Author : Ummu Afan Category : Arewa Hausa Novels
musu yasha
Aikuwa yaji kunnenshi kaman zai yanke dan dadi
Kodan ya hadu da soyayyane oho
Kafin yayi magana Abba yashigo dattijon arziki
Duk suka mike tsaye sai da Abba yazauna suka zauna suka kwashi gaisuwa
Ya shamsu yagabatar dasu
Abba yace a manya baki ne damu agidan Ashe
Nan shima yashiga musu godiyar hidimansu akansu
Sun dan taba hira kafin Abba yashiga daki yabarsu nan da ya shamsu
Hakeem yace Gaskiya ya shamsu wannan zobon asamin awani Abu natafi dashi zansha zuwa
dare
Ahmad yace narigaka azuci karigani a baki dan kasan duk inda nasha abinda yamin dadi sai
narage wa madam
Hakeem yayi murmushi yace kai man kafadi gaskiya
Ya shamsu dai dariya yakira Husnah yace tasamo jugs guda biyu ta zubo zobo tace to
Hakeem tabita da kallo komai na yarinyar yamishi Dari bisa Dari
Tana da duk wasu qualities din dayake bukata ga mace
Husnah ta zuba takawo ta ajiye
Ta yigaba abinta
Sai da akakira magrib suka yi sallama da su umma da Abba da anty kubra
Husnah tana kan sallaya idan tayi magrib bata ta shi sai tayi isha
Hakeem yaso yasake ganin Husnah
Amma taki fitowa
Ahmad ya ajiye bandir din kudi 'yan dubu dubu yace a ba wa kanwarsu tasai kayan kwalliya
Ya shamsu yace dan Allah karmuyi haka kudauki kudinku
Ahmad yace ai nariga na ajiye kuma ma aibakai muka ba ba kanwarmu muka ma kyauta
Da kyar ya shamsu yabar kudin nan
Suna cikin mota Hakeem ya karya kwana zuwa baibi hanyar gida ba
Ahmad yace man yana zaka kaimu kuma Hakeem yayi murmushi yace sa ido kawai kayi kallo
man
Ahmad yace OK baringa ikon Allah to
Hakeem yayi parking adai dai gurin wani malamin almajirai suka sauka
Malam na ganin HAKEEM yataso yazo sannu da Zuwa professor Hakeem yayi murmushi suka
gaisa da malam Garba
Malam Garba yace mukarasa daga taburma nan suka karasa
Hakeem yace malam bawani Abu yakawoni ba illa Neman wata alfarma
Malam Garba yace alfarma kuma alhaji da kanka
Hakeem yace a malam
Aure nake nema malam
Amma kasan rayuwa ta baci yanzu sai aureka badan anasonkaba sai dai don abinda kakedashi
Malam yace hakane
Hakeem yaja dogon numfashi
Ya kalli Ahmed da ya kagu yaji dalilin abokin nashi nazuwa nan
Hakeem yace malam zanje Neman aure da sunan talaka talakan ma futuk Mara iyaye
Koda anzo Neman tarihina guringa za azo dan
Kai zanfada a matsayin malamin danayi karatu agurin shi
Kai kuma inason kanuna tun ina karami aka kawo maka ni
Wannan kadai nakeson kamin malam
Malam Garba yayi murmushi yace gaskiya alhaji kana da tunani mai kyau Allah ya tabbatar da
alkairi
Hakeem da Ahmad suka ce amin malam
Nan suka wa malam sallama Hakeem yadauko bandir din kudi yaba malam yace gashi a
rabawa yara sadaka
Ya ba malam wani kuma yace Gashi wannan nashine
Malam Garba yayi ta musu addua
Acikin mota Ahmad yace amma meyasa makayi wannan tunanin haka Hakeem
Ahmad yace kana nufin bazasu ganeka ba wai kome
Hakeem yayi murmushi yace duk zan shirya wa hakan
Ahmad yace Allah yasa amma dai yakamata duk wani abinda zakayi wallahi kayi sauri kafin
wani yariga ka
Hakeem yayi murmushi yace inaji ajikina wannan yarinyar rabonace
Ahmad yace to tunda kana da tabbacin haka
Meye na gwada ta kuma
Hakeem yace inason nasan mena aura ne kuma rayuwata zanbata kaga kuwa ina bukatar
bincike sosai
Ahmad yace sai prof komai naka daban ne wallahi gaskiya bazan boye maka ba I like your life
style Bros
Keep it up
Hakeem yayi dariya yace baka jiya abokina
Ahmad yace ai bazangaji
Komai naka is so special
****
Bayan sati uku Hakeem yayi order na fuska daga India
