ARZIKI RABO Complete Hausa Novels by Dijensy.txt

Author :  Dijensy Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 21

3K to 6K   out of 61.6K words

    "Eh be dawo ba". Ta amsa.

      Mommy ko 'kala bata cewa inba wai Reyhana ta tambayeta ba.Suna zaune a haka su Bassam da Walida('Kannen Reyhana) suka dawo daga islamiyya.Da gudu Walida ta 'karaso tana mata oyoyo.

      " Walida 'yan mata an dawo". Reyhana ta fad'a tana rungumo ta.

      "Eh yaya,dama zaki so?" Ta tambaya.

      "Eh gani na zo". Ta amsa tana murmushi.

     Bassam shima 'karasowa yayi ya gaida Ahmad sannan ya gaida ta,itama Walidan se lokacin ta lura da Ahmad ta gaisheshi.

       " Toh Walida aje a sauya kaya ".Ikram ta fad'a lokacinda ta 'karaso.

     Ma'ke kafad'a tayi wai bazata bar yaya ba." Good girl jeki ki cire uniform d'in kinji seki dawo ina nan".Reyhana ta fad'a tana lalla'bata.

      "Toh".Ta amsa sannan ta kyalla da sauri zuwa d'aki.

       Shima Bassam nashi d'akin ya wuce.Inno(me aikinsu) ce ta kawo musu abinsha bayan sun gaisa.Mommy tashi tayi ta koma d'aki dan zaman ya isheta,se Ikram da Walida suna zaune kusa da Reyhana.

        Reyhana itace 'yar fari a gidansu,su biyar ne duka.Maza biyu mata uku,daga Reyhana se sageer ,Ikram,Bassam then Walida auta.Reyhana nada shekara 1½ aka haifi sageer saboda haka basuda tazara sosai.Reyhana tana da shekara 22 a yanzu se shi 20½,Ikram tana da 18 yrs,Bassam 15 then Walida 9yrs suna da tazara.

      Reyhana tana kammala degree nata ta auri Ahmad dan karatunta yayi sauri ko secondary school da wuri ta gama,Bsc microbiology ta karanta.Sageer a yanzu haka yana level 2 MLT yake karanta,Ikram kuwa year d'innan tayi graduation na secondary se Bassam yana SS1 Walida kuma primary 3.

      Mommy kuwa business woman ce tayi-tayi Abba ya barta tayi aiki amma ya'ki ,shiyasa business ta du'kufa kuma dama a gidan su yawanci 'yan kasuwa ne.Abba kuwa babban professor ne a university Buk.

     Sun kasance happy family kuma yaran sunfi sabo da Abbansu musammman Reyhana da Sageer kasancewar Mommy mace me zafi ,Abba yafi ta sau'kin kai.Toh wannan kenan.

      Wajajen 6:00pm Abba ya shigo ,cikin rissinawa ya gaishe da Abba itama Reyhana haka."Kice yau kune a gidan".Abba ya fad'a fuskarsa a sake.

      "Eh Abba d'azunnan muka zo". Ta amsa.
   
     " Toh mashaAllah yayi kyau Allah yayi albarka". Ya fad'a.

       "Ameen" .Suka amsa.

      Daga baya Reyhana d'akinsu ta wuce,sukuma mazan suka tafi masjid tare da Ahmad.

      Mommy seda taji fitarsu ta fito daga d'akinta ta shiga d'akin Ikram ,da tare suke kwana sanda Reyhana tananan yanzu kuwa ita kad'ai ta'ki bari Walida ta komo d'akin.

      "Ana san a had'u ayi ta hira da 'yan uwa amma baza a dinga waya dasu ba". Mommy ta fad'a sanda ta 'karaso.
    
         " Laaa! Mommy ina fa kira". Reyhana ta fad'a.

      "Ba wani,kuma da kika san zaki zo ba seki fad'a ba". Cewar Mommy tana shirin zama kan wani kujera dake d'akin.

      " Nima bansan da zuwan ba jinai kawai yace na tazo muzo gida".Reyhana ta fad'a.

      "Toh seku tashi ai kuyi sallah". Mommy ta fad'a.

     " Mommy idan zasi tafi zan bisu". Walida ta fad'a kanta a cinyar Reyhana.

     "Base ki bisun ba,tashi ki wuce ki sallah!". Mommy tai mata tsawa.

      Ba Walida ba har Reyhana seda taji ba dad'i" Mommy meyai zafi haka ?" Reyhana ta furta.

      Mommy ko amsata batayi ba ta fice daga d'akin,Reyhana kallo kawai ta bita dashi a ranta tana fad'in Allah ya kawo ranar da zata dena jin haushin aurennan nata...

