Chapter 6 Reading ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt Arewa Novels

ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 13

15K to 18K   out of 38.9K words

am sallamesu.

Daƙyar Ashrab ya kuma kwana a asibitin da safe ko ta tada balli dole tasa aka sallameshi badan ya warke ba se dan tsabar masifar kiran sunan rumana da ya kwana yanayi,lamarin da ya sasu a duhu

Muje xuwa

Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*Mura nake kwana biyu🙏🏻*

*19*


"Ya kamata ka futo fili ka sanar damu aynihin abinda ke faruwa da kai tsakaninka da rumana,yin shuru ba abinda ze amfanar,"cewar me gari bayan sun isa gida sun zauna a falon megarin.

"Abba rumana kawai nakeso adawomin da ita,wallahi bazan rayu ba in babu ita"cewar Ashrab yana share ƙwallar data tarun masa a idanunsa.

"kai karka raina mana hankali,uban waye tsaranka anan,yarinya har da ciki na shege tayo tazo maka dashi gida amma ka kasa bayani gamsasshe da zamu fahimta,kafa fita idanuna magaji in rufe "cewar mahaifiyarshi cikin fushi da taje ji kamar ta zaneshi.

"cikin jikin rumana hajiya ba shege bane,nawa ne, hasalima nine namiji na farko data fara sani"ya faɗi ba tare dayaji kunyar komai ba.

Salati hajiya ta ɗauka gamida tafa hannu tace tana riƙe da baki.

"ta POS ka turo mata cikin kenan taje ta amso?yau naji abinda ya girmeni ni Aisha"

"Abokina nasa yazo har nan ya ɗaukota yakaita can gidana a abuja,ta kwana biyu,"ya faɗi haka ne dan kariya ga zubewar mutuncin rumanar in aka ji cewar basu sanma da aure tsakaninsu ya kwanta da ita.

"magana ta ƙare Ashrab tunda ka amshi ciki,bamu da ja,"inji me gari


"ni ina da ja,wallahi ay yarinyar cewar tayi gurin yawon bariki ta samoshi"


"ni nace tace hakan"ashrab ya faɗawa mahaifiyar tashi data fara kaishi wiya.

Shuru hajiya tayi tana tuno kuma abinda zata ƙara cewa,zuwa can ta yunƙuro zatai magana da sauri me martaba ya katseta da cewa

"ciki ya amshi abunshi nashi ne hajiya,dan Allah maganar ciki ta wuce daga bakinki"


"Zancan auranshi da sameera fa?"

"Bana sonta hajiya dan Allah kibarni in dawo da matata kawai ta isheni rayuwa"cewar ashrab a marairaice.

"wallahi in baka amince da auranka da ita ba,wannan fitsararriyar yarinyar kai da ita har abada"cewar hajiya tana huci.


"hajiya yanzu koda hakan yana nufin baƙin cikina?"

"Koda hakan yana nufin mutuwarka ne magaji,shashasha wanda besan abinda ke masa ciwoba,aure da sameera wallahi ko bayan rai nane se ka aureta inde nice uwarka"tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice daga falon ranta a ɓace.

"wallahi Abba bana sonta dan Allah kaba hajiya haƙuri,bana sonta"ashrab ta faɗi yana kuka.


"ka natsu ashrab ka kwantar da hankalinka,kai namijine na mace har huɗu,kuma kowacce da halinta zata zauna,bana son wannan koke koken.kayiwa mahaifiyarka biyayya dan a zauna lafiya ka de ji ko"


Shuru yayi ya kasa magana to shi taya ma ze zauna da mace biyu wacce yakeso sa wacce beson ko jin sunanta ace kuma ze yi adalci,anya hajiya ba ticket ɗin shiga wuta ta yanka masa ba?.

Mahaifinshi ya jima yana kwantar masa da hankali kamin ya natsu yace.


"To Abba rumanar fa,kuma sakin da nai mata fa?"

"Tunda ciki gareta ashrab kana furta ka maida ita shikenan ta dawo matarka,sede igiyar auranku me makon uku ta dawo biyu"

Tun kan Abba yayi shuru ashrab yake furta na maida ta yafi so goma.

Murmushi megari yayi yace.
"kaje kasamu kai wanka ka kimtsa habu ya raka ka gidan nasu kadawo da ita,tunda ta dawo mazauninta na matarka"


"nagode Abba nagode nagode"cewar ashrab lokacin daya miƙe da gudu ya rungume mahaifin nasa,sannam ya fice daga falon da saurinsa yana kirab numbar habu.


