Chapter 2 Reading ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt Arewa Novels

ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 13

3K to 6K   out of 38.9K words

asibiti wlh,muna tafiya a hanya hisham ya buge wata yarinya ƙarama wlh, da mota,to kasan case ɗin naku"

"subhanallahi,hope de ba seriours case bane,?"Umar ya tambaya

"Ta de karye a ƙafarta wlh kuma ga raunuka sosai ajikinta"


"Allah bata lafiya,zan zo kuma insha Allahu zaayi duk abinda ya dace"

Daga haka sukayi sallama ya kashe wayarshi.

dubansa yakai gun Ameera wacce se ɓarin sanyi take,yace a nutse"ki kwantar da hankalinki zata warke fa"

Kuka ta rushe dashi sannan tace"to ay dukanmu yunwa muke ji,wallahi,"

Da sauri ya ƙarasa gurinta ya kamo hannunta ba tare da tunanin komai ba danshi kallon yara yake musu,ita ko se ƙoƙarin ƙwace hannunta takeyi daga ruƙon da yay mata,da taga beda niyyar sakinta ne yasa tace.

"Dan Allah ka sakar min hannu,wallahi mu iya yawon bariki kawai,muka fito ba yawon iskanci ba,ka sakarmin hannu"ta faɗi tana kuka.

Ba Ashrab ba hatta hisham dake gefe zaune cikin damuwa seda ya yi mamakin jin abinda tace,

Junan su suka kalla shi da shi,sannan hisham yace"yawon bariki fa kikace,?"

Da sauri ta gyaɗa musu kai ta ƙara da cewa"tunda muka zo garin nan muke barikin kawai de kuɗine bamu samu ba"

"yanzu nufinki ku ƴan bariki ne?"hisham ya sake jefa mata tambayar.

"kai riƙaƙƙu ma kuwa,yini mukayi yau muna bariki,"


Ashrab tsaki yayi sannan yace"look hisham ka bar tambayarta,tunda ta riga ta faɗima abinda ya kawosu,muje mu siya mata abinci"ya faɗi rai a ɓace.

.Ficewa sukayi zuwa restaurant ɗin asibitin sukayo mata takeaway.

Ga mamakin Ashrab hannu baka hannu ƙwarya take cin abincin har ta kammala.

Ruwa tasha tayi gyaza tai hamdala sannan ta dubesu tace"nagode Allah ya biyaku da gidan aljanna in ƙawata ta tashi dan Allah itama ku siya mata bata iya jure yunwa"
Ta faɗi hawaye na biyo idanunta.

"ba damuwa zaa siya mata"hisham ya bata amsa.

Umar police ne ya iso cikin kayansa na ayki,kai tsaye gurin doctor suka kaishi,sannan suka ɗunguma zuwa gurin da ummu rumana take,sosai ya tausaya mata gami da mata fatan samun lafiya.

Duk abinda ya dace yayi a matsayin ɗansanda shi yayi sannan yabar asibitin.


Doctor safiyyace ta nemi ganinsu dan haka basu ɓata lokaci ba suka je,bayan sun zaunane tace a tsanake"Ashrab zaku iya zuwa gida yanzu sabida dare ya fara kuma ƙaida ta asibitin nan kunsan bama bari ayi jinya mu muke kulawa da komai"

"ba komai doctor,zamu tafi in yaso gobe ma dawo da safe before muje office"cewar Ashrab yana duban agogon hannunsa.

Ficewa sukayi Ameera ta nemi guri ta zauna dan tsoron binsu take,hisham ne ya kalleta yacs"amma da hausa tayi magana,zaki nemi guri ki zauna"ya faɗi cikin fushi.

miƙewa tayi tabi bayansu dan Ashrab ko kallo ma bata isheshi ba,ya yi gaba abunsa.

Koda sukaje gurin motar,buɗe mata gidan baya hisham yayi ta shiga,in banda ƙarin rana ba abinda takeyi.

Suna gama shiga Ashrab yaja motar da gudu suka fice daga Asibitin ya nausata kan titi,yana tuƙi hankali kwance.

