Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
daya fara,saninta.
Itako se bacci take sakamakon alluran da aka mata na bacci.
Suna asibitin har gari ya waye inda megari ya kira wayar Ashrab ya tambayi jikin na rumana ya shaida masa da sauƙi.
Ya gama wayar yakai dubansa gurinta,ga mamakinshi ta farka shi take kallo,da sauri ya ƙara matsawa kusa da ita,yace"Rumana ya jikin naki?zakici abinci?"duka a ruɗe ma yake jefo mata tambayar.
Kauda kanta gefe tayi bata kulashi ba,dan duk abinda ya faru tun daga zuwa gidansu ya ɗaukota duk ta sani.
Ganin tayi shurune yasa ya sake mata magana a sanyaye"rumana kiyi haƙuri don Allah,ki daure kimun magana"yayi maganar kamar zeyi kuka.
Yamutsa fuska tayi sannan tace"to ni me zance ma"
"kice min komai ma rumana koda zagine kimun don Allah amma banaso kiyi shuru baki kulaniba"
Wata uwar harara ta watso masa gami da cewa"Ay ba sama nakewa duster ba dazan zagi mijina salon Allah ya ƙona ni"ta ƙarasa maganar harda murguɗa baki.
Wani sanyi yaji azuciyarshi kiranshi mijinta da tayi,murmushi yayi ya kamo hannunta yace"ay shi murguɗa bakin da hararar ba Abinda Allah zeyi akansu ko"
Shuru tayi batace komai ba,sema ƙwace hannunta da tayi daga ruƙon da yay mata.
"Bari inje mota in dawo,ki kulamin da kanki"
Bata kulashi ba tade bishi da kallo,ficewa yayi da sauri yaje motarsa,danshi vayan boot ɗin motarsa ba abinda baya ajiyewa na ci sabida koda yaje meeting ko zezo ƙauyensu.
Brush sabo ya ɗauko da maclean,ya dawo ɗakin,a zaune ya sameta taci kunu.
Buɗe brush ɗin yayi yaje ya ɗaurayo shi a toilet ɗin cikin ɗakin,sannan,ya matsa mata maclean,ya dawo ya miƙa mata yace"zaki iya ko in taimaka miki?"
Banza tai masa tasa hannu ta amshi brush ɗin ta miƙe da ƙyar ta nufi toilet ɗin ta kullo ƙofar.
Wanke bakin tayi sannan ta ɗauro alwala,ta fito,ga mamakinta har ya shimfiɗa mata abun sallar.
Hawa tayi abunta hankali kwance dan tasan a motarshi yaje ya ɗaukota sallahr tayi ta asuba dan sauran se dede lokacin yinsu zata rama.
Ta idar kenan likitan ta shigo fyskarsa ɗauke da faraa yace bayan yaba ashrab hannu sun gaisa.
"jiki yayi kyau madam se gida kuma ko?"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa wanda hakan sosai yayiwa ashrab daɗi dan ra ƙara ƙima a idonsa.
Tambayoyi yayi mata ta amsa masa,hakanne yasa ya sallameta bayan ya ɗorata kan magani.
Haka suka jero zuwa mota,se cika take tana batsewa.
Buɗe mata gidan gaba yayi ta shiga ta zauna,dan tasan baze ƙyaleta ba amma da bazata bishi ba.
Koda suka kama hanya ƙara haɗe fuska tayi,dole ya ƙyaleta dan yaga da sauran darun dole ya lallaɓata.
Sun iso garin nasu sede ga mamakin ta hanyar gidan megari ya bi,da sauri ra dubeshi tace"malam gidanmu fa zaka kaini meye haka?"
Be kulata ba sema maida kansa kan hanya da yayi,ayko sosai ya tunzurota se masifa take har suka isa gidan.
Muje zuwa.
A samin babyna a addua Allah bata lafiya.
.Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*25*
Koda suka zo gidan ƙin fitowa tayi,magiya ba wacce be mata ba amma tai funfurus ta shareshi,hakanne yasa yace.
"ko ki taka da ƙafarki ko kuma in zagayo in ɗaukeki,zaɓi ya rage naki,"yana gama faɗin haka ya zare key ɗin motar,ya fito,ay kamin ya gama fita ita ta rigashi.
Har da ɗan gudunta take haɗawa ta nufi sashin nasu,tana waigenshi.
Koda ta shiga falon a tsaye ta tsaya tana maida numfashi,gami da tallabe cikin nata,dan sosai ta ji cikin nata ya dunƙule.
Da saurinsa ya ƙaraso cikin falon,saura kaɗan ya bugeta ya ankare.
Ƙarasawa yayi kusa da ita yana faɗin"se yaushe rumana zakiyi hankali kisan inda ke miki ciwone?"cikin fushi yayi tambayar.
Harara ta watso masa sannan tace tana turo vaki gaba"se ranar da aka sallamoni daga dawanau"
Duka ya kaiwa bakin nata,ayko da sauri ta goce be sameta ba,
"da kin tsaya ay da na nuna miki nawa ɗanyan kan"
"kaga malam nifa bansan dalilinka na ajiye ni awannan gidan ba,dan haka gida nakeso in tafi gaskiya"
."kiyi haƙuri rumana,batun gaskiya tunda akwai aurena akanki ni bazan iya yarda ki barni ba,kuma ke da cikin jikinki kuna buƙatar kulawa ta musamman,dole in matso daku kusa dani dan ingancin lafiyarku"ya faɗi a tausashe.
"tun kan insan inda yake mini ciwo nake rayuwata a gidanmu ruwa ko abincin gidan be taɓa cutar dani ba,se yanzu da zan haifo ɗan ƙaruna"Ta ƙarasa tana fari da idonta.
Kamota yayi yana faɗin"wallahi duk abinda kika ga dama ki faɗi,dama yanzu ay naga kin rainani,wai ku mata me isa duk ƙanƙantarku inde kuka taɓa ganin kanden namiji kuma shikenan se rashin kunya ta shiga tsakaninku,da haka kikemin?"yay mata tambayar yana kallon idanuwanta.
.Wata azababbiyar kunyace ta kamata wacce bata taɓa tsammanin jin ta ba a daidai wannan lokaci.
Sunkuyar da kai tayi ƙasa bata ce masa komai ba,se bakinta dake motsi amna ta rasa harafi ko guda ɗaya akanshi.
Kan kujera yakaita ya zaunar sannan yace"minti biyar,give me just five minutes,"
Shuru tai masa ba amsa,ganin bata musa masa bane yasa ya saketa ya juya ya fice daga sashin.
Be jima ba ya dawo ɗauke da flaks na abinci daya je ya amso agurin hajiya inna amaryar mahaifinsa.
Kallo rumana ta bishi dashi gamida yamutsa fuska ta kauda kanta gefe,ƙarasowa yayi ya ajiye abincin kan centre table sannan ya jashi gabanta.
Kitchen ɗin sashin yashiga ve jima ba ya fito da ruwan tea dayasha kayan ƙamshi da madara da milo a hannunsa,yazo ya dire mata kusa da abincin.
Sannan yasamu guri gefenta ya zauna har cinyoyinsu na gogar na juna,da sauri ta waigo tana kallonshi,murmushi yay mata gamida riƙe kunnuwansa duka biyu yace.
"ki daure kici abincin nan kisha maganinki,se kiyi wanka ki kwanta ki huta kuma don Allah"ya haɗe hannayensa alamun roƙo.
Bata bashi amsa ba,kuma alamunta sun gwada baze samu amsar ba.
Ɗan zamowa tayi daga kan kujerar,tasa cokalin ta fara ci,tana ɗan kurɓar ruwan tea ɗin.
