Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
kawo wanda ko kallo basu ishi rumana ba
Dan tana arba da ita zafin mutuwar ɗanta ta dawo mata sabuwa,sabida itace silar faruwar komai.
Anata ɓangaren sameera ko tasha alwashin raba rumana da mijinta,dan bazata jure kallonsu a tare ba zatai duk meyiwuwa wajen ganin ta koreta ko ta shiga tsakaninsu.
Batun muamala ta aure kuwa bata kuma gigin kai kanta ba, sabida azabar data sha bata wasa bace.
*********
Watan rumana guda Ashrab ya samu pass a office beyi ƙasa a guiwa ba yadawo gida da laasar cike da farin ciki ya samu sameera zaune tana kallo,
Ga mamakinta,zama yayi kan kujera ya dubeta cikin faraa yace"Ki min list na adadin kuɗin da zasu isheki,yanzu zan wuce kano ne"
"kano kuma?da yammanan sekace korarre?"ta bashi amsa cike da mamakin tafiyar tashi.
Gyara zama yayi yace"rumana ba wasa ba sameera, yanzu zata iya yin fushi dani in banje ba"
Wani zafi taji a ranta amma seta basar tace"to me ze hana muje tare sabida in dubata nima"
Kallonta yayi na ƴan sakwanni sannan yace"baki da matsala inde zakije ɗin inde duba rumanata ne"yana kaiwa nan ya miƙe ya wuce ɗakinshi cikin sauri.
Ko be faɗiba tasan shiryawa yaje yi,hakanne yasa ta miƙe sa gudu itama ta nufi nata ɗakin dan ta shirya gudun ya tafi ya barta.
Basu jima ba duk suka fito a shirye sameera janye da akwatin kayanta.be ko bi ta kanta ba ya kashe duk abinda ya dace suka fice.
Gidan gaba ta hakimce ita ala dole ga me miji ,tada motar yayi suka kama hanya bayan sunyi sallama da me gadi
Koda suka kamo hanya sameera se ziba take tum yana ɗan biye mata har ya gaji yay shuru
Seda suka iso ƙarfi sannan ya tsaya dan suci aninci suyi sallah
Suna kammalawa be tsaya ba seda suka iso garin na kenya hore
Murnar haɗuwa da masoyiyars Rumana besa ya tuno da sameera dake zaune gaban mota ba se zakwaɗi yakeyi.
[10/25, 7:39 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*39*
koda ya iso ƙofar gidan nasu rumana,sameera bin shi kawai take da ido dan abun tsoro ya soma bata.
Se alokacin ya farga da sameera dake zaune agaban motar tana cika tana batsewa,
"sameera nan gidan su rumana ne,kuma gaskiya nan ni na sauka ko yaro zan haɗaki dashi ki ƙarasa gidan megarin?"
A fusace tace masa"yaro kuma? look ashrab wai meyasa baka da mutuncine lokuta da dama"
"rashin mutuncin me nayi miki kuma?" ya tambaya yana me ƙare mata kallo.
"dan bani da sauran b"mutunci a gurinka shine dalikin daze sa ka ɗaukoni zuwa gidan su kishiyata sannan kace anan ka sauka shin kasan sameerah kuwa"
Rai a ɓace yakai dubansa gunta yace"au ke har sahun masu mutunci kike sa kanki,?,ina mutuncin yake,look nazo ganawa da matata ne ke baki isa ki hanani ba, dan haka zaɓi ya rage naki.".
Yana kaiwa nan yasa kai yayi ficewarsa daga motar ya shige gidan nasu rumana.
Sameera kasa aywatar da komai tayi dan tsabar takaici
Da sallamarsa ya shiga gidan,rumana wacce fitowarta daga wanka kenan tana ɗaura alwala,gashi ɗan towel ɗin jikinta Da kaɗan ya wuce ɗuwawunta,dan inna ta gama mata faɗan zuwa wankan dashi kenan ya shigo.