AR²💖

# Comment
#  Vote

Jasko💕

   
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 0⃣3⃣

Bayan sun idar da sallah ne ikram ta d'akko mata wasu hotunan na bikin ta da bata gani ba.

     "Yaya kalleki a nan". Ikram ta nuna wani pic da Reyhana ta rife idanunta.

     Dariya dukansu sukai suka cigaba da kalla.Misalin 'karfe 7:08pm Inno ta gama abinci lokacin Abba suna parlour shida Ahmad suna 'yar hira.

     Bayan an kawo wa Ahmad abincin Abba ya tashi domin ya bashi waje dan ya kula ya kasa sake wa.Reyhana kuwa a d'aki suka ci tare da Ikram.

       Sageer shima lokacin ya shigo ,hannu ya mi'kawa Ahmad suka gaisa." Sageer ya school?" Ahmad ya tamabaya.

     "Alhamdulillah,kun shigo kenan?"

     "Eh d'azunnan". Ya amsa.

     " Ok,bari na watsa ruwa ". Sageer ya fad'a.

       D'akinsa ya wuce ,Reyhana kuwa ta shantake kamar bazata tafi ba hira ta'ki 'karewa.
  
      Koda ya gama yana zaune shi kad'ai a parlour sega kuma Sageer harya fito.D'an hira suka soma yi har lokacin isha'i yayi.Suna dawowa daga masjid yayiwa Reyhana text.

    " Toh Azizaty se a fito dare yana yi"
       
      Tana gama karancewa ta kalli agogo taga 8:13pm,nan take ta sauya fuska dan ji take kamar karta tafi sosai tayi kewar gida.

     "Ya de?" Ikram ta tambaya dan ta lura da chanjin fuskarta.

       "Ya Ahmad ne wai na fito mu tafi". Ta amsata.

       " Ayya! Yaya amaryar Ahmad ".Ikram ta fad'a cikeda tsokana.

      " Zan doke ki Ikram". Reyhana ta fad'a.

      "Sorry sister nice fa".

      " Toh ni ba wannan ba,yaushe zaki zo ki yinammin?"

       "Au wuni kad'ai zaki gayyaceni watoh banda kwana koh?" Ikram ta fad'a tana kallon Reyhana.

        "Ke dallah idan kwananma nace ai 'bata bakina zanyi". Ta fad'a.

       " InshaAllah zanzo bada dad'ewa ba yaya, yanzu de muje parlourn kar ya Ahmad yaji shiru". Ta fad'a.

     Parlour suka sauka se kuma suka iske Mommy ma tana parlourn gefe Abba da alama shiya kirata ta sakko da bazata zo siyi sallama ba."Reyhana kun fito kenan". Abba ya fad'a.

     "Eh". Ta amsa sanda ta 'karaso.

      " Sageer ashe ka dawo?" Cewar Reyhana.

       "Eh tun d'azu ,kina d'aki kunata hirarku". Ya amsata.

       " Toh ya school? "

       "Alhamdulillah". Ya amsa.

         Abba ne ya bawa Sageer key d'in motarsa yace akaisu gida,Mommy kuwa ta'be baki tayi taso yace akaisu a tata da anga tsiya.A haka sukai sallama itade Mommy fuskarta ba sakewa.

    Har 'kofar gida Sageer ya kaisu ,bayan sunyi sallama ya juya.Koda suka shiga gida ba light shiyasa da wuri suka kwanta tunda dama sunci abinci a gida.

                 ***

  Washegari 7:20am Ahmad ya gama shirinsa har breakfast ma ya kammala."Yau me za'a dafa da rana?"Reyhana ta tambayesa.

          " Ni duk abinda kika dafa yayi". Ya amsata yana zira takalmi.

         "OK dear seka dawo toh". Ta fad'a tare da mi'ka masa hularsa.

          " Wata'kila sena yi sallar juma'a zan dawo". Ya fad'a.

         "Ohh na tuna yau Friday koh". Ta fad'a.

         " Duk wannan kwalliyar danai baki tuna bama? Wait kinko ce nayi kyau ma?" Ahmad ya fad'a ya tsireta da ido.

        "Laa na fad'a abinda ma ko yaushe kyau kake, kawai de na sha'afa". Cewar Reyhana tana murmushi.

         " Au hakane ,toh sena dawo Azizaty karnayi late".

       "A dawo lafiya".Ta fad'a.

       " Ameen".Ya amsa daga nan ya fita.

     Kamar koyaushe nan da nan tayi aikin gida tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfa blue me ratsin fari da ba'ki.Ga turaren wuta daya turnu'ke ko ina Reyhana bade tsafta ba.

