Chapter 5 Reading AKWAI LOKACI 1 BY UMMU AFAN .pdf Arewa Novels

AKWAI LOKACI 1 BY UMMU AFAN .pdf

Author :  Ummu Afan Category :  Arewa Hausa Novels

Chapter   5 / 15

12K to 15K   out of 44.6K words

wasa fa watan meenat shadaya amma amma haryanzu
mahaifinta baizoba


Suby tace wai Ku meye kuka damu sai yadawo ne bakusan idan yadawo Baku basamun abinda
kuke samu yanzu ba """""


Laila tace nimadai haka nagani
Nifa wallahi tunda acikamin jaka da abinda nakeso yashekara goma ma baizoba ba abinda
yadameni


Hajiya rukayya tace duk kurinta ne yake damunku inba yarinta ba ai wallahi idan yashigo hanu
zamufi yadda muke yanzu

Dan sai abinda tace zaibata komai ta tambaya zaiyi jiki na bari

amma hakan bazaiyu ba sai
Yaci abinci da maganin har na wajen wata daya inji malam

To ta yaya hakan zaifaru idan bata jawo shi jikinta ba

Laila tace kuma fa hakane mama yanzu manene shawararki mama


Hajiya rukayya tace yauwa anzo gun danakeson azo

Kinga yanzu abinda zakiyi ke Laila kisamu Daddyn Hakeem kice kizakibi mijinki can saudin


Nasan shi da hangen nesa bazaiso shiga hakkin waniba

Idan kikaje can duk wani Abu na biyayyya ki kirkiro kiringa mishi inda zamusamu yasaki jiki
dake sosai inda har zaki bashi abinci kuma yaci


Laila tace to mama yanzu dai zanshirya na tafi gidan mummy hafsat
Zanfada wa daddy komai

Hajiya rukayya tace yauwa yar gari tashi maza kishirya kiyi kama hanya

Suby tace anty Laila zanrakaki
Lailatace shirya muje

Hajiya rukayya tace kuje kawai kubar min yarinyar

Laila tace dama bazamu jeda itaba



****
Laila sukayi sallama a falon mummyn hafsat tana zaune tace a a

Laila kune atafe

Laila tace a mummy Allah yasa daddy na nan
Munzo gurinshi ne

Mummy hafsat idan da sabo tasaba da zuwa Neman daddy agunsu Laila

Mummy tace yanan yanzu zaishigo ya fita sallah ne

Nan su Laila suka zauna zaman jiran daddy

aikuwa daddy shigowa suka gaisa
Yace Lafiya kuwa Laila kokuna bukatar wani abunne

Laila tafada mashi damuwarta nason bin mijinta

Daddy yace wannan ba wani abinda damuwa bane

Kishirya kawai kije kiyi passport agama komai kafin jibi sai kitafi

Laila tace To daddy Allah yakara girma yace Ameen
Ina amaryar tawa

Suby tace tana wajen hajiya

Yace to ace angonta na gaisheta

Nan suka wa mummy sallama suka fita

Daddy ya kalli mummy yace Lafiya kuwa mummyn Hakeem

Mummy tace wallahi alhaji mutanen kotata ban yarda dasuba
Mezaisa tabishi har can yabari mana ai komai daran dadewa zadawo

yanzu haka uwartace ta kitsa mata komai

Daddy yayi murmushi yace insha Allah ba abinda zaisamu Hakeem
Kokin manta Dan naki
Ma abocin riko da addini ne
Dakuma yawaita adduoin tsarin jiki

Mummy tayi murmushi tace hakane daddyn Hakeem
Gaskiya Hakeem kam akwai addua
Sai dai muce Allah yadada tsare mana shi


Daddy yace Ameen

Washagari daddy yagama wa Laila komai nashirin tafiya
Wanda jibi jirginsu zaitashi

Zuwa Saudi

Hajiya rukayya da hajiya suwaiba ne suka sata gaba kan yadda zata yi anfani da magun gunan
dasuka karbo daga gurin malam


Komai Laila ta haddace Dan hartafara hango kanta cikin daula



Washagari jirginsu Laila yadaga zuwa Saudi
Inda tabar meenat 'yarta agurin mahaifiyarta hajiya rukayya


Daddy yadauki waya yakira Abdul Hakeem cikin ladabi Abdul yagaida mahaifin nasa
Daddy yace kashirya kaje airport kadauki matarka
Tana hanya

Cikin mamaki Abdul Hakeem yace Laila kuma daddy
Meyasa zata biyoni har nan

Gaskiya takoma gida kawai Daddy

Daddy yace Haba Dan albarka aure fa ba abin wasa bane

Na kusan shekara bakanan
Ta nemi data zo tagan ka ai baza a hanata bako

Hakeem yace amma daddy
Daddy yace karkace komai ka je airport kadauketa kawai kaji ko

