Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
ya fara biyan kuɗinsa yanzu,ba ragi dan kar kice arage baay ba kiji haushi*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*6*
A falon gidan na saukar baƙi ya barsu,sannan ya ƙarasa inda yasan ze ga su Ashrab ɗin.
Zaune suke a falon yayinda ƴan matan sun kai su goma fararen fata kowacce cikin shigar Allah wadai,se rausaye rausaye suke agaban ashrab ɗin shiko gogan ya hakimce akan kujera yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya,
Kowacce nayin abinda tasan zata ɗauki hankalinsa ya fara da ita, dan dukansu sun kwaɗaitu da Ashrab ɗin.
Ameera da Ummu rumana dake falon farko gajiya sukayi da jiran dawowar hisham hakanne yasa suka miƙe ameera ta kama ummu rumana suka nufi hanyar da suka ga ya bi,ayko ɗoɗar se gasu abakin ƙofar falon da ake sheƙe ayar.wanda su na ciki basu ma san sunzo gurin ba.
Hisham hannu yaba abokan nasa sannan yasa hannu ya latsa ɗuwawun wata dake ta rawa kamar an ɗaura ruwa,yace yana duban ashrab.
"mutumina ka fara da wannan,irinsu kwai ruwa,inde barikice,to wallahi wainnan ƙarshe ne"
Ummu rumana da ameera junansu suka kalla sannan sika maida hankalinsu cikin falon.
"Ay bariki Allaji inde kasamu irinsu to kai tayima kyau,na jima ina dubawa kan na zaɓo su"cewar haisam yana shafo boobs ɗin wata acikinsu.
Shiko ya mutsa fuska yayi gami da taɓe baki yace a ƙasaitance"kayi ƙoƙari haisam sosai gaskiya,dama ni riƙaƙƙun ƴan bariki nafiso kuma gasu ka samo,sabida..."be ƙarasa abinda yakeson faɗi ba ameera da ummu rumana suka ƙaraso tsakar falon suna kuka.
Cikin kuka rumana ta ƙarasa gaban Ashrab tace"riƙaƙƙun ƴan bariki kode ƴan iska?naga tunda muka haɗu muka shaida muku mu riƙaƙƙun ƴan barikine,me zakuyi da wainnan tsinannun bayan gamu bariki wacce irice bamu iyaba,zakuje ku kwaso wasu ƴan iska wanda ko taunar cingam ɗin ma banga sunayi ba bare akai ga batun ɗaurin ɗan kwalin amma har kuke kiransu ƴan bariki,wallahi wainnan ƴan iskane mune nan riƙaƙƙun ƴan barikin"ta ƙarasa maganar hawaye nabiyo idonta.
Ameerace ta amshe zancan da cewa itama cikin kukan"muamala da wainnan ay mutuncinku ne kawai ze zube, da darajarku dan wainnan ƴan iskane mune ƴan bariki san Allah ku sallamesu kuyi barikin nan damu dan Allah ba abinda bazamu muku ba daya shafi bariki kutaimaka ku vamu dama"
Ba su ashrab ba su kansu watsatstsun ƴanmatan sunyi mamakin ganin ƴan fici ficin yaran agurin,dan basu tsamnaci ganinsu ba,dan shi kanshi hisham daya kawosu ya mance dasu ganin haja a ƙasa.
Ashrab a karo na farko kenan da yaji wata ɗiya mace baya ga ƙannensa ta burgeshi,ba kowa bace face ummu rumana,tsintar kanshi yayi dayin murmushi har haƙoransa na bayyana a waje.sosai ya shagaltu da kallonta.
Gabanshi ta ƙarasa tana ɗingisawa,tace murya na rawa,"ka fisu tausayi kuma kai ɗin me kamala ne,mutuncinka me girmane a idon jamaa,kada ruɗin duniya yasa ka biyewa wainnan ƴan iskan matan,datti ne su wanda ake wankewa da wutar jahannama,bariki mune bariki ka biyamu zamuyi muku variki amma ku sallami wainnan tantiran dan kallonsu a haka ma makantace ranar gobe ƙiyama haka ummana ta faɗa mana"
Idonshi Akanta batare daya ɗaukesu ba yacewa haisam
"A biyasu biya na musamman,atanadar musu jirgi gobe su koma ƙasarsu na sallamesu"
"what!!!!!!!!"cewar hisham da haisam atare dan sosai umarnin nasa ya kaɗa su,hisham bakinsa har rawa yake wajen faɗin.
