Author : Ummu Afan Category : Arewa Hausa Novels
Hajiya suwaiba ta sauka har kasa tace Dan Allah abubakar kayafe min wallahi duk sharrin
shaidan ne hakan bazai kara faruwaba
Daddyn Hakeem yace haba Hajiya ai duk da abinda kika min bazaisa nadaina ganin ki a
matsayin uwaba
Dan haka kitashi daga tsuguna min
Hajiya suwaiba tace nagode Allah yamaka albarka kaida zuriarka
Hajiya rukayya ma tana kuka taba wa daddyn Hakeem hakuri daddy dayake shiba meruko bane
ya yafemata
Hakeem ya kalli mahaifin nasa yaga daddy na goge kwalla
Bakomai yasa daddy kukaba sai rashin imani irin nasu
Idan ya tuna sune sillar rabashida mahaifiyarshi da ko kamannin ta baisaniba saiyaji wani kunci
Daddy kasa jurewa yayi yatashi yashige bedroom dinsa
Abdul Hakeem yabi bayansa mummy hafsat ma tashi tayi tabisu
Hajiya rukayya tabuga tsaki aikin banza wallahi wannan kukan danayi bazai tagi banzaba
Hajiya suwaiba tace towayafada miki dama tubar gaskiyace
ai kawai ganinayi asirinmu yatonu shiyasa na bullo musu tanan
Laila cikin kuka tace yanzu dai kuna gani Hakeem zaikawo wata dasunan mata
Suby kanwar Laila ta ce ai wallahi duk wacce tayi gigin shigowa gidan ki anty Laila wallahi taja
wakanta balain duniya Dan wallahi sai mun nakasa rayuwarta
Hajiya rukayya tace ai zama bai kamamuba
Ke Hajiya bari musa driver yamaidake gida
Gobe zamuyi nijar saboda ke Laila yau kije kibashi hakuri
Kinuna kinyi ladamar abinda kika aikata har dai yasamu yabarki gobe mutafi
Laila tace shikenan hajiyarmu Allah yabar mana.ke kina kokari ganin farin cikinmu
Nan sukatashi kowa yakama gabansa
Laila ta koma part dinsu tazauna tana tunanin abubuwan da suka faru
Wanda sana diyarshi allura ta tono garma
****
Laila sundawo daga nijar yanzu tana zaune ne zaman jiran amarya Dan tafara aiwatar da
niyarta
Hakeem kuwa sake tsarin gidannasu yabayar akeyi badare ba rana
aiki ake zabgawa
Zama yayi yaga gaskiya a yanzu yakamata dadinsa yadaina fita office
Shiyakamata yayi komai su su huta
Kuma bashida da sha'awar raba gida da mahaifansa
Yayi shawarar dawowa A B U Zaria sunfi kusa da nan
Zaisamu daman da dazaije ya kula da harkokin kasuwancin daddynsa
Ahmad ma yace shima kawai kadunan zaidawo yacigaba da rike company daddynsa
Shiya sama yasa ma aikata gyaran gidanshi na Kaduna
Sunyi parking gabadaya zuwa Kaduna Aisha matar Ahmad ta tare a sabon gidanta dake
Kaduna
Hakeem ankam mala komai ainda aka fitar wa da kowa dinshi
Part din Hakeem yana tsakiyarsu
A babban folon PROF zai iya shiga part din kowacce falon nashi guda biyu akwai a sama
Wanda idan ka haura sama falon PROF shima daga gefe kuma wasu maka makan bedroom
dinshi guda biyune
Kai gaskiya dai naira tayi kuka a gidan Prof
Gabakidayansu yasakewa was furniture's har daiyayensa
Komai yazuba wa Husnah Wanda uba yake wa 'yarsa Prof ya dau nauyin komai
Bakin ciki kamar zai kashe Laila amma ba yadda ta iya dole tanuna bakomai saboda tasamu ta
cimma burin ta akan amaryarsa
Mummy hafsat gobe zasu daga zuwa Dubai itada mummyn Ahmad
Hado kayan lefe
*******
Biki ya rage saura kwana hudu Hakeem ne cikin motarshi yana zaune agefen mai zaman banza
Yayinda Ahmad kuma yake driving zasu kano gidan su husnah
Ahmad yace kai prof gaskiya kacanja wallahi gaskiya Allah yawa husnah albarka data saita
mana kai
Dafa magana wahala yakebaka
amman yanzu sai a zauna dakai asha hira musam man ma na husnah
Hakeem yayi murmushi yace kaikuma dadina dakai sa ido wallahi
Ahmad yace aidole ne asamaka ido yadda yarinya karama tacanja ka
Hakeem dai murmushi yayi yace bazaka kanebane abokina bakasan yadda nakejin babyn a
raina bane ko
