Chapter 8 Reading ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt Arewa Novels

ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 38.9K words

biya dani,ay an cuceni wlh"ta kai ƙarshen maganar tana share hawayenta da hannunta.

"ya isa haka dena kuka,gaskiya baa kyauta miki ba,kuma nima baa kyauta min ba,sabida mace kamar rumana tafi ƙarfin biyan bashi da ita,cancanta yayi dukiya tai kuka wajen aurota domin kyau da cikar halittarta"ya faɗi fuskarsa ɗauke da murmyshi,

Itama faraace a fuskarta fall,tama rasa ina zata sa kanta taji daɗi.se faraa takeyi.

Haka yay ta janta da hira har ta saki jikinta,
koda dare yayi be je gunta ba ɗakinshi ya zauna dan beson ta sake birkicewa tace bazata zauna ba.

*********

Haka aka shiga hidimar bikinshi da sameera wacce ke can ƙasae egypt tana karatu se ana eh gobe bikin zata dawo,

Itako rumana kamar ba ita akewa kishiya ba,dan hankalinta a kwance yake,duk abinda takeso samu take har ma wanda bata buƙata ba,shiyasa ta mance da batun a maidata gidansu, uwa uba batason zafi gidan megari ko harda A C shiyasa ta ƙaunaci zamam gidan.

Aisha ko Ameera umman
ta take aykawa gidanta su gano mata ita.

********

Ashrab ko da wai baya ƙaunar auren sa da sameera amma hajiya ko kamar wacce akawa albishir da gidan aljanna

Amarya ta dawo cikakkiyar mace meji da kanta boko ta zauna sede fagen kyau bata kama ƙafar rumana ba,amma da ike tafi rumana wayewa da iya ado se yazamana itama tana kyau.

Haka hajiya tasa aka kai lefe harda key ɗin danƙareriyar mota,aciki,wanda sosai hakan ya burge sameera da iyayenta.

A daren ashrab yasamu rumana acikin ɗakinta tayi rashe rashe da tulin apple a gabanta tana ta ci kamar wacce bata ci abinci ba.

"maman biyu apple ɗinne?"yayi mata tambayar yana ƙoƙarin zama kusa da ita yasa hannu ya ɗauki yanka ɗaya yakai bakinsa.

Murmushi tayi tace"eh "

"gashi zuwa nayi muyi magana kuma naga kamar bazaki saurareni ba tunda apple kikeci"

Murmushi tayi ta ture plate din daga gabanta tace"ina jinka Allah"

Murmushin shima yayi yace a sanyaye,"rumana batune dama akan auren da hajiya takeso inyi,shine nazo inji kema me kikeso abaki amatsayin kayan faɗin kishiya"

shuru tayi batace komai ba tana juya maganar aranta,a sanyaye tace "dama da gaskene zaa yimin kishiyar?"tayi maganar kwalla na taruwa a idonta.

Sosai tausayinta ya mamaye koina na zuciyarsa janyota yayi jikinshi ya rungumeta,yace a tausashe"ke kaɗaice rumana guna baki da kishiya,kiyi haƙuri hajiyace taso hakan amma ni banida raayin yimiki kishiya"

Mije zuwa

Don Allah maganin ciwon kai gefe guda likitocin gidan ku faɗa pls,
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*29*


Bayan fitar Ashrab umma jan rumana tayi ƙuryar ɗaki tace cike da kulawa.

"rumana base kince min komai ba,nasan komai,sede inaso in miki nasiha da kiji tsoron Allah rumana Allah vaze barki ba,kiyiwa mijinki biyayya abokiyar zamanki kuma ki mutuntata ku zauna lafiya,me gari ya faɗamin komai na fahimta"

Tinda ta fara maganar rumanar take kuka harda majina seda taji umman tayi shuru sannan ta dibeta a tsanake tace cikin kuka me tsuma zuciya.

