Author : Ummu Afan Category : Arewa Hausa Novels
Sai dai adduar da akeyi lokacin da miji zai sadu da iyalinsa
ai kuwa dai Laila tafada musu
Tagane shayi ruwane
Yanagama abin da zaiyi ya tureta ya kwanta abinshi
Ita kuwa Laila tana cikin farin ciki Dan ita yadda taji din ne kuma bazata iya hakuriba """""
Kullum zata kawo kan nata indai zai biya mata bukatarta kafin ta shekashi lahira taci dukiya
Nan itama ta kwanta bacci ya dauketa cike da farincikin kasancewarsu da Hakeem a Daren
nan .
Washagari Hakeem kota kanta baiyiba yana gama shirinsa cikin wata yadi mai tsadar gaske iri
daya ma sukayi da Ahmad
Yadin ash colour ne sai yasa bakin takalmi da hula Wanda akekira da senator
Duk Wanda yakalli Hakeem sai yasake kallonsa Dan ya hadu iya haduwa
Yana fitowa Laila ta tareshi tace abdul ga break fast dinka fa mai aiki tagama ,
Wani matsiyacin kallo yamata yace kinga nayi miki kama da mai cin abincin masu aiki """
Ban guri nawuce ni
Tabishi da kallo tace aikuwa sai dai idan bazaka ci abinci agidan nan ba Dan ko kwai ban iya
soyawa tayi dadi batare da ya kone ba """
Hakeem suna break fast daddy yace mishi
Shi Ahmad din yashirya kuwa Dan naga kaman kai ka matsa kutafi
Hakeem yayi dariya yace bahaka bane dad kasan fa I want to be come professor like you kaga
yakamata indage ko dad
Daddyn Hakeem yace hakane but please son take care of your self sosai kaji ko banda harka
da mutanen banza """
Mummy tayi murmushi tace kai daddyn Hakeem duk komawarshi school saikayi mishi wannan
nasihar yanzu fa babban mutum ne tunda ya ajiye iyali
Daddy yayi murmushi yace wai haka son
Shidai Hakeem baice komaiba
Daddy yace nifa wallhi ina mantawa yarinyar nan tana cikin gidan nan
Ya bara kace tazo akarya da itaba .
Hakeem yace daddy ai tana da mai aikinta har tagama komai sunci abincinsu
Daddy yace duk da hakadai ai itama yar gida ce
Mummy tace kasan alamarin yara sai a hankali
Kawai kabarsu nan dai mummy ta canja magana
Tace jirgin safe zakubi ko
Abdul Hakeem yace da asuba makuwa mummy tace aikuwa kaman nasani nagama hada ma
komai
Mummy Allah yasa kinmin wanna cake din naki medadi
Tace ai duk abinda kasan ina maka ba abin da na rage
Cikin jin dadi Hakeem yace that's my mom Allah yabar minku iyayena
Daddy da mummy sukace ameen Allah yamaka albarka
Yauma da daddare sai da Laila takai kanta gurin Hakeem
Tun karfe uku yatashi yagama shirinsa tsaf bai Dade da gamawa ba Ahmad ya kira yace man
kataho tafa nigani a air port ma
Hakeem yace OK gani nan
Yadauki cheque ya rubuta dubu Dari biyar yasama Laila akan bed
Da kuma short note
Yafita daddy da mummy shi kawai suke jira suka rakashi
Next page
Your comment is needed fan's
踫踫踫踫踫踫
[30/04, 5:49 PM] UMMU AFAN 潤撕: 踫踫踫踫踫踫
潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤
BISSIMILLAHI RAHMANIR RAHIM
潤HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN潤
DEDICATE THIS PAGE TO MY ONE AND ONLY HUSBAND
ABU AFAN (DOCTOR SULEIMAN)欠踫
潤GORGEOUS WRITERS FORUM潤
潤G.W.F潤
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPAERT WRITER'S WE ARE THE BEST
AMONG THE REST
潤AKWAI LOKACI潤
潤PAGE 26 to 30 潤
Laila ta tayi taga ba Hakeem
Sai ta tashi tashiga tayi wanka tana fitowa idonta yakai kan takardar da ya ajiye mata
Tadauka ta duba taga cheque ne na kudi """""
Nan da tawashe baki tace kai tun yanzu bata gama rufe baki ba taga wani guntun takarda .
