Author : Ummu Afan Category : Arewa Hausa Novels
kubra umma kuma tanacan bangaren dattijai mata
Ahmad yace kaga ikon Allah malam shamsu kai ne anan kokuma wa
Ya shamsu yajuyo jin ankira sunanshi
aikuwa yaga su Ahmad da Hakeem
Hakeem ma jin an ambaci sunan malam shamsu
Yasa yadago mai suka yi murmushi gadayansu
Nan ya shamsu yabasu hanu suka gaisa
Yace wasuka zowa Ahmad yace daughter dinmu ai nan take karatu
Kaifa yace nikuma kanwata ce anan
Kubra tace ina wuninku Hakeem da Ahmad suka amsa
Ahmad yakalli inda madam dinshi Aisha take yatashi yaje yarada mata magana akunne aikuwa
Aisha ta task da sauri
Tana zuwa ta kama hanun kubra tace alhamdullilahi yau dai nima na hadu da kawata
Kubra ma dayame wayayyiyace tace nima naji dadin haduwata dake
Nan Aisha taja hanun kubra suka koma gurin su daban
Nan kuma ya shamsu da Hakeem da Ahmad suka can gaba wajen special guest
Nan akafara taron da addua
Can principal tafara jawabinta kamaryadda aka saba
Daga can kuma ta ce itada kanta zatakira best student of the year
Wanda duk shekara akeba principal dama tazaba da kanta ta kuma bata kyauta duk karshen
shekara haka akeyi
Wani daga cikin teachers dinsu ya tashi yakarbi Mike din hanun principal da list din hanunta
Yafara kiran suna kaman haka
Best student of the year
Kowa ya kasa kunne
ASMAU SULEIMAN SHAMSU
aikuwa duk student aka dauki tafi raf raf raf
Dan daga malamai har student sunsan Husnah ta cancanta sosai
Cikin nutsuwa Husnah ta tashi ta isa gurin principal
Nan principal tace wazata kira ya tayata karba
Husnah tace wa principal ya shamsu za akiramin
ya shamsu suna zaune duk hankalinsu yakoma kan head girl
Shi ya shamsu baifada musu wacece kanwar tashiba
Sai jisukayi ankira ya shamsu yatashi cike da alfahari da 'yar kanwarshi bata bashi kunya
kokadan
Ahmad da Hakeem suka hada ido
Ahmad kaddai itace kanwar tashi
Hakeem yayi murmushi yace ga zahiri amma fa yarinyar taburgeni matuka
Yayi maganar yana kallonsu Husnah
Cike da mamaki Ahmad yakalli abokin nashi
am I dreaming ?
Man what are you saying
Hakeem bai kalleshiba murmushi kawai yayi ya dauke idonshi daga gurin su Husnah ya mayar
da kanshi kan wayarshi
Murmushi Ahmad yayi dai dai lokacin ya shamsu yadawo yazauna
Ahmad yace kanwarkace ya shamsu yayi murmushi yace yar karamar kanwata kenan
Yace masha Allah
Allah ya albarkaci rayuwarta
Ya shamsu da Hakeem suka ce ameen
Daga nan kuma sai akafara ba wa prefect satificate dinsu ya rage sauran na social prefect da
Head girl
Aka kira social prefect AMINA HAKEEM ABUBAKAR
Nan akabata sertificate dinta da kuma gift dinta maman Laila ita tayata karba
Hakeem kallo daya yamusu yacigaba da abinda yakeyi
Can akakira me gayya mai aiki wato head girl
Husnah taje ta karba itada yaya shamsu principal Tamika kyautar aka musu hoto
Duk wani kyauta da akerabawa Husnah ita takarbi na farko abin yaburge kowa ana karshen
Husna ta tashi zata karba sai kawai tafashe da kuka Dan tasan koba komai yayanta zaiyi
alfahari da ita
Principal ta rungumeta tana share mata hawayen
Tace asmau Allah ya albarkaci rayuwarki
Ya shamsu yaji dadin adduar principal
Yace Ameen hajiya mungode Allah yabar zumunci
Nan fa students sukayi tazuwa suna daukar hoto da Husnah suna mata fatan alkairi
Masu bata gift nabata kai gaskiya Husnah tayi farin jini sosai har malamai suna tururruwar hoto
da ita
Meenat zaune abin duniya yadameta tana matukar jin bakin ciki abin da kefaruwa da Husnah
Laila tace wai ita wannan yarinyar fa saikace aljana komai ta handame ita kadai
Meenat tace kyaleta dama yunwa ne yakawota school din Dan dama 'yar matsiyata ce
Scholarship taci tashigo
