Chapter 9 Reading Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc Arewa Novels

Kumallon Mata Complete Hausa Novel By Ummi Aisha.doc

Author :  Ummi Aisha Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 14

24K to 27K   out of 40.2K words

son jin abinda zatace amma sai faman shasshekar kuka takeyi taki magana wanda har hakan yasoma fusata wasu daga cikinsu musamman ma mahaifiyarsu,

"Wallahi badiyya idan nataso sai jikinki yagaya miki, wannan ai zancen banzane..... Zakiyi magana ko kuwa?" Baba mahaifiyarsu tafada tana huci dan bakin ciki,

"A'a yimata ahankali mana, badiyya ke muke sauraro ki fada mana waye wanda yayi miki wannan cikin?" Baba yafada yana tattara hankalinsa gaba daya ga badiyya,

Cikin kuka ta daga kai takalli baba,

"Yaya abdurrahman ne mijin anty shamsiyya....."

Kowa dake zaune awurin saida maganar ta girgiza shi mutuka ita kuwa shamsiyya mikewa tsaye tayi zumbur kamar wadda aka tsikara tana kallon badiyya wacce tahade kai da gwiwa tana wani sabon kukan mai ban tausayi........


*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/23, 2:05 PM] Nawartye&: 13***Cikin rawar jiki shamsiyya ke nunata da yatsa jikinta sai karkarwa yake tamkar mazari,

"K'arya kikeyi algunguma munafuka wallahi badai mijina ba..... Kije can kinemi Wanda ya kunsa miki wannan abun kunyar amma badai uban 'yaya na ba......"

Kuka badiyya keyi sosai tana shassheka, cikin rashin kwarin jiki gwaggo amarya takamo shamsiyya ta zaunar da ita tana fadin,

"Ya isa shamsiyya zauna ayi maganar a tsunake mana......"

"Badiyya kikace abdurrahman ne mijin yar uwarki yayi miki wannan cikin?"

"Wallahi baba shine..... Last zuwan da nayi gidanta cikin dare yashigo dakin da nake....."

"Zan fasa miki baki idan baki daina shiryo karyarki ba akan mijina..... Wallahi baba karya takeyi abdurrahman bazai taba aikata wannan mummunan aikin ba.... Tadaije tanemi wanda yayi mata awani wurin amma ba mujina ba...."

"Shamsiyya kiyi mana shiru kibari mugama da ita mana...." Baba yafada cikin fada yana kallonta babu shiri ta nutsu ta shiga taitayinta,maida kallonsa yayi ga badiyya wacce tahade kai da gwiwa tana faman gursheken kuka wanda sautinsa yacika gidan,

"Badiyya....." Baba yakira sunanta babu alamun wasa,

"Ki fada mana gaskiya karki yarda kiyi min karya dan idan kika yi kuskuren fada min karya to wallahi sai ranki yayi mutukar baci..... Kifada min waye yayi miki cikin nan?"

"Wallahi baba shine, abdurrahman ne mijin anty shamsiyya"

"To dama can akwai wani abu atsakaninku ne?"

Girgiza kai tayi har lokacin idanuwanta basu bar zubar da hawayeba,

"To yaushe kuka fara wannan mugunyar rayuwar tare dashi har hakan takasance?"

"Wallahi baba babu ruwana ba laifina bane.... Wannan zuwan da nayine na karshe hakan tafaru shiyasa ma nadawo gida..."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un....." Baba yafada yana dafe kansa bayan yajingina ajikin bango,kowa nagidan jikinsa yayi sanyi kalau da jin wannan mummunan labari wai abdurrahman ne ya aikata haka amma dayawa basu yarda ba musamman ma shamshiyya dan ita anata ganin ma kawai kazafi badiyya tayiwa mijin nata kuma uban yayanta shiyasa takasa yarda azuciyarta cewa dagaske abdurrahman din ne yayiwa badiyya ciki ai kuwa yazama dole ta nemoshi awaya acikin daren nan dan taji gaskiyar lamari duk da tasanma karya ake yimasa,

"Yazama dole gobe naje gidan waliyyin abdurrahman akirashi nasakoshi agaba muzo tare domin kawo karshen wannan maganar.... Ke badiyya idanma karya kike yimasa tun wuri kifada dan gobe zai zo kuma sai kin maimaita abinda kika fada yanzu"

Daga kai tayi alamun tayarda tana faman fitar da hawaye shamsiyya kuwa saboda tsabar tafarfasar da zuciyarta keyi kasa zama tayi nan tamike tawuce daki da sauri tadauki wayarta tafara neman abdurrahman saboda tasan ai yanzu yadawo daga saudiyya tun shekaran jiya ko jiya,

