso, fita yayi yashigo dashi su hanfa suka yanyameshi suna kiran, "Abba salim oyoyo...."

"Lallai Abba salim yau kaine da rana tsaka haka? Kodai batan kai kayi" bilkisu tafada tana dariya,

"Hajjaju takanas yau gidan nan nazo..."

"To muna yimaka maraba"

Daga haka tajuya kansu hanfa tana cemusu,

"Maza atashi aje ayi shirin islamiyya abarsu daddy suci abinci... Oya let's go mana,muje wurinsu anty mariya su shiryaku"

Saida fahad yaga tafiyarsu sannan yamaida kallonsa kan salim,

"Abokina nidai anya kuwa bazan fasaba? Allah bana son bacin ran hajjaju sam"

"Kai kasani, idan kaga zakayi kai kasani idan kuma kaga fasawar zakayi shima duk kai kasani.... Nidai bani abinci inci"

Daga haka yamike yasoma zuba abinci ahaka bilkisu tafito ta tarar dasu, cikin sauri tace,

"A'a Abba salim dakanka.... Bari azuba muku mana..."

Karba tayi ta zuzzuba musu sannan takoma kusa da fahad ta zauna, sunata yar hira kadan kadan amma mafi yawancin hirar itada salim keyi yana yimata hirar budurwarshi shi fahad yaki sakewa ayi dashi da haka suka gama cin abincin a lokacin ne salim ya fuskanceta,

"Hajiya bilkisu magana nazo muyi ta fahimta saboda abokina yakasa fada miki shiyasa ni ya gayyatoni dan insanar dake...."

Tattara hankalinta tayi zuwa kan salim tana kallon fahad,

"Lafiya? Ina sauraronka dai...."

"Yawwa.... Dama fahad ne yace insanar dake zai kara aure.... Zai dawo da tsohuwar matarsa husnah....."

Ai bilkisu ji tayi tamkar anbuga mata guduma atsakar kanta wannan dalilinne yasa numfashinta ya dan tsaya cak na wucin gadi babu bata lokaci idanuwanta suka kada daga farare izuwa jajaye jur......


*ANFARA ANFARA....Tagwayen littattafai guda biyu tamkar da dubu sune aka fara sharbar romonsu wato mulki ko sarauta Kashi na biyu na marubuciya phertymah xarah da kuma takwaransa kumallon Mata wanda ke dauke da cigaban labarin kamar da wasa wanda marubuciya ummi Aisha ta rubuta... Wanda ke bukatar wadannan dadadan littattafan guda biyu zai biya 500 mai son guda daya kuma zai biya 300 ta wadannan lambobi kamar haka.*=?G?

2083371244
Aisha M.Salis.
Zenith Bank

Sai atura shaidar biya ta wannan no=?G?
+447894142004

Ko kuma recharge card ta wannan no=?G?
08169334980


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/21, 5:06 AM] Nawartye&: ? *HASKE WRITERS ASSO*.



*KUMALLON MATA.....!*=???



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



*D'andano daga labarin kumallon mata*


*3*


***Kanta ta dafe da hannunta guda daya sakamakon sarawar da taji gefen kanta yayi cikin karfin hali da dauriya ta kalli salim tana kokarin daidaita nutsuwarta wacce tayi bulaguro daga gangar jikinta na wucin gadi,

"Masha Allah..... Kace gidan namu zai samu karuwa nan bada jimawa ba.... To Allah yasanya alkhairi...."

Juyawa tayi ga fahad wanda yayi sakare yana kallonta cikeda mamaki kamar wani soko haka yasaki baki da hanci yana kallonta, cikin murmushin karfin hali tace,

"Yanzu dama akan wannan maganar ne ka gayyato Abba salim kaki fada da kanka? To me kake son nuna masa? Kenan kana son nuna masa kai matsoracine ka kasa sanar dani zaka kara aure? Well.... Congratulations, Allah yasa ayi damu..."

Shiru fahad yayi daga shi har salim bilkisu tabasu mutukar mamaki, "anya kuwa matar nan babu wani abu wanda ta boyewa ranta? Anya da zuciya daya take yin wannan maganganun?" Wannan itace tambayar da yake tayiwa kansa acikin zuciyarsa, mikewa yaga tayi fuskarta dauke da murmushi,

"Ku dan bani 2 minutes bari nadawo.... Zan karasa shirya yara zasu tafi islamiyya..."

Bata jira cewarsu ba tawuce ciki inda su hanfa suke Mariya nata kici kicin shiryasu ita kuma mimi uwar kiriniya sai faman wasa take da kayan da ta baro daga saman mirror dinsu,duk abinda takeyi kawai dauriya take yi amma harga Allah jin zuciyarta take yi tana yimata wani irin zafi tamkar zata kama da wuta ta kone,

Da taimakon su Mariya suka karasa shirya su hanfa mariya da maryam suka kwashesu suka tafi domin driver na waje yana jiransu,canjawa mimi kayan jikinta tayi sannan ta dauketa suka fita har lokacin su fahad nazaune basu dawo daga duniyar mamakin da bilkisu takaisu ba, zama tayi tana ajiye mimi akasa tana nuna mata salim,

"Baby kinga Abba salim can fa, bazaki je ki gaidashi ba?, ce Abba salim ina wuni?......."

