Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
akai ba,dan nauyinta nakeji,shi mara kunyan yaje da kansa"cewar megari cikin faraa.
"wannan shi yafi komai sauƙi gurin magaji tsab zeje wlh bade rumana bace,ay abinda yafi haka ma ze aykata "cewar hajiya tana dariya.
Shiko Ashrab da izzarsa ya shiga sashin nasu,inda ya samu sameera hakimce akan kujera tana chattinh,
Sallamar shi tasa ta ɗago ta ƙare masa kallo a wulaƙance,be kulata ba yasa kai ze wuce da sauri tasha gabanshi ta riƙe ƙugu,tana kaɗawa tace "se yanzu kilakin taka ta baro ka kenan?"
Mumushi yayi sannam yace"zuwa nayi in sauya kaya in koma kinsan amarcin namu yafi gaban kala ɗaya"ya faɗi yana dariya dan yasan ya tsokano ta zata fara masifa.
Muje zuwa
[10/29, 1:45 AM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*45*
"Sabon yi a titine yasa koda kuka rikiɗe daga ƴan barinkin baku mance barikin ba,"cewar sameera cikin fushi.
Murmushi yayi me ƙayatarwa yace"wallahi fa sameera kinde ganmu,mun rasa tsugul aranmu,se ƙara yin abinda ke zubar sa ƙima da darajarmu muke,bacin munsan mu ɗin fankon ashana yafimu,vari kedai sameera ay bariki batayi ba"
Ko ajikinta bata fuskanci baƙar magana ya faɗa mata ba,dan haka masifar ta taci gaba dayi yana maida mata,har de yaba banza ajiyarta ya wyca ɗakinshi yayi wanka ya fito kenan ya samu sameerar a ɗakin ta riƙe ƙugu se jijjiga take,sabida bayan ya wucene ta fahimci wannan fankon da yace da ita yake.
"lafiya kuwa kika shigo min ɗaki?"ya tambaya yana goge ruwan jikinshi,rushewa tayi da kuka tace cikin kukan.
"kadena yimin haka,tun kanayimin be damuna yanzu damuna yake,nace ma school life ne kaƙi fahimta,meyasa ne kakemin haka"ta durƙushe agurin tana kuka.
kaico baiwar Allah ita kawai school life ne yasa ya isheta hujjar riƙewa adena aybatata,tausayinta yaji ya kamashi,ƙarasawa yayi inda take durƙushen tana kuka yasa hannu ya ɗagota ya rungumeta ajikinshi,ya fara shafa gadon bayanta yana faɗin"laifinkine sameera,kece kike tsokanoni yasa nake miki haka,amma na dena daga yau,namiki alƙawari,kema inaso kisani ba wani school life daya baki warrant na kije kiyi fasiƙanci,haramunne,kuma kuskure me girma,wanda se kin duƙufa neman yafiyar ubangiji kamin ya yafe muki"
Gyaɗa mishi kai takeyi,yajima yana rarrashinta sannan tayi shuru,kan gado yaje ya zauna itama ya zaunar da ita,yace mata a tausashe.
"Sameera dan nayiwa hajiya biyayya na aureki hakan bashi ke nuna bazan kare mutuncinki ba,sabida aure ba abune na wasa ba,inaso ki kama girmanki ki natsu ki fita harkar yarinyar nan rumana,rainaki zakisa tayi in kina shiga shirginta wanda hakan baze haifar da ɗa me ido ba,dan haka ki natsu kisan me kikeyi rumana tana da daɗin zama inde kin fahimceta"
"kishiya bata da wani daɗin zama komai daɗinta matuƙar mijinka take aure yaƙi ne tsakaninku"ta faɗi tana harararsa.
