Chapter 12 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 14

33K to 36K   out of 40.2K words

ta yanke shawarar komawa gida aranar ai kuwa aranar suka kama hanyar gano itada badiyya bayan tabar musu duk tsarabar da ta taho musu da ita daga kauye..........


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/30, 2:08 PM] Nawartye&: 19***Bayan tafiyar badiyya da yan wasu kwanaki abdurrahman yashirya yabita can kauyen gano,gaba daya kanta yagama kullewa domin tana son abdurrahman Amma kuma bata son zumuncinsu yasamu rauni ata sanadiyyar haka tunda tasan ayanzu dai idan za atambayi shamsiyya babban makiyinta to ita zatace wannan dalilinne ma yasa da abdurrahman yayi mata maganar turo magabatansa tace sai tayi shawara,langabe kai yayi yana tambayarta wai wacce shawara kuma zatayi tunda dai tana sonshi duk da haka dai bata aminceba tace yajira zata kirashi.

***

Har bahijja tayi zazzabinta tagama tafara rubuta exam dinta yaya sagir baya daukar wayarta,text massage kuwa tayi masa shi yafi akirga amma bai taba replying dinta ba kuma har lokacin bai sanarwa matarsa da abinda yafaru ba ita kuma gashi sosai suna gaisawa da bahijjan dan kusan kullum sai sunyi chaten,

Abangaren bahijjan kuwa har yau dai hali na nan babu abinda ya canja fitarta club tare da faruk babu abinda yaragu shiyasa karatun exam dinma sama sama take yinsa danma suna samun interval sosai amma duk da haka bata yin wani karatu sosai kamar da dan yanzu har takai takawo bata shigowa makarantar sai ranar da takeda paper dan wani guest lodge faruk yakama musu suke sha'aninsu sosai yake kashe mata kudi har abin yafara bata tsoro,suna zaune dakinta ya bararraje kan gado tana zaune kusa dashi tana kallon kyakkyawan zoben gold din da yabata dazu daga fitarshi yadawo dashi, daga ganin zoben kasan mai tsadane dan yanada kauri sosai ga kyalli da yake faman yi,

"Guy.....wai a Ina kaketa samun kudin nan haka? Naji last time kuma kana cewa account dinka yayi kasa....."

Dan tashi zaune yayi ya kalleta,

"Baby kawai ki basar..... Dad na yiwa 419....."

Shiru tayi tana kallonsa wato ayanda ta fahimta faruk yayiwa kudi mummunan sabo sam bazai iya rayuwa batare da kudi ba tabbas kashe kudi dabi'arsace da bazai iya canja ta ba sai dai wani kadari na Allah. Lumshe idanuwanta tayi tana kallonshi,

"Faruk 419 kuma? Dad din naka?"

"Baby to ya hanani kudi yahanani inji dadin rayuwata kinga kuwa ai dole nima inrinka ha'intarsa......"

"Gaskiya guy karka kara ai mahaifi babu kamarsa aduniya.....kaji?"

"Naji baby....yanzu bari naje nayi bacci kafin zuwa yamma sai mu fita ko?"

"Babu matsala guy....ina jiranka"

Tashi yayi yafita ita kuma taci gaba da zama tana kallon zoben da yabata,to me faruk yake nufi? Ita dai tasan bawai soyayya suke yiba amma dai suna kulawa da juna a matsayinsu na abokai, Koda yake watakila shima kawai yabata dinne amatsayin friendship bawai soyayya ba.

Aranar tunda suka fita dashi basu waiwayo masaukinsu ba sai karfe 1 nadare,washe gari tashiga school tunda sassafe domin tanada exam da rana,adakinsu lady tayi masauki ta iskesu suna baccinsu na asara kamar yadda suka saba bayan sunyi kurbe kurbensu.