Wani sanyi yaji har cikin ransa ganin tana ciyar sa ɗanshi dake cikinta kuma itama tana ci,haka kawai ya tsinci kanshi da sakin tattausan murmushi.
Sosai taci abincin ta kammala kenan aka banko ƙofar falon aka shigo,ba sallama,hajiya ce,rai aɓace,
Da sauri ya miƙe ita ko rumana ko ajikinta tana zaune dan dama zuciyarta ta bata itace.
"sabida baka da mutunci tun jiya nake nemanka ban gankaba,kamance da batun auranka da sameera,kazo mu zauna asan me zaa mata na lefe,amma kaƙi zuwa sabida ni ka rainani "
."hajiya kiyi haƙuri don Allah,wallahi rumana ce ba lafiya muka kwana a asibiti can cikin birni,shiyasa ban shigo ba"cewar ashrab kamar zeyi kuka.
"dallahcan sakarai sa bisu kawai wato rumana ta fini,shiyasa uzurinta ya danne nawa,wlh ka taka sannu dani magaji akan karyar yarinyar nan mara zuciya ita da uwarta zaka samu matsala dani"
A zafafe rumana ta yunƙura zatai mata wankin babban bargo se idonta ya sarƙe cikin na ashrab dake bata haƙuri da idanun alamun kartayi magana tayi haƙuri.
Ajiyar zuciya tayi sannan ta koma ta zauna ranta na mata zafi zagin ummanta sa tayi .
"dama ay har marina kinyi yunkurin yi,to yanzu da kikayi yunƙurin zagin nawa me ya hanaki,fitsararriya mara kunya,to aure zan masa da ƴar gidan daraja,gidan kuɗi gidan ƴenci ba irinku faƙirai ba,tazo ta haifamin jikoki halastattu ba rabi bariki rabi sunna ba"
Dafe kai ashrab yayi idanunsa sukayi jawur nan take gashin jikinshi ya firfito,dan tsananin ɓacin rai,jin abinda mahaifiyar tashi ke cewa,karab ya tsinkayo muryar rumana na cemata.
"hajiya ay ita bariki alalen gero ce in ka iya kasha in baka iya ba ta kwaɓe maka,mu tamu barikin tayi kyau,tinda muka bugata ƙarshe kuma ta koma ba laifi ba"
"rumana inaso ki sarrafa harshenki wannan mahaifiyatace fa"cewar ashrab kamar ze rufeta da duka.
"to se me dan tana mahaifiyarka,nace se me,ko auran soyayya nayi dakai bazaa dinga zagin iyayena ina shuru ba,bare bashin takin zamani aka biya dani,kuma gwara daka faɗamin ita ta haifeka,daga yau in sani dan ni da kallon yayarka nake mata".
Kwalar rigarta ya shaƙe ba tare da tunanin cikin jikinta ba,yace cikin fushi"ya isheki hak rumana ki iya bakinki,mahaifiyatace wannan"
.
Da ƙyar ta kwace riƙon da yay mata tace tana haki"ko kasheni zakayi se na faɗi taka fin tawa tayi,da zata zagarmin uwa kuma ace bazan tanka ba,nace taka fin tawa tayi".
Hannu ya ɗaga da nufin marinta,hajiya tai sauri ta riƙoshi ta baya tace.
"meye naka na marinta ba ji zatayiba,marin da zata ji shine wanda zaka mari rayuwarta wato aurenka da sameera muje mu kammala komai kaji ɗan albarkana"taja hannunshi suka fice daga sashin.
Itako rumana kuka ta rushe dashi ta durƙushe agurin tana rera kayanta me tsuma zuciya.
Seda ta gaji dan kanta tayi shuru.
Miƙewa tayi da nufin ta tafi gida sede ƙofar a kulle take, abinda bata saniba daze fita yaja ƙofar da ƙarfi germlock ya shiga ya zare key ɗin va tare da hajiya ta lura ba.