Shuru yayi yana nazarinta kamin yace"yaƙi da rumana baze haifar miki da ɗa me ido va sameera kama girmanki shine darajarki agurinta,amma fa shawarace"ya faɗi yana murmushi,
Harararshi ta kuma yi ayko hannu yasa ya damƙota,rigarta ya fara rabata da ita yana faɗin"wa kike harara? ni saankine"yana kaiwa nan ya fara ƙoƙarin rabata da pant ɗin jikinta,ayko nan take zufa ta keto mata data fahinci manufarsa,riƙeshi tayi gam tashiga bashi haƙuri tan Faɗin"na tuba dan Allah kayi haƙuri wlh bazan ƙara ba"ta faɗi jikinta na rawa.
Dariyar mugunta yayi yace"au kice ba kya kuma son gakkin naki?"
"Da zafi kakemin shine yasa na haƙura"
Tausayi ta ba shi yace "to ay kece tsiwarki yawa gareta kuma ku mata tanan kawai ake faɗa muku magana kuji,shiyasa nai miki gargaɗi"
Shuru tayi itade fatanta ya saketa,kar ya gana mata azaba.
Aykko sannu a hankali yabi da ita,har yasamu ta saki jikinta,dashi suka raya daren,shide lami ne agurinsa itako sosai lamarin yay mata daɗi har tana fatan akuma.
A washe fari a waya yaba rumana umarnin ta kimtsa duk abinda zata buƙata,dan da safe zasu tafi beson tafiyar rana,memakom su tafi lahadi ya fasa asabar yakeso su tafi kamar wanda ake tsikara agarin.
.
Rumana inna tasamu ta faɗa mata abinda yace innako dariya tayi tace"shifa da kanshi ya kawoki rumana,dan kuma yazo yace ze ɗauka se cibi ya zama ƙari,aa ba haka nake ba ni Allah ya kaiku gida lafiya"
Sosai hakan da inna tace yay mata daɗi,dan haka godiya tayiwa innar tata.
.
Duk abinda tasan zata buƙata ta Ɗauki abin ta.
Da misalin ƙarfe shida na safe suka yiwa iyayensu sallama suka dauki hanyar abuja,tafiyar sa iyayensu kejinta daban,haka zalika su masu tafiyar jikinsu asanyaye yake yayin tafiyar sunde tafinne dan basu da yadda zasuyi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[10/29, 8:32 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*46*
Tafe suke ba me cewa kowa komai,sameera an hakimce a gaban mota yayinda rumana ke zaune a bayan motar,
Hannun ashrab sameera ta kamo ta riƙe,da sauri ya kalli mirror dan yaga reaction ɗin rumana,ga mamakinsa murmushi tai masa ta ɗaga masa gira gami da kashe masa ido.
Kaɗan ya rage kan motar ya kwace masa dan har ya sauka a titi,wanda itako sameera ta ɗauka riƙeshin da tayine,dam haka cikin kirsa da kisisina tace"becarefull fa my d"
Bece komai ba,sema maidawa rumana martani da yayi.
Haka suka ci gaba da tafiya,sameera na riƙe da hannun Ashrab yayinda rumana ke riƙe da linzamin zuciyarsa.
Suna tafe direbobin dake dawowa suke shaida musu hanya ba lafiya,ana fashi,dole suka yada zango a wani ƙaramin ƙauye,inda duka suka fito daga motar dan su sha fresh air.
Rumana bata fito ba ƙafafinta kawai ta fito dasu yayinda Ashrab ya fito itama sameera ta biyoshi abaya manne dashi ko kallo basu ishi rumana ba,wanda hakan sosai ya burge ashrab,har seda ya faɗi a bayyane "undergraduate with class,"komai nata akwai aji acikinsa ba hayaniya ba baragada.
Zagayowa yayi ta gefenta yace yana murmushi"madam azumin magana akeyine yau?koko tsada tayi"
Fari tayi da idonta tace cikin salon ɗaukar hankali"ko kaɗan ranka ya daɗe,inade jira mu isa gida ne"
Wata uwar harara sameera ke wurga mata wacce rumana tayi kamar bata gani ba,
"tunani me kyau gimbiyata,har na ƙosa mu isa gidan,"ya faɗi yana kashe mata ido.
"kaga malam ay girkinane se abari sena fita kwayi maganar"cewar sameera cikin fushi.
