Chapter 6 Reading AKWAI LOKACI 1 BY UMMU AFAN .pdf Arewa Novels

AKWAI LOKACI 1 BY UMMU AFAN .pdf

Author :  Ummu Afan Category :  Arewa Hausa Novels

Chapter   6 / 15

15K to 18K   out of 44.6K words




Yanashiga yasamesu akan dining da mummy da daddy


Daddy yace Dan halal kaki anbato yanzu nace baka shigo break fast ba mummyn ka tace ai
tasan kana hanya

HAKEEM yayi murmushi cike da kaunar iyayensa

Yace ai mummy tafadi gaskiya Dan bazan taba karyawa a wani waje ba matukar muna tare da
mummy

Mummy tace yauwa son fada mishi dai

Nan mummy tayi serving din HAKEEM abinci yafara ci


Bayan sungama break fast ne mummy zata kwashe kwanukan Hakeem yace haba daliba
yazakimin haka kuma

Kezaki kwashe kayan zuwa kitchen nikuma meye anfani na

Mummy hafsat tace nabari tashi ka kawashe

Daddy dai dariya yake musu yakoma kujerar falo yazauna

Hakeem bayan yagama kwashe kwanukan zuwa kitchen saiya dawo falo Dan hira da iyayen
nasa


Daddy yace wai acikin makarantu biyu dasuke bukatarka wanne kazaba kayi lecturing din agun

HAKEEM yayi murmushi yace ai daddy daga ni har Ahmad munzabi muje BUK kano


Daddy yace Allah yasa haka shine alkairi

Mummy hafsat tace amin

Daddy yace kace kuna tare da amaryata kenan

Mummy hafsat tayi murmushi tace MEENAT ko rigima

Yakama ta ma suturota tazo tagaida iyayenta ai

Daddy yace karkice komai tunda basuyi hakan ba shi saiyaje yaganta


Kafin Hakeem yayi magana wayar daddy yadau kara

Daddy yadaga sai sukaga daddy yace subuhanallla a wani asubiti

Mummy da Hakeem suka maida kallonsu kan daddy

Bayan daddy yakashe wayar ne suka tambayeshi abinda kefaruwa

Yace Abba na aka kai hospital

HAkeem yace subuhanalla muje kawai daddy

Mummy hafsat tace nima bazaku barniba muje tare

Suka he asibitin Hakeem ne me driving dinsu

Suna isa suka sami alhaji shuaib bayadda yakara ji

Dan yanajin jiki sosai

Alhaji shuaib yarike hanun Dan nashi wato daddy
Yace Allah yamaka albarka abubakar da kai da zuriarka

Ba abin da zance dakai sai Allah yàmaka sakayya da gidan aljanna duk inda akeneman yaro
nagari ka kai abubakar

Ya kamo hanun Hakeem yace jikallena ga mahaifinka nan nabar maka amanarshi duniya da
lahira

Kabishi kamar yadda yabini

Ya kalli mummy hafsat yace kema Hafsatu Allah shizai biyaki akan yadda kika nuna kaunarki ga
abubakar

Duk yadda aka kai cutar dashi kinki bada damar hakan

Allah yamiki albarka

Tunda alhaji shuaib yafara magana suke kuka musamman daddyn Hakeem

Da mummy

ABDUL HAKEEM ne kawai ya daure amma shima idonshi yayi ja sosai


Can dai likitoci sukace sufita zasu samishi
Oxygen Dan numfashinsa yafara kasa

Alhaji abubakar ne kawai akabari a dakin


Can wajen La asar 'yan kano suka iso asibitin

Kuma harda meenat

Hajiya rukayya itama a rikice tazo jincewa jikin mahaifin nasu ya tashi

amma anhanata shiga taganshi

Hakan kuma ya bata mata rai sosai

Amina kuwa tana ganin daddynta Hakeem tare da mummynshi takarasa wajensu cike da
murnar ganin uban nata

Bayan tagaida Hakeem ne take tambayarsa dad ina mummyna yace tana gida yanzu zata zo
itama

Amina ta kalli mummy hafsat tace wato ma bazaki kimin magana ba ko

Mummy hafsat tace kaga jaira kinga babanki bakima San ina wajenba zaki ce ban miki
maganaba

Sannu uwata mummy hafsat takarasa maganar tana tsokanarta

Amina tace ai wallahi duk abin kidai saina auri mijinki sai naga yadda zakiyi

Mummy hafsat tayi murmushi tace kishigo mana kigani da tabarya zan koraki ai nan mummy
Hafsat tana jikinta ajiki sukata Dan hirarsu amma cikin jimamin rashin lafiyar alhaji shuaib