Daburcewa tayi ta rasa inda zata ɓoye kanta,shiko bin ta kawai yake da ido yana ƙare mata kallo,sosai ta burgeshi
,wani ƙayataccen murmushi ne yake fitowa daga bakinshi na ganin da yay mata.acikin hasken wutar lantarki daya haska ƙaramin gidan nasu.
"au magaji kaine tafe da dare haka"cewar inna dake ƙoƙarin fitowa daga ɗakinta jin sallamarsa.
"wallahi inna nine,"ya faɗi yana shafa kansa cikin alamar dake nuna jin kunya.
Tsugunawa yayi har ƙasa ya gaisheta ta amsa masa amutunce, sannan tace
"ka ƙarasa ciki ku gaisa kaga dare yayi,ni zani in kwanta ba daɗi nakeji ba sosai"ta faɗi lokacin data shige ɗakinta.
Rumana tsayawa tayi da buta a hannunta ta kasa koda ƙwaƙƙwaran motsine sabida kunyar data rufeta.
Murmushi yayi ya taka cikin takusa na ƙasaita ya isa inda take tsaye hannayensa zube cikin aljihunsa.
muje zuwa
Surbajo for life.
[10/25, 7:40 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*40*
Ƙasa ta sakeyi da kanta tana wasa da hannayenta dan ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki takeji dan tsabar kunya.
" manya kaurin gayya,wanka kikayi ne?"ya faɗi yana murmushi, bata iya cewa komaiba se kai kawai ta gyaɗa masa,
Tsureta da idon da yayi ya mata yawa motsi na arziƙi ta gaza yi,se ƴan soshe soshe take dake nuna atakure take.
Ganin ta kasa motsawa ne yasa ya kamo hannunta yajata zuwa ɗakinta yana faɗin"muje in miki jagoranci naga kamar kin mance hanyar ɗakin "
Ƙoƙarin ƙwace hannunta takeyi,dan bataso ya riƙetan,shiko ko ajikinshi be Saketa ba seda ya kaita ɗakin nata da aka ware mata tun vayan zuwanta wanka.
Suna shiga ya jata jikinshi ya rungume,ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya a hankali ya ɗago kanta yay mata kiss a goshi sannan yace a hankali.
"nayi kewarki da yawa rumana ta pls ki amince mu tafi tare"ya faɗi yana shinshina wiyanta
maƙale kafaɗa tayi gamida ƙoƙarin kwacewa Daga rungumar da yay mata amma yaƙi bata damar hakan duk iya yinta ta kasa raba jikinta da nashi.
"dan Allah ka sakeni insa kaya ajikina sallah zanyi fa"ta faɗi kamar zatayi kuka.
Murmushi yayi yace"nufinki har yanzu kina da alwala?"
Da sauri tace"shigowarka fa na ɗaurota,ina da ita mana"
"duk da na rungumeki alwalar bata karye ba?"ya sake jefa mata tambayar yana shafo lips ɗinta.
Gano manufar tambayar tashi tayi wacce kuma sosai kunya ta kamata ta sinne kanta a ƙirjin shi gami da runtse idonta.
ɗaukarta cak yayi zuwa gefen ƙaramin gadon dake ɗakin ya zaunar da ita akan cinyarshi bayan ya zauna.
Rumana tana jin daɗin kasancewarta da mijin nata sosai takeson hakan.ƙara shigewa jikinshi tayi tace"shine kayo tafiyar dare ko?"
"Rumana na kasa bari gari ya waye ne yasa na taho ko nayi laifi?"
Ɗan ƙara shagwaɓewa tayi tace"ina ka baro aunty sameerah?"
"Tana mota tana jirana"
A ɗan tsorace ta dubeshi tace "tun shigowarka kuna tare"
"eh muna tare mana"ya bata amsa yana ƙare mata kallo.
"baka kyautaba gaskiya,taya zaka barta jira har haka a waje tashi muje in raka ka in yaso da safe ka dawo"ta faɗi tana miƙewa.