Bata da sauran zaɓi daya wuce ta nufi ɗakin baccinta ta kwanta dan ba isasshiyar lafiyace da ita ba.Dan ta lura ƙaddarar tata me tsayice agidan .
Muje zuwa
Nagode da adduoi ta samu sauƙi🥰💃
Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*26*
"lefe sonake ayi nagani na faɗa,magaji,banason harkar ƙaranta,dan so nake akaisu da mota,dan in nunawa saa na iya haihuwa"Cewar hajiya bayan,sunje sashin nata.
"kome kikeso hajiya shi zaayi sede ina roƙon ki da kiyiwa girman Allah ki dena shiga sabgar rumana kina zubar da mutunci na, dan Allah hajiya ki kama girmanki"ya faɗi kamar zeyi kuka.
"ay yarinyar in ka kula bata da kunya ne shiyasa amma inda me kunyace bazatayimin abinda take min ba".
"nide roƙon da nai miki kenan ki fita harkarta dan Allah"
Daga haka ta yanka masa kuɗin daze bayar be musa ba yace mata"ki kwantar da hankalinki,zan turawa habu a acct ɗinsa se kuje ku cire ku siyo"
Albarka tasa mishi sannan ya tashi ya baro gurinta,zuwa sashin nasu,dan zaune de yake agurin amma hankalinshi na gun rumana.
Koda ya buɗe falon yayi mamakin rashin ganinta,a falon,beyi ƙasa aguiwa ba ya bita ɗakinta,kwance ya sameta akan gado tayi shuru.
Sallama yayi ya shiga ya samu guri ya zauna,a gefenta yace yana murmushi"rumana daru,ɗaki kika dawo kenan?"
Bata kulashi ba,be damu da hakan ba,ya ci gaba da cewa"kiyi haƙuri rumana,dan Allah ki dinga tausasa zuciyarki,mahaifiyata nasan laifintane,sede duk son da nake miki vaki kama ƙafarta ba,darajarta tafi taki agurina,to kitaimaka ki dinga haƙuri da ita nasani bata kyautawa sede addua kawai"
Shuru tayi sede kallo ɗaya yay mata ya fahimci,ta gamsu da bayanin nasa.
Hijab ɗin jikinta ya fara ja da sauri ta riƙe,shiko jikinshi yaja ya matsa kusa da ita. ya kamo hannunta yana murzawa,yace"rumana ban sanki da daru ba naga yanzu duk kin iya,dade barki da barikin ki de ke amma yanzu gaba ɗaya kin sauya don Allah kiyi haƙuri mu zauna lafiya,wlh ina sonki."
Sosai maganar ta taɓa zuciyarta kuma ta fahimci akwai gaskiya cikin batun dan haka a hankali tace"ko yanzu koyamin akayi agidanku ni kuma na koya na iya"
Mirmushi yayi yace yana murza hannunta"iya faɗa kika koya a gidanmu,baki koyi ladubban zaman aureba?"
"Banga anayi bane shiyasa ban koya ba,wanda naga anayi shi nafi riƙewa"taja bakinta da tsuke,dan ita iya gaskiyarta ta faɗi.
Rasa abun faɗi yayi dan beda sauran magana se wasa da hannunta da yake,zuwacan yace.
"rumana inaso ki fahimci rayuwa yadda take,shi komai muƙaddarine,Allah ne ta hukunto hakan zata faru,to a matsayinmu na musulmi nagari yarda da ƙaddara zamuyi,se kiga Allah ya bamu mafita,"
Shuru tai masa amma ya fahimci zancen ya ratsa mata zuciya
Dan haka sake matsa hannunta yayi yace"nasan bakya sona right?"
Da sauri ta ɗago idonta tana kallonshi dan zancan bata tsammaci jinshi ba
be damu da yanayin nata ba ya ɗora da cewa,"to amma ay kinsan de ni mijin kine,akwai alfarmomi da dama da Allah yay min agurinki,ciki kuwa harda yiwa iyayena biyayya right?"