Bayan sun kammala exam dinsu gaba daya bata tafi gidaba saida ta kara sati daya awurin faruk aranar da zasu tafi umarah shida dad dinsa aranar itama tatafi gida,

Tasamu kyakkyawar tarba awurin marakisiyya matar yaya sagir amma shi kam bai sakar mata fuskaba fushi yake da ita sosai da sosai duk da yana kokarin boyewa dan kar matarshi ta gane,

Wani abu dake kara daure masa kai shine tunda bahijja tadawo bata da wani aiki sai na barci wuni zatayi tana kwance duk lokacin da zai tambayi marakisiyya ina bahijja amsar guda dayace shine tana bacci babu wani aikin gida da take taya marakisiyya sai gayyar bacci nan yasoma tsarguwa da wannan baccin nata marar karewa,

Fara saka mata ido yayi sosai ko zai gano wani abu amma batare da saninta ba,yau yakasance weekend yana gida itama marakisiyya na nan amma tace masa zataje asibiti dubiyar mijin yayarta,yana zaune afalo Bayan fitar marakisiyya bahijja tafito cikeda bacci a idonta ta shiga kitchen,daki tawuce rikeda filet dinta na abinci da robar lemu,

Saida tagama komai ta koshi sannan ta daga katifar dake kan gadon ta dauko kwalbar syrup tabude zata fara sha kenan taji andauketa da wani gigitaccen mari dukanta yashiga yi da kafa babu kakkautawa domin tuni tafado kasa daga kan gadon,ahaka marakisiyya tazo ta sameshi duk kafarsa na ciwo sakamakon bubbugewar da yayi wurin dukanta sannan itama bahijjan tana daki sai kuka takeyi dan ta daku sosai ba kadanba sai faman murkususu take yi,

Cikin tashin hankali marakisiyya ta shiga ta riketa tana tambayar ta abinda ke faruwa amma takasa magana sai kuka takeyi,shima kuma yaya sagir din yaki fadin laifin da tayi masa da yagama ta dameshi da tambaya hade rai yayi yawuce dakinsa yana cemata ta dafa masa ruwan zafi zai gasa kafarshi,

Yana gefen gado azaune abun duniya yataru ya isheshi marakisiyya tashigo dauke da ruwan zafin ta ajiye agabansa tana kallonshi,

"Kafafuwa na Zaki gasa min please...." Yafada yana kokarin kwanciya,

Batayi magana ba ta dauko towel karami ta tsoma tafara gasa masa kafafuwan nashi saida ta kusa gamawa sannan tayi magana cikin sigar lallashi,

"Amma yaya sagir ni ina ganin koma wanne laifi bahijja tayi maka bai dace karinka yimata irin wannan dukan ba,nasiha zaka rinka yimata da kuma bada shawara amma duka baya gyara.... sannan kadai san ita ba lafiyayya bace baka gudun ka ja mata wata lalurar kuma? Yanzu dan Allah meye amfanin wannan dukan da kayi mata kamar wata karamar yarinya...."

Shiru yayi bai tanka ba yanajin zuciyarshi nayi masa radadi ganin alamun bazai yi magana ba yasata tashi tafita dauke da ruwan zafin da yasoma hucewa,

Wurin bahijja tasake komawa wacce har lokacin tana kwance tana kuka,zama tayi agefenta tasoma yimata magana cikin kwantar da hankali,

"Bahijja koma wanne laifi kika yiwa yayanki nasan mai girmane dan haka kawai bazai kamaki awannan shekarun naki yace zai dakeki ba....kefa yanzu ba yarinya bace,dan Allah kidaina laifi irin wannan....yanzu kiyi hakuri kiyi shiru ki daina kuka idan yaso anjima sai muje kibashi hakuri....kiyi hakuri kinji"

Dakyar marakisiyya ta shawo kanta tatashi tahau saman gado ta zauna ita dai marakisiyya sai bin dakin take da kallo ko wai zataga wata alama wacce zata bata haske akan laifin da bahijja ta aikata amma bata ga komai ba domin tuni yaya sagir ya tattare duk wasu kwayoyi da syrup da yagani akasan gadon yaje ya boye a inda bazasu taba ganiba,domin acikin motarshi ya boye,

Cigaba da lallashinta marakisiyya tayi daga bisani tafita tabar dakin ta nufi nata,tana fita kiran faruk yashigo cikin wayarta da number dinshi ta waje domin bayan sun bar saudiyya da Dad dinshi kasar Spain suka wuce,

Muryarta adashe da alamun kuka ta dauki wayar tana sharar hawaye,

"Baby.... me kuma yafaru? Najiki kamar kina yin kuka, what's happening? Tell me please"

Kwashe abinda yafaru tayi ta fada masa tana sake zubar da wasu hawayen,

"Ayyah baby....gaskiya wannan brother din naki baida kirki.......am very sorry kinji,kiyi shiru kin san ban son kukanki........"