"umma banason kishiya,kuma gashi hajiya tasa anmin,banason zama da ashrab gashi kunsa dole sena zauna dashi umma na rasa ya zanyi"ta sake fashewa da kuka.

Tausayinta ne fall zuciyar umma dan har seda ƙwalla ta taru a idonta amma ta basar,ta ruƙo ta jikinta tace"Rumana ta jarumace ko acikin maza bare mata,komai in kikayi haƙuri zakici ribarshi,ki dage da addua baason me ciki da sa damuwa aranta"

Haka umma tai ta mata nasiha da ƴan dabaru na mata harda kirsa ta ƙwace miji agurin kishiya.


Sun jima sina tattaunawar rumana sosai taji daɗin bayanin umman kuma ta gamsu da komai,

Yini sosai tayi agidansu,

***********


Tuni aka shirim ɗaurin auransa da sameera ya kankama,wanda zaa ɗaura acan Abuja kasancewar gidansu acan yake ita da iyayenta.

An kai lefe na ƙarya gidansu sameera kamar yadda hajiya ta buƙata,kana daga bisani aka dawo shirin bikin

Kuɗi ashrab ke baddawa bana wasa ba tunda satin bikin ya shigo.

Megari sosai yake masa nasiha kan yayi adalci agidansa dan wanzar da zaman lafiya.

Yaso tafiya ranar sunday amma hakan bata samu ba acewar hajiya sede ya jira atafi da ƴan ɗaurin aure,hakan be masa daɗiba dan beso hakanba.


Soyake yaje da rumanarsa asibiti acan aduba masa ita da kyau da abinda ke cikun nata
amma hajiya ta hana.

******-*


Dubban jama'a ne suka taru ƙofar gidan megari dan tafiya ɗaurin auran,ashrab ko na cikin gida gurin rumana yana ta rarrashinta yana tayata kimtsawa,sabida cikinta tsohone komai se a hankali take yinsa.

Seda yasa mata kaya da kanshi sannan ya yafa mata mayafi bayan ta zira takalmi,hannunta ya kamo suka fito falon tana tafiya daƙyar.

Hajiya ce ta banko ƙofar ta shigo,ranta a ɓace,wanda sosao ta basu tsoro.

" maza kaje ku tafi mana kabar mutane a ƙofar gida anata jiranka"ta faɗi tana hararar rumana dake tsaye sunkuye da kai.


"fitar da zamuyi kenan hajiya,dan atafim ne ay"ya bata amsa yana gyarawa rumana tsayuwar mayafinta ajikinta.

"kai kaɗai zaka tafi in yaso daga baya akaita,amma wallahi bazaku tafi tare ba kazo ka wuce ku tafi"


Rumana kukane ya ƙwace mata na takaici agurin ta zame ta zauna.shiko ashrab yama fita damuwa,bakinshi har rawa yake wajen faɗin.

"hajiya rumana da bata da lafiya,kuma gurin aykina vazasu ƙara bani hutu in dawo nan kusa ba me yasa haka ne hajiya,yarinyar nan bafa abinda tai miki"

"wallahi bazaku tafi tare ba,ta ɗauke ma hankali daga kan amarya,in kuma banice na haifeka ku tafin"tana kaiwa nan ta juya tai ficewarta.

Ashrab sosai ranshi ya ɓaci,yama rasa me zeyo dan yaji daɗi,zuciyarshi zafi take masa ga sautin kukan rumana dake sake hargitsashi.


Kusa da ita yaje ya zauna ya kamota,ayko shigewa jikinshi tayi tasa sabon kuka,tana faɗin"karka barni anan wallahi tsoro nakeji,katafi dani"

Rungumeta yayi ajikinshi ya runtse idonsa tausayinta na ratsa ko ina ajikinshi yace a raunane"zan dawo in tafi dake rumana wani satin kiyi haƙuri don Allah hajiya tayi rantsuwa ki daure ki tayani yimata biyayya,na fiki damuwa da rashin tafiyarmu tare,ji nake kamar wata babbar asarace zanyi,dan Allah kidena kuka"


"naji to amma ka kaini gidanmu in zauna acan dan Allah"ta faɗi a marairaice.