Abin haushi wayar bata shigaba haka tayita gwadawa amma bata shiga ba haushi kamar ya kasheta ga wani irin zafi da ciwo da zuciyarta keyi mata tana jin haushi da tsanar badiyya na ratsa kowacce kafa dake zuciyarta akanme tazabi tayiwa mijinta sharri? Akan me zata dangantashi da wannan mafi munin laifin? Ko kaffara bazata yiba abdurrahman ba mazinaci bane sannan baya harkar mata,

Acan waje kuwa dakyar baba ya iya yunkurawa yatashi yashiga cikin dakinsa sakamakon nauyin da kafafuwansa suka yimasa tun bayan da badiyya tasanar dashi wanda yayi mata wannan aika aikar, nan yabarsu a inda suke babu wanda yasake iya motsawa acikinsu har tsawon wani lokaci kowa akwai abinda yake sakawa acikin ransa bama yakamar mahaifiyarsu wacce bacin ranta yafi na kowa, ita kuwa badiyya har lokacin bata bar kuka ba daga karshe gwaggo amarya ce tazo ta kama hannunta suka tafi dakinta nan taci gaba da kukanta tana mai danasanin rayuwarta, ita meye amfanin rayuwarta ayanzu? Tazama mujiya acikin tsintsaye kowa ya juya mata baya babu wanda ya yarda da ita kowa haushinta yakeji yana ganin laifinta, kwana tayi tana kuka gaba daya muryarta ta disashe kuma idanuwanta ma sun kumbura suntun sunyi jajur saboda tashin hankali ga rashin bacci ga kuka,

Duk gidan su harisu ne kadai suka samu bacci amma kowa haka yakwana idonshi tangararau dan tashin hankali shamsiyya kuwa kwana tayi tana gwada kiran wayar abdurrahman amma bata sameshi ba sai wurin karfe 3 nadare nan wayar tayi tagama har ta tsinke bai daukaba, haka taci gaba da kiransa amma baya dauka daga karshema sai taji yakashe wayar nan damuwarta da tashin hankalinta suka kara nunkuwa.

Wayewar garin tunda sassafe baba batare da yayi ko karin kumallo ba yafita acewarsa zai koma gidan alhaji mai kwano domin yazama dole yakira masa abdurrahman yazo yawarware wannan kullin sannan yafitar dasu daga duhun da suke ciki,

Kamar jiya yauma haka tabi dakin iyayen nasu mata ta gaishesu daya bayan daya, tababa tana zaune kan abin salla cikeda matsananciyar damuwa koda yake ai yazama dole tashiga halin damuwa duba da irin yanayin da take ciki abu goma da ishirin ne yahadu yatarar mata aka, lokacin da tashiga dakin gwaggo amarya suna tare da badiyya gwaggo amarya sai Nasiha take yimata cikin harara shamsiyya ta kalli badiyyan wacce ke durkushe tana hawaye,

"Ai dama kin daina wannan kukan munafurcin kin fadi gaskiyar Wanda yayi miki ciki, sannan wallahi idan kika kuskura kika kara ambaton sunan mijina mai rabani dake sai Allah.... Banza munafukar Allah ta'ala" daga haka tasaka kai tafice hakan yasa badiyya sake fashewa da kuka musamman ma da zuciyarta tayi mata wani bahagon tunani,yanzu idan abdurrahman yazo ya musanta maganarta ya karyatata mecece madogararta? Kuka taci gaba da yi gwaggo amarya na bata hakuri amma ina bata sanma tanayi ba har saida tagaji dan kanta sannan tayi shiru,kowa dake gidan yana daki akunshe wanda sai ka rantse da Allah mutuwace akayi musu, inna sabuwa ce kadai tasamu kuzarin fitowa tazo ta dora karin kumallo tayi duk yan aikace aikacen tsakar gida har zuhuriyya tasamu itama tafito ta tayata sukayi tare. Shiru gidan ya wuni babu wani motsi har yamma lokacin da baba yadawo nan aka shimfida masa tabarma yazauna yana sanar dasu inna sabuwa cewa yanzun nan waliyyin abdurrahman yakirashi wato alhaji mai kwano yasanar dashi cewa gasu nan tafe shida mijin shamsiyya shiyasa yayi azamar baro wurin sana'arsa yataho gida.

