Author : Ummu Afan Category : Arewa Hausa Novels
í ¼í¾—AKWAI LOKACIí ¼í¾—
í ¼í¾—PAGE 46 to 50í ¼í¾—
PROFESSOR HAKEEM yace ina sauraronka malam shamsu
Ya shamsu yayi murmushi nan yabashi kadan daga cikin tarin rayauwarsu
Hakeem yace kace kai din dai har yanzu dai gaurone murkusheshen gaurone
Ya shamsu yayi murmushi yace a nakusa fita a layin gaurayen tunda nasamu abinyi
Hakeem yace hakane
Ya kalli kudin da ya shamsu ya ajiye mashi akan tebur
Yadauko wani rafar ya hada mashi dasu yace
Kadauki wannan kudin kaje kamuku cefane
Sannan kuma ka Isar min da gaisuwata wajen Abba da umma
Da kuma yar kanwarmu
Ya shamsu yace amma ai kudin sunyu yawa yallabai
Hakeem yayi murmushi yace karkadamu
Malam shamsu kana da sha awar cigaba da karatu ne
Shamsu yayi murmushi yace
Zanyi kokari bayan aure na ga nasamu ko degree na samu insha Allah
Hakeem yace Allah ya nuna mana ya shamsu yace nagode Allah yasaka da alkairi
Hakeem yace godiyan yana yawa kuma.banason godiya malam shamsu
Ya shamsu yayi murmushi yace ai ka canci hakan ne yallabai
Nan dai suka Dan taba hira har lokacin tashin Hakeem yayi suka tafi shida Ahmad
Ya shamsu kuwa yana fita yaje kasuwa yamusu cefane sosai har kaji da lemuka masu sanyi
Yana isa kofar gidansu mai adai daita sahu ya tsaya yabiyashi yafito da ka yansa
Yashiga cikin gidan da sallaman shi
alokacin Husnah tana alolar La asar
Tana ganinshi ta karasa wanke kafarta ta zo takarbeshi tana mishi sannu da zuwa
Yace alolar mekikeyi tace LA asar ya shamsu yace haba Husnah yazaki bari lokacin sallah ya
wuce kina da lafiyanki
Kafin tayi magana umma daga kitchen tace ai yau Husnah bataji dadiba ne
Tun da tadawo daga makaranta take kwance kanta naciwo
Ya shamsu yace ashsha barin je nasiyo miki magani
Yanzu zandawo
Husnah ta rike rigar ya shamsu tace wallahi naji sauki yaya
Dama abin da ya haddasa min ciwon kan ma
Wani taro akayi a school dinmu kuma nice presenter
Hayaniya ce yasani ciwon kan amma Dana dawo gida umma tabani magani nasha na kwanta
yadaina
Ya shamsu yace kinta tabbata
Husnah tadaga kai alamun ta tabbatar
Abba ne yayi sallama yashigo
Da Leda a hannunsa Husnah ta ajiye Wanda ya shamsu yakawo akan taburma tayi saurin
karbar na Abba alkamace Abba ya auno Dan Abba akwai son tuwon alkama dashida ya
shamsu
Bayan sun zauna ne ya shamsu yace Husnah dauko kayan can kiraba mana
Husnah ta tashi ta dauko
Plate guda uku da tasawa Abba kajin da kuma Irish potato wato dankalin turawa
Ta ajiye mashi maltina Dan tasan zaifi sonshi
Kafin tasawa umma itama maltina tamata
Sai ta hada musu itada ya shamsu ta dauki lacasera
Ta dauka wa ya shamsu fanta dantasan abinda kowa yakeso
Umma ta ce yau fa shagwaban yatashi Abba yace a din tayi baruwanki ai sunfi kusa yakarasa
maganar yana dariya
Husnah tace yauwa Abba fada mata dai
Ya shamsu yayi murmushi Dan yanason yadda suke rayuwarsu cikin son juna acikin gidansu
Suna gamawa Husnah ta tashi tadauko Dan karamin kula tasaka naman da komai yadda
sukasha sai wannan lemu sunkai uku
Tasaka a Leda tace ya shamsu wannan na anty kubra ne idan kaje kace mata inji sweet
kanwarta
Umma tace kai wannan soyayya da Husnah takewa kubra
Inba auren nan akayi ba hankalin Husnah bazai kwanta ba ba
Abba yace ai soyayyar Dan uwantane yashafi khadijan
Husnah tace gaskiya Abba kana da ganewa wallahi yadda anty kubra takeson ya shamsu yasa
na ke ganin girmanta
Shidai shamsu inbanda murmushi ba abinda yakeyi
Nan yawa mahaifinsa da ummansa bayanin yadda sukayi da maigidansa
Abba yace Allah yasa hakan shine mafi alkairi
Kaga girman alkawariko
To haka akeson mutum aduk inda yake ya rike gaskiya