Ko kaɗan beso hakan ba sede beda zaɓin daya wuce ya amince ɗin tunda nan ba gidan sa bane gidan sirikaine.
Doguwar riga ta zura akan tawul ɗin jikinta sannan tasa hijab tace"muje ko"
Ashrab wanda duk kasala ta gama saukar nasa da ƙyar ya iya miƙewa,ya kama hannunta suka fice itade a kunyace take.
Sameera wacce taci kuka ta ƙoshi tunda ya barta,hangosu sun nufota ne yasa ta share hawayen idonta,ta buɗe murfin motar ta fito ta riƙe ƙugu har suka ƙaraso kallon uku saura kwata take musu.
Ɗan rusunawa rumana tayi tace"Aunty sameera ya hanya"
"uwarkice auntynki ba ni ba munafuka"cewar sameera cikin matsanancin fushi.
Sosai abun ya ɓata ran rumana da ashrab ,dan haka afusace yayi kanta ze kifeta da mari,rumana tai saurin riƙoshi,sannan ta shiga tsakaninsu tace tana murmushi wanda shi kanshi ashrab ya basa mamaki.
Gyara mai tsayuwar rigarshi tayi,gamida ɗan kakkaɓe masa,wanda shi yama rasa me take kakkaɓewar tace asanyaye"haba yallaɓai rumanarka bata sanka da haka ba fa,ay wannan faɗan mune na mata naka kallo ba hukunci ba,"tun kan ta ƙarasa sameera ta amshe zancen da cewa.
"au ke nan har mace ce,da zaayi faɗa da ita,ay sede inci ubanki inba da laada,sabida ni ba class ɗinki bace"
Waigawa rumana tayi tana murmushi tace"karfa ki mance mijin wata kika aura,ban tuhumeki meyasa ba,ko yanzu da kike haƙilo a kansa nasan zafin kishi ne sabida duba ɗaya zakiwa mijin nawa kisan ya cika namijin da zaay hakan akansa,to amma me ki bari in dawo semu gyagije,gashinan na baki aronsa kiji daɗinki,sede don Allah ki ƙyara zage dantse wajen kulawa dashi dan yanayinsa ya nuna yana cike da kaɗaici da kewa,"tana kaiwa nan ta waiga gun ashrab wanda tunda ta fara bayanin yay suman tsaye fuskarsa ta shafa,gamida rungumeshi tace ciki kirsa"kaci gaba da haƙuri na kusa dawowa,gareka kaje gida ka huta"tana gama faɗin haka ta juya zata bar gurin jin an ruƙotane yasa tai saurin juyowa,ashrab ne fuskarsa ɗauke da murmushi,ya ruƙo kanta ya manna mata kiss a baki sannan yace"cikin kewarki nake kullum mu kwana lafiya"
Ƙwacewa tayi daga ruƙon ta ruga gida tana ɗaga masa hannu.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[10/26, 9:25 AM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*41*
Sameera a fusace tabi bayan rumana tana zage zage,sede ashrab be bata damar cimmata ba,ya ɗaukota cak ya saka a mota,yaja suka bar harabar gidan nasu rumanar.
"in kai ta shanyenka to ni daidai nake da ita wallahi gwara tun wuri kaja mata kunne,inba haka ba wallahi zatayi danasanin shiga gonata"cewar sameera cikin matsanancin fushi
.
Murmushi yayi me ƙayatarwa yace hankali kwance"Toni kuma awa sameera,tace faɗankune na mata da kukeyi kan kishi in kun gaji zaku bari,shawara ɗaya zan iya baki itace ki kama girma da mutuncinki,dan rumana ta jima da wuce duk inda kike tsammaninta".
Ci gaba da masifa tayi har suka iso gidan megari,shi be kulata ba.
Part ɗinsu ya kaisu sabida kowa na gidan yayi bacci dan dare yayi sosai.
Tunda ya nuna mata ɗakin dazata shiga be sake bi ta kanta ba,seda gari ya waye.