Shi kuma megari ya nufi ɓangaren hajiyar ashrab ɗin dan suyi magana ta fahimta.







Muje xuwa

Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*Mura nake kwana biyu🙏🏻*

*20*


"Hajiya shifa yaron da kakeso yay maka biyayya ba haka akeba,wannan fushin naki me makon suyi miki biyayya,tsoronki zasu ji,bare yaro kamar Ashrab ace be wuce ki zageshi ba,dan kawai kin haifeshi,meyasa kike haka ne?"cewar megari a tausashe bayan ya sameta a sashin nata.


"kafi kowa sanin halin magaji,ko kaɗan beda sauƙin kai,in nace ta lalama zan bishi bazeyi abinda nake so ba"

"yanzu in ya auri sameera wuta ta mutu?"

"Eh ta mutu,"

"ze aureta,sede ze maido matarsa rumana"

"sam ban amince da ci gaban zamansa da rumana ba"cewar hajiya

"to babu auransa da sameera har abada matuƙar baze zauna da rumana ba inde nine maɗaurin auran"yana kaiwa nan ya miƙe ze fice
...
Sanin hali akace yafi sanin kama,tasan inde yayi fushi irin haka yana da wiyar sha'ani,hakanne yasa tai saurin shan gabanshi ta zube guiwa ƙasa tace "tuba nake ranka ta shi daɗe na amince yadawo da ita,kuma ya auri sameerar ayimin afuwa"

Tsayawa yayi bece komai ba,ya jima a tsayen ita kuma tana durƙushen,kamin yasamu guri ya zauna,ya sauke ajiyar zuciya yace.

"ba damuwa Allah ya basu zaman lafiya,sede ina me ƙara jan hankalinki ki dena shiga sabgar da bata shafeki ba,koda ya dawo da matarsa ba ruwanki da ita,shiga sabgarta da kikene yasa ta rainaki wanda ko ɗan cikin ki ne kikace zakiyi masa hakan bazaku shiryaba, ki kama girma da matsayin da Allah ya baki"

Amsawa tayi da to kawai badan ranta yaso ba,haka de yay ta nusar da ita kamin ya baro sashin.

********


Ashrab wanka yayi sannan ya buɗe maajiyar kayanshi wacce tafi shekara rabon daya sa kayan cikinta,tun lokacin da iyayen nasa suka fara bijiro masa da matan da sukeso ya aura.

.Zaɓo wasu masu kyau yayi,yasaka ya feshe jikinsa da turare,sannan ya zo falo inda habu ke zaune zaman jiransa ya fito su tafi bikon rumanar....
"habu amma de maajiyar jayan ban nawa,ana kulawa dasune ki,nagansu fesss kamar ban jima bansaba"ashrab yayi tambayar yana murmushi.


Murmushi habu yayi sannan yace"watanni shida kenan rumana na kulawa da komai na sashin nan,itace ke gyara maka kayan ba tare data san naka bane"ya faɗi yana murmushi.

Wani sanyi ashrab yaji aransa jin rumana ke kulawa da kayansa.

"muje da sauri habu,na ƙosa in sata a idona"cewar ashrab lokacin da suka shiga mota.

Tafiyar ba me nisa bace suka iso ƙofar gidan nasu rumana,sosai tausayinsu ya kama ashrab ɗin ganin inda suke rayuwa.


Sallama sukayi a ƙofar gidan ,Ameerace ta fito dan taga ko su waye,sosai tayi mamakin ganin ashrab tare da habu,bakinta har rawa yake gurin faɗin"kuk. ...kkune?"


Murmushi yayi yace"mune ƴan barina"ya faɗi yana murmushi....


Dariya tayi gamida rufe fuskarta tace a kunyace"sannunku da zuwa,bari in faɗa musu"

Juyawa tayi ta koma cikin gidan tana mamakin ganin ashrab,to dama shine mijin na rumana,?lalle rumana me saa ce,shine zancan dake shawagi a zuciyar ta Ameera.


"rumana na miki zancan fara zuwa awo amma kinki ko,ke bame faɗa miki kiji haka kika zaɓa ko?"cewar umman ta dama hirar da sike kenan,akai sallama ameera ta fita

Shigowar ameera a daburce ne yasa suka maida hankalinsu kanta,itako cewa tayi.