Ya shamsu yace hanekam
Nan yabawa mahaifin nasa kudin gabadaya yace ya ajiye agunsa
Ya tashi yashiga wanka Wanda Husnah ce takai mai yana fitowa yayi alwala zuwa sallar
magriba
Bayan ya dawo daga isha ne yadauki kayan da Husnah tabashi yakaiwa kubra
Ya fesa turarensa mai Dan arha duk da talaucin su ya shamsu baya rabuwa da turare danshi
mutum ne mai tsafta sosai Dan gado sukayi a wajen iyayensu
Saikuma Husnah tace matsa kaban guri akan tsafta kokadan Husnah bata son datti
Yana isa gidansu kubra ta fito da hijabinta dogo
Duk yadda takai taboye abinda aka mata agida kubra takasa sai da yagane
Yace Lafiya naga fuskarki haka kubra
Kubra tayi yake tace bakomai wallahi abune yafada min a idona amma nacire
Kafin ya shamsu yayi magana wata kanwarta wadda suke uba daya tazo tace wai kizo inji
mama kicigaba mata da abinda tasaki
Kubra tace kice inzuwa yarinyar tajuya takoma zuwa cikin gidan
Tausayin kubra Yakama shamsu sosai yace kiyi hakuri kinji watarana sai labari nasan duk
akaina kikaganin wulakanci Dan kin ki bada hadin kai
amma namiki alkaqarin komai yazo karshe insha Allah
Yace karbi wannan inji kanwarki tace nakawo miki
Kubra tace Allah sarki Husnah Dan Allah kace mata nagode sosai
Yaciro dubu uku a aljihunsa yace karbi wannan kirike a hanunki
Kubra ta kalleshi ta kalli kudin tace haba sahibina ya daga samun aiki zaka fara barna da kudi
kawai kabarshi
Yace ai duk abinda zansamu kina da kaso aciki kikarba kawai kubra idan baki karba ba zaki
bata min rai
Cikin sanyin jiki kubra ta karbi kudin
Tace nagode Allah yakara budi yace amin
Maza koma gida kikarasa abinda aka saki karkiyi laifi ko
Tace to sai anjima ko kuma saigobe ba inji ya shamsu
Washa gari dasafe ya shamsu yagama shirin zuwa aiki bayan sun karya
Yafito yace wa Husnah muje ko
Husnah tace to yaya suka wa umma sallama
Suna futa kuwa suka yi sa ar keke napep yaya shamsu yatare musu sukashiga
Suna tafiya suna hira yace inga jakanki tabashi bata kawo komai a ranta ba
Ya shamsu kuwa yafaketa yasaka mata 1000 a ciki dubu daya kenan
Suna zuwa dai dai gate din su Husnah ya shamsu yace wa driver tsaya ta sauka nikuma kayi
dani BUK Husnah tasauka tana daga wa ya shamsu hanu
Yayi dai dai dannowar motar copper bash
Yaji lokacin datace ya shamsu kanan ya shamsu ne acikin keke napep din nan
Inkuwa shine zanbisa namishi bayanin komai
aikuwa copper bash yayi ta bin yaya shamsu abaya har yasauka a gate din BUK
Bayan ya shamsu yabiya kudin yayi gaba abinsa
Copper bash yayi parking yafito
Yabi bayan ya shamsu
Har yaje yayi signing yazo kafin yaje can kujerashi kofar
PROFESSOR HAKEEM yazauna
Copper bash yamishi sallama ya shamsu ya amsa yace kozan iya taimakonka
Copper bash yace a daman taimakon nazo nema
amma a gurinka ya shamsu
Yadda copper bash yakirashi ya shamsu yasan duk yadda akayi yasanshi ne
Ya shamsu yanuna mishi kujera
Nan copperbash yafada wa yaya shamsu irin son da yake wa kanwar shi
amma taki bashi dama hakan
Ya shamsu yace bazata ta taba amince maka har sai nabata izini
Umarni nabata nima kuma bazan taba amincewaba har sai nayi bincike akanka kafin nan kuma
na tabbatar tana sonka na uku kuma zakamin alkawarin barin ta tayi karatu bayan kinyi aure
amma wannan zaizone bayan nayi bincike nagar tarka
Copper bash yace wallahi ya shamsu indai akan asali ne bana shakku aje ayi bincike fata na
kawai idan kabincika bani da matsala ka amince min nakawo sadakina gidanku shikadai ne
zaisa hankalina yakwanta
Ya shamsu yayi murmushi yace karka damu Allah yashige mana gaba
Nan yawa ya shamsu sallama yatafi
*******
HUSNAH zaune kan kujerar class dinsu teacher din dazata shiga musu ta haihu shiyasa suka