"darajar mace ɗakinta rumana kiyi haƙuri ki zauna anan ɗin,sati kamar yaune zakiga na dawo na ɗaukeki"

Duk yadda tas ya amince ƙin yarda yayi yay ta rarrashinta har ta amince.


Ƴan mazan kuɗi ya ajiye mata gamida wayarshi guda ɗaya yacire security ɗinta ya nuna mata numbershi da kuma yadda zata kirashi,seda ya nuna mata komai sannan yatashi ya tafi suna waingen juna,yana gama ficewa daga falon ta kife agurin tana kuka me tsuma zuciya.ga mararta dake mata wanj irin mahaukacin ciwo.



Ayi haƙuri banda lfyne
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*30*


Da ƙyar ta miƙe ta shige ɗakin ta sabida ciwon da take mata bana wasa bane.

Duk sanyin Ac dake ɗakin ita gumi ne ke karyo mata ta koina kiran sunan Allah take idanunta na zubar da kwallah.

Wayarta ta lalubo wacce ya bata ɗazu ta fara neman numbershi cikin saa ko ta danna kira,

Ashrab dake zaune a bayan mota,yayi tagumi hannu bibbiyu,abun duniya ya dameshi koda kiran ya shigo be tsaya duba ko waye ba yayi rijecting,

Kiranshi take tana kumawa yana kashewa ba tare da yasan itace take kiranba,ƙarshema kashe wayar yayi gaba ɗayanta dan kiran da ake masan ya fara damunsa dan yasan ƴan Allah sanya alkhairi ne.

Rumana kuka ta rushe dashi ta koma kiran sunan Allah. kan ya taimaketa.

Tayi kukan tayi kukan ƙarshe ma bakinta ya rufu gam Bata cewa komai se shure shure da takeyi.

Ashrab sun isa abuja ƙarfe uku na yamma kuma alokacin aka ɗaura auran,sa da sameerah,bayan an kammala ɗaurin aure nan aka shiga gaggaisawa da jamaa, kowa se murna yake tayashi shide ransa a ɓace yake.

Walima aka yi a harabar gidan nasu sameera,kamin amarya ta buƙaci ganawa da ango,saɓanin shi angon ya buƙaci ganawa da ita.

Su haisam dasuke gurin dan habu ya sanar dasu batun auran na yayansa kuma yabasu address sosai sukayi mamaki lokacin da saƙon na sameera ya iso kunnen su daga bakin ƙawarta.

Tsaki da ashrab yake saki agurin yafi dari,dan ya tsani rashin kamun kai agurin mace,

Takawa yayi ya isa sitroom ɗin da akace yaje ɗin,koda ya shiga a zaune take,taci ado kamar ba gobe,masha Allah sameera tana da kyau kuma kwalliyar tai mata kyau ba da wasa ba,

Ɗan sakin fuska yayi ganin itama se murmushi take masa,kan kujera yaje ya zauna,tasowa tayi daga kujerarta,ta dawo inda yake zaune waigowa yayi ya kalleta ganin yadda ta wani naniƙe masa,murmushi tai masa ta kwantar da kanta gefen kafaɗarshi,tace cikin siririyar murya"naji kuna shirin tafiyane yasa na nemoka mu gaisa,tunda nazo bamu haɗuba se yau"

Zame kafaɗarshi yayi da dabara yace yana diban agogo,"eh wlh sauri muke mu samu sallar laasar a jam'i,ykk"

"lafiya lau mijina,and you?"