Gidan hisham ya nufa,da sauri hisham ya waigo ya dubeshi bakinsa na rawa yace"Ashrab kafa san halin zainab sarai da ɗan banzan kishi yanzu tsab zata iya illata musu yarinya pls"

"relax zan mata bayani,kasan ni tana ganin girmana"

"wallahi bazata fahimta ba sabida jiya ban kwana agida ba kuma gashi har dare yayi se yanzu inje mata da yarinya wallahi bazata yarda ba"ya faɗi kamar me shirin kuka.

Be kulashi ba kuma yasan baze kulashin ba kuma be fasa nufar gidan na hisham ba,

Horn yayi a ƙofar gidan megadi ya leƙo,sannan ya koma da sauri ya buɗe get ɗin, dan ya fahimci motar ta ubangidansa ce.

Shide Hisham ji yake kamar zeyi kashi a wando sabida tsoron daya kamashi,

Shiko Ashrab ko ajikinsa,yayiwa Ameera umarnin ta fito ayko fitowar tayi sika nufi falon gidan.

Ƙararrawar sanarwa ya latsa hisham na tsaye ƙiƙam yana kallonsa.

Ayko aka buɗe ƙofar,masha Allah kyakkyawace ajin farko,ba abinda Allah be bata ba,fuskarta ɗauke da faraa,tace"ustaz Ashrab kaine tafe a tsohon darennan?"

"to ya na iya zainab tunda kina auran rago tsoronki yake,gidan ma se na rakosa"ya faɗi yana murmushi.

"Bissimillah ka shigo mana ka tsaya awaje".ta faɗi tana kaucewa dan su shige.

Se alokacin ta lura da Ameera dake bayan Ashrab a tsaye se rawar sanyi take kasancewar garin iska ke kaɗawa.

A falon gidan suka zauna Ameera se waige waige take alamun ƙauyanci muraran a idanunta da jikinta da suturarta.

Nisawa Ashrab yayi sannan yace"Zainab nasan abokina me laifine agurinki,sede ina me ƙara baki haƙuri akan nada,in har kin yarda dani,to wallahi agidana ya kwana,mun fito da safe zamu zo nan(ya faɗi dan ya kare aminin nasa)tsautsayi ya rutsa damu,hisham ke driving ya buge ƴar uwar wannan yarinyar(ya nuna Ameera)yanzu haka tana Asibitin aminiyarki doctor safiyya akwance,to ni kuma da nike gwauro,kinga bana tafi da ita gidanaba,shine maƙasudin zuwanmu"

Sosai ta gamsu da bayanin na Ashrab,dan kafatanin abokan mijin nata shi takewa kallon salihi mumini me tsoron Allah.

"kiyi haƙuri baby"cewar hisham kamar me shirin yin kuka.

"Amma jikin yarinyar da sauƙi ko?"cewar zainab cike da kulawa.

"da sauƙi zainab sede ta karye a ƙafarta ta hagu"

"wayyo Allahna da dare beyi ba ay da naje dubata,sannunki kinji ya sunanki"takai dubanta gurin ameera dake ta zare idanu.

"Sunana Ameera"ta bata amsa.

"kiyi haƙuri kinji ko,ƴar uwarki zata samu lafiya,ku yafewa mijina da saninshi baze bugeta ba kinji ko?"

Gyaɗa mata kai tayi,miƙewa zainab tayi takama hannun Ameera tace "muje ki samu kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta"

Ɗakin da suka tanada domin baƙi ta kaita ,sannan ta dawo falon,Ashrab ta samu a tsaye alamun tafiya zeyi,

"bazaka tsaya kaci abinci ba naga kana shirin tafiya?"cewar zainab dake ƙarasowa cikin falon.

"kukuna nasan ya tanajeni zainab mu kwana lafiya"ya faɗi yana murmushi.

"ade daure acika ustazancin nan ayi aure Ashrab"cewar zainab tana dariya.

"lokaci de zainab"ya bata amsa a gajarce.

Daga haka sukai sallama ya fice zuwa mota hisham na taka masa.

"kayi ƙoƙarin zama namiji agidanka ji duk yadda ka zuge,wai dik akan mace nifa kagani wallahi wannan iskancinne bazan ɗauka ba agidana"cewar Ashrab bayan ya tada mota.