samu Free time
Meenat tace gaskiya Husnah baki da kirki yanzu kakan dad dina da mummy na ya mutu amma
kikasa Neman gidan mu kije kiwa kakata ta aziyya
Husnah tace afuwan aminyi insha Allah ranar asabar zanzo gidanku nawa kakanmu ta aziyya
Meenat tace kai amma danaji wallahi har na matsu asabar tayi
Hajiya ta taganki labarinki kawai takeji agurina
Husnah tace aikuwa zanzo nagaisheta
Tace amin Allah yasa daddy ma yazo sai kigaisheshi
Kinsan tun yadawo kano aiki duk Saturday yake zuwa yaganni
Husnah tace to Allah yakaimu ranar
Suna haka wata junior tashigo tace anty husnah wai kizo inji uncle bash
Husnah tace OK kice ganinan zuwa
Meenat ta kebe baki tace wai meke tsakaninku da copper bash ne
Husnah tace sirrine amma zakiji nan gaba tashi muje kirakani kawai
Meenat ta tashi jiki a sanyaye tabi Husnah zuwa office din uncle bash
Suna shiga suka gaishe da bash ya amsa idonsa akan Husnah
Takaici Yakama meenat
Dan ita ba namijin datakeso irin copper bash
Tayi shishigin amma bata samu karbuwa ba
Ya kalleta yace zaki iya jiranta a kofa magana zamuyi
Meenat cike da bakin ciki ta fito
Copper bash ya kalli Husnah yace munhadu da ya shamsu
Cikin sauri husnah ta dago kanta da sauri tace meyace maka shikenan nasan yaya zaiyi fishi
dani
Copper bash yace karkidamu ba abinda zai miki shima naga alama yana da fahimta
Nan yafada mata yadda sukayi da ya shamsu
Cike da jin dadi Husnah ta tashi tayi hangar waje
Yana kiranta amma taki juyowa saboda kunya
Tana shiga sukacikaro da meenat
Kuka shabe shabe a fuskar meenat
Husnah cikin tashin hankali tace lafiya kuwa meenat cikin rashin sanin mezatace tafara in inna
Tace wallahi bansan menayi wa copper bash ba ya tsani yaganni aguri sai yakoreni
Husnah tace kiyi hakuri zanmishi magana kuma I sha Allah zaiyi dai dai
Meenat ta share hawayenta tace Husnah na tambayeki meketsakaninku da shi baki fada min ba
Husnah tayi murmushi tabata labarin komai
Meenat tace yanzu kinaso kice min kun Dade kuna soyayya da shi
Husnah tayi murmushi tace a
Amma ni banbashi daman zuwa gidan mu ba
Shine yanzu yake cemin ya wa yayana magana
Meenat tarike kai alamun jiri nason yarda ita
Husnah ta taimaka mata tazauna tace Amina Hakeem anya lafiyarki kalau kuwa
Gaskiya kitashi mu dispensary
Abaki magani
Meenat tace gida ma zantafi tai maka min da phone dina acikin bag
Husnah tabude jakar meenat taga wasu hadaddun wayoyi masu tsadar gaske kuda biyu aciki
Ta kwaso duka tace gasu meenat ta karbi daya takira driver din ta
Taba wa Husnah wayar ta mayar mata dashi jaka
******
Bayan kwana hudu ankai sadakin yaya shamsu gidansu kubra
Sannan kuma Abba yasai block da yashi ma aikata sukafara aikin gyaran inda ya shamsu zai
zauna acikin gidan ne amma ciki da fall da bayan gida acikinshi
Har Dan karamin kitchen dinta basai ta fito tsakar gida ba
Komai nasu aciki yake
Umma da Husnah sukaje kasuwa suka nemo akwatunansu masu kyau guda uku
Aciki akafara zuba kayan lefe
Wanda yanzu kusan duk asabar sai sunfita kasuwa
Dai dai gwargwado dai aka hada lefen ya shamsu
Aka kai gidansu kubra
Nan da sati biyu za adaura auren
Dubu ashirin ya shamsu yaba wa kubra tayi hidiman biki dashi
*****
Hakeem zaune kan kujerar yana hada wani muhimman file
Sai Ahmad yashigo yace wai baka gama ba har yanzu kasan time kuwa
Hakeem yace nagani ai nan da Kaduna dai insha Allah komai dare
Ahmad yace Allah yasa nidai kai nake jira kawai nagama shirina
Hakeem yayi dariya yace bantaba ganin ango merawankai irinka ba Ahmad
Ahmad yayi dariya yace ai gwamma ni kai inkatashi karawa ai bansan dokin dazakayi ba