Tamkar wata jaririya haka yasata agaba yana rarrashi har ta saki ranta, lokacin da marakisiyya tazo ta isketa tana zuba fara'a da hira sosai sai abin yabata mamaki nan tafita tabarta da murmushi akan fuskarta,

Har dare bata yarda tafito falo ba gudun kar su hadu da Yaya sagir asalima kunyar ganinshi take ji gashi bata jin dadin jikinta gaba daya kuma dan ganganci sai tayi wanka da ruwan sanyi,ahaka dai taketa daddaurewa amma ita kadai tasan me take ji ajikinta,

Tana kwance tukunkune cikin bargo Yaya sagir yayi sallama yashigo fuskarshi adaure,

"Ki shirya kayanki zuwa gobe zamu je tarauni zan kaiki gidan hajiyan tarauni dazu ta kirani awaya tace inkaiki kije ki karasa hutunki acan",daga haka taga yajuya yafita bai jira yaji abinda zatace ba,shi harga Allah baya son bahijja tayi nisa da gida ayanzu saboda wadannan munanan halayen da ta koyo to amma babu yadda ya iya tunda hajiya itace takirashi da kanta tace yakaita,tun acikin daren ta kintsa kayanta ta zuba cikin jaka duk abinda tasan zata bukata ta sakashi ciki daga nan ta kwanta,tana nan kwance marakisiyya tashigo suka dan taba hira zuwa 9:30 tayi mata sallama tafita,faruk ta kira tana sanar dashi hutun da zataje.

Washe gari bayan ta kammala breakfast wanka tayi tashirya cikin doguwar riga ta atamfa ta yafa mayafi taja jakarta tafito inda yaya sagir ke jiranta fuskarshi babu walwala marakisiyya na tsaye gefenshi,

"To yan hutu kuma sai yaushe za adawo?"

Murmushi bahijja tayi sannan cikin rashin kwarin jiki tace,

"Before akoma makaranta dai..."

"To shikenan Allah yakaimu,ki gaida su hajiyan, yaya adawo lfy"

Ciki ciki ya amsa sannan yafita bahijja na biye dashi,bai kulataba har saida suka fara tafiya sannan yace,

"Wato ke irin rayuwar da kika zabawa kanki kenan ko? Bahijja wai me kikeso ki zamane? Mai kunnen kashi? To karki fasa ina mai tabbatar miki da nima bazan fasa jibgarki ba tunda jununki taurin kai....yanzu gidan da zakije can dinma idan kinje din karki kama kanki kizama ballagaza kiyi shaye shayen har susan bakida tarbiya"

Har sukaje tarauni bai yi shiruba yanata zuba mata fada saida yagansu akofar gidan sannan yayi shiru bayan yaja mata kunne sosai,

Babban gidane ginin zamani mai dauke da kayan alatu domin mijin hajiyan mai hannu da shunine sosai dan yaransu ma ko karatu basayi akasar nan,

Tare suka shiga yana gaba tana biye dashi har zuwa cikin gidan,a babban falo suka iske samarin gidan guda biyar suna kan dining table sai lokacin suke yin breakfast kusan karfe 12 da wani abu,

Dukkansu zubo musu ido sukayi suna yimusu sannu da zuwa ga kuku yanata sintiri tsakanin kitchen da dining area,

Sosai abun yabata mamaki yanda taji yaya sagir nata ambaton sunan samarin daya bayan daya,haidar,khalifa,mubarak, Faisal sai Annur,haidar ne yatashi da kanshi yahau sama domin kiran hajiya bayan ya kalli bahijja yace,

"Ke yar kauye kin manta mu ko? Gashi ko gaishemu bakiyi ba sai kinyi tsallen kwado..."

Gaba dayansu dariya sukayi harda yaya sagir nan haidar yahaye sama domin kiran hajiya. Kan kujera tasamu ta zauna tana bin tafkeken falon da kallo acikin ranta tana sake jinjina uwar dukiyar da aka narkar wurin kawata falon,duk samarin sun sake da yaya sagir sai hira sukeyi gaskiya duk yadda akayi dama can sun saba da juna sosai amma ta kula wanda yaya sagir yakira da suna Faisal shi kamar bai cika saka baki cikin hirar tasu ba sai jifa jifa,sai cin breakfast dinshi yakeyi cikin nutsuwa yana kurbar ruwan tea,

Tuni haidar ya sauko shi kadai da earpiece a kunnenshi yana dariya da alama waya yakeyi,zama yayi akusa da ita bayan yacire earpiece din guda daya daga cikin kunnensa,

"Ke yar kauye wai wakike jin kunya ne? Ki tashi ki shiga kitchen yau ke zaki dafa mana abincin rana kuku yahuta....."