Ahmad yakaraso hospital din shima cikin jimami

Hakeem na ganin Ahmad yace Man ka karaso kenan

Ahmad yace ai kana kirana nace wa mummy zanzo hospital namata bayani

Itama zasu zo tanason gama abincine sai ta taho dashi

Hakeem yace Allah yakawota Lafiya

Ahmad yace barinje na gaida su mummy suka karasa harwajensu mummy

Yagaishesu yamusu ya maijiki

Amina tace daddy Ahmad ina wuni yace Lafiya qalau daughter ya mummyn ki

Tace banganta ba mu yanzu mukazo daga kano

Kafin Ahmad yayi magana daddyn Hakeem yafito daga dakin yana goge hawaye

Hakeem da Ahmad suka karasa dasauri Hakeem yace daddy yajikin alhajin

Daddy abubakar yace Hakeem Allah ya yi wa mahaifina rusuwa
Alhaji yatafi yabarni Hakeem

Yanzu bani dakowa dama bansan mahaifiyata ba shikadaine min aduniya

Shima yatafi

Duk matan dake gun sukasa kuka


******

Bayan arbain din alhaji shuaib

ABDUL HAKEEM da aminin sa suka fara lecturing B U K

Dan karakaran gidaje makaranta tabasu a matsayinsu na professional akan aikin su

Yanzu Haka suna shirye shiryen auran Ahmad kuma a kano zaitare da matarsa

Itakuma Laila tayi tayi yabarta tadawo kano yaki

Sai dai yazo masu Hutu yakoma

Yanzu haka bikin Ahmad saura sati biyu cas a daura auren Ahmad




*****

Yaya shamsu zaune akan kujera yar tsugune umma kuma na hada zobo Dan duku gidan suna
azumin Monday da alhamis

Itakuma Husnah tana kan hada musu abincin buda baki a kitchen

Kanin kubra budurwar yaya shamsu ne yayi sallma yashigo ya tire

Ya gaisheda umma kafin ya ajiye abincin yace yaya shamsu gashi anty kubra

Kafin shamsu yayi magana umma

Tadauko naira hamsin tace zoka karba ko kace mata angode Allah yasaka da alkairi

Yaron yaki karbar kudin umma yaya shamsu yace haba kanina karba mana ai ba roka kayiba

Yakarba yayi godiya zaifita kenan
Husnah ta tace sani kace wa anty kubra gobe zanzo kitso
Sani kanin kubra yace to zanfada mata


Umma tace kajita kaman wani kitson takeso
Yanzu zatace maka zata kitso taje tadawo da kalba

Husnah tayi murmushi tace umma wallahi banason kitso nafison dai amin kalban kawai


Tagama kwashe komai ta ajiye musu akan taburma

Jelouf din taliya ta musu Wanda ya shamsu yakawo dazu yace a dafa yasan tana son taliya
sosai

Umma tace wallahi yarinyar nan kubra akwai kokari
Bata gajiya da aiko maka da abinci duk Monday da alhamis


Husnah tace gaskiya kam wallahi anty kubra Nada kirki

Yaya shamsu Allah yabaka kudi wannan sallar dai kasamu kamata kayan sallah

Umma tace amin gaskiya kam ta cancan hakan


Shamsu yaja numfashi yace kuma wallahi umma kubra bata jin dadin gidansu

Indai ba abbanta yana gidaba

Kishiyar mamanta tana matsa mata sosai
Yanzu fa wai akwai Wanda yamata magana yanson kubra shine tadage sai kubra ta amince da
auran wani baniba

Dan taki amincewa shine take bata wahala
Kuma abbanta yace bazai mata auren doleba
Sai Wanda takeso zaibata

Shine tayi bakin jini agidan


Umma tace Allah sarki marainiyar Allah

Allah yabaka abinda zaka auro yarinyar nan karabata da gidan nan

Shamsu yace amin umma
Husnah ma tace amin

Yaya shamsu yace barinje sallar magriba indawo muyi buda baki



Shamsu yana fita Husnah tace wallahi ummu yaya shamsu yana bani tausayi

Dan wallahi shima yana son kubra sosai

Umma tace bakomai AKWA LOKACI

watarana sai labari Husnah tace Allah yanuna mana lokacin amin ummu tace

Suma tashi sukayi Dan gabatar da sallah



**
Bayan kwana biyu wani abokin shamsu yabashi
Shawarar mezaihana yakai takardunsa Neman aiki B U K koda masinja aka bashi zai rage zafi
ai