Murmushi yayi a taƙaice yace "lafiya lau,to ni zan wuce jirana akeyi,"ya faɗi gamida miƙewa tsaye,ayko ba kunya ta miƙe ta rungumeshi tana faɗin"se mun haɗu a gidanmu kuma"

Beson bada ita yasa ya rungumeta shima,yana ɗan dukan bayanta yace"see you later"sakinta yayi ya fice daga ɗakin yana mamakin dalilin dayasa beji komai ba daya rungimeta saɓanin rumana wacce bata ma kaita ba amma ko idonta ya kalla se yaji feelings.

Cikin abokansa ya koma,nan ko sukace dawa Allaj ya haɗasu bada shi ba,ganin jambakin,sameera ajikin rigarshi,duk yadda yaso kare kansa sunƙi dena zolayarsa hakanne yasa yace.

"inma spam kuka gani ay ba komai matata ce,wanda ko ubanta baze tambayeni baasin hakan ba"ya faɗi cikin fushi.


Ayko suka sa masa dariya ganin zasu haukatashine yasa yayi shuru ya ƙyalesu suka gaji suka bari.

Gidan haisam suka je dan gidan ashrab ɗin cike yake da ƴan biki dake ta faman gyara sashin amarya.



Har dare yana can,se bayan ishai misalin ƙarfe tara,suka rakoshi gida,be buƙaci sukaishi wajen amaryar tashi ba,dan haka sallama sukai masa suka tafi shi kuma ya shiga hannunsa riƙe da tsarabar da akayo ma amaryar.

************


Rumana tun tana iya motsi har yazamana ta gaza koda ɗaga hannunta.

Tuni jini ya ɓalle mata ita kaɗai a ɗaki,har Allah yasa ta haifi bakwainin ɗanta,wanda se shushshura ƙafa yake,sanyi ya masa yawa,tun da ransa har ya mutu.

Duka akan idonta hakan ta faru wanda baƙincikin hakanne yasa itama ta sume,.


************



Koda ya shiga cikin ɗakin nata zaune take gefen gado taci ado har ta gaji,da haɗuwa.

ledojin hannunsa ya ajiye sannan ya zauna gefen gadon nesa da ita yace"ina miki barka da zuwa sameera cikin rayuwata"


Murmushi tayi me ƙayatarwa harda fari da idanu,sannan tace"nagode mijina"

"in baki sani ba to ki sani ina da mata wacce nake matuƙar sonta tana can gidan kanyahore,aurena dake ƙaddarace daga Allah wacce na amsheta hannu biyu dan haka inaso ki kwantar da hankalinki,ku zauna lafiya dake da ita"

"mu zauna lafiya da undergraduate ɗin?kasan me kake faɗi kuwa?look duk labarin ku ba abinda ban sani ba dan haka to ka sauya tunani,kama dena wannan magana karka ɓatamin firstnight"ta faɗi ranta aɓace.


Ɗago ido yayi ta ƙare mata kallon uku saura kwata sannan yace,a kausashe"with all your qualification,baki kama ƙafar rumana agurina ba,kuma inde zamane zakiyi danni a gidannan to wallahi se kin zauna lfy da matata,kinde ji na faɗa miki,wannan dare agunki yake first night,agurina kuwa second ne dan first na jima da yinshi da rumana ta"


"a barikin"ta bashi amsa afusace.


Kwasheta yayi da mari,me gigitarwa,sannan yace"bariki ay alalen gero ce,mu tamu tayi kyau,ni bana ɗaukar reni ki iya bakinki"yana kaiwa nan yasa kai yayi ficewarsa daga ɗakin ya nufi nasa ranshi na mishi zafi.


koda yaje ɗakinsa se huci yake,wanka yayi ya hau gado sannan ya kunna wayarsa dan ya kira rumana yaji lafiyarta.


Muje zuwa


Surbajo fir life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*31*


Sosai hankalinshi ya tashi daya kirata bata ɗaga ba,saukowa yayi daga kan gadon ya koma kan kujera yaci gaba da kiranta amma steel no answer.