Dariya salim yayi yataso ya dauketa yana yimata wasa shi mamakin da yakeyi shine rayuwar nan yanzu batada wahala masifar gudu takeyi wai yau fahad ne keda yara har guda hudu, lallai duniya komai fararre ne kuma kararre,

"Gaskiya hajjaju kinyi mutukar burgeni... Ban taba zaton haka daga garekiba, wallahi abinda nakawo shine ina fada miki zaki tsigaleni tas sannan ki koreni daga gidan nan kuma ki kirani da munafuki kamar yadda sauran mata keyi idan ansanar dasu mijinsu zaiyi musu kishiya...."

Dariya bilkisu tayi tana mikawa mimi hannu,

"Haba Abba salim dan jahilci ko dan me? Ai anwuce wannan era din yanzu... Allah yasa mudace dai kawai"

Maida kallonta tayi ga fahad wanda ke kallansu amma yakasa furta koda kalma daya,

"Ango kagama cin abincin ne?, anjima ina son fita fa kafin yara su dawo kuma motar naga kamar babu isasshen mai ko zaka samo mana?"

Kasa magana yayi sai daga kai kawai daga haka yamike shida salim, salim sai sakawa bilkisu albarka yake yana yimata fatan alkhairi saboda harga Allah ta burgeshi sosai tayi abinda yasan mata da yawa bazasu iyaba wato su boye kishinsu, suna tafiya tashiga daki ta zauna tana rikeda mimi sai lokacin taji hawayen da suka jima suna kwaranya acikin zuciyarta sun fara fitowa ta idanuwanta, duk da mimi kusan jaririya ce amma abinka da mahaifi ganin bilkisu na kuka itama sai tafara tsaga kuka, saida tasha kukanta ta gama sannan ta tashi ta goya mimi taje dakin fahad ta dauko maganin ciwon kai tasha, har lokacin idanuwanta jajur suke saboda kukan da tasha duk da tasaka kwalli tana fitowa daga cikin dakinsa sai gashi yashigo yana rikeda waya wanda bata san ko da wa sukeyi ba, ko kallonshi bata yiba ta raba ta gefenshi zata wuce saurin riko hannunta yayi tajuya tayi masa mugun kallo cikin sauri ya sakar mata hannu tawuce zuwa falo, baiyi kasa agwiwa ba yabi bayanta, wato sufa mata wani lokacin tamkar masu aljanu suke ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yanzun nan zasuyi maka abun kirki idan anjima kuma suyi sabanin haka.

***

Tunda aka fara aikin gyaran part din amarya shamsiyya tasake shiga cikin bakin ciki da tashin hankali kwata kwata taki bari kowa yaji dadin zaman gidan domin hatta masu aikin akule take dasu tana jin kamar duk duniya bata da makiyan da suka fisu, shi kuwa mai gayya mai aiki wato abdurrahman ji take bata ko kaunar ganinsa, ta daina yin girki dashi, ta daina yimasa magana mai dadi sai ta cin fuska da bacin rai,gashi kullum cikin fada suke gaba daya yarasa ya zaiyi da ita dan hatta yaransu ma tadaina kulasu ta daina yimusu wanka ta daina komai da yadace ace uwa tana yiwa yayanta, duk tabi ta lalace shima tasashi yafara fita hayyacinsa, masifar safe daban ta rana daban ta dare kuma tafi ko yaushe domin bata barinsu su rintsa sai har idan bacci barawo ne yayi nasarar saceta.

Cikin nasara yau aka gama gyaran dayan part din da akeyi hakan yasa abdurrahman yace itama tafadi dukkan abinda take bukata na gyara sai azo ayi mata jin yafadi haka yasata fara surfa masifa da bakaken maganganu,

"Ehh dama mana.... Ai dole kafadi haka tunda za acuceni za auro min bakar daga... Yarinyar da ta gama iskancewa tagama karade gari taki aure shine yanzu ni za akawo min ita to wallahi bazai yuyuba, ko kaffara bazanyi ba wallahi bazaka yi wannan fitinannen aurenba marar albarka.... Macuci kawai azzalumi wanda bai san alkhairiba butulu, inbanda butulci tun fa baka da komai nake tare dakai.... Amma yanzu dan tsabar rashin imani daga yin arzikinka shine zakace zaka karo min kishiya... Dama namiji ba dan goyo bane, kuma duk matar da ta dauki namiji uba to tabbas zata mutu marainiya, ada baka da komai ni nazauna tare dakai amma dan tsabar rashin adalci shine yanzu kana yin kudi bazaka barni inzauna ni kadai ba...."