Sosai megari yayi mamakin ganinshi a sahun sallah a masallacin gidan.
Bayan an idar ne suka jero har zuwa sashin megarin,bayan megari ya zauna ne Ashrab ya duƙa har ƙasa ya gaisheshi.,cike da jin daɗi ya karɓi gaisuwar ta ashrab,sannan ya ƙara da cewa.
"magaji komai ya faru da sanin Allah,banaso ubangiji yayi fushi dakai,sabida duk ɗan dake fushi da iyayensa ya taɓe,baa kyauta ma ka ba nasani kuma kowa ma yasani,sede haƙuri shine maganin komai,"
"Abba damuwata duka akan rumana ne,amanarta nakeson riƙewa shine yasa na fusata,amma kayi haƙuri Abbana nayi kuskure agafarceni"cewar ashrab yana me sunkuyar da kai ƙasa....
"Amanar rumana ashrab na fika son ariƙeta,sabida mahaifinta kan ya kwanta ya mutu,ni ya damƙawa,kade san komai to kaga ko ay dole naso rumana,"
murmushi yayi na jin daɗin kalaman na megari.Dan duk me sonshi kawai yaso rumana.
"kaje gurin mahaifiyarka ku gaisa dan tin bayan tafiyarka bata da isasshiyar lafiya,sabida bata ji daɗin abinda ya faru ba kuma tayi danasanin hakan"
Jiki a sanyaye ya miƙe ya nufi ɓangaren na mahaifiyar tashi,dan Allah yasa masa sonta azuciya fiye da komai ko fushin da yayi da ita mutuwar ɗanshi ce tasa yaji zafi.
A zaune yasameta kan abun sallah,tana ganinshi ta ware hannayenta tana murmushi gamida zubar da ƙwalla.
Da sauri ya isa gareta,ya rungumeta yana share mata kwalla,shima idonshi na zubarwa yace"karkice komai hajiya,duka munyi kuskure kuma mungane zamu gyara,dan haka kiyi haƙuri kidena zubar da hawayenki akaina"
"Dole inyi kuka magaji inde ba yafiya nasamu daga matarka ba,"
"rumana bata da riƙo dan haka ki kwantar da hankalinki,komai ze wuce insha Allahu"
"ina fatan hakan magaji"
Daga haka hira ta ɓarke tsakanin su kamar komai be faruba, se hira suke sha.
Be baro part ɗinba seda ƙarfe tara na safe,shima dan yanason zuwa gurin rumanane.
Muje zuwa
.Surbajo for life.
[10/26, 9:52 AM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*42*
Koda ya shiga ɓangaren nasu sameera yasamu hakimce akan kujera tana kaɗa ƙafa gamida yatsina fuska.
Banza yaba ajiyarta yayi wucewarshi ɗakinshi ya shiga wanka, yana fitowa a gaggauce ya shirya ya ɗauko wayarshi da key ɗin mota,yayo waje.
A falon ya sameta,ɗauke kai yayi ze wuce da sauri tasha gabanshi tana faɗin.
"kai malam yunwafa nakeji,naga taketakenka,tunda mukazo ƙauyannan kakemin wulaƙanci,look nafa jima da girmewa wulaƙanci dan kaji in faɗa maka akan me zaka wulaƙantani"
"kinga sameera banason hayaniya,ina da rarin shedules agabana,yunwa kuma in kika shiga cikin gida ay zaki ci abincin,wulaƙanci kuma ni banma iyashi ba,dan dana iya,daga ranar da na sameki fanko zaki ga tsagwaron wulaƙancina,kinga ni wajen rumana zani ki kula da kanki in kuma bakyacin abincin gidan ki ayka asiyo miki"ya ajiye mata kuɗi masu yawa akan kujera ya raɓa ta gefenta ya wuce ransa fess ya ciro wayarsa ya kira rumanarsa.