Hankalinshi in yayi dubu ya tashi se gumi ke keto masa ta koina sabida tashin hankali.

"fushi tayi danine?bata da lafiyane?ko bata kusa da wayarne?"sune abubuwan da yake ta ayyanawa azuciyarshi.

Yaso yasa aransa bacci tayi amma zuciyarshi tafi karkata kan akwai matsala de babba.

Yaso kiran habu yaje ya diba masa ita amma daya tuno habu na Abuja seya fasa zuciyarshi taci gaba da bugawa.

Misalin ƙarfe ɗaya na dare yaji gaba ɗaya in yaco gaba da zama ze iya mutuwa agurin sabida zullumin da zuciyarshi ke masa,dan ya kira wayarta yafi so ɗari bata ɗaga ba.

Doguwar rigace ajikinshi jallabiya key ɗin mota kawai ya ɗauka,ya fice daga ɗakin nashi

Da har ze wuce se kuma ta dawo setin ƙofarta yaui nucking,dama ba bacci takeba sabida baƙincikin daya kumsa mata,

"na tafi kano,kizo ki kulle falon"ya faɗi ba tare daya tsaya sauraronta ba,

Kasa cewa komai tayi sabida batun nasa daskarar da ita yayi,seda ya fice ta bishi da saurinta sede kan ta ƙarasa yaja motarsa ya fice daga gidan duk da cewa ya hangin tahowar tata gurinshi.

Tsayawa tayi tana haki tana hangenshi har ya fice,ta juya ɗakinta tana zubar da ƙwallah .

*********

Ware motar yayi sosai akan titi,dan beƙi ya isa kano a minti talatinba .

AWA huɗu ya kwashe kan ya iso garin nasu wanda ya iso da asiba,ana ta sallah a masallatai.


Kowa na gidan yayi mamakin ganinshi,adede lokacin,sabida suna sallar jam'i ya samesu.

Wucesu yayi kamar kububuwa zuwa sashin nashi hajiya ta mara masa baya tana faɗin"mahaukacin ina ne kai zaa kaima amarya jiya ka barota"


Be kulata ba seda ta sake jefo masa tambayar sannan yace"wayar rumana nake kira bata ɗaga ba shiyasa na zo dan inga ko me ke faruwa dan jikina be vani komai lafiyaba"

Salati hajiya tayi ta Sanar da Allah,sannan tace tana riƙe baki "sabida zafin silalen macaronin asara,shine ka baro sabuwa kataho gun fsohuwa dan kawai ka kira waya baa ɗaga ba"

Be kulata ba ya buɗe ƙofar falon nasu ya shiga itama ta bishi abaya,koda ya nufi sashin ɗakunan baccinsi itama binshi tayi abaya,


Kanshi tsaye ya tura ƙofar ɗakin na rumana ya kutsa kai ciki,hajiya na biye dashi abaya tana surfa masa masifa..

Abinda suka gani shinr ya ɗaga hankalinsu












Muje zuwa


Surbajo fir life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*32*



Da wani mahaukacin gudu yayi kanta,yana jijjigata yana faɗin"rumana ki tashi rumana nooooo karkimin haka wake up!!!!!!!!"yana jijjigata yana kuka da idanunsa,


Hajiya ta tsorata sosai da ganin rumana da jinjirinta a halin da suka samesu,ta kasa koda tarine.

Miƙewa yayi da sauri rungume da ita dan babyn kallo ɗaya yay masa ya fahimci ya mutu duba da jinin daya gani busasshe a hancinsa ya zubo,

Ta gaban hajiya yazo ya fice da gudu ɗauke da ita yakaita mota,yana sakata be jira komai va yayi ribars ya fice da mahaukacin gudu daga gidan zuwa asibiti.

Faɗan da likitocin suka dinga yi baze faɗuba dole se toshe kunne yayi ƙarshe da suka dameshi se yace hawaye na biyo idonsa cikin ƙaraji.