Shamsu yace gaskiya naji dadin shawarar nan daka bani kabiru
Allah yabar zumunci

Kabiru yace bakomai ai zaman taren kenan

Kaga ni a secondary school nake masinja amma alhamdulilla ina samu

Ya shamsu yace hakane yanzu zanyi wanka nakai kuwa

Bayan ya shamsu yashirya zuwa kai application dinsa

Saiya wa umma sallama Yakama hanya



Bayan yakai akace za anemeshi idan yasamu idan kuma baisamuba zaiji shiru

Yabasu number dinsa

Yatafi gida yana ta aduar samun nasara

Idan Allah yasa yasamu aikin nan zaiyi kokarin raba kubra da gidansu tazo suyita maneji
yasan kubra zatayi hakuri da abinda zaibata umma kuma bata da matsala zasu zauna Lafiya


*****

Professor Abdul Hakeem zaune a office dinsa yana duba wasu takardu sai wata mata tashigo
tagisheshi

Tace wai itace sabuwar sakatariyarsa


Abdul Hakeem yace OK zaki iya tafiya sai na nemeki

Tafita
Tana fita Hakeem yakira management din makarantar

Suna ganin wayar office dinsa
Aka je dasauri Dan yanakirane

Manager nashiga yagaishe da professor Hakeem

Hakeem yace ina buka tar a canza min secretary ma ana bayason mace

Namiji yakeso akawo mishi

Manager yace angama sir

Hakeem yabashi izinin tafiya

Sukaje suka zauna meeting

Nan akayi shawarar daukar SHAMSUNDEEN SULAIMAN a matsayin secretary na THE
YOUNG PROFESSOR ABDUL HAKEEM



Yaya shamsu yana kofar gidansu kubra yaje zance
Sai yaga kira da bakuwar number

Yayi picking call din

aikuwa kubra taga yana ta fara a yana godiya
Bayan ya kashe wayar ne

Ya kalli kubra yace kiyimana murna munsami aiki kinga kenan burinmu yakusa cikako

Cikin tsananin farinciki kubra tace alhamdulillahi
Gobe zafara azumina kenan

Da mamaki shamsu ya kalli kubra yace azumin mekuma zakiyi

Kubra tayi murmushi tace aina wa Allah alkawarin cewa duk randa kasamu aiki sainayi azumi
uku cas

Shamsu yace aikuwa bazakiyi kekadaiba tare zamuyi

Nan dai yamata sallama ya wuce gida Dan yasanar wa umma


**
Umma tayi farinciki sosai haka ma mahaifinsa

Husnah kuwa tsalle taringa yi tana murnar ankusa kawo musu anty kubra gidansu

Mahaifinsa yace gobe zaka fara zuwa kenan
Yaya shamsu yace a daga gobe sukace wai karfe takwas zandinga zuwa

Sainaje ma zasubani dokokinsu

Nan iyayen sukayi ta albarka


Washagari yaya shamsu yashirya zuwa wajen aiki

Bayan yayi sallama da su umma

Ya wuce gidansu kubra itama tamishi adawo Lafiya



Yana isa aka gama komai aka turashi office din PROFESSOR HAKEEM


yana zuwa yayi nocking akace yashiga

Professor Hakeem yanakan kujerar shi yana fama da wasu takardu

Shamsu yashiga yagaisheshi professor Hakeem ya amsa batare da kalleshiba

Yace ta akayi malam

Shamsu yace daman nine sabon secretary din da aka turo office dinka

Professor Hakeem yace OK dafatan zamuyi da gaskiya malam

Shamsu insha Allah sir

Sai alokacin professor Hakeem yadago kai ya kalli ya shamsu

Yace ko zan iya sanin sunan malamin
Yaya shamsu yayi murmushi yace Shamsuddeen

Hakeem yace malam shamsu Allah yatayaka riko za iya tafiya

Shamsu yayi godiya yace nagode sir


Ya wuce abinshi professor Hakeem yacigaba da aikinsa

Can wajen shabiyu da rabi professor Ahmad yashigo office din Hakeem yace ya man muje muyi

lunch kasanfa bana jure yunwa

Hakeem yayi murmushi yace wai damma ka kusa shiga daga ciki
Aisha Nada aiki wallahi sai dai ta ringa samaka wani flask



Ahmad yayi dariya yace ai dani dakai duk jirgi daya yakwàso mu

Nan dai Hakeem ya tattara suka fito tare Hakeem yakalli shamsu dake kan kurarshi yace

Abokina zamufita ga key din office din take care

Shamsu OK adawo Lafiya



Suna zaune a gurin cin abinci Ahmad yace waini wannan Dan gayun ne sakatarenka

Hakeem yace kaima kaji mamaki ko

Da naso namishi tambayoyi sai naga rashin dacewar hakan gwamma nagama fahimtarshi kafin

Naji tarihinsa

Ahmad yace hakan ma yayi
amma mutum very responsible person kaman wannan ace yana sakatare


Shamsu yashiga office din maigidan nashi yaga kudi a kasa
Ya dauka ya ajeye mishi a saman tebur