Tadauka taduba
Cewa yayi Nina wuce ga kudi nan
Idan kina bukatar wani Abu zaki iya samun mummy
Laila na gama karantawa ta wurgi da takardar tace kutuman uba Ashe tafiya yayi yabarni anan ,
Nida nake ta burin tafiya Saudi
Ashe ma badani zaitafiba """
Tadauki wayarta takira hajiya rukayya
Tanadawa Laila tafashe da kuka
Hajiya rukayya tace Lafiya kike kuka Laila cikin kukan Laila tace mama kinsan
Abdul Hakeem yakoma Saudi yau """
Maman tace yakoma fa kika ce
Lalle ma yaron nan wato badake zai wuce ba kenan """"
Laila tace ai niban Masan yatafi ba rubuta min yayi
amma yabarmin dubu dari biyar yace kuma idan ina bukatar wani Abu na sami mummynshi ,
Hajiya rukayya tace aikuwa sun ja wa Kansu
Nan da jibi kice kina bukatar kudi
Kinga sai musamu mufara shiri kafin yadawo ,
Laila tace to mama wallahi amma naji haushin rashin tafiya dani din nan dayayi ,
Hajiya rukayya tace kwantar da hankalinki zai dawo ne ai zai shigo hanunmu daga shi har
iyayensa .
Yanzu zanzo gidan naki nakarbi kudin na ajiye su a wajena
ai gwamma ma da yatafi abinsa kinga matara kafin yashigo hanu mu kawar dashi banza"'''''
******
Bayan kwana biyu Laila taje gidansu daga nan itada mahaifiyarta suka wuce gidan hajiya
suwaiba wato kakan Laila kenan ,
Suna isa hajiya suwaiba takira hajiya larai kishiyar suka shige can dakin hajiya suwaiba
Laila ta kwantar da kanta akan cinyar kakarta
Nan hajiya rukayya tafada musu komai abin da Hakeem ya ma Laila
Hajiya suwaiba tashafa kan rukayya tace hakuri kinji jikalle zai shigo hanun mu ne kinji ko ,
Dazaran yashigo hanun mu sai yadda kikayi dashi kinji ko
Cikin jin dadi Laila tace Allah yasa haka kakalle na
Dakuwa kinga gata Dan sai na canja maki gida kekadai basai da wannan tsohon ba
Hajiya rukayya tace a lalle ma uban nawa ko
Hajiya larai tace Dana dashi aka ware
Hajiya suwaiba tace a dinta ji anwarekun
Nan dai suka ta kulla tsiya
Sai can wajen karfe goma na dare kafin Laila ta tashi tayi hanyar gida
Dan dama ita tasaba da driving din dare ,
tana shiga maigadi yabude mata gate din yana gaisheta ko ta amsa mai .
Tana parking sai daddyn Hakeem yafito yace Laila daga ina a wannan Daren haka
Laila tace daddy daga gidansu alhaji nake a can na wuni .
Daddy yagane wani alhaji take nufi wato alhajinsa,
Yace kin tabbata tace a daddy kakira ma katambaya
Yace a a shikenan karkisake kai dare a waje haka kinji ko tace naji Daddy
Yace maza wuce dakin kin dare yayi
Namishi saida safe
Tana shiga falonta tayi wurgi da gyalenta tace nifa bana son sa ido haka kawai mutum yafita
amma ana gadinsa
*****
Bayan wata biyu Laila ce kwace cikin lallausar kujerun falon Hakeem tana kallo
Sai tafara jin tashin zuciya
Ta tashi tayi hanyar bathroom tafara amai sosai take amai kaman zata fitar da kayan cikin ta
Kanwarta suby wacce taci sunan hajiya suwaiba ce tazo
Tana ta sallama amma shiru
Dan tunda Hakeem ya tafi suby tadawo gidan gurin yarta ,
Itama dai duk halin nasu dayane da yaruwarta
Taje siyo wa Laila balangune a bakin titi
Taduba bedroom din Laila bata ganta ba tace anty Laila da karfi
Can ta duba bathroom din falon Hakeem aikuwa nan taganta tayi sharaf ,
aikuwa suby ta rude ganin yar uwar tata a kasa jiki ba karfi tadauki waya takira uwarsu hajiya
rukayya tafada mata tace gatanan zuwa
Can dai taga karfa Laila ta mutu Dan haka sai ta
Tashi tayi hanyar part din mom din Hakeem
Mummy hafsat tana kitchen Dan daura abincin rana sai taga suby kaman anjifota
Tace lafiya kuwa suwaiba zakishigo ba sallama
Suwaiba tace kiyi hakuri mummy anty laila ce balafiya ,
Mummy hafsat tace meyasameta tace wallahi bansaniba nima naje aika kafin nadawo
nasameta a haka
Mummyn Hakeem tace wace muje naganta
Wannan shine farkon shigowar mummy hafsat part din Dan nata