"koma de me zakace naji nakuma gode da ceto ni daga hukuncin zee da kayi"cewar hisham yana dariya.

Ficewa yayi daga harabar gidan ya nufi nashi hankali kwance.

Hisham cikin gida ya koma,ga mamakinsa yana shiga ya samu zee ɗinsa ta cire lulluɓin da tayi ɗazu,kayan dake jikinta fan dubunka tsirara,dan basu da maraba da babu, tana tsaye tana jifansa da wani niimtaccen murmushi.

Wani daɗi ne yaji yana ratsa masa zuciya,wato ita halaƙ daban take da haram komai muninta,haka haram komai kyanta bata kai halak ba.

Rungumeta yayi jikinsa na ɓari tun afalon ya fara jefa mata kiss masu zafi,da ƙyar ta jashi suka wuce ɗakin barcinsa.

Muje zuwa


Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

_(Romantic love story)_

*Zahra Surbajo*


_BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM_

*Wannan littafi nayishi dan maauratane,in baki da aure kika karanta ruwanki,nide na faɗa,kuma ba free bane,na kuɗine 300,page ɗaya kullum,in kuma vip zaa saki 500,page biyu kullum,in dan ki siya ki fitarmin ne kar ki siya,*

*banyi shi don cin zarafin kowa ba,nayi shi ne don ilimantarwa da faɗakarwa gami da nishaɗi,soyayya zazzafa me tsayawa a rai,da kuɗi kaɗan ki kwashi garaɓasa*.

*20 Free pages zanyi,dan haka me buƙata ya fara biyan kuɗinsa yanzu,ba ragi dan kar kice arage baay ba kiji haushi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*5*


Sun ɓarji soyayya awannan dare tsakanin hisham da matarsa zainab,sannan suka samu sukayi bacci.

Ameera ma baccine me daɗi yayi awon gaba da ita batare da tunanin komai ba tunda dama agajiye take baccin take buƙata

Ashrab koda yaje gida kasa bacci yayi yana ta tunanin maganganun Ameera da tace barki suka fito.

"Yanzu wanne mara imani ne ke kwanciya da yaran nan dan ya basu kuɗi,bashi da imanine, bega sunyi ƙanƙanta ba?"sune tambayoyin dake yawo akansa da kuma ya rasa me amsa masa su.

Ranar be samu wadataccen bacci ba,dan haka gari na wayewa yayi wanka ya kimtsa cikin shigar zuwa office da ta dace da kyawun halittarsa.

Ashrab Sulaiman Abdullahi,matashi ɗan kimanin shekaru 30 da haihuwa,fari dogo,amma ba siriri bane yana da murɗaɗɗen jiki,ga baƙin gashi kwance a kansa,gefen fuskarsa kuma zagaye da saje haɓarsa ɗauke da gemu irin na zamani.

Yana da idanu masha Allah gwanin burgewa,ga wani kyakktawan dimple dake fito masa aduk lokacin da yake cikin nishaɗi.

Maikacine a CBN shine marketer,batun kuɗi a gurinsa ma be taso ba,hanshaƙin me kuɗine bana wasa ba,yayi makaranta a oxford university dake can nahiyar turai,

Mutum ne me tausayi,shiyasa da dama jamaa ke sonsa.

Wannan kenan.

Be biya ta gidan hisham ba,kai tsaye asibitin ya nufa,ga mamakinsa sun rigashi zuwa ma.

Sosai yayi mamakin ganin marar lafiyar a zaune zainab matar hisham na bata ruwan tea tana sha sa'i da lokaci tana share hawaye a idonta. wanda besan ko na meneneba.

Bayan sun gaggaisane ya sake dubanta akaro na biyu yace "ƙanwata ya jikin naki,?"

A hankali ta ɗago idaninta suka haɗa ido,dukansu kowa seda gabanshi ya faɗi da ganin ɗan uwansa,seda suka kalli juna na ƴan seconni sannan ta lumshe idanunta tace a sanyaye "da sauƙi nagode Allah ya biyaku"

"amin"ya amsa mata

Office ɗin doctor yaje suka gaisa,sannan yay mata godiya sosai bisa gudunmawar data bayar wajen kulawa da marar lafiyar.