"ku zaneni amma don Allah ku taimakeni ku kula da matata,karku bari ta mutu,dan Allah"


Sosai ya basu tausayi,dan haka maida hankali sukayi kanta,kowa na gwada basirarsa.

Jini suka shaida mishi zaa ƙara mata,da yake shi ɗin donor ne baa samu wata matsala ba aka ɗebi nashi bayan ansashi yaci abinci dole badan daɗiba.

An ɗaura mata jinin,kuma Alhmdllh numfashinta yana sauka da kyau zama yayi kusa da ita yasa ido yana kallonta gaba ɗaya ji yake kamar ya mayar da ita cikinshi, dan tausayinta da yake ji.

Share kwallar data zubo masa yayi da tafin hannunsa,yana faɗin"kingama kuka rumana insha Allahu matuƙar ina raye,kome kikayi daidai ne,zan miki gata rumana wanda Se kin zama abar kwatance acikin mata,sanadina kin jima kina wahala,in ban soki na tausaya miki ba rumana inyiwa wa,?ki gafarceni tafiya da nayi bada ke ba sani dole akayi"ya faɗi yanz kamo hannunta.

Baiwar Allah bata ma san yanayi ba,tana tsakanin mutuwa da rayuwa.se abinda Allah yayi.


Kayan jikinta duk warin jini suke hakanne kawai yasa ya barota a asibitin yazo gidan dan ya ɗebar mata kayan sawa yaje ya sauya mata..


koda ya shiga sashin nasu yayi mamaki da be ga gawar yaron ba,abinda be saniba bayan fitarsa hajiya zani tasa ta ɗauki yaron jiki a sanyaye tana ƙare masa kallo,duk da ƙanƙantarshi hakan be hanata hango kamannin ashrab atattare dashi ba.kamar yayi kaki.

Ɗaukarshi tayi ta nufi sashin matan gidan dashi,takirasu kowa ta sanar dashi abinda ya faru.


Amaryar me garin ce tace"wallahi yaya ki san me kikeyi,lokaci yayi da zaki dena sa kanki cikin sabgogin gidan Ashrab,wannan masifa da yawa take,"

Hajiya wacce gaba ɗaya a tsorace take tace baki na rawa"wallahi amarya tsautsayine da kuma ƙaddara,wanda megari ma ya hanani nice de naƙi ji,shi kanshi magajin yasha roƙona "ta ƙarasa maganar tana kuka dan sosai tai nadamar abinda ta aykata.

Koda ya ɗauko kayan sauya na jikinshi yayi sannan ya baro sashin ya nufi na iyayen nasu.

Sosai ranshi ya ɓaci gani yadda sika sa masa ɗa agaba suna kallo,hajiya na matsar kwalla wacce shi agunshi ta munafunci ce.


Ƙarasawa,yayi da saurinsa ya kutsa cikinsu ya ɗauko ɗansa ya juya ze fice muryar hajiyacs ta katseshi"magaji ina kuma zaka kaishi?"

"ba agidan zoo aka samoshi ba bare akewaye ana kallonsa wannan jini na ne,ɗanane hajiya!!!"ya faɗi cikin ƙaraji,dan ji yake kamar ya rufeta da duka a halin da yake ciki na baƙin ciki.


Sosai jikinta yayi sanyi jin furucin nashi ta kasa basho amsa se hawaye datake zubarwa.


Amaryace ta dakatar dashi tace"kawoshi nan magaji,megari na faɗawa a waya,shine yace a ajiyeshi gashinan ƙarasowa yay masa sutura,kayi haƙuri munyi kuskure ajiyeshi a waje da mukayi"ta faɗi lokacin data ƙarasa gabanshi tana miƙa masa hannu,ya bata shi.

Murmushin ƙarfin hali yayi sannan

8 / 13