Chapter 5 Reading ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt Arewa Novels

ALALEN GERO COMPLETE HAUSA NOVELS BY ZAHRA SURBAJO.txt

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 38.9K words

gida in gaisa dasu hajiya,"be jira amsar ta ba yasa kai ya fice daga falon.

Rumana rasa meke damunsa tayi,anya ba zarginta yake bane yasa yake mata haka,ta ɗauka ay lafiya zasu zauna.tunda ta sauko ita.

*********

Bayan wata shida,da zuwan rumana gurin ashrab,abubuwa da dama sun faru.ciki harda ƙauracewa zama inda take,da sabon wulaƙanci da habu ke mata,

Ita kuma a lokacin wata irin soyayya ce tashi ke tasiri azuciyarta,shi takeso,amna ta lura shi bata gabanshi,sosai hakan yake jefata cikin danuwa

Tsaye take gaban mudubi tana kallon kanta,dan babu ma kaya ajikinta se ɗan pant.

Hannu ta ɗora akan cikinta tana shafawa tace"ya Allah wannan ciwo dake sawa nake jin motsi acikina kuma cikin nawa yayi tauri,ga girma da yayi Allah ka bani maganin sa,"ta kai adduar cikin yanayi na damuwa.

Shiryawa tayi sannan ta sako hijab ɗinta,kamar yadda ta saba,dan tun lokacin data fahimci cikin nata yayi girma takesa hijabi dan in ba wanda yasan laluraba ba me cewa ba ciki bane😆.

A Falo ta samu habu yana hangota ya miƙe ze fice,da sauri ta ƙarasa kusa dashi,tace tana haki"don Allah gidanmu nakeson zuwa"

"se kin dawo"ya bata amsa a gajarce.

"ƙafafuna kumbura suke,dan Allah ka kaini"ta faɗi muryarta na rawa kamar me shirin yin kuka.

Shuru yayi yana ƙare mata kallo,tun daga ƙasa,sosai gabanshi yake harbawa,lokacin daya hango tudun cikin jikinta,

Jikinshi har rawa yake ya isa gabanta ya yaye mata hijab,wayyo Allah,sakin hijab ɗin yayi a firgice ya koma ya zauna daɓas a ƙasa hankalinshi atashe.

Ɗagowa yayi ya dubeta yace"garin yaya naga ciki ajikinki,ta yaya haka ta faru"ya daka mata tsawa.

Durƙushewa tayi itama agurin jikinta na ɓari tace baki na rawa "wallahi ba ciki bane,lalura ce,shine ma nakeso inje in daɗawa mamana abani magani"ta ƙarasa maganar hawaye na biyo idonta.

"sede ko uban lalura,ni zaki rainawa hankali,ciki ajikinki kice dani lalura ce"ya faɗi a fusace.

Kuka ta rushe dashi tace"dan Allah ka rufamin asiri,ni wlh bansan ciki bane"

"tunda a ruwa kika sha ko,bari in sanar acikin gida asan matakin ɗauka"yana kaiwa nan yayi ficewarsa zuwa ɗakin mahaifiyarsa.

A falonta ya sameta a zaune,ko sallama be iya yi ba,yace "Hajiya yarinyar can fa ciki ne da ita"

A firgice hajiya tace"wacce yarinyar?"

"Amarya mana"

"mun shiga uku mun lalace,ciki fa kace habubakar?"tayi tambayar cikin tashin hankali.

"hajiya muje ki ganewa idanunki mana"yana faɗin haka ya kama hannunta zuwa sashin na rumanar.

Rumana wacce tun bayan fitarshi kuka kawai take ta kasa tashi agurin. har shigowar tasu da mahaifiyarshi.

Kai tsaye taje ta yaye hijabin ba tare da tunanin komai ba tasa hannu ta taɓa,salati ta kwasa tace"wulaƙancin da tozarcin da kikazo yimana kenan agida dama,haba koda naji ashe rashin tarbiyyar taki daɗaɗɗiyace"

"dan Allah kuyi haƙuri ku rufamin asiri,wallahi sharrin shaiɗanne,da son zuciya ku yi haƙuri"ta faɗi tana kuka me tsuma zuciya.