"Ashrab anya kasan abinda kake faɗi kuwa,ka mance mahaukatan kuɗin da aka kashe kan akawo maka su shine zakace a sallamesu ba tare daka kama koda hannun ɗaya daga cikinsu ba sabida wainnan berorin sunce sun iya barikin?"
"And so what?"cewar ashrab cikin fushi.
"look ashrab,karka maidamu ƙananan mutane,baze yiwu tunda muka janyo raayinka ka shigo barikinnan ba,ace har yau babu macen datai maka,daka kwanta da ita,duk wacce zaa kawo se ka kushe,dede da hannunsu baka riƙewa se kasa a sallamesu shin kai taka barikin wacce kalace,?"cewar haisam shima cikin fushi.
"i dont have time for all this,what i know is kuɗide nawane,ni nake spending all so bandamuba kuma yadda nakeso zaaymin,ba damuwarku bace dan na gayyatosu kuma banyi amfani dasu ba na sallamesu,basuyimin bane in aka samu wainda suka yimin zan jarraba dan ni nafison virgin"
"ah ba bariki kafito ma alhji wato virgin acikin ƴan bariki,wallahi,sede a mafarkinka,sede kasamu sauran wani amma ƴan bariki duk abuɗe suke"cewar haisam yana dariya.
.
Su Ummu rumana basu fahimci komai ba a zancan nasu shiyasa sukayi shuru suna raba ido,
Haisam beda yadda ya iya dole ya kwashe hajarsa ya fice dasu daga gidan zuwa hotel da aka saukesu,sannan ya basu haƙuri yavasu kuɗaɗe masu yawa kamar yadda ashrab ɗin yace.
Bayan fitarsu,ashrab yakai dubansa gun ummu rumana yace yana murmushi
"To na sallami ƴan iskan ku ƴan barikin ku matso kumin naku barikin in gani"
Muje zuwa
..Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
_(Romantic love story)_
*Zahra Surbajo*
_BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM_
*Wannan littafi nayishi dan maauratane,in baki da aure kika karanta ruwanki,nide na faɗa,kuma ba free bane,na kuɗine 300,page ɗaya kullum,in kuma vip zaa saki 500,page biyu kullum,in dan ki siya ki fitarmin ne kar ki siya,*
*banyi shi don cin zarafin kowa ba,nayi shi ne don ilimantarwa da faɗakarwa gami da nishaɗi,soyayya zazzafa me tsayawa a rai,da kuɗi kaɗan ki kwashi garaɓasa*.
*20 Free pages zanyi,dan haka me buƙata ya fara biyan kuɗinsa yanzu,ba ragi dan kar kice arage baay ba kiji haushi*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*9*
Koda dare su aisha suka tafi suka barta ko ajikinta,illa ma mimmiƙewa da tayi akan haɗaɗɗen gadonta,tana mazurai da idanu alamun bata son wasa.
Ƙarfe sha biyu na dare taji ƙarar buɗe ƙofa,bata ko tsorata ba,dan tasan kwanan zancen,miƙewa tayi ta riƙe ƙugu tana karkaɗa jiki,alamun kota kwana.
Turo ƙofar ɗakin akayi da sallama,angon nata ne cikin shiga ta kamala,bame cewa shine ke ƙwalewa,yayi kyau sosai,se ƙasa ƙasa yake da kai yace bayan ya zauna kan kujera"barkanki da shigowa zuriaarmu,ina miki fatan alkhairi da kuma dauwamamman zaman lafiya,ba zuga ba amarya kin more miji"
Wani dogon tsaki taja gamida balla masa harara tace"nayi saa ko nayi asara,ace kaf rayuwata ta rasa inda zata kawoni se wannan ƙazamin gidan naku,to wallahi na gwammaci zaman titi da wannan gidan naku"ta ƙarasa maganar tana fari da ido.