"ƴan gidan me gari ne"

Tsaki rumana tayi gamida kauda kai gefe,itako umna hijab ta ɗauko tasaka sannan tasa ameera shimfiɗa musu tabarma taba ameera damar taje ta shigo dasu.


Itako rumana ɗankwalinta ta turo gaba ta jefa cingam a bakinta ta fara taunawa


Ameerace a gaba suna binta a baya,koda ya shigo idanunsa kan gimbiyar tashi ya sauka,kallo ɗaya yay mata ya fahimci barikince ta motsa .murmushi ya tsinci kansa dayi,har ya samu guri gefen habu shima ya zauna yana ƙarewa gidan kallo.








Muje xuwa

Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*




*21*


"umma barkanmu da warhaka"cewar habu yana murmushi,

"barka de habubakar kunzo lafiya?"

"Lafiya lau umma"

Ashrab wanda sam bemasan anayiba hankalinshi na kan rumana,ba abinda yakeso irin yaji ta ajikinshi,yadda take taunar cingam ɗin sosai ya burgeshi,sede ya rasa fushin ko na menene take yi.

Habu ne ya ɗan taɓoshi da hannu,sannan yayi firgigit ya dawo hayyacinshi kunyace ta kamashi na ganin sun haɗa ido da umnan rumanar tana kallonshi.

Sunkuyar da kai yayi ƙasa,yace
"antashi lafiya umma"



"lafiya lau ɗana ya ayki?"

"Ayki Alhmdllh umma,mun sameku lafiya?"

"Lafiya lau ya wajen su hajiya?"

"duk suna lfy suna agaisheku"

Murmushi umma tayi dan tasan zancan ba haka yake ba,dan babu ta yadda zaayi hajiya tace tana gaishesu.amma a fili se tace"muna amsawa"

Shuruce ta biyo baya ta ƴan wasu daƙiƙu,kamin habu yace"umma munzo ne dama mu bada haƙuri rumana ta koma ɗakinta a mance da komai"


"munyi magana da megari kamun zuwanku anan ta waya,sabida haka ni ba ruwana a wannan magana bakumin komai ba,kuma kaima habu kyanshi ka cire kanka a sabgarsu,in sunga zasu shirya su zauna lafiya Alhmdllh,in sunga basa son auran su rabu wannan itace magana ta ta ƙarshe akan wannan sabgar taku "cewar umma hankali kwance.

"wannan gaskiya ne umma Allah kuma ya saka miki da alkhairi ya ƙara lafiya da nisan kwana"cewar habu yana me ƙara sadda kai ƙasa.

Miƙewa umma tayi tabar gurin shima habu miƙewa yayi ya fice zuwa ƙofar gida yana me cewa ameera"muje ki tayani hira ko"ba musu ta bishi abaya zuwa inda motarsu take,ya rage daga ango se amaryarsa zaune wacce se cika take tana batsewa.

Ɗago ido yayi a hankali ya sake kallonta ko kaɗan ita kallonshi be dameta ba,

.A hankali ya matsa kusa da ita yace a tausashe"Rumana,babu ko gaisuwa"

Wata uwar harara ta watso masa da daradaran idaninta,ta sake turo ɗankwalinta gaba ta kauda kai gefe.

Beji daɗin hakan ba,dan shi baa masa irin hakan akoina bare kuma abar da yake so ce take masa kallon kashi yafi shi.

Ranshi ya sosu sosai amma se ya danne yace a tausashe"kiyi haƙuri rumana komai da yafaru ya farune a rashin sani kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki mu fahimci juna"

"wai ni wannan surutun da kake tayi na menene,da barikice ta haɗamu,ta juye ta dawo iskanci,ta juye ta komo aure,ta ƙarƙare a saki to meye yayi saura a tsakaninmu?"tamai tambayar cikin ɓacin rai,

Yayi mamakin fitar maganar a bakinta,amma se ya cije yace"rumana akwai so me ƙarfi da nake miki,be kamata ki ɗora laifin komai akaina ba"

."so kode sha'awa,kaga malam dama tashi kayi ka fice a gidannan daya fiye maka danni bani da lokacin sauraron ka"


Da ƙarfi yasa hannu ya janyota kusa dashi ba tare da laakari da cikin jikinta ba yace cikin fushi amma a tausashe,"ko shaawar taki nake laifine?ko baki kai ay shaawar taki bane?karfa kice zaki rainani dan haka ta faru"

Ƙoƙarin ƙwacewa take daga ruƙon da yay mata,tace"ba aure tsakaninmu kadena riƙeni,dan nan ɗin ba dairar gidan fasiƙanci bane na abuja"

maganar tai masa ciwo amma yasan ta faɗi gaskiya,dole shi ze sauko da kansa ya bata haƙuri.