Tsanar Ashrab ce me tsanani a zuciyarta,ji take da zata ganshi da se ta kashe shi,shine ya wargaza mata komai na rayuwarta.

"ka kira me martaba a fada yazo"cewar mahaifiyar habu.

Muje zuwa
....
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze sakamin*

*17*


Rumana ko ajikinta illa ma cewa da tayi"shide yayi asara inna,nifa sam bana sonshi, shiyasa na godewa Allah ma daya furta ya sakeni"ta faɗi tana ƙyaɓe baki.

Ameerace ta matso kusa da inna tace a sanyaye,"inna kince rumana tayi asarar miji zaɓin mahaifinta,abinda na kasa ganewa anan shine,taya mijin rumana ya zama zaɓin babanta bacin irin tashin hankalin da muka shiga sabida mu gujewa tarkon megari?"

"yauwa ƴar gari tayani gani de"cewar rumana tana dafo Ameera.

"bazaku gane ba a yanzu amma nasan nan gaba zaku gane,dan haka ku dena tambayata"cewar inna cikin haɗe rai.

Bako su sake tambayarta ba,rumana ta miƙe ta shige ɗaki abinta,ranta fess,Ameera ce ta shigar mata da jakar kayanta cikin ɗakin tana jimama mutuwar auren na Rumana.

*********

Ashrab asibiti aka nufa dashi dan ceto rayuwarshi,sosai hankalin me gari da habu ya tashi fiye da tunani,dan sun rasa abinda ya haddasa masa hakan.

Bayan awanni biyu,likitoci na kansa,sannan suka fito,likitan ya buƙaci ganinsu a office ɗinsa.

"Binciken mu da muka yi akan Ashrab ya gwada mana ya kamu da ciwon damuwa,wanda hakan ke barazana wa lafiyarsa,yanzu haka wannan suma da yayi akwai abinda ya gani ya firgitashi"

"meko ze gani ya firgitashi doctor,nufinka aljanu ko me kake nufi?"cewar habu cikin damuwa

"hmmm ko kaɗan ba zancen iska nake ba,abinda nakeso ku fahimta de shine ku bashi abinda yakeso koda yaushe,dan ɗorewar lafiyarsa"

"insha Allahu likita zaayi yadda kace yanzu ya jikin nashi?"cewar megari kamar zeyi kuka

"da sauƙi sosai yanzu bacci yakeyi zuwa anjima zaku iya ganinshi"cewar likitan yana murmushi.....


Haka suka baro office ɗin suka nemi guri suka zauna zaman jiran a basu damar ganin nashi.

Kowa se saƙawa yake yana warwarewa,sum rasa gano kan maƙasudin ciwon nasa.


*******


"Wallahi inaga bacin rashin kunya da tarbiyya inaga yarinyar nan mayyace ma,yo inba mayya ba taya daga haɗa ido da ita ze suma?"cewar mahaifiyar Ashrab da suka baro a gida

"wallahi hajiya nima kwanaki nace haka sabida idanunta farinsu yayi yawa kamar wata ƴar ƙwaya,bana raba ɗayan biyu mayyarce"cewar hafsat ƙanwar Ashrab ɗin

"dako ra taro masifa,dan bame cimin ɗa ya kwana lfy inde ina raye,maza ki rakani gidan nasu inja musu kunne"cewar hajiya lokacin data miƙe ta ɗauki hijabinta.

Ayko hafsa abin nema ya samu da sauri ta ɗauko hijab ɗin tazo sika rankaya zuwa gidan nasu rumana,hafsa seƙara zuga mahaifiyar tasu take.

Ko sallama basuyi va suka shiga gidan,wanda hakansosai ya firgita su rumana dake zaune suna tsince wake.

Sheƙeƙe rumana take binsu da kallo, na renin hankali.dan tasan ba arziƙi ya kawosu gidan nasu ba ....

"daga kallonki ɗana ashrab ya faɗi,to wlh ahir ɗinku in kuna cin ƙasa to ku kiyayi ta shuri"

rumana murmushi tayi sannan tace"ina ƙudan yake bare romonsa,acan de gurin yawon barikinsa yahaɗu da daidao shi ba muba"

Inna dake ɗaki jiyo hayaniya yasata fitowa sa sauri,koda tazo taga abinda ke faruwa ɗauke rumanar tayi da mari har so biyu tace Cikin matsanancin fushi.