Kusan atare suka iso da Maman su Lalai hajiya rukayya
Mummy hafsat tace a a yaya ashekema kinzo
Hajiya rukayya tace a gani nan ai
Mummy hafsat tace bara na dauko mota akaita asibiti ko
Hajiya rukayya tace duk yadda kikayi
Mummy hafsat tace afito da ita mutafi ko
Hajiya rukayya ta kalli mummy hafsat wato ita bazata kamata afita da ita ba sai dai tabasu
command
Hajiya rukayya da suby suka kama Laila zuwa mota
Mummy hafsat ita taja motar zuwa hospital
Bayan gwaje gwajen da aka wa Laila likita yagano tana da cikin wata biyu
aikuwa hajiya rukayya da suby dama ita kanta Lailar murna suka hauyi sosai ko kunyar
mummy hafsat basaji
Itadai mummy hafsat tunda doctor yace Laila cikine da ita
Bata ce komai ba tausayi kawai danta yabata hada zuria da irin hajiya suwaiba
Nan dai tana ta tunanin zuci
Hajiya rukayya tace hafsat bakice komai ba zamuyi jika mummy hafsat tayi murmushi kawai
tace Allah yaraba lafiya
Yanzu dai bari na sami doctor nabiya komai sai muzo muwuce gida
Hajiya rukayya tace ai inaganin zan wuce da ita gida kawai idan tasamu lafiya sai ta koma
dakinta
Mummy hafsat tace badamuwa hakan ma yayi zama Ku iya bari saita haihu sata dawo
Hajiya rukayya maganar mummy hafsat yamata zafi sosai wato subasa ma bukatar zaman
Lailar agidan kenan
Hajiya rukayya tace tokuma idan mijinta yadawo fa
Mummy hafsat tayi dariya tace ai daga har ta haihu son bazai sami damar zuwa ba
Hajiya rukayya tace duk karatun ne zaisa yaki dawowa gida
ai yanzu idan kika kirashi kikafada mishi zai iya samin lokaci yazo yaga matarahi kafin yakoma
ko
Mummy hafsat tace sai dai nabaku numbar nashi ita lailar saita kira tafada mishi
Cike da jin haushi hajiya rukayya tace ai ashikenan takira tafada mishi da kanta
Mummy hafsat tace dayafi dai bara na biya kudin nazo mutafi ko
Hajiya rukayya tace a a kibarshi kawai driver na zaizo yanzu yamaida mu gida
Mummy hafsat tace to Allah yabata lafiya ni na wuce
Laila tayi saurin cewa mummy baki bani numbar abdulhakeem dinba
Mummy tace OK kawa wayar taki na samiki
Laila Tamika wa mummy hafsat wayar
Nan tasamata numbar HAKEEM
Laila tace thanks mom
Mummy Hakeem tawuce abinta
aikuwa tana fita hajiya rukayya tace zanyi maganinkine
Muza ayi wa wulakanci duk abin mutaum dai
Ciki dai sai an haife shi tsaf
Ta kalli Laila tace kekuma harda wani godiya Dan anbaki numbar mijinki
Suby tayi dariya tace kai mama kaman Bakisan halin anty Laila ba
Tasan metakeyi fa
Laila tayi dariya tace Haba mama anfada miki Dan Allah nayi godiyar caf
Nan dai sukayi gidan hajiya suwaiba suka shaida mata abin farin
aikuwa harda gud'a hajiya suwaiba tayi Dan murna tace kaman muzuba ruwa a kasa musha
Dan dadi
Hajiya rukayya tace kinga yanzu saimuyi addua ta haifi namiji Dan mukasa mutsare gidan
aikuwa hajiya suwaiba tace ai namijin ne ma zata Haifa kuzuba ido kugani
ai tunada wuri zamuje gurin malamin nan yabamu taimako
Haka dai sukulla wannan su kulla wancan
*****
Mummy hafsat bayan daddy ya dawo gida ta shaida mishi abin dake faruwa
Daddyn Hakeem yace kai amma naji dadi Allah yaraba lafiya
Kice son dina yagirma fa
Harda da d'a
Mummy dai bata ce komai ba
Yace ai sai a tura musu kudin dazai ishesu kula da ita abin da kecikinta
Mummy hafsat tayi murmushi tace hakane
Nan daddy yakira yayarshi wato hajiya rukayya maman laila
Tana ganin kiran daddyn Hakeem tasan sunwarke Dan tasan zai jikasu da kudi
Nan da nan tadaga wayar daddyn Hakeem yafara gaisheta kafin yace yaji abin farinciki Allah
yaraba lafiya
Sannan kuma inason kuturo da account number dazanturo muku da abinda zatayi anfani dashi
aikuwa farinciki Yakama hajiya rukayya tace yanzu kuwa zanturo
angode fa Allah yakara arziki
Tunda yake bai taba jinta tamishi godiya ba sai yau yace bakomai