Ana kiran la asar suna shiga gidansu husnah ya shamsu yataresuda murna yace kaga
manyan kannena
Ahmad yayi murmushi yace fada dakyau ya shamsu girma fa Allah yabaka
Hakeem yace kana mamakine yaya shamsu
Ya shamsu yayi dariya yace waneni da mamaki Dan na zama yayan manyan maza
Daga shiya shamsun dayayi maganar harsu Ahmad da Hakeem sai da sukadara
Ya shamsu yace bissimilla mushiga daga ciki
Hakeem yace mudai fara gabatar da sallah tukun
Nan suka wuce masallacin unguwar
Husnah zaune itada anty kubra
Anty kubra tace Dan Allah husnah kisanar da kawayenki
Maganar bikinki
Husnah ta yatsina fuska tace nifa bazanyi taroba ma
Nibana mason hayaniya wallahi
Kuma da kika damu bagakiba dake da anty Aisha kusai kuzama kawayena
Kubra tarike baki tace lalle husnah wuyanki ya isa yanka
Nice ma zan zama kawarki ko
Husnah tace to Baku kuka dage saina aureshi ba
Anty kubra tayi murmushi tace aini dadina da gobe saurin zuwa
Kaman yaune zakizo kinacemin anty kubra
Wallahi inason mijina
Husnah tayi murmushi tace humm anty kenan nifa nafada miki auren biyayya kawai zanyi
amma ba wai danso ba
ai nagama soyayya
Anty kubra tace shikenan tunda haka kikace akwai ranar maida martani
Anty jumai wacce aka dauko tunda Sudan saboda gyaran amarya tunda akasa bikin washagari
ummu tayi Sudan dama can ita mutuniyar cance
Anty jumai tadubi husnah tace tashi muje kishiga wankar tunda
Hadin yayi awa biyu da shafawa
Husnah tace anty wai Dan Allah yaushe za adaina min wannan shafe shafen nan da shaye
shayen nan
Anty jumai tayi dariya tace sai randa kikabar gidan
Kuma kuji dakyau dawasu zaki taki tafi
aikuwa Husnah ta turo baki ta tashi taje ta shiga wanka
Tana kansaka kaya taji muryar su yayanta da PROF suna gaisawa da umma a falo
Tayi niyar kwalliya tafasa Dan mutumin nan yabata tsoro ranar
Riga da skirt tasaka nawani tsadaddan net tayi kyau bakadanba
Powda kawai tashafa sai man baki
Tana kan maida kayanta cikin durowa anty kubra tashigo tace amarya ango nakira yana
falonmu husnah ta turo baki tace anty kinfara ko
Zanrama wallahi nasan abinda zanmiki kema
Kubra tace ya hakuri 'yar kanwata nadaina
Dan nasan ki sarai wallahi
Husnah tayi murmushi tace a to dole abani hakuri dai
Tadauki mayafin kayan tayafa
Kubra tace kai husnah kedai komai baki baiwane
Wallahi kinwani canja ne fa gabadaya
Kinciko tako ta ina
Jin abinda anty kubra tace yasa husnah tunani tabbas ko itakanta tasan komai nata yacanja
Kuma acikin sati biyun nan da akafara mata gyaran jiki ne
To gaskiya bazata tasa gyaleba
Ta ajiye gyalen tadauki jibgegen jijabinta
Anty kubra tace haba Dan Allah mijinkine fa yazo zakije masa da wannan katon hijabin
ai gwamma dai kidau ki mayafin dakikayi niyar sawa
Kinga zaisake shiga hanu kafin nan da kwana hudun nan
Husnah tace aikuwa kinja ma wallahi rayuwar hijabin zanyi agidansa
Ta wuce anty kubra tayi falon
Tashiga da sallama ya amsa mata tamkar wani balarabe
Kamshin sa yacika falon
Husnah tanemi kasa tazauna
PROF yakureta da kallo wani kyau yaga tamishi
Kaman yau yafara ganinta
Husnah tagaisheshi bai amsa ba jin bai amsa ba yasa tadago suka hada ido yakafeta da
idonshi
Kasan yasauko yazauna yana fuskantarta yace haka ake tarbar miji baby
Tayi shiru batace komaiba yace babay magana nake fa
Husnah cikin shagwabarta Wanda ita bada niyya tayi shiba tace menama kuma
Yace nafarko nace kidaina samin hijabi idan zakizo gurina bakida mayafaine
Tace tokai meyasa bakason insa hijabin
Hakeem very good question
Nafarko inason hijabi amma a muhallin daya dace asaka kaman kiganni da wani ko abokaina
da kuma sauransu
amma banda dagani saike kisaka
Bakisan nazo naganki Dan nasamu nutsuwabane ?