Jin abinda baba yafada yasa shamsiyya taji wani irin sanyi cikin ranta yawwa ko babu komai abdurrahman zaizo yayi bikonta sannan ya musanta sharrin da badiyya ta kulla masa, su mardiyya ta kalla,

"Ku fara tattare min kayana dan yau dinnan zan koma gidana inbar muku dakinku yanmata"

Dukansu dariya sukayi ita dai alla alla takeyi su abdurrahman suzo amma basu karaso ba sai bayan sallar la'asar dawowar baba daga masallaci kenan suka ganshi yashigo tare da alhaji mai kwano da kuma abdurrahman wanda yake sanye cikin shadda ruwan toka harda hula, ta window shamsiyya ke lekenshi gaskiya yayi kyau sosai musamman ma da ta kwana biyun nan bata ganshi ba sai taga yasake zama wani handsome fiyeda da,

Mintuna uku baya taga gwaggo amarya ta leko dakinsu takirata hijabi tasaka sannan tafita taje ta zauna kusa da inna sabuwa,

"Abdurrahman rannan saiga shamsiyya tazo tana kuka tace wai ka saketa batare da kuma tayi maka laifin komai ba,muna son kafada mana abinda yafaru"

Sunkuyar da kai yayi kasa sannan cikin ladabi yace,

"Ehh baba abinda tafada gaskiya ne na saketa saki daya kuma bata yimin laifin komai ba"

"To dama ana sakine batare da laifi ba?" Alhaji mai kwano ya bukata yana kallon abdurrahman din,jin yayi shiru yasa yaci gaba,

"Maganar ka saketa babu laifin tsaye ba na zaune bai tasoba ka maida matarka kuje kuci gaba da rike yaranku"

"A'a Abba bazan iya maida itaba, gaskiya bazan iya sake zama da itaba amatsayin matata...."

"Tana yimaka wani abune wanda baka so?" Baba yabukata,yayinda ita kuma shamsiyya jin abinda abdurrahman yafada tuni hankalinta yatashi tashiga damuwa,

"Baba babu abinda take yimin kawai dai bana kaunar sake koda ganinta ne ahalin yanzu...."

Fashewa shamsiyya tayi da kuka mai sauti,

"Wallahi baba dama saida nafada muku tsohuwar budurwarsa ce tayi masa asiri dan ta rabamu....."

Sai lokacin abdurrahman ya kalleta ranshi nayi masa zafi saboda jin abinda tace,

"Ya isa shamsiyya yi shiru, to abdurrahman tsugunne fa bata kareba...... Sabuwa kirawo badiyya"

Har badiyya takaraso cikin sassarfa shamsiyya kuka takeyi ita wanne irin laifi tayiwa abdurrahman da yake ikirarin bazai maida ita dakinta ba?, tsaigata kukan da take yi tayi saboda jin abinda baba ke cewa,

"Ke badiyya yimana bayanin da kikayi abaya da bakinki kowa yaji ga abdurrahman ga waliyyinsa...."

Cikin kuka badiyya tafara rattabo jawabi kamar yadda tayi abaya nan bacin ran shamsiyya yasake nunkuwa jin har yanzu badiyya nakan bakanta tana cewa abdurrahman ne wai yayi mata ciki, cikin masifa da bacin rai tace,

"Kajiko... Kaji sharrin da yarinyar nan keyi maka ko abban musaddiq...."

"Ke shamsiyya kiyiwa mutane shiru kibarshi ya amsa da bakinsa, abdurrahman menene gaskiyar lamari?" Baba yafada yana dubanshi,

"Ehh baba duk abinda badiyya tafada hakane kuma gaskiyane....."

Yafada hankali kwance kuma cikin nutsuwa sam bai nuna alamun tsoro kokuma alama ta rashin gaskiya ba.....



*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*


*_Ummi Shatu_*=?L? [1/24, 9:08 AM] Nawartye&: 14***Kowa dake wurin shiru yayi sakamakon mamaki da tashin hankalin da ya mamaye zuciyarsa saboda jin abinda abdurrahman yafada wato amsa laifinsa da yayi cikin hanzari da kuma sauki batare da ya wahalar da zukatansu ba,

"Abban musaddiq idan rufa mata asiri kake son yi ko taimakonta ai basai ka dauki laifin da ba naka ba....." Shamsiyya tafada cikin tashin hankali dan ita har yanzu zuciyarta takasa gasgata mata cewar shine ya aikata wannan danyen aikin,

"Abdurrahman kace Kaine kayi wannan aika aikar? To shin kamanta ne cewa badiyya kanwar matarka ce uwa daya uba daya?" Baba yafada yana cikeda damuwa,

"Baba ban manta ba,tsautsayine da k'addara da kuma sharrin shaidan...."