Hajiya rukayya dole ai yanzu naji batu
Motar school ce ta kaiwa Husnah gift dinta har gidan
****
PROFESSOR HAKEEM yana zaune cikin falonshi kusan sati kenan da graduation dinsu
Husnah amma kullum da ita yake kwana da itayake tashi aranshi
Kuma tunda yake a rayuwarshi bai taba saka 'ya mace a rayuwarahi ba
Kuma a yadda ya fuskanci zuciyarshi takamau son 'yar baby nan
Shida kanshi yake wa kanshi dariya
Ya duba agogo yaga sai yanzu 8:30 nadare tayi
Yaje ya hada Kofi
Yanasha kadan yana tunanin Husnah
Abinda baisaniba shine Ahmad yadade a bakin kofa yana kallon abokin nashi daya fada shauki
Ahmad yayi gyaran murya hade da sallama
Hakeem yajiyo suka hada ido da Ahmad
Ahmad yace abokina wai meyake faruwa ne
Kwana biyu naganka kaman akwai wani Abu
Hakeem yayi murmushi tareda kurbar copee yace shine kabar matarka kazo gulma ko
Ahmad shima dariyar tare da dauko lemu maisanyi a fridge
Yadawo yazauna
Ahmad yace inkarashida gulma kaikaso
amma dai ni bazan bar nan ba sai kafada min
Hakeem yatashi yakoma bayan kujera yace
Ahmad am in love
Ahmad yayi dariya yace daman nasani
Duk wannan boye boyen naka duk kallonka nakeyi
amma gaskiya idan har kasamu yarinyar nan kayi sa a wallahi
Hakeem yace wace yarinya kenan tunda nidai ban fada wacce nakeso da bakinaba
Ahmad yayi dariya yace karka rainawa wa kanka hankali mana
Kawanwar shamsu koba hakabane
Hakeem yayi murmushi yace amma ya akayi kagane hakan dawuri
Ahmad yace shekaru talatin muna tare fa dan uwa taya za ayi barangane matsalarka ba
Hakeem yayi murmushi yace hakane amma bazan fada ba sai na musu
Jarabawa daya kaga daga tabbatar gidan danaje Neman iri
Next page
Your comments is needed fans❤❤❤❤❤
Anfara wasa fa fans❤❤❤❤
Sainaji ku
[05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN :
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN
FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION
F.C.T.W.A
HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION
DEDICATE THIS PAGE TO sis JIDDER (BAEWAR ALLAH)
WANNAN PAGE IN NAKI
SABODA KAUNA DA KIKE NUNA WA WANNAN
NOVEL NAWA NA
AKWAI LOKACI
Allah yabar zumunci keep it up ❤❤
Masu comment ina sane da Ku kafin na kamla littafin nan duk sai kunji sunanku daya bayan
daya so kucigaba da bin ummu afan takuce ❤
AKWAI LOKACI
PAGE 66 to 70
PROF HAKEEM zaune kan resting chair dinsa a bakin sweeming fool yana shan iska dan
yanzu yafito daga cikin ruwan
Wayarshi ta daukara yana dubawa yaga dalibata wato mummynshi kenan dan sunan dayasa
mata kenan
Bayan sungaisa Hakeem yace mummyna albishirinki mummy hafsat tace goro
Yace naga matar aure a kano fa
Cikin tsananin farin ciki mummy hafsat tace alhamdulilla naji dadin wannan albishir
Yaushe zakazo katura mahaifinka gidansu yarinyar
Hakeem yayi murmushi yace daliba kenan ai ban ma taba fada wa yarinyar ba nikadai nake
kida kuma nake rawa na
Mummy tace shirme ni harkasani ina murna to idan bazaka iya fada mata nika nuna min
gidansu yarin sai naje
Ayau saina zo kano wallahi akanka my son
Hakeem yayi murmushi yace nasani mummy na
Nasan zakifi kowa farinciki shiyasa nafada miki tunkafin na fada wa yarinyar
Sai mummy Kinsan masu soyayyar Allah kadan suke aduniyar nan
Kuma dadin da dawa ma yarinyar danagani din ba masu karfi bane
Kinga idan naje kaitsaye Kuma akayi rashin sa a saikiga sun soni don kudina badan Allah
Mummy taja numfashi tace hakane son sai dai zuciyata tana bani bazataba son abinda baidace
dakaiba
Hakeem yayi murmushi yace Kinsan menakesonyi mummy tace a a son sai kafada
Yace zan jarabasu nagani zanje amatsayin talaka banida komai
Ingani zasu karbeni kokuwa