"rumana dama rashin kunyar taki takai har haka?sabida baki da mutunci mahaifiyar mijinki ba mahaifiyarki bace"ta sake kwasheta da wani marin,sannan tace.

"duƙa ki nemi yafiyarta ko na ci miki mutunci"

Kuka take takai guiwowin nata ƙasa da ƙyar tace cikin kuka"kiyi haƙuri hajiya ki gafarceni"

"hakan be wanke ki ba a gurina,dan rashin kunya da tarbiyya de ay na jima da sanin baki dashi,tunda ga ciki nan na shege ajikinki kuma da auranki,kinga ay asara anan ta ƙare"cewar mahaifiyar ashrab ɗin.

"cikina ba shege bane,ƙaddara ma shegen ne ay to jininki ne"rumana ta bata amsa tana kare fuskarta gudun kar inna ta daketa.

"hajiya ya kamata in mun girma mudinga sanin yakamata,rumana ƴar cikin ki da bata wuce kisa bulala ki zaneta ba be dace haka na shiga tsakaninku ba"cewar innar rumanan dan taji haushin abinda hajiyar tace.

"koma de menene shegen cikin nan nata ta dena alaƙanta mu dashi,in har zatayi haka ko dukana tayi bazanji haushi ba"

"dama ana shege agidan ubansa ne hajiya,ke rumana cikin jikinki na waye?"Cewar inna cikin fushi.

"na ashrab ne inna"cewar rumana hawaye na biyo idonta,sannan ta ƙara da cewa"ta koma ta tambayeshi taji in ze musanta"

"to hajiya kinji,dan haka kije ki tuhumi ɗanki,koya san da batun,tashin hankali bana sonshi tsakaninmu"cewar inna.

"zanko je in tuhumeshin,in ya musanta kun shiga uku daga ke har ƴar taki"cewar hajiya cikin fushi ta finciki hannun hafsat suka fice daga gidan fuuuuuuu.

Bayan fitarsu rumana durƙushewa tayi agurin tana kuka,

Muje zuwa

Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*LAST FREE PAGES*


_FREE PAGES A 15 ZE TSAYA,NA ƊAUKA DAMA ZE KAI 20 NE TO A 15 LABARIN YA ISO INDA NAKE SON TSAYAWAR,ƊARI BIYAR NE GA ME SO YA TURO KUƊINSA,ƳAN MATA KUMA NAJI ƘORAFINKU ZAKU IYA SIYA,ABUBUWAN DAKE CIKI ZAA SASSAUTA KAMAR YADDA KUKA BUƘATA,SAURA PAGE ƊAYA FREE YA ƘARE,IN DAN KI SIYA KI FITAR MIN NE KIBAR KUƊINKI_

*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*15*


Me gari beyi ƙasa a guiwaba ya amsa kiran na me ɗakin nasa,dan tana da ƙima a idanunsa.


Koda yazo yagansu tare da rumana tana kuka mamaki ne ya kamashi,dan haka cikin zaƙuwa yace"me ke faruwane anan,?na ganku cirko cirko atsaye?me tayi muku?"yayi tambayar yana me tsaresu da ido.

"ciki ne tsoho ajikinta"cewar hajiya tana harararta.

Daɓas me gari ya koma yaauna,ya warware rawaninsa,da gumi ya jiƙa masa lokaci guda.

Salati yake yi da dukkanin zuciyarsa kamin yasamu natsuwa tazo masa.habu ya kalla,yace "kai na damƙawa amanarta shin da sanin ka haka ta faru koko yaya?"

"Ranka ya daɗe gatanan da ranta da lafiya wlh in banda yau gyalenta ban taɓa riƙewa ba,shima na yau na ɗagane dan in tabbatar da abinda idona ya gani"cewar habu cikin biyayya.

Dubansa yakai gun rumana akaro na farko da magana ta fatar baki ta haɗasu,ga mamakin rumana cikin tausasawa yake mata maganar yace"ummu rumana abinda habu ya faɗi gaskiya ne?"

"gaskiya ne ya faɗi"tasake rushewa da kuka.