"Rumana nasan na sakeki kuma nace na dawo dake,kinga kina nan a mazaunin matata,kuma ina me miki albishirin cewa aurenmu mutuwa ce kawai zata raba""


Shewa tayi ta miƙe tace "zako ka mutu da wuri inde rumana ce"

Muje xuwa

Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*23*



"Abba bani da raayin auren sameera ko kaɗan a zuciyata,zan de yi biyayya amma badan ina so ba"cewar ashrab cikin matsananciyar damuwa.

"tun farko g
Hakan naso kayi amma kaƙi,ƙarshema se ka gujemu,shi lamarin aure abarwa Allah komai yafi"cewar megari cikin sigar rarrashi da tausasawa.

"bakomai Abba Allah yaymin jagoranci amin"

"yanzu ita me ɗakin naka yaushe zata dawo ɗakinta?"

Shuru yayi bece komai ba, sema girgiza kai da yake yi yana gyaɗawa.

"da matsalane ashrab?"cewar megari cikin kulawa.

"da akwai Abba,rumana baƙaƙen maganganu take faɗamin,kuma ni na kasa jure hakan shiyasa ban kuma zuwa ba"cewar ashrab cikin fushi .

murmushi megari yayi sannan ya dafo kafaɗarsa da hannunsa sannan yace a tsanake"su mata karkatattune dole se ka haɗa da haƙuri in kace bazakayi hakuriba zaman baze yo daɗiba kaje ka sake dubota sabida juna biyun dake jikinta bazaka dinga nesa da ita ba"cewar megari yana murmushi

"ni narasa fushin me takeyi Abba,ban san me nayi mata ba"

"haƙurin de shi zakaje kai tayi,musamman yanzu da kake shirin ƙara aure dole se kayi hakuri"

"insha Allahu na tashi daga nan zanje sabida inason wucewa bakin aykina,amma abun ya faskara"


**********


Amai take kamar zata amayar da abinda ke cikun nata sati guda kenan bata da lafiya amma taƙi amincewa da akaita asibiti umma tun tana faɗa ita da Ameera har ta koma basu tausayi.


Riƙe da ita Ameera take tana wani sabon yunƙurin aman,sallamar Ashrab ta karaɗe ko ina na gidan.


izinin shigowa aka bashi sannan ya shigo kansa a ƙasa alamun kunyar sirika.

Ko gaisawa da umna basuyo ba ya hangi rumanarsa na sheƙa amai.


Da gudunsa ya ƙarasa gurinta ya tallafota agigice yake faɗin"me ya sameki,me kika ci?"amma sabida halun da take ciki ta kasa cewa komai se yunƙurin amai.

"to gatanan de,tun shekaran jiya nake fama da ita taje asibiti taƙi amincewa,komai taci se ya dawo"cewar umma dake gefensu a zaune.

"umma bari muje asibitin mu dawo"cewar ashrab duk aruɗe.

"da de yafi kam"cewar umna.


Haka ya tallabota batan tasoba se da n batada yadda zatayi jiki va kwari ga ba lafiya.

Hijab kawai aka sa mata ya wuce motar da ita,gidan baya yasata ya kwantar sannan ya ja motar,suka nufi asibitin.




Muje zuwa

Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*22*


Ƙoƙarin wucewa take ta gefensa,da sauri yasha gabanta,ya kamo hannunra yace kamar zeyi kuka"ba ƙya so nane kike burin na mutu rumana?"

"Au kai har tambaya ta ma kake,to bana sonka ni,banma taɓa jinka araina ba,barikice ta haɗamu kuma ta raba se ma ribar barikin da aka samo"takai maganar tana nuna cikin jikinta.

Jikake tasss ya ɗauketa da mari,cikin tsananin fushi yace yana me cije baki"kowanne tozarci zan ɗauka daga gareki,amma ko da wasa karki kuma sheganta min ɗana,in ba haka ba,zakisha mamaki"yana kaiwa nan be jira amsar ta ba yasa kai ua fice daga gidan ransa na suya.

Riƙe kumatun tayi ta rushe da kuka,me cin rai,ta jima tana kuka,umma bata ce mata komai ba ta ci gaba da ayyukanta.