Yace naji daddy Allah yakara Lafiya daddy yace Ameen
Allah yamuku albarka Hakeem yace ameen daddy

Suna gama waya da daddy yace ya Allah

Ahmad yace Lafiya kuwa Man naganka haka
Hakeem yasauke ajiyar zuciya yafada wa Ahmad komai

Ahmad yayi murmushi yace kace nakoma dayan part tunda amarya zata zo

Hakeem dai baice komai ba
Yazauna akan kujera

Karfe hudu dai dai yaje yadauko Laila

Tana ta rawar kai shikuwa Hakeem tunda tagaisheshi ya amsa bakaracewa komai

Wannan shine mafarin zaman Laila a saudiya

Dan bata koma ba


*******
Bayan shekara goma shabiyar
PROFESSOR ABDUL HAKEEM ABUBAKAR

Dan shekara talatindashida aduniya
Cikakken saurayine Wanda ya amsa sunan

THE YOUNG PROFESSOR

ko ina haka akeranshi gida da wajen kasan nan

Yayi suna sosai aduniya saboda kudi da kuma ilimin da Allah yabashi

Har yanzu yanazama a sauddiya ne a inda yake koyarwa a jamiar Saudi Arabian

Dashi da babban abokinshi professor Ahmad

Wanda a yanzu suke shirye shirye komawa kasarsu Nigeria

Laila anzama manyan mata koda wasa bazaka kaga Hakeem kace shine mijinta ba

Ba alamun dacewa a tsakaninsu

HAKEEM bashida rowa koka kadan kudi masu sunan kudi yana cika
Laila dasu
Dan yanzu taza business wuman sosai suke kasuwanci da kanwarta Suby

Idan ta saro kaya a Saudi sai ta tura wa Suby Nigeria

Su duk aganin su Hakeem magani ne yake aiki akansa
Wanda abin bahaka bane dai niyya kawai yayi yake mata abinda yake mata


Amina kuwa agurin hajiya rukayya take sun shaku sosai Dan yarinya dai tayi mugun gado

Shiyasa basa shiri da kakarta mummyn Hakeem Dan tana mata wa azin tabi a hankali kartayi
mugun gado

Yanzu haka ma basa Kaduna suna can kano nan hajiya rukayya takoma Dan mijinta yayi ritaya
sai ya koma garinshi kano

Shiyasa hajiya rukayya tadauki jikarta meenat suka koma can
Yanzu meenat ta Dade a kano

Tana zuwa Hutu Saudi gurin iyayenta

Wannan kenan


KANO

Malam sualaiman yana zaune a wata unguwar talakwa ne dake nan kano

Yana da mata daya da rana biyu

Yaya shamsu shine babba zaikai shekara 36 aduniya

alokacin da umma ta haifi yaya shamsu sai da yashekara ashirin cas

Kafin tasamu cikin asmaullahil husna
Wato asmau kenan

Inda akecemata husnah

Husnah ta taso cikin gata da tattalin uwa Dana uba da kuma Dan uwa rabinjiki wato yaya
shamsu

Tunda aka haifi husnah shamsu ne me dawainiya da ita kasancewar yadade baisamu kani ko
kanwa ba


A yanzu haka husna tasamu scholarship a wani makarantar masu kudi a inda take s s two a
halin yanzu


Husna tana da hankali da nutsuwa ga kuma uwa uba kyau da needed

da Allah ya horemata

Husna yar kimanin shekara shabiyar aduniya

Sun hadu da Amina Abdul Hakeem abubakar

A school lokacin da husna ta samu scholarship tashigo itama Amina alokacin tashigo
makarantar

Amina taso husna Dan Abu guda biyu ne na farko iliminta farinjininta da kuma kyau

Dakyar husnah ta amince wa Amina suka zama kawaye sosai duk inda kaji ance husnah to za
ace amina


Muje zuwa 踫 anfra fa

Fan's kubiyo ummu AFAN

Kawai

Your comments is needed
[30/04, 5:53 PM] UMMU AFAN 潤撕: BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


潤HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN

潤GORGEOUS WRITERS FORUM潤

潤G.WF.潤

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS WE ARE THE BEST AMONG
THE REST


潤DEDICATED THIS PAGE TO MY ENTIRE FAMILIES潤



潤AKWAI LOKACI 潤



潤PAGE 36 to 40潤




HUSNA nata saurine saboda tayi latti yau Monday yau ne za a Nada zabin prefect a school
dinsu