"Rumana garin ya hakan ta faru to,"me gari ya tambaya cikin rawar murya.

"a ƙoƙarina na in gujewa zama da habu ne na gudu nabar gidannan na tsawon kwana biyu,shine wannan ƙaddarar ta faɗamin da wani"ta sake rushewa da kuka.


"dama bada son raina akai auran nanba,tunda tun farko sameera naso ya aura kaƙi yarda to wallahi sakinta zeyi"cewar mahaifiyar habu tana cika tana batsewa.

"don Allah kuje zanyi tunanin hukuncin dazan yanke akan wannan maganar,"cewar megari da ƙyar yake iya motsa bakinsa.

Ficewa sukayi suka bar falon ya rage daga ita se me gari,wayarshi ya ciro ya danna wata number,baa jimaba ya ɗaga.

"Awa biyu na baka ka iso gabana,inba haka ba kaje na yafeka"cewar megari,be kum Jira amsar sa ba ya kashe wayar,yakai dibansa gun rumana yace.

"ƴata me isa kika yi haka,kinsan burin mahaifinki akanki kuwa?"

"koma me nayi ay kaine sila,da bakasa na auri ɗanka ba,duk haka da bata faru ba dan haka na shirya gwagwarmaya daku wallahi wannan ciki dole na ɗanka ne ba wanda ya isa ya shegantamin ɗa,"cewar rumana cikin matsanancin fushi,dan shi kanshi me garin ji take kamar ta shaƙeshi.

Murmushi yayi na yaƙe sannan yace,"ko aure be ba ɗana cikin jikinki ba tunda kin amsa ba nashin bane,gata ɗaya zan miki insa a ɗaukeki daga garinnan akaiki nesa ki haihu dan gudun ɓacin suna"

"a gabanku na amsa hakan a gaban kowa ko na ɗanka ne,bakusan wacece rumana bane,insha Allahu seka mutu da baƙincikina kwatankwacin wanda ka jefani ni da mahaifiyata,kuma ba inda zaa kaini".


"na kira ɗana awaya,ze kaiki can gurinsu ki haihu,cikin rufin asiri zaa kai ɗan gidan marayu acan"cewar megari cikin damuwa.


"zamu gani ashe ka taro wa kanka tonon silili"

Me gari bece komai ba yasa kai ya fice daga ɓangaren.ta koma nashi.ranshi a ɓace.


********

Bayan awa biyu


Motace ƙirar ƙamfanin mercedez baƙa,me baƙin glass ta faka a harabar gidan na megari,

Driver ne ya fito da saurinsa ya buɗe masa ƙofa,ya sako ƙafafunsa waje.

Farine dogo me jiki amma ba da yawa ba,kyakkyawane ajin farko duk abinda ake nema ajikin ɗa na miji ya mallakesa,ga kwarjini a idanun me kallonsa,shi ɗin namiji ne na shiga tsara.

Duba ɗaya wanda yasanshi ze masa ya fahimci baya cikin jin daɗo na halartar gidan a wannan lokacin,

A hankali yake takawa,hakan ze fahimtar dakai beda ƙoshin lafiya,

*ASHRAB KENAN ƊA GA ME GARIN NA SU RUMANA*

"ga yaya magaji ga yaya magaji jama'a ku fito ga yaya magaji yazo"haka ƙanwarsa salma ke faɗi lokacin datai arba dashi,


Ayko kamar jira suka dinga ɓullowa daga lungu da saƙo na gidan manya da yara,suka yo kanshi cikin murna kowa se rungumeshi yakeyi.

Duk da beda isasshiyar lafiya haka yay ta yi musu murmushi,yana rungumesu,


Ya jima kan su barshi ya dangana da iyayen nasa,dake zaune zaman jiran shigowar tashi.


Glasss ɗin idonsa ya cire lokacin daya isa gaban megari da hajiya.


Sosai suka ji daɗin ganinsa,karma de hajiya.

Duƙawa yayi ya gaishesu cikin girmamawa sannan ya nemi guri ya zauna.