Murmushi yayi sannan yace"wannan raayin ki kenan ummu,ni kuma habu meye nawa,inade miki fatan alkhairi,na barki lafiya"yana kaiwa nan ya miƙe,ya fice, daga ɗakin Bayan ya ajiye mata ledar gasassun kaji da madara.
Tsaki tabi bayanshi dashi gamida harara,ledar ta janyo dan dama yunwa takeji,ba tare da tunanin komai ba ta hau aykawa cikinta.
Seda taci ta ƙoshi ta godewa Allah sannan ta ture,gefe.
Toilet ta shiga ta wanko bakinta sannan tazo tai ɗare ɗare agado tashiga baccinta.
Seda aka kira sallar asuba sannan ta farka.alwala tayi tay sallah Sannan tayi adduoi,ta ja sauran kajinta na jiya taci tasha madara tajita ƙat sannan ta miƙe tayi wanka sede ba kayan sauyawa,hakanne yasa ta maida wanda ta cire ta zari hijabi tayi waje.
.
A falo ta iske angon nata,yana waya,tana ƙarasowa yay saurin kashewa,sannan ya dubeta ataƙaice yace "barka da asuba amarya "ko kallo be isheta ba,sema tsaki data ja tace"gidan tsiya da talauci suturar da zansa ma ta gagareni,to naje gida in ɗauki kayana"bata jira amsarshi ba tasa kai tayi wucewarta.
Da sauri tabi vayanta yana faɗin"kiyiwa girman Allah karki fita tozarci zaki janyowa gidan nan da mijinki,ki bani minti biyar zan kawo miki kayan sawa,".
"Ay duk abinda ze janyo muku zagi agarinnan sena aykatashi"tana gama faɗi tasa kai tayi ficewarta,kowa se kallonta yake,ana mamaki amarya ba ko kunya,haka tazo ta wuce megari da ƴan fada tasa kai ta nufi gidansu.
Lokacin data shiga gida sosai Aisha da Ameera suka tsorata da ganinta.
"lafiya kuwa ummu?"suka haɗa baki gun tambayarta.
Guri tasamu ta zauna tana murmushi tace"lafiyarce ta kawo haka,kayan sawata nazo ɗauka".
Umnanta dake kwancs a gefe tace cikin muryar rashin lafiya."dan baki da hankali rumana kina aure a babban gida ina ke ina fitowa yanzu meyasa kikayi haka?"
"Umma to kayan sawane babu fa"ta faɗi a shagwaɓe.
"se ki jira har akai miki meye naki na fitowa"cewar umma da ƙyar.
"kiyi haƙuri umma bazan kuma ba"
"da de yafi miki kam,kuma kitashi ki koma aisha zasu kawo miki kayan"
Ba musu ta miƙe ta fice daga gidan ranta aɓace,ta koma gidan na me gari,
Koda ta koma a tsakar gida ta samesu kamar jiranta dama akeyi.
Hafsa ƙanwar mijin na rumanace ta tari gabanta tace "ke dan uwarki me kika taka da kike mana rashin mutunci harda fita waje dan ki janyo mana zagi"
"kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa,ki tambayi tsohonki ko me natakan da yasa nake hakan"
.
Hannu hafsa ta ɗaga zata kwasheta da mari ayko carab ta riƙe hannun sannan tace cikin zafin rai.
"wallahi in kika mareni sena kwasawa uwarki mari,dan bazanyi dake ba"ta faɗi tana hararo sashin da uwar mijin nata ke tsaye tana kallonsu.
ƙarasowar habu gurin ne ya kawo ƙarshen taƙaddamar,inda ya tsawatarwa hafsa sannan yaba Ummu haƙuri.
Ayko cikim izza tasa kai ta wuce ba tare data kalli kowa ba ta ko ma ɓangaren nata.