Husnah tayi shiru tana wasada da zobenta
Murmushi Prof yayi Yakama hanunta tana kokarin janye hanunta prof yacire zoben hanunta
Kafin yasaketa
aikuwa Husnah ta kalleshi a tsorace tace Dan Allah kayi hakuri kabani zobenan
Yace meyasa zan baki tace nima bani akayi
Yace wakenan tayi rau da ido kaman zatayi kuka
Tace masoyina ya muallim
Yace zan baki amman saikinbi maganana kicire wannan jijabin
Dan ba anan yakamata kisaba
Husnah tace Dan Allah yaya kayi hakuri kabarni da hijabina nariga nasaba
Hakeem yace OK yasaka zoben a aljihunsa
Yace nawa kike bukata game da events din ki
Husnah takalleshi tace nima bana bukatar komai
Ya kalleta da mamaki yace saboda me tace bakomai wallahi ni duk wani Abu dayashafi bidia
bana kaunarsa
Dan Allah yaya daman inason na roki alfarmar events din dakukasa akatin nan wallahi banaso
Dan Allah kabarshi kawai
Hakeem yace duk abindakikace haka za ayi amma bashi ne
Duk randa kika haifamin baby zan baki mamaki duk abinda ba ayi a bikin nan ba saina yishi
Husnah tayi shiru can tace tokabani zoben yashare zancen
Yafito da kudi dubu Dari shida ya aje mata yace gasu nasan zaki bukaci kudi banason kitambayi
ya shamsu ko Abba
Duk abinda kike bukata let me know OK
Ya cigaba da kallonta kawai kaman yasami TV
Husnah tace maganar zoben
Yace sakinyi abinda nace miki
Husnah tace nayarda amma saidai nakoma na dauko mayafina
Baice komaiba sai binta dayayi da kallo
Shigowar husnah Hakeem kusan suman zaune yayi Dan baitaba tunanin abinda idonshi
zaiganiba kenan
Da sauri yace baby go and wear your hijab please
Husnah takoma da sauri
Tana shiga dakinta fashe da dariya
Dan bakaramin dariya yabata ba
Hakeem dafe kai yayi take hankalinsa ya tashi
Nan yafara tambayar kansa
Meyasa sai akan yarinyar nan yake jin feelings haka
Maiyasa komai nata is so special to me
Da kyar yaja kafarsa yafita zuwa gurinsu Ahmad da ya shamsu
Ahmad yace muwuce ko PROF yace
Hakeem yace muje muma su umma sallama
*******
Laila takira meenat tafada mata duk abinda kefaruwa
aikuwa meenat kaman tayi tsuntsuwa tazo Nigeria
Tace kiyi abinki mummy babu matar data isa kiyi kishi da ita wallahi
Idan mukazo koni ko 'yar iskar da tayi kasadar auran daddyna
Suna gama waya da Mummynta Laila
Tadubi Bashir tace kaji kuwa mekefaruwa agidanmu
Bash yace saikin fada
Takwashe komai tafada mishi
Tsaki bash yayi yatashi
Yabar gun
Next page
Your comments is needed fan's
Love u all
踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫
[05/05, 8:53 PM] UMMU AFAN 潤撕: 潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤
潤潤潤潤
潤潤潤
潤潤
潤
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
踫踫踫踫踫踫踫
潤撕FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION潤撕
潤撕潤撕 (F.C.T.W.A)潤撕潤撕
潤撕HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION潤撕
潤I DEDICATE THIS PAGE TO YOU Hauwa'u idris ( maman daddy )
Allah yabar zumunci inajin dadin comment din ki Allah yabar kauna keep it up踫踫踫踫踫潤
潤AKWAI lokaci潤
潤PAGE 101to105潤
PROF yashigo direct dakin amaryar ya wuce sai yaji kofa gam
Kuma gashi bashida spire key
Duk guda hudun suna hade da juna
Ya koma dakinsa yayi wanka
Ya koma kan bed dinsa yadauki waya
Yasoma dialing din number husnah yayita ringing
Husnah bata daga wayar ba
Prof yayi mirmushi Wanda shikadai yasan abinda yasashi murmushi
Ya rufe ido Dan bacci amma bacci yace baisan zancenba
Yadauki wayarshi kawai yakira Ahmad
Saida yakira Ahmad sau biyu kafin ya dauka
Ahmad yace kai ango yadai kira da wannan lokacin
Hakeem yace kai dai bari wallahi man
Wallahi yarinyar nan ta kulle min kofa