Yau yakesaran za akawo mishi
Hakeem ya zaune wani abokin
Wayar shi tadau kara yana sai yaga number din Wanda yaba sautun siyo mishi fuska
Yadaga wayar yace badai har kun isoba
Doctor isah yace gani ma acikin school dinku
Hakeem yace what's a surprise
Ganin zuwa
Hakeem yafita yaje yashigo da doctor isah
Nan Bayan sungaisa doctor isah
Yafito mishi da sakonsa
Hakeem yakarba yace masha Allah kuma gaskiya kayi yadda nace
Doctor isha yace to ai kasan aikan manya irinku ba kasafai akacika muku shirme ba
Hakeem yace zakafara kaima ko
Doctor isha yayi murmushi yace ansamu ragi sosai yallbai dan Rabin yakai dubu Dari da
hamsin
Hakeem yace OK zaka iya barinshi a wajenka yazama naka doctor
Doctor yace a yi haka yallabai
Hakeem yace karka damu ai kamin komai
***
Da daddare Hakeem ya fesa wanka yadauki jallabiyya yasaka yadauko fuskarsa yasaka kafin
yadauki carbi yarike a hanu
Yadauko wayar Nokia da yasa akasayo mishi second hand wacce duk tasha dauri da roba
Ya kalli kanshi a madubi shida kanshi yaba kanshi dariya
Yadauki kudi yan hamsin da kuma 'yan goma yasaka a aljihunshi
Ya kulle gidanshi yafita zuwa gidan Ahmad yayi sallama
Maigadin yace sannu malam daga ina haka kuma gurin wakazo
Yace inason kamin sallama da maigidan ne
Bayan Ahmad yafito ne yaga mutum ustaz har da gemunshi
Yace assalmu alaikum
Hakeem ya amsa mishi cikin canjawar murya
Hakeem dai yakasa danne dariyar shi yacire fuskan
Ahmad wazaigani Hakeem ne
Cike da mamaki Ahmad yace amma ka shammaceni
A ina kasamu masks nasan dakyar akesamu a Nigeria
Hakeem yace daga India aka kawo min
Kaga kai ma danake tunanin zaka ganeni baka ganeniba
Bana tunanin shamsu da mutan gidansu zasu ganeni
Dan haka ni wuce daga yau zafara basu exam's din su
Hakeem ya mayar da fuskarshi yagyara da kyau yadda baza a ganeba
Yayi bakin titi yatari kekenapep zuwa anguwar su Husnah
Next page
Tofa fans za afara wasa fa
Your comments is needed
Ina alfahari da masoya novel na潤 AKWAI LOKACI潤
踫踫踫踫踫
[05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN 潤撕: 潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤
潤潤潤潤
潤潤潤
潤潤
潤
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
踫踫踫踫踫踫踫
潤撕FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION潤撕
潤撕潤撕 (F.C.T.W.A)潤撕潤撕
潤撕HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION潤撕
潤I DEDICATE THIS PAGE TO YOU sister surayya auwal ina matukar jin dadin comments din
ki amma Dan Allah sister kikara yawan comments din ki ina alfahari da Ku da da comments din
ku潤手手手手
潤AKWAI LOKACI 潤
潤PAGE 86 to 90潤
HUSNAH zaune tana gyaran farcenta Umma tace auta nikam ya kukayi da Alhaji ne naga jiya
yazo
Husnah ta bata fuska tace wallahi Umma guduwa nayi dakin anty kubra na buya Dan wallahi
Umma nibana sonshi
Umma tayi salati tasanar da ubangiji
Tace aidaman zaran hijabin dakikayi kaman kinje
Bazuwa kikayi ba
To ma wai meyasa bakya sonshi meyamiki husnah karki zamo me saka alkairi da sharri mana
Tunda Allah baiyi aurenki da shi abdullahinba sai ki ba
Wannan dama kodan halinsa na kirki badan abin hanun shiba
Anty kubra tace wallahi Umma kullum sai namata wannan nasihar amma kamar anshuka dusa
Husnah tace wallahi ni kwatata bana jin zan iya son wani bayan ustaz ne
Kuma bana son na aureshi nakasa yimashi biyayya Umma na Dan Allah kufahimceni
Umma tace ai shi so ahankali yake shiga
Kyawawan halaiyar wannan yaro kadai zaisa kifara sonshi azuciyarki
Dan yana da duk wani nagarta atare dashi
Kafin Husnah ta yi magana ya shamsu yayi sallama yashigo yazauna