Ɗaki tashige abunta tai kwanciyarta tana wassafa abubuwa da dama a zuciyarta.
.
Muje zuwa
..Surbajo for life
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
_(Romantic love story)_
*Zahra Surbajo*
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
_BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM_
*Wannan littafi nayishi dan maauratane,in baki da aure kika karanta ruwanki,nide na faɗa,kuma ba free bane,na kuɗine 300,page ɗaya kullum,in kuma vip zaa saki 500,page biyu kullum,in dan ki siya ki fitarmin ne kar ki siya,*
*banyi shi don cin zarafin kowa ba,nayi shi ne don ilimantarwa da faɗakarwa gami da nishaɗi,soyayya zazzafa me tsayawa a rai,da kuɗi kaɗan ki kwashi garaɓasa*.
*20 Free pages zanyi,dan haka me buƙata ya fara biyan kuɗinsa yanzu,ba ragi dan kar kice arage baay ba kiji haushi*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*8*
Cikin tsananin farin ciki suka shiga cikin gidan bakunansu ɗauke da sallama,
Ba kowa a tsakar gidan dan haka da ƙwarin guiwarsu suka shige cikin ɗakin.
Yayar ummu rumana Aisha ce zaune tana gogewa mahaifiyarsu jiki da ruwan sanyi,idonta na fitar da ƙwalla.
"yaya Aisha"ummu rumana ta kirata jiki a sanyaye.
firgigit ta waigo,dan bata ji shigowarsu ba kuma bata tsammaci jin muryar adaidai wannan lokaci ba,da sauri ta miƙe ta ƙarasa gurin rumanar ta jata jikinta ta rungume ta sake fashewa da sabon kuka,
Rumana ummansu take kallo,taga itama ita take kallo,hawaye na biyo idonta,cikin kuka Aisha tace.
"ummu ina kuka shiga,kun jefamu cikin tashin hankali,ranar da kuka hau mota a tasha labari yakai kunnen megari wai kun gudu,haka yazo gidannan yaciwa umma mutunci,shi da kawu bello,me gari yace duk inda zaki shiga sede ki shiga da auran ɗansa,aranar kawu bello ya aurar dake ga ɗanmegarin"ihun da rumana ta saki ne yasa aisha yin shuru.
"wallahi bazan zauna da ɗan shaye shaye ba,wallahi bana sonsa,wayyo na shiga uku na lalace,da in auresa gwanda in koma ƴar iska wallahi"ta sake rushewa da kuka.
"zo nan rumana"cewar mahaifiyarta cikin muryar rashin lafiya.
Zuwa tayi jikin mahaifiyar tata,ta rungumeta ta sake sakin wani kuka me tsuma zuciya,
"karki kuka rumana ta,komai muƙaddarine daga Allah,yafi mu sanin abinda ya ɓoye acikin auran nan naki,ki ɗauki ƙaddara Allah yagani munyi iya yinmu amma ya nuna ikonsa akanmu,to ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki"cewar mahaifiyarta da ƙyar dan tausayin ƴartata gaba ɗaya ya cika koina na zuciyarta,dan inde habu ne ɗan megari tasan ƴar tata na cikin mawuyacin hali.sede addua kawai.
nanfa suka sata agaba harda ameera suna rarrashinta da ƙyar tai shuru.
Ita dama ameera a hannun mahaifiyar rumana take da zama,kasancewarta ƙawar rumanar a makaranta,rasuwar mahaifiyarta yasa mahaifinta ba mahaifiyar rumanar ita dan kwanciyar hankalin ameerar dan akwai aminci tsakaninshi da mahaifin rumanar.
Kuɗin da aka basu suka fito dashi suka nunawa mahaifiyar,tasu,sannan suka shaida mata duk abinda ya faru tun daga barinsu gida,
Sosai mahaifiyarsu ta godewa Allah bisa tsare mata su da yayi daga faɗawa rayuwar Allah wadai.
"wannan kuɗi sisi banaso ku taɓa ku adana su wataran zasu muku amfani ko bayan rainane"
Ummu rumana de shuru tayi tana kallon komai kamar film,wai itace matar habu ɗan megari,kai amma kawu bello ya cuceta,sede kanshi yayiwa,dan wallahi bazata zauna ba.