"Kaji maganar banza, tsautsayi a ina? Babu wata k'addara da wani shaidan kai ne nan babban shaidanin...gaskiya abdurrahman you highly disappointed me....dama abinda kake aikatawa kenan?" Alhaji mai kwano yafada cikin bacin rai da bakin ciki,

Kasa magana abdurrahman yayi illa sunkuyar da kansa ma kasa da yayi alamun jin nauyi,

"Yanzu malam menene abin yi? Wanne mataki kake ganin yadace mu dauka?" Alhaji mai kwano ya bukata cikin tashin hankali,

"Ai alhaji Ina ganin kawai sai dai mujira zuwa lokacin da zata haihu tunda haka Allah ya kaddaro amma gaskiya ni baza ayi kisan kai agidana ba kaga idan akayi haka kamar andora wani laifinne akan wani.....muyi hakuri mu dauki k'addara mujira lokacin haihuwarta...."

Wani kuka shamsiyya tafashe dashi sannan tamike tashige daki tana gursheken kuka,har lokacin iyayensu mata basuce komai ba sakamakon jin iya mazanne ke tattaunawa ba asako bakinsu ba aciki.

"To maganar mayar da shamsiyya dakinta kuma fa?" Inji alhaji mai kwano,

"Abba gaskiya bazan mayar da itaba kawai idan ta kammala idda tana samun miji tayi aure....."

"Allah yasa haka shine yafi alkhairi..." Inji baba,mikewa alhaji mai kwano yayi Wanda daga gani kasan cikin bacin rai yake nan baba yatashi yabishi yana bashi baki yana cemasa babu komai k'addara ce,shi kam abdurrahman yakasa hada Ido da mutanen gidan akunyace jiki asanyaye yatashi shima yabi bayansu baba yabar su gwaggo amarya wacce ke rarrashin badiyya sakamakon kukan da take ta faman rerawa sannan itama shamsiyya daga dakin da take ana dan iya jiyo nata kukan, mahaifiyarsu kam takasa cewa komai bama ita kadai ba kowa dake zaune wurin duk jikinsa yayi la'asar.

Sumi sumi yake biye dasu abaya har zuwa gaban motar da suka zo da ita cikin bacin rai wanda ya bayyana karara saman fuskarsa alhaji mai kwano yabude kofar motar yashiga yana sake baiwa baba hannu domin yin musabaha shikam abdurrahman jiki asanyaye zuciya abace shima yashiga gaban motar yaja suka tafi wanda har sukayi nisa alhaji baice dashi ko ci kanka ba yasan hakan bai rasa nasaba da fushin da yakeyi dashi.

Dakyar gwaggo amarya ta daga badiyya zuwa cikin dakinta bayan fitarsu abdurrahman inbanda gunjin kuka babu abinda takeyi sannan itama shamsiyya tana daki tanata rusar nata kukan shiyasa hankalin mutanen gidan gaba daya atashe yake nan suka taru sunata bawa shamsiyya baki,tabbas yau tana cikin kaduwa tareda tashin hankali marar misaltuwa cikin kukan da taketa faman rusa tamika hannu tajanyo wayarta tana rage sautin kukanta sakamakon hakurin dasu zuhuriyya ke bata suna zaune zagaye da ita,

Number abdurrahman taketa faman kira amma yaki ya dauka domin Shi lokacin ma yana zaune kasa afalon alhaji mai kwano shida matarsa hajiya lubna sun sakashi agaba sai fada suke zuba masa kamar zasu koneshi saboda abinda ya aikata sai bayan da suka gama yabasu hakuri yataso yafito lokacin yasamu zarafin daga kiran da shamsiyya keta faman yimasa,cikin bakin ciki yace,

"Wai malama menene kika wani tisani agaba da kira kamar naci miki bashi?"

Cikin shasshekar ku??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ka tace,

"Yanzu abdurrahman abinda ka aikata kayi daidai kenan? Kanwata uwa daya uba daya ka iya rab'a?"