Dariya suka kwashe da ita gaba ɗayan su atare rumana harda tuntsirewa,ashrab da ƙyar ya gintse dariyar yace"sameera shi kwanan girkin har akan titi ake rabonshi,?sannan waya ce miki in mace bata da girki vaa magana da ita?"
"Abunne naga ze wuce gona da iri in maganar ta Allah ce ayita sak mana ba tare da wani kwarkwasa ba,"
."au Magana zanyi kamar namiji aa Wlh bazata saɓuba"rumana ta faɗi tana murmushi.
"nan de ba filin dandi bane"cewar sameera cikin fushi.
"ya isheku haka maza ku shiga mu wuce an saki hanyar"cewar ashrab lokacin daya ,zaga ya shiga motar.
Shiga sukayi kowa ta rufe yaja suka tafi,sameera se mita take tana ta takalar rumana amma ta ba banza ajiyarta.
Muje zuwa
.Surbajo for life
[10/29, 9:23 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*47*
Sun iso Abuja lafiya se tarin gajiyar zama,suna biyo hanyar unguwarsu sameera ta dubi Ashrab tace"ya zamu wuce gida ba kayo mana take away ba"
Rumana dake zaune abaya ce tayi hanzarin cewa"take away kuma,mu meye amfaninmu da bazamu dafa ba,gaskiya nide kar ayo dani"
"kaji munafuka mu kwaso wannan uwar tafiyar shine har girki zamuyi?dan munafunci,to ni take away ɗin nakeso,"
"wannan ay ba abin faɗa bane muje asiya miki naki mu in mukaje gidan se adafa muci har kema in kina buƙata se azubo miki"
"Allah ma ya kyauta inci abincin wannan kazar"ta faɗi tana kyaɓe baki alamun ƙyama ga rumanar da ƙasƙanci.
Ba wanda ya kulata acikinsu har suka je gidan abincin aka siya mata,,bata dena masifa ba.
Suna isa gidansu,Ashrab yayi hanzarin fitowa ya buɗewa rumana ƙofa yana murmushi yace"barka da dawowa iyalina,nayi kewarki sosai"fitowa tayi tana murmushi ta taka cikin salon ɗaukar hankali ta shige jikinshi ya rungumeta,
Sameera dake tsaye kamar gunki afusace ta ƙaraso gurin,tana faɗin"Ashrab me kakeyi ne haka,wai kai meyasa baka da tsoron Allah ne girkina agabana kuma kake rungume wata wallahi Allah se ya sakamin"
"muje ka rakani jasan na kwana biyu rabona da gidan nawa na mancs abubuwa da dama"cewar rumana cikin kirsa.
."baki da matsala gimbiyata"yafaɗi gamida riƙe hannunta suka nufi part ɗin nasu.
Sameera afusace ta mara musu baya sede kan ta cinmusu sun shige sun turo ƙofar.
Muje zuwa
Surbajo for life
[10/30, 6:28 AM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*48*
Bubbugawa take da duk ƙarfinta amma basu damu ba bare ma su nuna sun jiyota.
Dole ta haƙura tabar gurin zuwa nata ɓangaren ranta na mata zafi.sede tasha alwashin koya musu hankali inde itace.
Rumana ko suna shiga,sashin nata ta zare mayafinta ta ajiye akan kujera ta fara kewaya falon fuskarta ɗauke da murmushi,tana faɗin"yayi kyau,sosai mijina,amma de da ba haka yake ba ko ido nane"
Takowa yayi ya iso gareta ya rungumeta ta baya ya ɗora kanshi kan wiyanta yana murmushi yace"lokacin tsoron mijin naki kikeyi shiyasa baki saki jiki kin tantance ba"yayi maganar kamar me raɗa,
Kwantar da kanta tayi a ƙirjinshi tana murmushi tace"da gaske baka sauya komai ba?"