*********
Satin su biyu da komawa megari ya turo ɗaukar amarya,nanfa hankalin mahaifiyarsu ya tashi ita dasu ameera saɓanin ita uwar gayyar,da ko ajikinta ta miƙe ta yi gaba hankalinta kwance.
Su Aisha haka suka mara mata baya, zuwa gidan na me gari dan ko mota be bayar ba wacce zaa ɗaukota a ƙafa suka tafi.
Koda aka kaita megarin kallo ma bata ishe shi ba,bare tasa ran karɓuwa,
Gurin mahaifiyar mijin nata aka kaita,ayko ba mutunci dan cikin faɗa take faɗin,"ƴar matsiyata arasa wanda zaa aura miki se ɗa na,to wallahi se kin koma gidanku,shi ɗan nawa ze zo ya sameni ne,dan inde nice na haifeshi seya sakeki"ayko rumana bata jira ta kammala ba ta amshe zancan da cewa.
"da zaki sa ya sakeni dana baki matsayi a zuciyata kwatankwacin mahaifiyata,dan ɗanki ba mijin aure bane,sede lalura"ɗauketa da mari tayi,ayko itama rumana cikin zafi ta ɗaga hannu zata rama da sauri aisha ta riƙeta ta hanata.
"da kin barni na gwada mata girman tsanar da naiwa tsinannan ɗan nata"cewar rumana hawaye na biyo idonta.
Itako uwar ango kasa cewa komai tayi ganin yunƙurin na ummu rumana.juyawa tayi ta shige ɗakinta ranta na mata zafi.
Haka aka ɗauki rumana zuwa sashin da aka tanada domin zamanta acikin gidan.
.
.Ba laifi komai akwai acikin ɓangaren dan megarin ba ƙaramin me kuɗi bane,shiyasa komai na ƙawa ansaka a ɓangaren.
Ko kaɗan ba abinda ya burge rumana acikin gidan bare har ta kalla.Tunda ta samu gefen gado ta zauna bata cewa su aisha komai ba,har dare ya fara,dole sukai mata sallama suka tafi gida zuciyarsu cike da tunanin irin zaman da zatayi a gidan.
muje zuwa
Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
_(Romantic love story)_
*Zahra Surbajo*
_BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM_
*ƳAN MATA BA HANAKU KARANTAWA NAYIBA,KAWAI DE LITTAFIN ƊAUKE YAKE DA ZAMAN TA KEWA TA AURE,SHINE YASA,KUMA KAWUNANKU AY BASA ƊAUKA BA*
*Wannan littafi nayishi dan maauratane,in baki da aure kika karanta ruwanki,nide na faɗa,kuma ba free bane,na kuɗine 300,page ɗaya kullum,in kuma vip zaa saki 500,page biyu kullum,in dan ki siya ki fitarmin ne kar ki siya,*
*banyi shi don cin zarafin kowa ba,nayi shi ne don ilimantarwa da faɗakarwa gami da nishaɗi,soyayya zazzafa me tsayawa a rai,da kuɗi kaɗan ki kwashi garaɓasa*.
*20 Free pages zanyi,dan haka me buƙata ya fara biyan kuɗinsa yanzu,ba ragi dan kar kice arage baay ba kiji haushi*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044*
*10*
'Dole in bar gidannan ko kuma rayuwata ta ƙare a banza,ba bu yadda zaayi in zauna aure da habu"
Tana tsaka da wannan tunani ne, Ameera ta shigo kawo mata kayan nata na sawa.
"Ummu rumana anya zamanki anan da alkhairi kuwa,kinga irin kallon banzan da akemin dana shigo,gaskiya ƴan wulaƙancine ƴan gidannan"cewar ameera tana riƙe baki
"hmmm basu da mutunci ko kaɗan wallahi,kuma se nayi maganinsu ɗaya bayan ɗaya tunda tsinannu ne su azzalumai".