Yana gaida umma kubra ta tashi tace sannu dazuwa tayi hanyar fridge tadauko mishi ruwa
maisanyi
Takawo mishi
Ya dauka yasha kafin yakalli umma yace mekuke ta tattaunawa ne ummana
Umma tayi murmushi tace wallahi wannan shasharce muke taba baki saikace wata uwarmu
Sai waina mu takeyi
Ya shamsu ya kalli Husnah yace wai meyake damun kine husnah
Ustaz yariga yatafi bazai dawoba
Wallahi husnah da ace zaidawo lokacin da akeshirin daurin auranki da Abdul Hakeem za afasa
a daura dashi
Sai dai kash ba a mutuwa adawo
Sai dai ina miki albishir dacewan Allah yamiki sakayya da mafificin alkairi
Mun dade muna Neman hanyar da zamu sakawa wadan nan mutane
Sai gashi Allah yakawo tunda yasawa yallbai kaunar ki aransa
Maizai hana kitayamu maida alkairi da alkairi husnah
Abdul Hakeem yamana komai a rayuwa kuma duk abubawan da yayi mana na tabbatar Dan
Allah yayisu
Kaman yadda kema zamu bashi dan Allah badan abin hanun shiba
Husnah tace shikenan yayana
Namaka alkwarin bazan baka kunya ba
Na amince da shi
Amma wallahi danku Dan wallahi yaya bana sonshi
Ya shamsu yayi murmushi yace Abu mafi mahim manci dai shine ki amince
Husnah ta turo bakin shagwabar tace wato bakadamu dani bako yaya na
Ya shamsu yayi dariya yace caf waya fada miki yar kanwata
Yace ai nafi jidake
Dan idan kikayi aure ma fa tare zamu tafi
Husnah tayi murmushi tace ai wallahi yaya da dagaske kake da naji dadi sosai
Amma nasan kana fada be kawai
Amma nifa kullum sai nazo gidan nan
Umma tace kwarai kuwa daga ke har yayan naki zan ga me hankali acikin Ku
Anty kubra tace gaskiya kam umma
Nima naga alama tana dariya
Ya shamsu yace dawa kikeyi yadauki pillow na gefensa ya wurga mata ta tashi
Tagudu yabita shima
Umma tayi murmushi Dan yadda Dan ta guda yake zaune lafiya da matarshi bata taba ganin
wani abun ki agurin kubra
Husnah tace umma Dan Allah yau kimana danbun tsaki da kanki
Kinga yau nice da girki
Umma tayi murmushi tace naki wayon sai girkin 'yata azo zanyi
aikuwa husnah tayi murmushi duk kugama badaini ba wato sai ran girkin anty kubra zakiyi ko
Shikenan nasan mezanyi muku a gidan kuma dole kuci
Umma tayi dariya tace kinga kuwa kyayi aiki har dare kenan
Husnah tayi murmushi ta tashi tace Abba yakusan da wowa
Barin yi kitchen
Tana shiga kitchen din tafara tunanin abinda zata daura
Taduba store dinsu taga suna da doya
Tadauki guda biyu tafere shi tas ta wanke
Ta rarraba shi kanana
Tazuba tunkuya takawo gishiri tasa dai dai misali
Kafin tadebo albasa attaruhu da tattasai dakuma tomatoes amma kwaya hudu tasa tomatoes
din bata bukatar tumatir dayawa
Nan ta wanke komai tas
Tafara greating dinsu a greater ba a blender ba
Dan bata bukatar suyi laushi
Nan tasoya su da mangyada saidataga tayi soyu sannan tadauko yankakkakun kayan namanta
kanana dake cikin fridge tafashashshe
Tazuba tadauko gyararran kifinta Wanda tariga tacire kayar tas shima tazuba tacigaba da
juyawa
Kafin tadauko maggi tazuba dai su curry da thyme da dai sauransu
Tahada tacigaba da soyawa haba ai nan da nan gida ya hau kamshin girkin husnah
Sai da ta tabbatar ya soyu kafin tarage gas din kadan
Tadebo kwai (eggs) guda biyar
Tafasa su a kwano daban tasaka magi guda daya takada
Kafin tadauko tana zubawa kadan kadan tana gaurawa har tagama tacigaba da juyawa
Gaskiya ko itada datayi miyar yakayatar da ita balantana Wanda saidai yagani kawai saici
Nan ta sauke tasama Abba a kulansa kafin tasa ma umma ma anata kulan
Ta ajiye a gefe
Tadauko nasu ya shamsu da anty kubra tasamusu dama tumsafe tayi kunun ayarta Wanda