Gyaɗa mishi kai tayi alamun eh.
"to don Allah rumana ki dinga haƙuri da hajiyata,duk abinda zatai miki ki ɗauka mahaifiyarkice itama,wataran zata gane gaskiya ta dena don Allah na roƙeki"yayi roƙon cikin sigar ban tausayi.
"insha Allahu na dena"ta faɗi kamar wacce akayiwa dole.
Murmushi yayi me ƙayatarwa,yasa hannu ya rungumota jikinshi yana shafa gadon bayanta,itade ba baka se kunne dan shine karo na biyu da hakan ta shiga tsakaninta dashi.
A kunnenta yake raɗa mata"rumana ke me kyauce,komai naki me kyaune,zanso ki haifamin kyakkyawar baby kamar ki,kuma ki dinga koya mata yanga irin taki"ya faɗi yana shafo cikinta akaro na farko kenan da rumana taji son cikin jikinta ya taɓa zuciyarta,
Hannunta takai kan cikin itama ta taɓa,sakin ta yayi ya ɗan ja baya sannan yasa hannu ya ɗaga rigarta cikin ya bayyana fari sol abinsa,hannu ya sake ɗorawa sannan yace yana kallon fuskarta"kinason shi rumana?"
Tsintar kanta tayi da sakin murmushi me ƙayatarwa,ta gyaɗa masa kai.
Ganin faraar rumana yau ya haifar masa da farin ciki mara misaltuwa.
Cigaba yayi da janta da hira,yace"in kika haihu wanne suna kikeso asawa babyn?"
Cikin azama tace fuskarta ɗauke da faraa
"sunan ummana zaa sa"
"to in namijine fa?"
"Sunan habu zaa sa"ta faɗi ba tare da damuwar komai ba.
Murmushi yayi yace"me gari da mahaifinki ba ƙyason sunansu?"
Turo baki gaba tayi ta ɓata rai tace"haɗa kai sukayi suka badani amadadin kuɗin takin zamani bazansa sunansu ba"Ta ƙarasa maganar hawaye na biyo idonta,
Sosai yarintar tata take burge ashrab,dan haka dariya yayi yana sake nemo abinda zesa tai masa shiriritar.
Wlh banida lfyne,nima🤦🏽♀️
Muje zuwa.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*28*
"Allah sanya alkhairi,ni bana buƙatar komai agurinka"ta bashi amsa tana murmushi.
"nagode sosai rumana ki tayani yiwa mahaifiyata biyayya insha Allahu nasarace agaba"yayi maganar yana wasa da hannunta.
Shuru tai masa bata kuma cewa komai ba,har ya kammala bayaninsa,gyara zama tayi zata kwanta da sauri ya kamota yace "wai bacci tun yanzu rumana?"
Gyaɗa mishi kai tayi, batare da ta ce komaiba,"Inzo in tayaki baccin?"yayi tambayar yana wasa da hannunta .
"aa base ka tayani ba,ni na saba kwana ni kaɗai"
"to badamuwa kwanta kiyi baccinki sabida inaso mu fita da safe ni dake,dan ranar sunday nakeso mu wuce abuja gaba ɗaya,dan sameera gobe zasu kaita"
Bata kulashiba ya tashi ya fice daga ɗakin bayan ya mata seda safe
komawa tayi ta kwanta,tana saƙa da warwara ta yadda zata iya zama da kishiya da ƙananun shekarunta.
*********
Koda gari ya waye kamar yadda tasaba bayan tayi sallah ta nufi kitchen,dan samawa kanta abinda zata ci.
tana tsaka da girkin ya shigo kitchen ɗin, ya kama ya tsaya a bakin ƙofar ya jingina bayansa gamida rungume hannunsa a ƙirjinsa yana dubanta yana murmushi.