"ni gani nake habun ma duk ya sauya kamar bashi ba"
"wallahi fa,amma dik sauyin sa hakan baze goge tsanar da naiwa wannan ahalin ba araina"cewat rumana rai aɓace.
"dama au sede ko gaba,amma a yanzu de kam basu cancamci yafiya ba"inji amira.
"saina wulaƙantasu kamun na bar gidanse na sawa megari ciwon daze zamo ajalinsa,inde besa ɗansa ya sake ni ba,,wamnan alƙawarinane"cewar rumana cike da ƙwarin kai.
Ranar Ameera yini tai mata,da kansu suka girka abincin da zasu ci akan rusho.
.Koda habu ya buƙaci abincin hanashi tayi kuma ta bishi da baƙaƙen maganganu.
***********
Watannin ta uku a ɗakin auranta,wulaƙanci suna mata tana ramawa,ko kaɗan bata dubansu a iyayen miji.rashin kunya ko suna ganinta ba kama hannun yaro.
Zuwa yanzu ta fara gajiya da zaman gidan,tasha cin kwalar habun tace ya saketa,sede ya bata haƙuri,kullum a haka sike duk da beda lokacinta,amma bata fasa masa wulaƙanci ba,
ita se take ganin habun kamar wani sabon da aka sauya mata,dan ko jaɗan bata ɗauka haka zata sameshi ba,dan zatonta ƙwanƙwararran ɗan iska ne,se taga ruwa ma yafi shi zafi.
Komai ta buƙata yimata yake,ga yawan haƙuri dayake bata,kuma koda wasa be taɓa neman ta ba,dan masifar rumana ma inyace ze nemeta ta iya kasheshi.
Ko ɗakinta in yashigo yazo su gaisa ne,ko yazo kawo mata wani abun daya siyo mata.
.Duk da haka a wulaƙance yake agurinta,dan ita kashi ma yafi shi daraja agurinta.
Kuma bata fasa taka ƴangidanba,duk wanda yay mata seta rama ko uban waye.shiyasa yanzu uwar mijinta bata shiga sabgarta.
******
Wasa wasa rumana tun tana sa ran saki yau ne gobe ne,taga abu ya miƙa bana ƙare bane.
Hakanne yasa tasha alwashi zama ƴar iska kawai ko ta jajibo musu abun kunya su koreta.
Cikin dare ta haɗa ƴan kayanta ta fice daga gidan ba tare da kowa yasani ba se me gadi.
Kai tsaye ta nufi tasha dan tasha alwashin ko ƴangidansu bazata faɗawa tunda yanzu mahaifiyarta ta samu sauƙi,bazata sake ɗaga mata hankali ba,shiyasa tai ficewarta.
********
Wannan karon rumana yawon iskanci ta tafi ba na bariki ba,wannan karon ma birnin na Abuja ta dira.
Sede shigarta garin ba wanda ya faɗo mata arai se ashrab,dan haka napep ta samu tace zata kwatanta masa gurin ita batasan sunan anguwarba.
Cikin ikon Allah da kwatancen ya kawota ƙofar gidan na Ashrab.
Koda taje ƙofar gidan megadi hanata shiga yayi,dole ta haƙura ta nemi bakin get ɗin jikin fulawa ta rakuɓe.
Ashrab yana office yaga hadari ya haɗa hakanne yasa ya ɗauki escuse ya baro office ɗin,dan dama ba daɗi yake ji ba sosai.
Sosai yayi mamakin ganin mutum a ƙofar gidan nasa cikin rashin fahimtar ko waye ya shiga gidan bayan megadi ya buɗe masa ƙofa.
Be ƙarasa parking ba yacewa megadi"wacece a ƙofar gidannan?"
"Ranka ya daɗe,tace wai ita ƙanwarkace to ni kuma naga bata kama dasu yasa na barta a waje"ya faɗi cikin girmamawa.
Cikin takunsa na ƙasaita,ya tako zuwa ƙofar gidan,yana me ƙare mata kallo,kanta a matse yake a cinyoyinta dan haka a hankali yay mata sallama,
Kamar