"wannan ba abin damuwa bane ashrab Allah de yabata lafiya kai kuma ya baka lada"cewar doctor safiyya tana dariya.

Ɗakin ya dawo gurin su hisham,bayan ya biya komai,
Dubansa yakai gun hisham yace"zamu iya wucewa offics yanzu sabida likita tace se nan da sati guda ma zaa iya sallamarta so muje office mu dawo se asan yadda zaayi asanar da iyayensu halin da suke ciki"cewar ashrab yana duban fuskar agogonsa.

Cikin muryar rashin lafiya ummu rumana tace "mufa ƴan barikine,babu wanda ze damu in baa ganmu ba,kawai sede wata matsala da muka fito barikin dominta"ta share kwallar data taru a idonta.sannan taci gaba da cewa

"megarin garinmu ne,yake bin mahaifina kuɗi naira milyan biyu kuɗin takin zamani,to ya rabawa manoma se akayi fari duk amfanin gonar beyi ba bare su biya,to shine megarin ya takura mahaifina akan kuɗin sanadin haka har Allah yayiwa mahaifina rasuwa be biya ba,shine ya komo kan mahaifiyata,kan seta biya kuɗin,ko ta auresa,ita kuma taƙi amincewa shine,yaci gaba da uzzyra mata kan kuɗin,ƙarshe de shine suka tsaida matsaya gaban manyan gari da ƙanin mahaifina kawu bello wanda duk gonakin mahaifina ke hannunsa ya hanamu.
kan cewa in ba'a biya kuɗin ba,acikin shekara guda,ranar da wa'adin ze cika za'a ɗaura aurena da ɗansa,kuma ɗan iskane ɗan nasa,to anbuga ba'a samu kuɗin ba,shine hawan jini ya kama innata,ni kuma naga da in auri ɗan nasa gwara in fito yawon bariki,in haɗa masa kuɗinsa,dan banason wannan ƙazamin ɗan nasa ,shine mahaifiyata ta yanke jiki ta faɗi ta samu macewar gefen jiki,se yayata ke kula da ita,ni kuma na fito bariki,yanzu saura kwana uku a ɗaura auran inde ban kai kuɗinba,dan Allah kusa asallameni yanzu inje in ci gaba da barikina,"ta sake rushewa da kuka.

Ɗaukar zancan nata sukayi a ƙarya dan shi ashrab ma gani yake inba bugagge ba waye ze kalli wainnan ƙwailayen yaran as mata har su bashi shaawar yin wani abu dasu. hakan nema yasa basu bi takan zancenba,suka fice daga ɗakin zuwa inda motocinsu suke su da hisham suka shiga mota ɗaya,ɗayar kuma matar hisham taja ita da Ameera zata je ne ta dafo abinci ta dawo.

kuka ummu rumana keyi tana faɗin "wayyo Allah na banason habu megari don Allah karku tafi ku tsaya infaɗa muku walkahi bana sonsa,kawu bello karka auramin shi don Allah kajira inyo bariki in kawo musu kuɗinsu"se rusa kuka take ita kaɗai a ɗakin har ta gaji tayi shuru.baccibyay awon gaba da ita.

Koda suka isa office Ashrab ya kasa natsuwa yayi aykinsa kamar yadda ya saba,manajojin bankuna da na manyan maaikatu sunzo ganawa dashi se sabon appointement yabasu,dan mamakin barikin da su Ameera suke iƙrarin faɗin shi suka fito yaƙi ya barsa.

Haka ya gama zaman office suka taso,koda ya koma gida be da wani kuzari ajikinshi,wanka yayi yaci abinci sannan ya fice a motarsa ƙirar range rover fara 2021model kyan motar ya isa da isarsa,

Tuƙi yake hankali kwance,ya isa Asibitin,samun abokinsa haisam yayi tare da hisham da Ameera a gurin Zainab bata dawo ba tana gida.

"Mun ɗauka wahalar office bazaka fitoba se kuma gobe"cewar haisam yana dariya lokacin sa suke gaisawa da Ashrab.

"mtsuuu,office ya gajiyar da ni amma ay kasan matsalar hisham tamuce musamman ma ni da muke tare time ɗin da abun ya faru,kaga dole inzo komai gajiyata"cewar Ashrab fuskarsa ba annuri.