"Diyar tawa ake yiwa wannan dan bikin daga zuwanta? Aliyu dama nasan sai kai ja'iri....."

Dukkansu dariya sukayi bayan muryar hajiya ta karade falon lokacin da take saukowa daga sama,

"Oyoyo 'yata........barka da zuwa" hajiyan tarauni tafada cikin murna da farin cikin ganinta, korar haidar tayi daga kusa da bahijja ta maye wurin tana jawo bahijja jikinta,cikin girmamawa yaya sagir yataso yazo ya durkusa ya gaisheta ta amsa cikin farin ciki itama bahijja zamewa tayi ta gaisheta ta amsa tana dagota,

"Wato bahijja da bance akawoki ba da shikenan bazaki ce bari inje ingaida uwata ba ko? Kaima sagir harda kaifinka ai yakamata ka rinka nusar da ita zuwa wurin dangi..... Dan Allah karku yar da zumunci"

"Kiyi hakuri hajiya insha Allah zata rinka zuwa...."

"Yakamata gaskiya,yanda kake zuwa itama tarinka zuwa"

"To shikenan hajiya...."

Daga haka yamika da niyyar tafiya dan acewarsa yanada inda zaije bayan yafita daga nan,tare dukkansu suka rankaya suka fita domin yimsa rakiya,hajiya na rike da hannun bahijja duk samarin gidan kowa yafita domin raka yaya sagir banda Faisal wanda ke zaune yana cin abincinshi,yaya sagir yaso su kebe da bahijja dan yakara jamata kunne amma bai samu wannan damarba sai kawai yatafi da niyyar zai kirata daga baya awaya,akan idonsu yatafi yana mai daga musu hannu.........


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/30, 2:08 PM] Nawartye&: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*



20***Ciki suka koma bayan tafiyar Yaya sagir ita dai duk bata wani sake dasu ba duk da irin janta din da suketa faman yi da wasa especially ma haidar wanda shine na biyun auta daga shi sai khalifa shine dan autansu,

Kusa da Bedroom din hajiya takai jakar kayanta dakin na jikin na hajiya nan ta ajiye bisa ga umarnin hajiyan sosai tasake da hajiya suna hira kamar wasu kawaye hajiya sai tambayar ta take yi cikin dabara yanayin irin zaman da take yi agidan Yaya sagir ma'ana zamanta da matarshi idan ko akwai matsala sai kuma sha'anin karatunta har hirar tasu ta gangaro kan samari anan kuma taji kunyar hajiya sosai da ta tambayeta waye yake zuwa wurinta ahalin yanzu nan tace bata dating kowa yanzu,

Saida lokacin salla yayi sannan hajiya ta turata dakin da ta bata tace taje tayi salla itama yi zatayi,

Koda ta idar da sallar ma bata fitoba acikin daki taci gaba da zama tana chaten dasu lady da faruk ahaka har yamma tayi nan kuma tafara jin yunwa na damunta dan lokacin cin abincinta tuni yajima da wucewa,ahaka dai ta daure tayi wanka tayi sallar la'asar tana idarwa taji ana knocking ta mike da niyyar budewa kenan tajiyo muryar hajiya na cewa,

"Bahijja kifito ga abinci muci...."

"To momy...." Tafada kamar yadda taji yaranta na fada mata,dan karamin pink din hijabinta mai santsi tasaka sannan tafita,duk samarin gidan na kan dining table kuku na serving dinsu sai hayaniya sukeyi suna al'adar tasu ta samari wato musun ball,kusa da momy ta zauna sannan tafara gaishesu daya bayan daya suna amsawa haidar kuwa sai tsokanarta yake faman yi,

Duk dai atakure taci abincin saboda rashin sabo shiyasa kowa yagama yabarta saida taga duk sun koma falo sannan ta sake taci takoshi,itama falon ta koma kusa da momy ta zauna wacce ke duba wayarta kafin ta dago ta kalli khalifa tace,

"Kalifa dauko min gilashina ka kawo min adaki....yi sauri"

Tashi yayi sannan ta maida kallonta ga bahijja,

"Bahijja kinata bakunta ko? Ki saki jikinki kinji, wadannan ma yan uwanki ne...."