Ƙara haɗeta da jikinshi yayi dan sosai yakejin daɗin tudun mazaunanta dake taɓo hajiya kande,shinshina wiyanta yayi sannan yace "mutum nada mace kamarki wacce kullum bata tsufa,ay dole komai nata adinga sabunta shi akan lokaci"ya ƙarasa maganar yana latsa cikinta.
Zillewa tayi tana dariya tayi hanyar da zata sada ta da step.da sauri ya ƙarasa inda take ya sureta yana faɗin"wlh rumana dawowarki ji nake kamar an gafartamin komai,rashinki kusa dani babbar masiface wacce bana fatan sake kaciɓus da ita"
Ruƙo wiyansa tayi tace tana ciccilla ƙafa,"nima haka mijina me sona"
Ɗakinta ya kaita,suna shiga ya direta,ayko sosai komai na ɗakin ya burgeta,maajiyar kaya ta buɗe ayko kaya ne maƙil aciki,duk sababbi,wanda sosai hakan ya bata mamaki,takalma ma da jakunkuna dik gasunan.
Takowa tayi ta dawo inda yake zaune yana kallonta,kan cinyarshi ta zauna,gamida saƙalo wiyanshi tace kamar wacce zatayi kuka"wainnan kayan fa?da yaushe ka siyosu ?"
Ruƙo ƙugunta yayi ya ɗora haɓarshi akan boobs ɗinta yace yana lumshe ido"tun daga ranar dana fara ganinki rumana nasa a raina kece uwar ƴaƴana,sede ina miki kallon ƙaramar yarinya alokacin wacce ko na faɗa miki damuwata bazaki fuskanta ba,"hararar datake jefo masa ne yasa yay shuru yana dariya,mintsininshi tayi tace tana riƙe masa kunne"ni ba yarinya bace,shekara 17 ba wasa bane kaji ko"ta faɗi tana zaro ido alamun gargaɗi.
."tuba nake aunty rumana"ayko gaba ɗaya suka kwashe da dariya,seda suka tsagaitane tace cikin shagwaɓa"aunty kuma ay ka maidani tsohuwa"
"ko kusa wai girmanki na baki ne aunty ruma"ya faɗi cikin sigar tsokana.
Duka takai mishi aƙirji,da sauri ya riƙe hannunta suna dariya yace."tun daga ranar dana amshi budurcinki rumana nasa araina inzan karaɗe duniya sena nemoki,kece mahaɗin rayuwata,rumana,to daga lokacin ba fara siya miki wainnan kayan,dan jikina kullum yana bani ke ɗin tawace"
"Takace ko ta har abada mijina"ta faɗi tana kwantar da kanta a ƙirjinshi.
Toilet ya shige ya ɗauro alwala itama taje ta ɗauro suka rama sallar azahar sannan ta miƙe tace"minti talatin kawai ya wadatat yanzu zan dawo"
Miƙewa yayi ya ruƙota yace"minti talatin baki kusa dani rumana daidai yake da shekara talatin,ki lamunce min na biki koma inane zaki"yayi maganar amatairaice.
Murmushi tayi dake nuna taji daɗin maganar tashi tace"to muje kitchen zani dama in sama mana abinda zamu ci"
Be barta ta tako da kanta ba da kanshi ya ɗaukota zuwa kitchen ɗin.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta sama musu abinda zasu ci kasancewar komai akwai,a cikin fridge,da store.
Bayan sun ciyar da juna ne sun ƙoshi,kowa ya nufi ɗakinshi dan ya watsa ruwa kamin akira sallar laasar.
Mije zuwa
Surbajo for life.
[10/31, 1:03 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*49*
Sameera ko na nata sashin taci kuka ta ƙoshi dan kowanne daƙiƙa akan idonta yake bugawa,sabida zabin abinda sukayi mata.
Daƙyar ta samu tayi wanka,ta zira doguwar riga tai sallah,ta koma falonta ta kwanta,dan bata jin zata iya cin abincin da ya siya matan sabida ɓacin rai.
Ashrab be waiwayi ɗakin sameera ba seda ya dawo daga sallar ishai,sannan ya nufi sashin nata.