aikafin yakai karshe Ahmed yafashe da dariya sosai yayi dariyarshi
Kafin yace amma wallahi husnah ta burgeni
Sosai
Hakeem yace Dan iska dariya zaka min ko
Ahmad yace aikaine abokina duk kabi ka tsorata masu yarinya aidole ta kulle kofarta
Dan batasan mezaifaruba idan akabarku Ku biyu
Hakeem yayi murmushi yace duk tagama buyanta badai ta shigo hanu ba
Zanbata mamaki zata shigo hanu ai
Ahmad yace wallahi dai kabi yarinyar mutane a hankali
Bafa babbar mace bace
Dan nasan kasaba da manyan mata
Yayi dariya yakashe wayar shi
Hakeem cikin murmushi yabi wayar da kallo
Yace zanrama ne
Kafin yakoma amma bacci fa yaki Sam
Daya rufe ido zaiga husnah alokacin da yake kissing dinta
Sai yayi murmushi ya rungume pillow kawai bacci yayi awun gaba dashi
Laila duk abinda kefaruwa tana lebe tana gani aikuwa ganin Hakeem ya burda kofa yaji akulle
duk ta gani
Har wayan dasukayi da Ahmad taji aikuwa cikin farinciki ta koma part dinta ta sanar da su
hajiyarta da kanwarta suby
Dan basu komaba ita suby auran nata ya mutu shiyasa zata zauna gurin Laila
aikuwa cikin farinciki hajiya rukayya tace aikin banza Ashe ma duk abinda suke yarinya bata so
Suby tace a a karku manta dama boka yace zai sa gaba a tsakaninsu
Watakila aikin ne boka ne yafara aikitakanta
Inbahakaba wazaiki yaya Hakeem a matsayin miji
Hajiyarsu tace tabbas maganarki hakatake
Kunga ganiba gwamma da muka sake mishi kudi gashi anfara aganin cigaba
Laila dai da farin ciki ta kwanta abinta zuciyarta fati kal
Karfe hudu dai dai na asuba Husnah tafarka cikin nannauyar baccin da ya dauketa
Tashi tayi tashiga bathroom alwala tayi kafin tayi nafilfilunta kamar yarda tasaba ana kiran sallar
asuba tayi sallarta tayi adduointa da karatun alkur'ani
Kafin tacire kayan jikinta Dan jiya bata samu daman cire kayan ba saboda gajiya
Tashiga wanka kafin tafito
Spray kawai da shuwa tashafa sleeping dress tasaka duguwar riga abinta tafada gado abinta
Sosai taji dadin baccinta Hakeem bayan yadawo daga sallar asuba yasake tana dakin husnah
shiru bata budeba
Direct dakinshi ya wuce dakinsa
Shima baccin yakoma
Karfe bakwai da rabi dai dai mai aikin mummy ta buga kofa
Suby kanwar Laila ita tabude kofar
Taga me aikin mummyn Hakeem ce
Tace sannu suby ta yatsina baki yadai ina zaki da basket din abinci haka
Tace hajiya ce ta aikeni nakawo ma amarya abin karyawa
Suby ta kebe baki tace to aikuma basu tashiba amma kawo saina na mika mata
Tabata abincin
Suby ta karba tashige dashi part dinsu gurin su Laila da hajiya rukayya
Laila cikin murna tace yauwa suby dauko maganin a side drawer kikawo
Aikuwa haka suka barbade komai da maganin nan
Farfesuf na kayan ciki sai kunun gyada da kosai
Kai kuma farfesun ganda Wanda yasha kayan hadi sosai
Haka suka bikomai suka badeshi tas
Hajiyq rukayya tace maza ke suby tashi kikaimata
Laila tace abarta ta kai Dan tanason ganin amaryar
Hajiya rukayya tace a a idan kika kai dakanki za azargi wani Abu
Zakiganta ai mudai burinmu kawai tabar gidan
Suby tace wallahi nimafa basanin amaryar nayi bama dan haushi
Husnah cikin bacci taji ana buga mata kofa ta tashi tayi hanyar falonta
Tayi kofa tabude sukayi ido hudu da suby
Suby sai tadauka kaman gezo idonta suke mata wannan irin zukekiyar yarinyar kuma daga ina
Husnah ta ce sannu suby tace ina antyntaki
Husnah ta yatsina fuska tace antyna kuma
Suby tace ina nufin amaya
Husnah tayi murmushi tace OK ai tashiga wanka
Tana ganin suby tasauke ajiyar zuciya
Husnah ta kibata hanya kuma
Suby tace ga shi inji hajiyar yaya Hakeem akawo mata
Husnah tace OK angode barin kaimata
Suby ta mika mata basket din husnah tarufe kofarta