Bayan su Hakeem sundawo yashiga office din sa
Sai ya kalli inda ya zubar da kudi yaga babusu
Dan dama da gangan yayi hakan Dan ya gwada shamsu ne kawai

Yazauna akan kujerarshi aikuwa idonshi yakai kan kudinshi da shamsu ya ajiye mashi su

Professor Hakeem yayi murmushi akaro na farko
Yaya shamsu yashiga ranshi

Karfe hudu dai dai Hakeem yatashi a office dayafito yaga kujerar da shamsu yake yaga yana
waya ne amma yanaganin fitowar Hakeem yawa kubra sallama

Hakeem yayi murmushi yace hala kaida uwargida kuke wayar kuma ka kashe

Yaya shamsu baice komai ba sai murmushi kawai

Hakeem yace natashi kaima zaka iya tafiya

Shamsu yace aisunce wai sai time din tashi yayi zantashi

Hakeem yace no zan musu magana kaje kawai abinka

Hakeem har yayi gaba ya dawo yace sunbaka kudi kuwa
Ya shamsu yace wani kudi kuma nida nafara aiki yau sir yakarasa yana murmushi

Hakeem yayi murmushi yace yakamata subaka kudin daukar aiki

amma zanbaka aro idan anbaka sai ka dawo mundasu ko

Ya shamsu yayi dariya kabarshi kawai sir kar azo basu baniba

Hakeem yayi murmushi yace idan basu baka na barma

Kuma banason musu yashiga tsakaninmu malam shamsu ka karba kawai karmuyi haka dakai

Shamsu yakarba yace nagode yallabai


Yace karka damu

Sai gobe kayi kokari ka koma gida


Shamsu yasake baki kawai yana kallon Hakeem

Yaduba damin kudin da Hakeem yabashi

Nan dai yayi wa Allah godiya cike da farinciki shamsu ya kulle kofar office din su

Yayi gida

Yana zuwa Husnah ta tareshi da murna oyoyo yaya na sannu da dawowa

Shamsu yayi dariya yace yauwa yar kanwata ina umma

Ummu ta fito daga daki tana daura dankwali tace a a dawuri haka

Yaya shamsu yace wallahi Allah ne ya hadani da shugaba nagari yace karfe hudu ma ina iya
tafiya


Umma ta ce alhamdulilla ai haka akeso
Yaya shamsu yace umma ina Abba tace yanzu zaishigo sunje gaisuwar Mara Lafiya shida
malam tanko

Kafin tarufe baki ma sai ga Abba yayi sallama yace a a Dan albarka har andawo

Nan suka zauna kan ta Burma yafito da kudin ya ajiye gaban mahaifinsa

Nan yamusu bayanin komai

Abba yayi gyaran murya yace to yanzu idan akazo ba a baka kudin daukan aikin bafa

Ya shamsu yace nima haka nagani dai
Na nuna yabar kudinsa kawai yace aishi yabani

Umma tace to kaidai duk inda kake ka tabbatar karike gaskiya kazauna da kowa zuciyarka daya

Ya shamsu yace insha Allah
Zankiyaye

Nan dai Abba da umma sukace baza a taba kudinba harsai

anbaka angani koba hakaba yaya shamsu yace hakan ma yayi gaskiya

Husnah tace Abba kawai da yaya shamsu yayi anfani da kudin gurin kai sadakin anty kubra

Koba a bashi tunda yana aiki saiya biyashi a hankali

Abba yayi murmushi yace uwatakenan ke yarinyace har yanzu bakisan duniyaba

Indai aure ne ai zaiyi insha Allah

Suka ce Allah yasa

Bayan kwana biyu ranar alhamis ya shamsu yaje wurin aiki aka kirashi akabashi kudin daukar
aiki naira dubu goma shabiyar

Da yadaqo gida yace wa ma haifinsa ambashi yanuna musu

Abba yace alhamdulilla kaga gobe saika mayar mashi da kudinsa

Allah yayi albarka ya shamsu yace ameen Abba

Abba yace yakabar kudin kuma anan
Ya shamsu yace Abba kayi abinda yadace kawai

Abba yace wa umma tadebi kudin ta ajiye agunta



Washagari ya shamsu yasami professor Hakeem a office yamishi bayani yamayar mashi da
kudinsa

Hakeem shi har ya manta ma yaba wa ya shamsu kudi

Ba karamin burgeshi ya shamsu yayi ba
Yace
Gashi kasiya wa yara sweet

Ya shamsu yayi dariya yace ai banida aure

Hakeem yakalleshi yace

Malam shamsu idan bazaka damu zanso jin labarinka




Next page

Your comments is needed
Fan's


[05/05, 11:08 AM] UMMU AFAN :



BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN


FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION

F.C.T.W.A



HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITERS OF THE NATION



DEDICATE THIS PAGE TO UMMU HANIF


6 / 15