Da sallamarsa ya shiga falon,zimbur ta miƙe zaune tana kallonshi,ba kinta na rawa.
Gefenta yaje ya zauna yana ƙare mata kallo,lokaci ƙanƙani har tayi zuru zuru.
"lafiya kike kuwa sameera?"ya tambaya cikin kulawa gamida ruƙo hannunta,
Hawaye ne ya kubce mata ayko tasa mishi kuka,ruƙota yayi gaba ɗayanta zuwa jikinshi,yana shafa gadon bayanta.
Ta jima tana kukan kamin zuciyarta tai mata sanyi ta yi shuru se ajiyar zuciya da take saukewa.
"tunda kinyi shuru yimin bayanin damuwarki"
"girkina ne fa yau amma ka tafi gurin matarka ba tare da ka duba hakan ba kyau ba"tayi mgnr tana share hawaye.
Murmushi yayi sannan yace"watakan in na fahimceki kishine ke damunki kenan ko?"
Shuru tayi bata bashi amsa ba, sede kallonshi tayi da rinannun idanunta.
Murmushi yayi sannan ya gyara zamansa yace a tausashe yana wasa da hannunta"sameera dan inason rumana hakan baze sa in tauye hakkinki ba,a matsayinki na matata,dan haka zanyi iya bakin ƙoƙarina in kare mutuncinki,yau ba kwanan girkin ki bane a ƙaida ta addinin musulunci,tunda yau rumana ta dawo itace da girki,sede in itace tace bazata karɓa ba,dan haka ki tashi ki share hawayenki,kiyi shuru,kar ki bari taga kukanki renaki zatayi,"
Share hawayenta tayi yana tayata,sannan ya miƙe tsaye riƙe da hannunta itama ta miƙe tsaye.
se alokacin ya lura da abincin nata dake ajiye kan centre table,da sauri ya dubeta yace."meyasa baki ci abinci ba bayan ke kikace asiyo miki?"
Shuru tayi batace komai ba murmushi yayi yaja hannunta zuwa ɗakin nata.
Suna shiga yace"oya yi maza ki shirya kiyi ado,dan banso a raina min ke,maza ki caɗa ado ki zo muje sashin rumana,zamuyi mgn"
Da zata musa amma kuma se ta fasa ta wuce toilet ɗin tayi wankan ta fito ta shirya duk yana kallonta yana ta yaba mata tana murmushi.
Ayko fess ta fito da ita,se ƙamshi take,ta zira takalmi ya kama hannunta suka fice zuwa sashin na rumana wacce kecan kan dinning tana shirya abincin dare data kammala tun ɗazu,taje tayi wanka ta cancaɗa ado,shine ta dawo shirya dinning ɗin.
Sallamar Ashrab ɗince tasa ta ɗagowa da sauri fuskarta ɗauke da faraa tana amsa sallamarsa.
Yadda ya ruƙo hannun sameera,tana wani narkewa a jikinshi,dan taba rumanar haushi,ayko bata ji daɗin ganinsu ba amna seta daure tayi kamar bata ankareba.
Ta ɗaya gefen nashi taje ta rungumeshi gami da sumbatar kumatunsa,ayko sameera wacce bata iya gani ta ƙyale,a fusace tace"tunda kikaganni ajikinshi ay na rigaki seki bari sena bari kizo kema"
Dariya rumana tayi tace"aunty sameera ay ba laifi bane tunda kafaɗun biyu aka masa ke ɗaya ni ɗaya"
"Shikenan ba faɗa kowa ta samu "cewar ashrab yajasu duka zuwa kan dinning ɗin sameera se cika take tana batsewa.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[11/1, 10:29 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*50*
Ko gurin cin abincin bata saki fuska ba kuma tana ci tana yatsina fuska alamun ba daɗi,alhali tunda take bata taɓa cin abinci me daɗin wannan ba,kishi ya hanata nuna hakan.
Ashrab cikin so da ƙauna ya ɗado yana duban rumana yace"madam wannan girki naki yayi daɗi sosai"
Murmushi tayi gamida fari da ido taca cikin muryar ɗaukar hankali"mijina nawa,Allah de ya barmin kai,wannan zuzutawa haka"ta faɗi tana ɗan riƙe baki.