"wannan gaskiyane,Allah de ta ƙara kiyayewa,abu beyi daɗi ba"Cewar haisam shima cikun alhini.

Daga haka ɗakin marar lafiyarka suka leƙa bacci take,hakanne yasa suka dawo reception zaman jira suga yanayin jikin kamin su tafi gida.

********


Wasa wasa seda ummu rumana ta kwashe sati guda kwance a asibitin kan asallameta,kuka magiya ba irin rokin da basuyiba ita da ameera kan abarsu su koma gida dan aurar da ita zaayi in ta wuce kwana biyar bata koma ba gashi har sati guda,tasan me fari da ƙanin ubanta sun aurawa habu ita.

,sandar dogarawa aka bata,sabida ƙafarta dake da karaya.


Hisham ne ya ɗaukosu a asibitin,sede yasan ƙaryarshi ta ƙare in yakaiwa zainab gida,cewa zatayi vazata amince su zauna mata gida ba,haisam kuma yasan baya gida yana gidan Ashrab
sabida yau ƴan mata da aka samowa ashrab daga ƙasar mexico suka iso Abuja,

haisam ɗinne ya tarbosu yakaisu gidan na Ashrab domin ya sheƙe ayarshi dasu.

Sude su Ameera sarautar Allah kawai suke saurare,haka ya nufi gidan na Ashrab dasu suna matsar hawaye.

Muje zuwa

.Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

_(Romantic love story)_

*Zahra Surbajo*


_BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM_

*Wannan littafi nayishi dan maauratane,in baki da aure kika karanta ruwanki,nide na faɗa,kuma ba free bane,na kuɗine 300,page ɗaya kullum,in kuma vip zaa saki 500,page biyu kullum,in dan ki siya ki fitarmin ne kar ki siya,*

*banyi shi don cin zarafin kowa ba,nayi shi ne don ilimantarwa da faɗakarwa gami da nishaɗi,soyayya zazzafa me tsayawa a rai,da kuɗi kaɗan ki kwashi garaɓasa*.

*20 Free pages zanyi,dan haka me buƙata ya fara biyan kuɗinsa yanzu,ba ragi dan kar kice arage baay ba kiji haushi*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

*7*



"A bamu cingam"cewar Ameera tana gyara ɗaurin ɗankwalinta zuwa ture kaga tsiya.

Ba musu Ashrab ya miƙe yaje inda yake ajiyewa ya ɗauko musu,dan ya ƙosa yaga ko menene zasuyi da cingam ɗin.

Ɓarewa sukayi kowa ta jefa abakinta,suka fara taunawa,yayinda ummu rumana ke tsaye riƙe da ƙugu tana tauna cingam se ƙaras take,ɗankwalinta gaban goshinta,ita kuma ameera se kaiwa take da kawowa tana rangwaɗa tana ƙaras da cingam kai yasha ture kaga tsiya.

Hisham da Ashrab baki suka saki suna kallonsu,ko kaɗan da da farko basu gane me sukeyiba,se daga baya suka fahimci wannan abin da suke su agunsu shine barikin.

Wata irin dunƙulalliyar dariyace ta tasoma ashrab,wacce yama rasa ta ina ze fitar da ita.

Duƙawa yayi ya gimtse bakinsa ya shiga tuttular da dariyar data taso masa,tunda uwarshi ta haifeshi be taɓa dariya irin ta yau ba.

shiko hisham baƙin ciki ne ya kamashi san bega abun dariyar ba.afusace yace dasu.

"kai ku dakata dan Allah,"jiki na ɓari suka waigo gunshi suna raba ido.....

"ya sunan wannan shashancin da kukeyi?"cewar hisham cikin fushi
.
"bariki"cewar ummu rumana cike da ƙwarin guiwa.

"lallene dama ance bariki alalen gero ce,wato ku taku kalar kenan?"hisham ya faɗi rai aɓace.....

Kasa bashi amsa sukayi se harara da rumana ke jefo masa asace.

"To dukanku yanzu zan maidaku ƴan barikin dan uban... ...."