Megarin ne ya gyara zamansa,sannan yace"Ashrab ni mahaifinkane da nakeson duk ci gabanka,naso ace kayimin biyayya amma se ka bijire,to ga illar da hakan ta haifar
*na maka aure kaki zuwa gurin matar taka,ƙarshe ta gaji tabi wani a waje yay mata ciki,Ba tare daka taɓa ganinta ba matarka na ɗauke da ciki tsoho"*cewar megari cikin damuwa.

"dan matar daka auramin nada tsohon ciki shine dalilin kiran nawa?"ashrab ya buƙata.


"ƙwarai kuwa,dan wallahi se ka sake ta bazaka zauna da ita ba inde nice na haifeka sameera nakeso ka aura"cewar hajiya kamar zata tashi sama dan masifa.


"hajiya ay base ma kin rantse ba dole zan saketa dan wallahi,bazan zauna da itaba,zaɓin naka Abba banaso kema hajiya banson taki inada zaɓina,dan Allah ku fahimceni nina fa mutum ne wanda keda zuciya ajikinsa"cewar ashrab cikin damuwa.


Habu megari ya kira awaya yace yazo masa da amaryar ashrab ɗin,


Koda habu ya kirata bata ƙi zuwa ba,,biyoshi tayi abaya batasa ko hijab ba ƙara ma turo cikin takeyi dan kowa ya gani.

Ƙarar cingam ɗinta ne yasa megari da hajiya waigowa yayinda shi ashrab ko kallo ma bata isheshi ba.

"yauwa ga tsinanniyar nan,"cewar hajiya cikin fushi.


"ko ba tsinanniya ba,"cewar rumana tana ƙaras da cingam cikin muryar da ita kanta batasan tana da ita ba.

"Hajiya banaso kina zubar da ƙimarki,bade ni na aureta ba to taje gidansu na saketa saki ɗaya, inada tarin damuwowi araina"yafaɗi batare daya dubesu vama.

"ahayye yau ake yinta kai kuma awa,me aurena daban kai me sakin daban to kaja bakinka ka tsuke shi habun ya sakeni"cewar rumana tana taunar cingam.


"ba da habu na ɗaura miki aureba da ɗana Ashrab dake Abuja na ɗaura miki aure,habu de kawai na ajiyeshi amatsayin sa ne dan kar ki fahimci ɗan nawa baya sonki haɗaku nayi,"


"kinga ko dan na sakeki ay ba laifi nayiba tunda ni aka ƙaƙabawa"cewar ashrab daya miƙe afusace yayo kanta da rashin kunyarta ta fara isarsa.


Ido cikin ido idanuwan Ashrab dana rumana suka sarƙe.


Hmmmmm aykin na gaba,da ɗari biyar ki more karatu.



Muje zuwa wainda kuka siya😁


Surbajo for life.
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze sakamin*

*16*


Jiri ne ya ɗaukeshi yayi luuuu baya ze faɗi da sauri me martaba ya taroshi,sede koda ya isa jikin me martabar tuni ya suma.

A ruɗe me martaba ke faɗin"kai magaji tashi buɗe idonka mana"amma ina tuni numfashi ya sarƙe.

Habu cikin yanayin firgici ya dubi rumana yace"rumana jeki gidanku yanzu"

Tsaye take tana kallon abun kamar film,wai Ashrab tantirin ɗan bariki lamba ɗaya data sani shine mijinta na aure uban cikin jikinta wanda da suke zaton shegene ashe da ubansa danƙari.

Jikinta ba ƙwari ta dubi habu tace"zaka zo to don Allah?"

"Eh zan zo maza ki tafi"ya bata amsa a gaggauce ba tare da sanin iyayen nasu ba dan gaba ɗaya hankalinsu na kan Ashrab.

Juyawa tayi batare da tace komai ba,tayi ficewarta zuwa part ɗinta,kayanta ta haɗa da zata buƙata sannan tazo zata fita,anan taga an kinkimo ashrab ɗin zaa sashi a mota,wanda ko tantama batayi asibiti zaa kaishi.

Tsaki tayi ta ƙarasa ficewa daga gidan,kanta tsaye gidansu ta nufa ba tare da damuwar komai ba

Koda ta shiga a tsakar gida ta samesu,duka suna hira,Ameera ce ta taso da gudu ta rungumeta,tana faɗin"ƴar halak kin ƙi ambato,yanxu umma ke cewa muje gurinki,mu jiyo mata watannin haihuwa,so take ta fara tarin gara"ta faɗi tana dariyar.