Murmushi tayi batare da tayi magana ba,gaskiya gidan yayi mata dadi dan saida daddare ma idan samarin gidan suka hadu suna hira sai sukai 11 basu tashi ba kawai dai Faisal ne ta dan lura kamar yanada tsare gida.

Washe gari da safe bayan tayi wanka tafito sai abin yaso bata dariya,ashe samarin gidan suke yiwa momy komai suke shara suyi mopping,sune ke gyara mata daki su wanke toilet suyi wanke wanken dishes da komai shikuma kuku aikinsa kadai yayi musu girki,shima kuma kukun ba wani babba ne dan momy tahaifi yashi,

Afalo tahango momy zaune tana cewa mubarak yaje ya gyara mata bedroom dinta tukunna sai yadawo ya yi mopping din time din Annur yagama sharar falon,

Durkusawa taje tayi ta gaida momy sannan tace mubarak yabarshi zata gyara,saida ta gyara bedroom din momy yayi tas komai neat sannan tafito ta karbi wanke wanken da Annur ke yi lokacin momyn bata falon,tana daf da gamawa momy tashigo ganinta tana aiki yasata fadin,

"Kai kai kai.... bahijja waya saki? Da kin bar musu kayansu sunyi sun saba"

Dariya tayi cikin jin kunya tace,

"Momy maza da aikin mata? Ai suna ma kokari wallahi"

"Wallahi sune ke min komai bahijja tunda banida ya mace,zagadan zagadan dasu sun gama jami'a masu bautar kasa nayi ai gara su rinka kama min duty roster ma da haidar yayi musu,babansu ma yayi yayi insamo mai aiki naki saboda bazai yuyu inkawo mace gidan nan ba duk yarana mazane and they are all matured gara su din suyi....yanzu kinga irin case mai alaka da wannan yayi yawa agari sai adauki yarinya budurwa aiki akaita cikin samari baligai a ajiye sukuma iyaye babu kula.....Allah dai yashirya mana zuri'a"

"Amin momy.... wallahi kuma hakane"

Ganin ita ke aikin yasa momy kama mata saboda kusan duk flate din abace suke dan aka'ida sau daya suke yin wanke wanke a kullum,tana daf da kammalawa kuku yashigo yadora breakfast,

Suna falo azaune samarin gidan suka fara shigowa daya bayan daya, khalifa ne yafara shigowa sai haidar domin sune keyin hidimar kasa a yanzu amma sauran duk aiki sukeyi. Cikin rashin sakin jiki yauma ta zauna tare dasu suna karyawa sai murmushi takeyi kadan kadan sakamakon hirar da su khalifa keyi da hajiya suna hirar Abba wato mahaifin su haidar wanda yau suke saka ran zai dawo daga garin kaduna domin acan daya matarshi take wacce asalinta baturiyace yar kasar Scotland,

Faisal shine last din fitowa sanye yake da bakaken suit kasancewarshi accountant, kowa yabude baki yana hira ban dashi shikam da hajiya kadai yake hirarsa har yagama yatashi yafita aiki suma sauran daya bayan daya suka rinka fita har wurin ya zama saura ita kadai da hajiya sai kuku dake cikin kitchen yana aikinshi,duk gidan kuma sai yayi shiru sakamakon masu rayashi da hayaniya sun fita,tare suka yita hirarsu tare da hajiya har 12 lokacinne hajiyan tafita part din Abba domin gyarawa ita kuma tanufi fridge ta dauki bakin lemo mai sanyi tahau sama wannan shine daya daga cikin illar shan kwaya domin duk ranar da baka shaba sai kajika kamar marar lafiya,da sanyinshi da komai ta kafa kai ta shanye take jikinta yasoma kakkarwa saboda sanyi.

***

Tunda suka hau table din kafinma tafara zuba musu abincin kamshi yaso gigita husnah itafa azamansu na baya bata taba cin abincin bilkisu ba soo shiyasa bata san kalar girkinta ba,

Yawunta ne ya tsinke daidai lokacin da taga bilkisu ta bude chicken salad wanda yasha decoration da kayan lambu,ita ta zubawa kowa cikin flate sannan ta aajiye agaban kowa sai lokacin takoma ta zauna tana kallon fahad wanda ya kafeta da nasa idanuwan,

"Ranka yadade ango Bismillah mana........."

Dan harararta yayi amma dai bai tanka ba shifa ya lurama kamar bilkisu farin ciki take da auren nan nasa to kodai

12 / 14