Bayan ta ɗaga gaisheshi fa fara yi da tambayar yarda suka je gida jiya.
Bayan ya amsa mata ne ya ƙara da cewa.
"ki tanadarmin abinda zanci nan da minti talatin zan ƙaraso"
"me kakeso yalkaɓai" cewar rumana wacce tin jiya Ameera tasa ta agaba ta hure mata kunne kan ta amshe mijinta daga hannun wata,kuma ta lashi takobin koyawa kowa hankali cikin masu son shiga tsakaninta da mijinta,ciki ko harda ita kanta hajiya mahaifiyar ashrab ɗin.
Sosai yaji daɗin maganar tata,dan haƙa cikin zaƙuwa yace"dani da zaɓina duk muna ƙarƙashin kulawarki gimbiyata"
"angama yarima na a ƙaraso lafiya".
Tana kashe wayar Ameera ta rungumeta tace"yauwa ta gurina ki buɗe wuta iya wuta,bariki ba ƙarya bace kuma baa fimu ba,koda wasa karki bata kafar shan iska tunda ita ƴar iskace mu ɗin ƴaƴan guguwane"tafawa sukayi suka bushe da dariya.
Dama tuni suka shirya masa abinci kala biyar masu rai da lafiya,suka gyare ɗakin na rumana gamida wadatashi da turaruka masu ƙamshi.
Inna ko ganin yadda suke ta shirin tarbar baƙon nasu ne yasa ta kimtsa da wuri taja ameera rakiya zuwa gidan Aisha,dan su dubota kasancewar batajin daɗi aka bar rumana ita kaɗai bayan ameera ta kwakkwafeta kan ta kula da kyau.
Kwalliya ta gani ta faɗa rumana tayi,wacce in ba wanda yasanta ba cewa zeyi ba ita bace,cikin riga da siket na leshi marun da ratsin golding sosai tayi kyau acikin kayan kuma sun fito da ƙirarta da kyau aciki ta yadda duk wanda ya kalla seya ƙara.
Ashrab ya iso ƙofar gidan cike da ɗokin son ganin masoyiyar tashi da yakeji kamar ya shekara be ganta ba.
Kanshi tsaye ya shiga soron gidan yana sallama,cikin takun isa da ƙasaita,gamida motsa ko ina na jikinta ta iso soron gidan ba tare data yafa koda mayafi bane tace tana murmushi"se kace ba gidan ku ba"ta faɗi tana fari da ido gamida murmyshin ɗaukar hankali.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[10/26, 8:42 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*43*
Suman tsaye yayi lokacin da yay arba da rumanarsa,wata irin ƙaƙƙarfar ƙaunarta ce ta mamayi ko ina najiki da jininsa.
Sosai ta gaza ɓoye jin daɗin ganinta da yayi a hakan.
Ɗan rausayawa tayi tasake cewa a shagwaɓe"ka tsaya a waje sekace baƙo,nan fa gidankune"ta faɗi tana ɗan turo baki gaba.
Murmushi yayi yace "wannan ay se kisa nayi rashin kunya agaban inna,kinganki kuwa rumana ta"
Fari tayi da ido gamida rausayar da kai gefe tace"godiya nake yarimana"
Ga mamakin Ashrab hannu ta miƙa masa tace "muje in maka jagoranci kan ay maka naɗin sarautar ɗan amanar soro"
Dariya ya yi ƙasaitacciya gamida ruƙo hannun nata,suka jera zuwa cikin gidan.
Ɓangaren ɗakin inna ya nufa,da sauri rumana tace"batanan inna ay sunje gidan aunty aisha"
Sosai yaji daɗin hakan,dan yanaso ya lallaɓa matarsa ta amince su tafi tare amma yanajin kunyar inna beso taga be kyauta mata ba.
Sina shiga ɗakin na rumana ya janyota jikinshi ya rungume ya shiga maida numfashi da sauri.wiyanta yake shinshinawa,yana limshe ido,itama hakance ta kasance da ita dam arayuwarta tana son ƙamshin mijin nata dan na musammanne.