Mummy tace hakan ma tayi son dina
Kuma ina maka fatan alkairi
Insha Allah zasuci duk wani jarabawar da zakayi musu
Wasunan surukartawa Hakeem yayi murmushi mummy ta sosa mishi inda yake mai kaikayi
Yace ai harma tazama surukarki
Mummy tace aiba surukaba ma 'yata zama son
Hakeem yayi murmushi yace asmau amma anakiranta da HUSNA
kai masha Allah ashema babban suna ne da ita
Insha Allah asmau zata Mata agareka tun kafin naganta naji inasonta
Hakeem yace shiyasa nakeson Ku iyayena kuna matukar daraja abinda nakeso
Allah yabani matar da zata bauta muku da zuciya daya badan kudinku ba ko kudin danku
Mummy hafsat tace aikasamu son zantayaka da addua
****
Washagari Hakeem Bayan sungama komai ya shamsu yazo musu sallama zai wuce gida dan
karfe hudu yake tashi a lectures
Ahmad yace wa ya shamsu yaufa kafanmu kafarka zamuje mugaida Abba da umma
Dan idan muka biye maka bazaka gayyace zuwa samun ladan nan ba
Ya shamsu yayi dariya yace shikenan idan kun shirya muna iya tafiya
Hakeem yace na dauka zaka kawo wani excuse ne ince ai ba umma kai kadaibane muma
namune
Ahmad da ya shamsu sukayi dariya
a motar Hakeem akatafi ya shamsu agaba Ahmad yabaya
Ya shamsu yana nuna wa PROF HAKEEM hanya
******
HUSNAH ce zaune tsakar gida tagama aikin gidan kenan tas ko ina yadau kamshi
Ita kuma anty kubra tana kitchen tana hada abincin dare Wanda sudama kafin biyar sungama
komai sun zuba a kula
Kuma aikin sukayi Husnah da kubra yau idan kece da aikin gida to dayar kuma saitayi abinci
Yau Husnah ce da aikin gida
Tagama komai da wuri tana wa anty kubra dariya tana kitchen dan yau ya shamsu yace ayi
tuwon semovita miyar kubewa danya
Har kudin danyar kifi yabayar
Anty kubra tace zanrama ai Allah yasa ran girkinki Abba yace sakwara yakeso
Husnah tayi murmushi tace kai ai danagane kuskurena kuwa
Umma datake jinsu tace tun tuni kinjuye ruwa Yakama kishiga kiyi kisamu kifito kije min aika ko
Husnah tace to umma
Umma ta kalli kubra tace sannu kinji kubra Allah dai yamaku albarka yabaku masu yimuku
kuma
Kubra acikin zuciyarta ta amsa da amin dan tana jin kunyar umma idan tace Allah yabasu
masuyi musu
Husnah tafito daga wanka tayi dakinsu tashafa mai tadauko powder tashafa sai kwalli sai tasa
lips glow alebenta
Tabude akwatin kayan ta tafara zaban wadda zata saka
aikuwa idon ta yakai kan wani material pink da kuma ratsin baki ajiki Wanda ya shamsu yamata
a bikin shi
Tunda tasa a biki batasake sawaba
Sai tadauko shi tasaka dinki duguwa Riga ce
Daga sama ya dameta sosai dan Husnah fa akwai kayan aiki
Shiyasa umma bata cika barinta fita da gyaleba saidai hijabi dan Allah yamata kira
Husnah takalli kanta a madubi itakanta tasan tayi kyau sosai
Sai kuma tasan dakyar umma zata bari tasaka gyalen material din
Itakuma yau mayafi takeson yafawa
tace barin gwada dai tagyara gashinta tadaure da ribbon fari
Kafin tayafa gyalenta dan bata saka dankwaliba
Kota saka dankwalima abanza
Dan bayazama akanta sabonda tsantsin gashinta
Tadauko turarenta tafesa kafin tadauki Jakarta na suwaga pink da takalminshi duk pink tasaka
Kai masha Allah da wannan kyakkyawar hallita
Tafito tace umma nafito
Umma ta kalli 'yartata tace au da wannan gyalen zakifita
Husnah tace Allah sarki umma na gyalen kayan nefa
Kuma kinga kayan ai yana da fadi sosai
Kafin umma tayi magana anty kubra taleko tace umma dan Allah kibarta wallahi tayi kyau kuma
kinga ai kayan yana da fadi
Umma ta ce wato bakinku daya ko to shikenan kije Allah yakiyaye hanya
Husnah tace to umma baki min bayaninba umma tace kinci gidanku yau kika saba karbomin
zuman ne
Husnah tayi murmushi dimple dinta tsuka lotsa sosai