Ummu tace husnah naga kina ta sauri yau Lafiya kuwa

Husnah tayi murmushi har dimple dinta suka lotsa tace wallahi ummu yau za a nad'a sabbin
prefect a school ne shiyasa mukeson muje muga wadda za a ba


Yaya shamsu yace kokuma kije a nad'a kuba
Husnah tace aini bandani yaya Dan an min

Interview ma naki bada amsa a hall din

Duk Dan kar abani damuwar nan

Yaya shamsu yace ai duk yadda kikayi sunsani tunda sunsan dalibarsu
Kokinyi shiru sunsan bawai baki sani bane

Tunda dama sunsan bakyaso
Bakince min saki dole akayi kiyi interview din ba

Husnah tace wallahi wani malaminmu ne copper yace lalle sai nayi interview

Kuma duk abinda suka tambayeni Nace I don't no
Komai I don't no kawai


Yaya shamsu yayi dariya yace kedai jekidawo kiban labarin wadda akazaba


Husnah tace to shikenan yaya
Tajuya ta kalli ummanta tace ummu sai na dawo

Ummu tace Allah yadawo dake Lafiya tace ameen umma na


Har takai bakin kofa yaya shamsu yace husnah kiyi hakuri kinji bakudi ajikina yanzu nakeson
zuwa nayi buga buga naga abinda za a samo acigidan

amma namiki alkawari idan nafita nasamu wani abin zana biyo har school dinku

Inbaki Abu mai dadi

Husnah tayi murmushi tace karka damu yaya na wallahi bani da damuwar komai Dan bancika
son cin komai a school ba ma

ai kana kokari yayana Allah yakawo maka aiki maitsoka nasan zamu huta sosai


Yace ameen yar kanwata jeki karkiyi latti


Tafita abinta tana murmushi


Umma ta sauke ajiyar zuciya tace wa yaya shamsu

Kasan wani Abu kuwa shamsu deen yaya shamsu yace a a umma saikin fada


Tace wato akullum na kalleku kaida kanwar ka ina wa Allah godiya daya mallakamin 'ya'ya
nagari

Dan ba abinda zance wa Allah sai godiya kawai

amma duk inda ake neman 'ya'ya nagari nasamu
Abba dayake shirin fitowa daga dakinsa yace munsamu dai zakice zainaba

Tunda Allah yasa shamsu yakawo kwari fa shiyake dawainiyya damu agidan

Shine komai na kanwarsa shine namu aiba abinda zamuce sai muce shima Allah yabashi mai
mishi

Umma tace Ameen malam

Malam sulaima yace babban damuwata shine inga kasamu aiki kayi aure Dan shine cikar
mutuncin mutum


Umma tace hakane ai baki yayi tunda yana da wacce yakeso khadija yarinyar kirki taki kowa
saishi take jira
Ko a yanzu aka tura za ayi komai tunda iyayen ma sun komai

Malam sule yaja numfashi yace hakane kam to Allah yabamu yadda zamuyi


Ya kalli shamsu da tunda suka fara zancen auranshi yashiga duniyar tunani


Dan yana matukar son budurwarshi khadijat wacce akekira da kubra kitama tana son yaya
shamsu sosai Dan

Shekarar ta daya kenan dagama secondary school
Manema sunzo Neman aurenta taki ita sai shamsu
Haka iyayen suka hakura suke zaman jiran shamsu yakawo sadaki a daura aure



Malam sule yakalli shamsu yace karka damu akwai Allah

Shamsu yace barinje Abba sai na dawo ya ma umma ma sallama ya wuce zuwa Neman abinda
zasuci


YAYA SHAMSU daga secondary bai kara gaba ba saboda rashin kudi daya musu katutu shida
mahaifansa

Dan haka kawai ya hakura yake Dan buga bugansa dahaka kuma har Allah yasa aka haifi
kanwarsa husna saiya yaci burin Husna zatayi karatu tunda shi Allah baisa zaiyi mezurfiba


Sai kuma gashi Allah yafara cikawa shamsu burinsa inda husnah taci scholarship


**
Husnah tana isa school tasamu anfara assembly
Ta tsaya daga bayan 'yan mate dinsu suna sauraron jawabi daga bakin principal dinsu



Can sai vice principal yace yace zamufara kiran new prefect dinmu daya bayan daya

Principal tace a fara da head girl ko

Sai copper bash yace am sorry ma
Gwamma afara da sauran kafin head girl
Zaifi Jan ra ayin su

Principal tace OK afara kira kawai


Nan akafara kiransu ana samusu hula da kuma belt
Dansu prefect din hula suke sawa green gabadayansu na head girl ce kawai ya banbanta Dan
nata read cap take sawa


Can taji ance social prefect AMINA HAKEEM ABUBBAKAR




Nan aka dau tafi raf raf raf ana murna

Can sai vice principal yayi gyaran murya yace yanzu zamu Kira me gayya me aiki wato our
head girl