Seda ta gaji dan kanta sannam ta miƙe a gurin ta koma ɗaki tana tuno wulaƙancin da zata masa wanda karema in yagani baze ci ba.


Shiko ko da suka tafi in banda huci ba abinda yake yi yana furzar da iska,tabbas ze jure komai amma banda wulaƙanta masa ɗa tun kan tazo duniya.

Habu dake gefe ta tafasa sauke be ceba har suka iso gidan,kamin yayi parking ma shi ya fice daga motar,ya nufi sashin nashi ranshi ba daɗi.

"me rumana take nufi ne,?meye nufinta"itace tambayar da yakewa kansa tunda ya ƙule a ɗakinsa.

Duk wata natsuwa tashi ya rasa ta,dan ya fahimci rumana ko kaɗan bata sonshi,dole ayki ne babba agabanshi na ganin ya jawo hankalinta gareshi.

********

"Dole a matsayin mahaifiyarki zan baki shawara,rumana aure fa ba abin wasa bane,ki natsu kisan abinda ke miki ciwo,mijinki zaɓin mahaifinkine kuma yana gargarar mutuwa ma batun auranku yake,dan me zaki bijire yanzu ki nuna bakya so"cewar umma mahaifiyar rumana lokacin da suka zo gurin bacci.

Share hawayenta tayi dake biyo idonta tace a raunane"umma bana Son ashrab kwatakwata,dashi da iyayensa,habu kawai nakeso,"

Doke mata bakinta tayi sannan tace"habu ƙanin mijinkine,wanda ba aure tsakaninku har abada,bama haka ba,haramunne da aure akanki kuma kiyi zancan wani,ki kiyaye harshenki kar ya kaiki halaka rumana"cewar umma cikin fushi.

"nide ki taimaka kisa yasake miki ni,sabida ubanshi kanshi be sona umma"cewar rumana hawaye na biyo idonta.

"zaki fahimci waye megari agareki masoyine ko maƙiyi,amma se nan gaba,abinda nake so dake ki jure amaidaki ɗakinki ko haihuwace kiyi acan se ki fito "cewar umma cikin yanayin da bazata gane wayau tai mata ba.

********

Bayan sati biyu da faruwar komai,Ashrab be sake yunƙurin zuwa gidansu rumana ba duk da hankalinsa na kanta.

Zaune yake gaban mahaifinsa suna mgn kan batun auransa da sameera da mahaifiyarshi ta uzzura kan a ɗaura daga baya ta tare in ya gama kimtsawa,

Muje zuwa

Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*24*



Tuƙin yake amma gaba ɗaya hankalinshi na kanta,cikin kano yakeson kawota shiyasa ya ware motar sosai a titi.

Koda suka zo asibitin cikin gaggawa aka karɓeta aka shigar da ita ciki,shiko ya kasa zama yakai gouro yakai mari haka ya dinga.

Likita ya jima kan yafito ya gayyaceshi office ɗinsa.

Bayan sun zazzaunane likitan yace"kai waye nata pls?"

"Mijinta ne ni"ya bashi amsa a hanzarce.

"good,cikin jikinta kasan watanninsa?"

"Watanshi shida da sati biyu"ya bashi amsa.

"bata zuwa antinatal,shiyasa duk wasu dokoki da ake bi don renon ciki ita bata bi,kama daga abinci abin sha dade sauransu,ko meyasa akayi sakacin haka?"

"Bana kusa da ita ne yasa hakan amma yanzu zaa kula sosai insha Allahu,da fatan de ba abinda ya samu cikin?"Ashrab yayi tambayar a ɗan tsorace.

"ba abinda ya sameshi for now,amma in baa kulaba wani abun ze iya faruwar"


"zama a kula insha Allahu"

Magunguna ya rubuta masa,ya biya kuɗin,sannan suka bashi damar shiga ɗakin da take kwance ana mata ƙarin ruwa.

Guri ya samu ya zauna jiki a sanyaye yana bin ta da ido yaga irin baƙin da tayi,ta rame,tausayinta ne ya kamashi,yaja kujera ya matsa kusa da ita,a hankali ya yaye rigar jikinta ya ɗora hannunshi akan cikinta wanda ya ɗan tasa,wasu siraran hawaye ne suka zubo masa sakamakon tunowa da yayi da ranar daya samar dashi,danshi ko haufi bayayi kan cikinsane,tunda shine mutum na farko

6 / 13