yasha madara tasaka a fridge yayi balin sanyi kuwa
Ta dauka nasu yaya shamsu tayi da shi part dinsu
Taje tana ta sallama taji shiru
Can saiga anty kubra tafito da gudu daga bedroom dinsu kanta ba Dan kwali ga gashinta duk
an hargitsa
Ga rigarta zif din agaba yake kana ganin kasan akwai magana Dan anfara Jan zif din amma
baikai kasaba
Kubra bata San ma da mutum a falonba ganin husnah kawai tayi tasake baki tana kallonta
Kubra ganin kallon yayi tace ke malama lafiya kuwa
Husnah tayi murmushi tace a a bakomai gani nayi kinfi to kamar wacce tayi dambe da zaki
Takarasa maganar tana dariya
Kubra tasan metake nufi
Itama tayi murmushi tace kema kwana nawane zakije fada da zakin
aikuwa husnah tabarai ta turo bakin tace zakifara ko anty kubra
Ta ajiye musu abincin tace gashi idan kungama soyayyar kwaci
aikuwa tana fadar haka tagudu
Kubra tayi murmushi kawai kafin ta koma ciki
Husnah wanka tafada tana fitowa tayi sallar La asar dinta kafin taje gaban dressing mirro dinta
tafara shafa mai abinta tanagama shafa maidin tadauko body spray tafesa kafin dauko wani
doguwar rigar English wear tasaka
Ta dauki gashinta daure da ribom baki kasancewar kayanta marun colour ne
Yana da bakin dankwali tadaura tayi daurin tauban
Tasaka jambaki shima marun colour gaskiya ba karya duk Wanda ya kalli husnah sai yaso
yasake kallo
Kayan dama dayane daga cikin kayan da mummy hafsat takawo mata ne
Ta fito tasami Abba da umma sungama cin abincinsu
Abba yayi murmushi yace autar Abba gaskiya abincin yayi dadi wallahi
Waya koya miki ne autar ummanta
Umma tayi murmushi aini wani girkin ma fa kirkiran abinta takeyi kuma saikaga yayi dadi
Husnah tayi murmushi tace aini a school dinmu Abba food &nutrition naza ba akan agriculture
Abba yace kai amma auta ta kinyi dabara
Umma ce takatse musu zancen nasu
Tace anya kuwa kinci abinci Dan nasan halinki sarai idan ba aganki ba saiki kai har goma na
dare bakici komai ba
Abba yace wai har yanzu rashin cin abincinta yanan
Umma tace sai abin da yakaru
Idan tagadama wataran dakanta zata dafa indomie
Ya shamsu ne yashigo falon yagaida iyayen nasa
Ganin fitowar ya shamsu yasa husnah zuwa gurin kubra
Wayar ya Shamsu yayi kara yana yaga yallabai kamar yadda ya saving wayar
Yadauka bayan sungaisa prof yakecewa gani acikin gidanku
Ya shamsu yace haba yallabai kaman wani bako kashigo mana
Hakeem yayi murmushi yace ai gurin matata nazo katurota Dan Allah yakashe wayar yana
dariya
Ya shamsu yafada wasu Abba Hakeem ne yazo
Abba yace ya zai tsaya a waje kuma kaje kashiga da shi falonku tunda yau surkunta yakeji
damu
Umma tayi murmushi tace ina ruwan Abdul Hakeem yaron kirki wallahi
Ya shamsu yaje suka shigo tare da Hakeem harkasa Prof yatsuguna yagaida su umma
Kafin ya shamsu yace mune daga ciki tana can ma
Suna sallama dai dai lokacin husnah take gwadawa kubra rawan ittiki
aikuwa Hakeem idonsa kyam akanta ya shamsu yace to dancer of the year
Anty kubra tayi dariya tace sannu dazuwa tana wa Hakeem cike da kulawa ya amsa tareda
tambayarta gida
Nan ta tashi tayi falon su umma Husnah zata bita ya shamsu ke dawo nan baki iya gaisuwa
bako
Cike da jinkuyar Prof tun ranar daya ganta half nacked bata kaunar su hada ido
Tadawo tazauna gefen ya shamsu kai a kasa
Ya shamsu yace to yallabai saika fito
professor Hakeem yace Weldon ya shamsu
Ya shamsu yayi murmushi yafita
Hakeem yamaida kallonshi kan husnah wacce take ta wasada da yatsunta daya sha Jan lalle
Batayi tsam Mani ba kawai taganshi agabanta