Dariya rumana tayi sannan ta ƙarasa cikun gidan,ta hau kan tabarma ta zauna da ƙyar,zamanta ba jimawa almajiran data ɗorowa kayanta suka shigo ɗauke da kayan,

A ɗan tsorace umman tata,tace"ɗafiya kuwa rumana?"

Murmushi tayi sannan tace"lafiya lau ummana,sakina yayi"

Salatin da umman ta ɗauka ne,yasa ta katse komai ta na jira taji me ya faru na salatin.

"rumana yanzu abinda kika zaɓawa kanki kenam ko,duk haƙuri irin na magaji amma yau kinsa kun rabu ko"

"umma dama kinsan magaji ne mijin nawa?"cewar rumana cikin kallon tuhuma.

"na sani manadan gidanku"cewar inna cikin fushi.

"to ni meyasa ban sani ba"

"sabida hankalinki be kai ki sanin ba shiyasa"

"komade menene nide na godewa tunda ba auransa akaina"ta faɗi hankalinta kwance.

"kinko yi asarar miji na nunawa saa,zaɓin mahaifinki kuma,Sannan har gobe kina nan a mazaunin matarsa har se kin haihu"cewar inna kamar ta zaneta.

muje zuwa

Zanyi me yawa da safe ngd
[10/17, 9:19 PM] bariki500: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ALALEN GERO*
*(BARIKI)*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Zahra Surbajo*

*Duk wacce ta fitar min dashi waje na barta da Allah,hakkina baze bar mutum ba,haka wanda ya karanta be biyaba na barshi da Allah shima,inde wahalatace Allah ze saka min*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*


*Mura nake kwana biyu🙏🏻*

*18*


Ta jima tana kukan ba tare da wani ya rarrashetaba,se da tayi me isarta sannan ta rarrashi kanta,ta miƙe da ƙyar ta koma ɗaki.

********

A firgice yafarka daga dogon suman da yayi,yana waige waige,da sauri habu ya ƙarasa kusa dashi ya riƙeshi, shiko ina ƙoƙarin ƙwacewa yake,da yaga habu beda niyyar barinshi ne ya ce

"budurwata rumana nagani ɗazu pls ka bari in isa gareta kar ta sake tsere mini"ya faɗiyana ƙoƙarin ture habu daga ruƙon da yay masa.

"yayamagaji ba fa budurwarka bace,matarkace rumana wacce ka saka"cewar habu yana ƙoƙarin maidashi kan gadon.

"aurena da rumana ay ba saki habu mutu ka raba ne,kadena cewa na saketa,zaka kasheni ne"ya faɗi hawaye na biyo idonsa.

Tausayinsa ne ya kama habu duk da be fahimci yayan nasa da manufarsa ba,amma ya tausaya masa.

Shigowar me gari ne yasa Ashrab yin shuru ya koma ya kwanta yana bin mahaifin nasa da idanu.

Gaban gadon me garin ya ƙarasa,ya kira sunansa be amsa ba sede ya ɗago idanunsa yana kallonsa.

"Ashrab ya jikin naka?"

Gyaɗa kai kawai yayi sannan ya dubi mahaifin nasa a raunane yace"Abba wacece kuka auramin,kuma hajiya tasa na saketa ,wacece inason sani"yayi tambayar yana hawaye.

"rumana ce ƴar gidan aminina,"

"me cikin nan ta ɗazu?"?cewar ashrab baki ba rawa.

Carab habu ya amshe zancen da cewa.
"eh yaya magaji ay itace amaryar taka da tayo cikin shege.. ."

"Ba shege bane nawa ne!!!!"ya faɗi lokacin daya shaƙo wiyan habu,sannan ya ƙara da cewa"cikin jikinta ɗan sunna ne, ɗana ne habu kar wani ya ƙara yunƙurin shegantamun ɗa"ya faɗi yana raba kallon gargaɗin harda idanun mahaifinsa.

Shuru dukansu sukayi sabida sun fahimci ciwon hauka ya fara taɓa kwakwalwarsa.

Nuni megari yayiwa habu kan yay shuru se

5 / 13