Tafiya tayi zata duƙa,tana faɗin"barka da asuba"da sauri ya ƙarasa gurinta ya kamota ya rungume ta ta baya yana faɗin"karki wahal min da kanki, maman twins kuna lfy,ya faɗi yana shafo cikin nata"
Murmushi tayi tace"lafiya lau,"a kunyace.
Kanshi ya ɗora akan wiyanta yace bayan ya kashe murya"me kike girka mana?"
"ba komai nake dafawa ba fa"ta bashi amsa tana ƙoƙarin kwacewa daga ruƙon da yay mata..
"wannan rowa kenan rumana, tunda baa dafa daniba"
Sakinta yayi yafice zuwa falon dan ya kalli news,yana kallonsa,
ta kammala komai tazo ta wuce ta gabanshi Zuwa ɗakinta,wanka tayi sannan tayi kwalliya ta sako doguwar rigarta me sauƙin nauyi. ta ɗanyi kwalliya bame wahala ba.sannan ta feshe jikinta,da turare,ta sako plate din takalminta,ta saka sannan ta nufi falon.
Tana zuwa falon ƙamshinta yakai masa,da sauri ya waigo inda take,samun kansa yayi da sakin murmushi, yana me binta da idanu.
Gabanshi ta ƙaraso, ta durƙusa tace"ga abincin can na kammala"miƙewa yayi ya kamo hannunta,ya miƙar da ita tsaye yana faɗin"muje mu karya da sauri, dan banaso mu ɗauki rana muje inda zamuje"
Koda suka zauna cin abincin se santi yake mata,tana murmushi. har suka kammala.
Ɗaki ta koma ta ɗauko mayafinta,sannan ta ɗauko handbag.
Tana zuwa falon ta sameshi ya na ƙoƙarin zuwa ɗakinta. yana ganinta ya faɗaɗa murmushinsa yana faɗin"kinyi kyau gimbiyata,kamar asace ki a gudu"
Bata ce komai ba haka yasa hannu ya amshi jakar ta,yayi gaba ta bishi abaya.
Motar ta ƙofar baya ya fita da ita gudun hajiya ta gansu ta ɓata musu budget.
Koda suka ɗau hanya rumana kallonshi kawai takeyi tana son ƙarin bayani na inda ze kaita ganin ba hanyar gidansu ya bi ba .
Fahimtar hakan yayi se yayi murmushi ya kamo hannunta,yace"cikin gari zamu shiga ki tayani haɗowa amarya ta lefe"
Maida kanta kan titi tayi sabida ta fahimci ba iya hajiyance bata son ta ba harda shi uban gayyar.
koda suka isa supermarket ɗin hannunta ya kama suka shiga ciki,
Kwandon turawa ya janyo,har biyu ya bata ɗaya suka tura,zuwa cikin gurin yace"ki zaɓa mata kaya daga naira ɗaya zuwa milyan biyar wanda kikasan kowa zeso su"
Gyaɗa kai tayi,sannan ta fara jido kayan ta zubawa.
Tam ta cike kwandunan da kaya na gani na faɗa ba abinda bata saka ba,seda suka cika kwanduna huɗu da kaya na alatu.
Ko pant da bra cewa yayi ta ɗauko dede ita da takalma, acewarshi size ɗinsi ɗaya da ita.
Biyan kuɗin yayi,sannan suka fito kai tsaye wajen siyan mota suka nufa
Nanma sata yayi ta zaɓi wacce takeso ayko zaɓa tayi ta dirje, duk azuwan na amarya ne.
Bayan sun gama address ɗinsu na abuja ya bayar yace akai masa ita can.
Bayan sun fito Gidan iyayenta ya kaita da kayan abinci kala kala,da sutura wacce shi ya, siyo musu.bayan sun gaisa da umma yay musu sallama kan ze, Dawo anjima ya ɗauketa.
Ayi haƙuri banda lfyne
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*27*
"Wanne irin bashin takin zamani kuma?"
"Bashi me gari yake bin babana shine aka