Hakeem yayi murmushi dayake kara fito da zallan kyanshi
Yace tabbas kuwa lokaci yakusa zuwa inji ajikina nakusa samun choice dina sai dai bansan a
inabane
Ahmad yace kai amma fa akwai rigima Dan madam Laila zatayi rikici bakadanba
Hakeem yayi murmushi yace zatawa kanta danzan iya komai akan matata da zan aura Dan
itace zabina
Kaga kuwa ta taka a sannu
Ahmad yace wallahi man I like your style gaskiya zanso Gina gidana kaman yadda kake
handling naka
Hakeem yayi murmushi yace banbaka shawarar hakanba
Dan na tabbatar Aisha ba halinsu daya da Laila ba
Kagakuwa ba za amusu hukunci iri dayaba ko
Ahamad yace gaskiya Dan hankalin Aishat nagani yasa har nayi shaawar aurenta
Ya shamsu yashigo ya musu sallama suka amsa suka mika mishi hanu suka gaisa
Ya shamsu yace wa Hakeem gani yallabai
Hakeem yace dama zanfada maka ne zamu tafi Kaduna
Sai nan da sati daya zamu dawo
Hakeem yadauko invitation card na auren Ahmad
Yabawa ya shamsu yace muna gayya tarka daurin aure
Ya shamsu yayi murmushi yace masha Allah
Allah yabasu zaman Lafiya
Sai dai ranar yazo dai dai danawa auren
Hakeem yakalleshi yace har ansa rana baka fada minba malam shamsu
Dama bakayi niyyar gayya tarmu bakenan kokana ganin inka fada ma bazamu bane
Ya shamsu yayi murmushi kawai yace aikuna kokari ma da aiki
Kuma har ga Allah bani tunanin inna Baku invitation zakuzoba
Saboda matsayinmu badayaba
Hakeem da Ahmad suka kalli juna
Ahmad yace haba malam shamsu karkace haka saikasa muga kaman mu ba mutane bane
Ya shamsu yace to afuwan
Nayi kuskure
Hakeem yace to yanzu dai bazamu samu zuwaba amma muna maka fatan alkairi
Tace ban account number din ka inbada nawa gudumawar asiyawa amarya kaji
Ya shamsu yace wannan yana daga cikin dalilin dayasa naji fada muku zamanin yanzu kowa
yana fama da kanshi
Dan Allah kabarshi karka damu kanka
Hakeem yace karka damu ni nayi niyya kuma kasan bakyau maida hanun kyauta baya
Ya shamsu yace hakane yakaranto wa Hakeem number account din
Shima Ahmad yanaji kuma ya kwashe number.
Hakeem yace zakaji alert Allah yabada zaman Lafiya
Ya shamsu yace ameen nagode
Sukayi sallama har wajen mota
*****
Da daddare suna zaune tsakar gida ya shamsu yace Abba da ina son ba wa manemin auran
Husnah dama yaturo iyayensa
Kaga tana gama makaranta sai aiyi aurenko
Baban yace ai nalura yaron nan bashir kaman da gaske yakeyi
Umma ta ce sau biyu yana kawo mahaifiyarsa muna gaisawa
Shamsu yace alhamdulillahi gaskiya konina yaba da bashir
Kara shigowar sako yaji a wayarsa yaduba yaga alert ne na dubu Dari biyardaga professor
Ahmad
Kafin yayi magana wani alert din yasake fadowa daga boss dinshi a office
Wato professor Hakeem
Shima dai dubu Dari biyar dinne yaturo
Sun hada mishi 1 million NIRA cas su biyu suka bashi
Nan shamsu yakalli mahifinsa yafada musu
Abba yace kai amma wannan uban gida naka Allah yasaka mishi da alkairi
Umma tace ameen wallahi ko a mafarki bamutaba tunanin samun dubu Dari nan kusaba
Ballantana har million daya Allah yasaka musu da alkairi
Kai kuma saika kazauna dasu da zuciya daya
Nan dai ya shamsu yakira Hakeem a waya yace ga Abba na zai muku godiya
Hakeem yace haba shamsu yanzu saboda kyautar da baitaka kara ya karya ba zaka wahalar
da Abba wajen gode mana
To gaskiya indai Dan inbari Abba yagode min ne zankashe wayata
Insha Allah idan nadawo zanzo nagaisheshi da ka ina amma banda godiya tsakanin malam
shamsu
Ka gaida umma da kanwarmu
Sai da safe
Dif
Hakeem yakashe wayarsa
Dama wayar ya shamsu a handsfree take duk su Abba sunji komai
Abba yace gaskiya duk inda akeneman shugaba nagari wannan yaro ya kai
Allah yarabashi da sharrin duniya Lafiya