Duk maganganun nan da takeyi yana zaune gefen gado yana jinta kuma yana kallonta yayi tagumi ya tallafe kumatunsa.

Saida yaji tayi shiru ta dan tsahirta sannan ya yi magana cikin sanyin murya,

"Shamsiyya yakamata fa ki rinka duba wani abu guda daya, namiji mijin mace hudu ne dan mata hudu aka halicceshi, ko agidanku mata ukune karkashin inuwar mahaifinki...."

"A'a Abdul.... Karka kuskura kasako iyayena cikin wannan badakalar taka.... Karka yadda wallahi, dan gidanmu mata ukune shikenan wannan sai tazame maka hujjar kawo min wata cikin gidan nan? To wallahi bazai taba yuyuwa ba ehe.... Inma banda sharrin d'a namiji wacce irin wahalarka ce ban shaba, tun kana fakirinka baka da ko taro nake tare dakai amma yanzu kace wannan sakayyar zaka yimin.... Namiji rigar kaya"

Sake gyara zamansa yayi ya kishingida yana kallonta, yarasa meyasa idanuwan mata ke rufewa akan kishi sam basa iya yiwa kalmar zan kara aure duba na tsanaki da nutsuwa sudai da zarar ka fada musu wannan Kalmar shikenan kazama abokin fada da gabarsu, bai sake tanka mataba saboda kawai yabarta taji da abinda ke damunta amma har acikin ranshi ya shirya mata tarin alkhairi wanda da ace ta kwantar da hankalinta da ko amaryar bazata fita gata ba,har ta karaci fadanta da banbaminta tabar dakin bai sake cewa uffanba.

***

Tana tsaye da mimi goye abayanta ta goya hannayenta abaya sai jijjiga Mimi takeyi yakarasa yana kallonta,

"Baby na sako miki mai amotar fa...."

Bata ko kalleshi ba taci gaba da lallaba mimi dake bayanta dan tasamu tayi bacci,

"Baby magana nakeyi fa... Kince min zakije unguwa dazu"

"Nafasa" tafada cikin kunar rai daga haka bata sake cemasa komai ba duk kuwa da irin magiyar da yaketa yimata akan ta daure ta sanar dashi laifinsa.

Har yara suka dawo daga makaranta bai samu ta kulashiba sai harkar gabanta take tayi, kitchen ta shiga ta dora tuwo bayan ta kwantar da mimi a dakinta, tana tsaka da tuka tuwon su hanfa suka dawo, su maryam ne suka zo suka tayata karasa girkin bayan sun cire uniform dinsu, har lokacin fahad na gida yana dakinsa kwance acan su hanfa suka sameshi. Bayan sallar ishah lokacin da zasuyi dinner ta dan saki fuskarta kamar yadda aka saba gudun kada yaran su fahimci wani abu especially ma su Mariya wadanda da wayonsu, sai da sukayi hira da yaran kamar yadda suka saba sannan sukaje tayi musu shirin bacci suka kwanta, ita kam dakinta tashiga tana shiga tarufe ruf da key, dakyar ta iya yin shirin bacci saboda tukukin da zuciyarta keyi sam yau bata b'ata lokaci wurin gyara jikinta ba saboda bazataje dakin fahad ba, wasu zafafan hawaye ke fita daga idonta wadanda tasan direct daga zuciyarta suke tahowa.

Fahad kam ganin shiru shiru bata dawoba yasashi sake shan jinin jikinsa domin kullum yasaba su zauna su sha hirarsu bayan yara sun kwanta, sai sun gama kallo sannan suke tashi suje su kwanta amma yau shiru, ko dakinsa baije ba yafara zuwa nata amma abun mamaki arufe, tsayawa yayi yaita knocking amma taki zuwa ta bude gashi wayarta akashe yakikkira bai sameta ba, saida yagaji da tsaiwa sannan yanufi dakinsa ransa duk babu dadi, to wannan salon fushin da bilkisu ta dauka tafara meye ma'anarsa, da damuwa aransa yayi wanka ya kwanta batare da yashafa ko da mai ba, turare kadai ya iya fesawa ya kwanta, juyi kawai yayita yi yana jin kunci na lullubeshi bai samu cikakken bacciba awannan dare sai bayan asubah sannan bacci mai nauyi ya daukeshi. K'arfe 9 da wani abu yatashi brush kadai yayi yafita falo saboda jin gidan shiru ai kuwa babu kowa sai shi daya, yara sun tafi school ita kuma tafita aiki amma gida gashi nan neat ta gyara ko ina sannan ga breakfast dinshi nan ta shirya masa akan table, tsayawa yayi cak yarike waist dinshi yana nazarin sauyawar da bilkisu ke neman yi daga jiya zuwa yau. Tsabar damuwa baiko buda abincin ba yakoma dakinshi yana shiga yadauki wayarshi ya kunna text din bilkisu ne yashigo

2 / 14