Ƙara shige masa take,shima kuma yana ƙara haɗeta da jikinshi,a hankali ya lalubi bakinta ya manna nasa akai ya shiga sumbatarta cike da ƙwarewa.da som mamtar da ita duniyar da take.
Tsayuwace ke shirin gagararsu da sauri rumana ta ƙwaci kanta ta koma gefe tana maida numfashi, dan gaba ɗaya ya gama birkitata,
Gefenta yaje ya zauna hannunsa ya ɗora kan nata ɗago ido tayi ta kaɗkeshi shima ita yake kallo da birkitattun idanunsa.
A hankali yace"don Allah rumana ki amince mu tafi abuja tare, wallahi rashinki na neman zautar dani,banajin daɗin rayuwata ko kaɗan sabida rashinki ki tausayamin ki mance komai daya faru abaya,kizo mu gina sabuwar rayuwa,har abada rumana ni me ƙaunarkine,hajiyace matsalar kuma itama tayi saduda,dan har yafiyarki hajiya take nema,don Allah "
Hannunta ta ɗora masa akan labbansa tace,a sanyaye"baka laifi agurina ɗan aljanna, na jima da mancewa da komai kaine kawai agabana mijina ga abincinka kaci kar ya huce"ta faɗi tana me miƙewa ta miƙo masa su gabansa ta bubbuɗe.
Bakin Ashrab yaƙi rufuwa musamman dayaji rumana ta mance baya,sosai yaji girma da darajarta sun ƙaru agurinshi,
"ki bani komai inci rumana inde hanninki ya sarrafashi ,zanci "
Zubo masa komai tayi sannan ta tura masa gabansa ayko beyi fulako ba ya maida hankali yaci ya ƙoshi.
Bayan ya gama ci ne itama yasata dole taci.
Kwashe komai tayi takai kitchem ɗinsu sannan ta dawo,suka shiga hirar su ta masoya da wasanni na faranta zuciya.
Sosai ta gamsu zata bishi su tafi tare, dan haka da ƙwarin guiwarsa yay mata sallama bayan dawowar su inna dan zashi ya faɗawa megari yayiwa inna magana ta bashi matarsa su tafi tare inze koma abuja nan da kwana uku.
Muje zuwa
.
Surbajo for life
[10/28, 10:09 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*44*
"Ashrab ka bari ta kammala duk shirin da takeyi ta maido maka da ita da kanta,mana,kwana nawa ne,in kayi haƙuri"cewar megari bayan ashrab ya sameshi kan yayiwa inna magana ta bashi rumana su tafi.
"to in banda ma rashin ta ido irin ta yaran yanzu taya zaaje ace abada yarinyar bayan wanka taje gida,an se an maido da ita dan kansu"cewar hajiya dake zaune gefe tana jinsu.
Gyara zama ashrab yayi yace kamar wani ƙaramin yaro"nide nafiso mutafi tare,gaskiya,danni na gaji da zaman nata anan"
"in banda abunka ay hannu da yawa maganin ƙazamar miya,naga matan naka biyu ne,akwai wata acan kabar ƴar mutane ta ƙarasa samun sauƙi"cewar hajiya tana murmushi.
Ɗan ɓata rai yayi sannan yace"kema de hajiya yanzu sameerar kike sawa a sahun mata yarinyar da batasan ci na ba bata san sha na ba,se taƙamar banza da wofi,nide matata kawai nakeso"yana kaiwa nan ya miƙe ya fice zuwa sashin nasu.
Bayan fitarsa megari ya dubi hajiya yace"hajiya ki duba kiga zamanin da Allah ya kawomu,zamanin da ko ko ganin matan baa barinmu muyi,Sede asako maka jinjiri a zani ka gani"
Dariya hajiya tayi tace"wallahi fa amma ka duba kaga wannan rashin ta ido da magaji ke mana akan matarsa"
"nide bazanyi magana