Nan aka kira sunan ASMAU SULAIMAN SHAMSU

cikin gigicewa Husnah tadago kanta aikuwa tana dogowa sukayi ido hudu da Copper bashir

Ya kashe mata ido daya

Cikin tashin hankali Husnah ta daga kafa dakyar tana zuwa ta hau kan stage

Principal ta rungume Husnah tare da
Da samata hulan head girl dinta read cap

Ta daura mata belt dinta read shima
aikuwa daga students har malaman dake wajen aka dautafi Dan sunburge kowa ga read cap
din yawa Husnah kyau sosai kaman Dan ita akayi hulan


Nan dai aka rantsar dasu Husnah a matsayin new prefect


***
Copper Bash ya tsare Husnah alokacin dazata wuce gida itada meenat


Copper bash yace asmau
Ya naga kina ta shan kamshi ne Yau

Meenat tafashe da dariya
Tace uncle ai Husnah fa batasan za abata prefect ba ballantana Head girl

Copper bash yayi murmushi yace ai kuwa ta yaudari kanta

To inba a bata ba waza aba wa
Meenat tace aifa dai kam


Husnah dai tana jin su batace komaiba

Nan driver din meenat yazo daukarta

Husnah kuma dama da kafa take zuwa take komawa

Meenat tace Dan Allah Husnah kizo musaukeki a gidan kinga sai naga gidanku ko

Husnah tayi murmushi dimple dinta suka lotsa

Copper bash ya tsaya kawai yana kallon Husnah komai nata cikin aji takeyinsa da nutsuwa
shiyasa takeda farinjini a school din


Husnah tace wallahi meenat idan ya shamsu ya ganni a mota zai min fada sosai .

Meenat tace kedai kawai bakyason kibimu sai kiyi tayiwa yaya shamsu sharri


Copper bash yace kinga kuyi sauri kutafi gida kar anemeku kuntsaya surutu


Meenat tace to shikenan sai mun hadu goben idan munzo ko

Husnah tace to meenat Allah yakaimu kigaida gidan
Nan sukayi sallama

Copper bash yace wa Husnah muje nakaiki gida da kaina

Tunda kinki kawarki takaiki

Husnah tace Dan Allah uncle kayi hakuri wallahi yayana yaganni da kai zaimin fada

Copper bash yace mezaisa yamiki fada baki kai a rakakin bane ko yaya

Husnah tayi shiru tace kayi hakuri Dan Allah

Yace wato har yanzu Husnah kinkasa yarda da sonda nake miki ko

Kibani dama nasan gidanku da iyayenki wallahi dagaske nake auranki zanyi Asmau

Husnah tace Dan Allah malam kayi hakuri kar yaya yasan da wannan maganar

Dan ya hanani kula koda kawace ballantana

Maganar soyayya tun yanzu

Da kyar yabani dama kawance da mina Hakeem ma



Copper bash yace OK na fahinceki
Ba wai nidinne bakyaso ba umarnin yayanki kikebi ko


Husnah ta rufe ido tana murmushi tayi hanyar fita daga gate din school din


Copper bash yayi murmushi tunda ya gano yafara shiga zuciyar Husnah

Zaisan hanyar da zaibi Dan yasan iyayenta da yayanta shamsu



Bashir Dan wani hamshakin maikudi ne sosai acikin garin kano

Bautar kasa wato NYSC yakaishi school dinsu Husnah
Tunda yadora idonshi kan Husna yaji yakamu da son ta

amma takibashi daman hakan



Next page
[05/05, 11:05 AM] UMMU AFAN 潤撕:
潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


潤HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN 潤


潤撕潤撕FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION潤撕潤撕

潤撕F.C.T.W.A潤撕

潤撕HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION潤撕



潤DEDICATE THIS PAGE TO UMMY 踫 KINA KOKARI WAJEN GANIN NOVELS DINA SUNA
KARBUWA A KOWANI GROUP ALLAH YABAR KAUNA 踫踫踫踫踫




潤AKWAI LOKACI潤




潤PAGE 41 to 45 潤




ABDUL HAKEEM THE YOUNG PROFESSOR

kwannansu biyu da dawowa daga saudiya dashi da madam laila


HAKEEM yana shirin zuwa sashen iyayensa ne don yagaishesu

Yafito daga wanka ne yashirya cikin wani farisol din jallabiya ya faffesa turarruka masu kamshi
Dan akwaishi da son kamshi sosai

Har yagama shiransa zaifita Laila bata tashiba

Ya kalleta kawai ya girgiza kai yayi gaba abinsa zuwa part din su mummynshi

5 / 15