"look hisham ya isa haka"ashrab ya katseshi yana me ɗaga masa hannu....

Shuru hisham yayi yana sauraran yaji shi wanne hukunci ze yanke musu.

"wainnan sun fiye min waincan shashashun ƴanmatan da kuka kawomin,infact da ace irin wainnan kuke kawomin ay nima da tuni nayi nisa a barikin,dan haka aje dasu asa,driver yakaisu garinsu,ka shirya musu kuɗi naira milyan biyar ta yadda bazaa fahimci me suke tafe dashi ba,na sallameku"ya faɗi fuskarshi ɗauke da walwala.

Da gudu suka xube agabansa suna masa godiya,Ameera tace"mungode sosai Allah ya biyaka ƙawata ta samu kuɗin fansar kanta,mungode"

Dubansa yakai gun rumana yace a tausashe yana murmushi"gashi har kun gama yimin barikin amna kuma bansan sunku ba"

Duƙar da kanta ƙasa tayi tana murmushi tace"sunana ummu rumana,ita kuma ƙawata sinanta ameera "ta faɗi tana wasa da sandar hannunta.

"ummu rumana"ya sake maimaita sunan gamida lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya yace,"suna me daɗi,to rumana ky gaida gida,nagode sosai"ya faɗi gami da miƙewa yabar Hisham baki buɗe rai aɓace.

Haka ya tarkata ƙeyarsu suka fice,kamar yadda ashrab yace hakan yayi,ya shirya musu kuɗin acikin buhun shinkafa daya ƙare,sannan ya kira drivern ashrab ɗin yabashi umarnin kaisu gida.

Be bi ta kansu ba yaja tashi motar yafice daga gidan ranshi aɓace,dan sosai yasa rai akan matan da haisam ya kawo amma wainnan ƙwailayen suka sa ya kore musu su.

Driver tambayarsu yayi yana murmushi yace"ƴanmata ina zan kaiku?"

"kanya hore"rumana ta bashi amsa tana murmushi.

Ido ya ware sannan yace"wai can in an fice daga kano ɗinnan?"

"Lah kiji ɗan gari,eh fa can zaka kaimu"cewar ameera tana dariya jin yasan garinsu.

Jinjinawa yayi yaga tafiyace doguwa amma aka bashi umarnin yinta lokaci guda,Allah de yay mana arziƙi.

Haka suka shige motar daya buɗe musu gidan baya rumana ta shiga sannan,ameera ta shige gaba yaja suka fice daga harabar gidan.

"saduwar alkhairi rumana,Allah kaiku gida lafiya ƴan barikina"cewar ashrab dake tsaye can saman benensa yana hango tafiyarsu,

Haka kawai se yaji ba daɗi bayan sun tafi,se ji yake yana kewarsu,adduar sauka lafiya yaci gaba da musu.

Driver ko wuta kawai yake ba motar ta uban gidan nasa mercedez benz 2020,

Acikin awa huɗu ya shigo garin na kano dasu,dukansu bacci suke,har seda yazo bakin hanyar garin,sannan ya tadasu.dan su kwatanta masa hanya.

sannu a hankali ya faka a ƙofar wani durƙusasshen gidan ƙasa dake barazanar faɗuwa akowanne lokaci.

Da sauri suka fito gami da ɗaukar buhun su,sannan sukayi sallama da driver su kuma suka shige cikin gidan ransu fess.

Jan motar yayi ya ƙarasa masauki dan baze iya kama hanyar abuja alokacin ba.

Muje zuwa


Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

_(Romantic love story)_

*Zahra Surbajo*


_BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM_

*Wannan littafi nayishi dan maauratane,in baki da aure kika karanta ruwanki,nide na faɗa,kuma ba free bane,na kuɗine 300,page ɗaya kullum,in kuma vip zaa saki 500,page biyu kullum,in dan ki siya ki fitarmin ne kar ki siya,*

*banyi shi don cin zarafin kowa ba,nayi shi ne don ilimantarwa da faɗakarwa gami da nishaɗi,soyayya zazzafa me tsayawa a rai,da kuɗi kaɗan ki kwashi garaɓasa*.

*20 Free pages zanyi,dan haka me buƙata

2 / 13