Tace to ummana afuwan nadauka bakaman na kullum bane
Tayi waje sukace mata adawo Lafiya
adai dai kofar gidansu ya shamsu yanuna wa Hakeem yayi parking
Suka fito atare Ahmad yace kashiga saikamana iso
Ya shamsu yace to shikenan yaya cikin gidan alokacin umma ce kadai a tsakar gida kubra ta
fito mata da taburma
Dan anna suke hirar Daren su gadaya
Ya shamsu yayi sallama umma tace a a ubana har andawo yace a umma yagidan nan dai
yagaida umma kafin yace umma daman su ogana na office ne sukazo gaisheku
Umma ta ce shine kabarsu a waje kuma sushigo ciki dan Allah haba waje
Ya shamsu yaje ya musu iso zuwa cikin gidan
Umma ta ce kashiga dasu daki Ahmad yace a umma mu kusa da ummanmu zamu zauna basai
munshiga dakiba
Umma taji dadin har ranta tace to shikenan 'ya'yan ummu kuzauna nan suka kwashi gaisuwa
agurin umma ta amsa cike da farin ciki
Nan kuma ta musu godiyar hidimar dasukeyi da su
Hakeem yace haba umma ai mu da shamsu Yanzu munzama 'yankuma bagodiya tsakaninmu
ai yiwa Kaine
Umma ta ce hakane kam Allah yake mutum da mutum
Kodai Allah yasaka muku da aljanna
Umma ta ce wa shamsu ubana aisai kayi maza kaje nan shagon mati ka karbo musu lemu mai
sanyi da ruwa
Hakeem yace haba dai umma mufa ba bakibane
Komai ummanmu tabamu cizamuyi
Ba umma ba harta ya shamsu yaji dadin wannan kara da Hakeem da Ahmed suke musu
Sallmar HUSNAH ce yasa Hakeem daga ido yakalli hanyar waje aikuwa suka hada ido cikin ido
Husnah tayi saurin dauke idonta dan dama akasi aka samu ta kalleshi
HAKEEM yasamu Kansa cikin wani yanayi Wanda yakasa fassarashi ba Ashe ganin da yayi
mata a school ma tafi haka
Husnah ta durkusa har kasa tagaishe da su Hakeem Ahmad ne karfin amsawa shikam ogan ba
baki
Yakasa komai ne
Ba Wanda ya kula da canzawarshi sai Ahmad
Ahmad murmushi yayi shikadai
Kubra tafito tagaishesu
Ahmad yace ai kawarki basan zamuzo ba dakinganta
Kubra tace dan allah yakawo mata Aisha Dan zaman da sukayi a gurin graduate dinsu Husnah
sun saba sosai
Ahmad yace ya mata alkawari ran sabar zai kawo Aisha tamata wuni daga nan tagaida umma
Umma ta ce Allah yakawo ta Lafiya umma na maraba da ita
Husnah da kubra suka kawo musu abinci a kula da biyu suka ajiye
Husnah tadauko plate guda biyu da serving spoon duk ta ajiye musu
Sai ta dauki jug ta kawo musu ruwa maisanyi na randar umma ta kawo musu da cups biyu
Umma ta ce maza hada musu zobo Husnah
Husnah tace to umma ai na dafa tunda dazu hadawa kawai zanyi saidai ba kankara
Ya shamsu yace hada barin karbo kankara
Ya shamsu yafita jimawa kadan sai ga shida kankara yakawo yaba wa husnah
Hadaddan zobo ta hada Wanda yasha kayam kamshi da cocumba
Tasa musu a jug shima takai musu kafin ta wuce dakin anty kubra umma tace bara nashiga kuci
abincin Ku
Ya shamsu yace bissimillarku kuci abinci
Hakeem yayi murmushi yace aiko baka fada ba
Ahmad yayi murmushi dan yasan dalilinsa na fadar hakan
Hakeem yayi serving kanshi
Tuwo daya yasaka sai sai yasa miyar baiga ruwan wanke hanuba sai
Yace yaya shamsu ruwan wanke hanu dan bana cin tuwo da cokali
Ya shamsu yayi dariya yace amma yallabai kaso barkwanci ninekuma yayan
Hakeem yayi murmushi baice komai ba
Ya shamsu yakira Husnah takawo ruwan wanke hanun
Takawo ta ajiye gaban ya shamsu shikuma ya mikawa Hakeem gabansa
Hakeem sosai yaci tuwon dai Bayan ya cinye Leda daya sai ya kara Ahmad nema yarage
kadan
Ya shamsu yace haba yallabai dan Allah kacinye wallahi umma zataji dadi
Hakeem yace rabudashi ya shamsu tsoron madam Aisha yakeyi kartatsareshi sai ya cinye
abinta yakasa Bayan yacinye na gidan umma
Duk suka kwashe da dariya
Hakeem yatsiyayi zobon da Husnah ta hada