Mudai fatanmu dai Allah yarabasu lafiya
Ameen hajiya rukayya tace takashe wayar nan da nan taba wa suby wayar tace ta tura wa
daddyn Hakeem account number din Laila
aikuwa suby bata Dade da turawaba sukaji alert din dubu Dari takwas cas
aikuwa murna awajen su kaman me
Hajiya rukayya tace wanna ma ai kadanne ne
Dan nasan nan da wani lokaci zai kara mana
Nan dai Laila ta dauki wayarta takira Hakeem sai da yayi ta ringing kafin yadauki
Tare da sallama cikin kwarewa da harshen larabci Dan bazaka kadauka bahaushebane
Can yace dawa nake magana please
Cikin sauri Laila tace Laila ce
Hakeem yace inajinki ya akayi
Nan tafada mishi what's kina da ciki
Laila tace a mummynka cema takaini asibiti
Hakeem yaja numfashi yace Allah yasauke ki lafiya daga haka baikara cewa komai ba yakashe
wayarsa
Laila tabi wayar da kallo ta kalli mahaifiyarta tace mama kodai shima baya farinciki da cikin ne
Suby tace kai bahaka bane kinsan halin ya Abdul yanzu hakama murna ne yasa yakashe wayar
Hajiya rukayya tace komai dai menene shine dai uban d'a
Da su so da karsu so duk uwa ubansu daya can ta matse musu
*****
Hakeem bayan ya kashe wayar ya kalli Ahmad dake fire musu doya
Dan basa cin abincin waje
Yace man kasan meye kuwa
Ahmad yace saika fada
Hakeem yace wai Laila cikine da ita har na wata biyu
Cike da farinciki Ahmad ya ajiye wukar yadaga hanu sama
Yace Allah mungode maka
Wai mune zamu baba
Hakeem ya watsa mishi harara
Yace dadina da kai Ahmad yarinta wallahi
Ahmad yace nayarda yarinta nedan gaskiya kam yanzu fa ka girmeni tunda gashi kana shirin
ajiye baby
Hakeem yace please man muyi maganar arziki mana
Nifa harga Allah banso samun da daga jikin lailaba
amma tunda Allah yabani Allah ya albarkaci abinda za a Haifa
Ahmad yace adduar kenan kawai
Allah yashige mana gaba
Nan Hakeem yace ameen
*******
Bayan wata bakwai
Abubuwa da dama sunfaru
Su hajiya dai an tatsi Daddy Dan abin kadan zasuce a turo kudi
**
Yau laraba Laila ta tashi da nakuda
Sukayi da ita hospital
Nan da nan aka shiga da ita labour room
Mummy hafsat itama ana fada mata tazo asibitin daddy ne yasauketa kafin yawuce office
bayan kaman awa hudu da shigarta
Ta haifo yarinyarta maikama da ita sak
Aka gyarasu itada babyn kafin akazo sanardasu mummy
ana ce ta haihu sukayi cikin dakin dasauri banda mummy hafsat
Tace wa likitar me akasamu likita ta癟e mace
Mummy Hafsat tace Allah yaraya
Takira daddy tafada mishi
Yace gashinan zuwa
Su hajiya kuwa ganin Allah baicika musu burinsuba yasa sukacika tam kaman zasu fashe
amma ganin yadda daddy yake farinciki da samunjika yasa suka kwantar da hankalinsu kadan
Nan daddy yakira Hakeem yafada mishi Hakeem yace Allah yaraya Daddy yace Ameen
Ameen
Yakamata kasamu lokaci kazo kaga yarinyar da ita Lailar ko
Hakeem yace ai daddy bayanzu Dan karatu yafara zafi sosai sai dai mumsami time zanshigo
Daddy yace Allah yamuku albarka inashi Ahmad din
Hakeem yace yashiga wanka
Nan sukayi sallama da daddy
Ranar suna yarinya taci sunan maman daddy wato amina
Mahaifiyar daddyn Hakeem kenan marigayiya
Alhaji shuaib yasaka sunan da kanshi ba ma daddynba
Haka Laila tacigaba da rainon yarta Amina
*********"********
Tofa
Yanzu akafara kubiyo ummu afan
Your comment is needed fans踫踫踫踫踫
踫踫踫踫
[30/04, 5:51 PM] UMMU AFAN 潤撕: 踫踫踫
潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
潤HAKKIN MALLAKA NA UMMU AFAN潤
DEDICATE THIS PAGE TO MY ONE AND ONLY HUSBAND ABU AFAN (DOCTOR
SULAIMAN)欠踫
潤GORGEOUS WRITERS FORUM潤
潤G.W.F潤
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WE ARE THE BEST AMONG THE
REST
潤AkWAI LOKACI 潤
潤PAGE 31 to 35潤
Laila kwance take tana danna wayarta
Yayinda hajiya rukayya takeba wa Amina cerelack
Hajiya rukayya tace kinga wasa