"Laifin waye? Duk bakece kika janyo min wannan masifar ba? Kece ummul aba'isin din shigarmu wannan bala'in,kuma wallahi Allah ya isa tsakanina dake....ban taba aikata zinaba amma saboda masifar kazamin zafin kishi irin naki kika shiga kika fita kika hanani kara aure daga karshe shaidan da sharrin zuciya suka kaini har na sabawa mahaliccina na aikata babban laifin da yayi hani dashi....kisani ayanzu banda makiyiyar data fiki kuma sai kinyi nadamar abinda kika aikata domin Dr Bala ya fayyace min komai...nayi nadamar kasancewarki uwar yayana nayi nadamar kasancewarki matata Ada...kash.... how i wish zan iya mayar da hannun agogo baya da wallahi nagogeki acikin tarihin rayuwata...azzaluma wacce bata san komai ba sai son kanta..." Daga haka bai jira amsar da zata bashiba yakatse wayar yana jiyo shasshekar kukanta gudun kada ta sake kiranshi ma gaba daya kashe wayar yayi ya cilla kujerar dake makotaka da ta driver yafigi matarsa aguje yabar gidan,gaba daya yanzu ji yake yatsani mata zaiyi wahala idan zai kara auren wata asauran lokutan da yarage masa acikin rayuwarsa.
***
Sai da taji fitarshi kuma ta tabbatar cewa fitar yayi sannan tafito daga cikin toilet din tana goge fuskarta da dan karamin towel,agefen gado ta zauna tana kallon yaransu dake kwance suna ta shakar baccinsu cikin nutsuwa jitake kamar zata fashe da kuka dan radadin da zuciyarta keyi mata kishi ne kawai ke dawainiya da ita shiyasa jinta take kamar daren yau shine mafi munin dare acikin rayuwarta jin kunci na neman lullubeta har shaidan yaci galaba akanta yasata soma ambaton Allah jin nutsuwa tasoma saukar mata yasata shiga tsakiyar su hanfa ta kwanta tare da kunna karatun alqur'ani awayarta kira'ar shaikh Ahmad sulaiman kano cikin suratul Ahqaf tun daga farkon surar har zuwa suratul juma'ah lokacin kam nutsuwarta tajima da dawowa gareta dan harma bacci yaci karfinta dakyar ta iya kashe karatun ta kashe wayar ta gyara kwanciyarta nan bacci yayi gaba da ita wanda ba ita ta farka ba sai karfe 7 nasafe wannan dinma Muhammad ne yatasheta kasancewar sun horar da yaransu yin salla akan lokaci ganin irin makarar da suka sheka abin yabata mamaki mutuka da azamarta tashiga toilet tayi alwala tafito tazo tayi salla lokacin suma yaran duka sun tashi amma banda Mimi ita kam har lokacin baccinta take ta sha.

Bata tsaya komai ba bayan ta idar da salla ta fada kitchen domin shirya musu breakfast da wayarta tatafi ta kunna karatun alqur'ani tana aikinta tana saurara sannan tana bi cikin lokaci kankani ta shirya egg rolls, chips sai kuma kidney vegetables sos da kunun alkama saboda yaranta shi suke sha safe da yamma wani sa'ilin ma har dare,

Sai da ta kammala komai tsaf sannan takoma daki lokacin karfe 9 saura wasu mintuna wadanda bazasu gaza biyu zuwa uku ba wanka tashiga saboda duk yaran bacci ta tarar dasu sun sake komawa har tafito basu tashi ba murmushi tayi tana tuno rashin jinsu da kiriniya shiyasa idan suka kwanta bacci kamar bazasu tashi ba saboda kowa kwallon kansane cikinsu.

Zama tayi ta tsara kwalliya sosai tasha riga da skirt na atamfa Holland dark purple mai zanen buta ajiki, Dubai gold dinta tasaka sannan tasha turaren oud kala kala,yaran ta rinka bi daya bayan daya tana tashinsu tana yimusu wanka bayan tagama duk ta shiryasu cikin kananan kaya yan kanti daga nan ta kwashesu zuwa falo domin dukansu sai karar yunwa suke yimata,bata jira ango da amarya ba tashiga tsakiyar yaranta suka karya tare bayan sun gama ta kunna musu cartoon na larabci suna gani lokacin karfe 11 nasafe harda wasu mintuna,

Abangaren ango kuwa yana can yana ta kwasar bacci domin jiya ya more amarcinsa hankali kwance har 10:30 yakai yanata bacci shida amaryarsa wadda saida yunwa ta tasheta sannan ta tada shi,agurguje sukayi wanka suka shirya bayan ta rakashi dakinshi domin duk kayanshi na can,sabuwar shadda kalar ruwan toka yasaka yasha turare sannan suka fito tana sake nanata masa maganar abincin karyawa amma sai taji yace suje ciki wurin bilkisu dan yasan ta hada musu,zumburo baki tayi saboda ita aganinta gara yaje waje yasamo musu amma sai wata zuciyar tace mata ai hakanma wani cigabanne ita da kwana tare da miji bilkisu kuma da dafa mata abinci,

Yana gaba tana biye dashi abaya lokacin da sukaje dab da babban falo sabanin da dayake rike da waist dinta,shine yafara shiga jin sallamarsa yasa yaranshi gaba daya tasowa da gudu suna kokarin rungumeshi itama bilkisu ba abarta abayaba tare da yaran suka hadu suka rukunkumeshi suna yimasa oyoyo.

9 / 14