Dariya yayi me sauti yace"ba zuzutawa a lamarinki rumana komai akace akanki kin cancanta,baa zuzutaki ba matata"
Sameera ce ta amshe zancan da cewa"au yanzu de ko,amma naga dana ce mata jahila dabba,jaka,cewa kayi,na rage mata matsayi?"
Da sauri ashrab yakai dubansa gunta har ƙwarewa yayi dan ya firgita da jin zancan na sameerah.
Dariyar da rumana keyi ce tasa yayi saurin waigawa gurinta,ruwan sanyi ta tsiyayo a cup ta nufo bakinsa tana faɗin"wallahi in ka ƙware bazan yarda ba"ta faɗi tana turo baki gaba.
Ruwan ya karɓa ya sha,amma har lokacin ya kasa magana ,rumanar ce ta sake cewa"aunty sameera ay gaskiya ya faɗi,kin rage min matsayi in kika kirani iya haka,dan haka ba komai yayi daidai be ɓata raina ba"ta faɗi tana bubbuga bayan ashrab ɗin kamar yadda akewa yaro inya ƙware.
"karki kuma cemin aunty ni ba auntynki bace"cewar sameera cikin fushi.
"To se me dan na dena ce miki auntyn ay nasan sunanki sameera girmamawa ce tasa nake faɗa miki auntyn daga yau na dena cewa se me?"rumana ta faɗi cikin ɓacin rai....
"rumana ban sanki da haka ba ya isa haka pls,banason hayaniya"
Tebur ɗin cin abincin sameera ta daka ta miƙe tace azafafe"au ni ga ƴar iska ko,shine ita zaka wa magana ta dena,to ni kasanni a hakan zanci gaba a hakan kuma wlh kin kirawo wa kanki masifa"ta faɗi tana nuna rumanar.
"ta tsaya akanki ita masifar,amma rumana ni na girmewa duk wani makircinki"
Bata Kulata ba ta nufi hanyar fita daga falon da sauri ashrab ya miƙe zebi bayanta dan yafi so su zauna lafiya da junansu,ayko rumana ta miƙe itama afusace tace masa.
"kan ka bita yana da kyau ka ɗauki duk abinda kasan zaka buƙata base ka dawo ba "tana gama faɗin haka ta ɗauki wayarta dake kan dinning ɗin tayi wucewarta ɗakinta ba tare data Sake kallonsu ba.
Sameera ganin ya tsaya ne yasa itama ta tsaya tace"Au tsayawa kayi?tunda ga hajiya ko?amma ko wlh ka rako maza,sallamar taka har takai haka dama"
Be bi takan zantukan nata ba ya marawa rumana baya da ɗan gudunsa,dan yana tsoron Allah yana gudun fushin rumanar,shiyasa ya hanzarta bin ta da gudunsa kan tayi zargin ko sameerar yaybj.
Da gudu ta fice a ɓangaren tana kuka,dan Allah kaɗai yasan zafin da ziciyarta ke mata na wannan wulaƙancin da Ashrab ɗin yay mata.
.Mije zuwa
.Surbajo for life.
[11/2, 9:31 PM] zahrasurbajo1: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*51*
A gaban mudubi ya sameta,tsaye tana jona wayarta a caji.
Ƙarasawa yayi gurinta,ya tsaya a bayanta yace"me yasa haka ne rumana?"Ya faɗi a tausashe,
Raɓawa tayi ta gefenshi ta wuce kan kujera sannan tace"da akai me fa?"ta faɗi cikin yanayi na halin ko in kula.
"yanzu nufinki biye mata zakiyi ku dinga tada min da hankali har ku jawomin reni a maƙwabta ko? "
"Au ni kaji haushi ma kenan akan abinda ya farun,?"tayi mai tambayar cikin yanayin tuhuma.
Kamo hannunta yayi lokacin daya matsa kusa da ita