      Wayarta ta d'auka ta kira Saudat ('kawarta ) tare sukai secondary school.
   
       "Amaryar Ahmad kin ya dani,daga kaiki gidanki se mijiki li'kwi bako flashing?"

        "Saudat da sharri yanzu gashi na kira ki ,kece ma kika manta dani baki zo ba". Reyhana ta fad'a.

         " Ina tafe ai ki shiryan kayan dad'i".Saudat ta fad'a.

        "Karki damu zaki zo ki kwashi girki na". Cewar Reyhana.

         Sun dad'e suna hira kafin daga baya siyi sallama.11:30am ta d'ora abinci ,a  hr d'aya da 'yan mintina ta kammala ,zo'bo ta had'a shima nan danan tasa a fridge.

             ***
  Gidan Mommy..

         Tana d'akinta  ,wata yayarta(Anty asma'u),suna d'asawa kusan halinsu yazo d'aya.

        " Ya amarya a gidanta?" Anty Asma'u ta tambaya.

        "Uhmm! Tana gidanta jiya ta shigo ma". Cewar Mommy tana ta'be ba'ki.

         " Ita kad'ai ko harda Ahmad d'in?"

         "Ita dashi ne".Mommy ta amsa.

         "Toh ke yaushe zakije keda Abbansu?" Ta tambayi Mommy.

         "Sede shi yaje dan ba zuwa zan ba,wannan d'an 'kurbibin gidan". Cewar Mommy.

        "Toh ya za'ai ? Yaran yanzu ne bajin magana suke ba kana d'ora su a hanya suna kaucewa". Anty asma'u ta fad'a.

       " Ai du Abbanta ne wlhy badan shiba da ba abinda zesa na yarda da aurennan".Mommy ta fad'a.

      "Eyyi ita dad'i miji zata gane me ake nufi rabu da ita". Anty asma'u ta fad'a.

       " Ni abinda yake sake cimin rai shine ko a karatu ta masa nisa shekarun kansu befi uku  ya bata ba yaro ne shakaf amma ita ta rife ido seshi".

      "Allah de ya sawwa'ke". Anty asma'u ta fad'a.

     " Ameen ".Mommy ta amsa.

                  ***

1:45pm Ahmad ya dawo gida ,koda ya shiga d'aki bata ciki suitcase d'in ya ajje ya fita zuwa sitting room." Laa! Dear yaushe ka dawo banji ba?" Reyhana ta fad'a tare da 'karasowa inda yake.

         "Azizaty najiki shiru ne". Ya fad'a.
    
         " Sannu da dawowa toh ".Ta fad'a.

        " Yawwa Azizaty".Cewar Ahmad tare da rungumota jikinsa.

        "Bari na  kawo abinci dan naga se hamma kake".Reyhana ta fad'a tare da yin dariya ta fita bata jira me zece ba.

       Girgirza kai kawai yayi yana murmushi dan kuwa bata yi 'karya ba tun daya baro school ya fara jin yunwa.A tray ta jero komai ta kawo.

     " Azizaty taya kiga gane ina jin yunwa?" Ahmad ya tambaya.

      "Naga kana ta hamma ne,gashi da'kyar kake magana". Reyhana ta fad'a ta 'kare da dariya dan ita kanta maganarta ta 'karshe ta bata dariya.

      " Azizaty da sharri kike,what ever de ziba min am grateful i have a special wife like you me gama abinci da wuri".Ahmad ya fad'a.

        A plate ta sa musu suka ci yana ta santi yana yaba girkinta,ita de kawai murmushi take a ranta tana jin dad'in yadda yake yaba girkinta da dad'ad'an kalamansa masu sanyaya zuciya.

          Bayan sun gama ci kuma suka tsiri yin photo ,kala-kala tayi ta selfawa sosai sunyi kyau (Naga su wa'e an le'ko 'yan ina ga selfie...lox bande fad'i suna ba😝).

                 ****    Rana Sunday da Asr Ahmad yace ta shirya suje gidan Umma.Ita kad'ai suka tarar gidan ko yaran ma'kobatan ma masu d'an le'ko mata basu shigo ba."Yau Reyhana ce a gidan,sannu da zuwa "Umma ta fad'a tana 'ko'karin shinfid'a tabarmar dake jingine a kusurwar d'akin.

      " Ina yini Umma"Reyhana ta gaisheta cikin rissinawa.

     "Lafiya lau Reyhana". Ta amsa.

      " Ya zaman shiru?"Umma ta tambayeta.

      "Alhamdulillah ". Reyhana ta amsa.
  
       Shima Ahmad gaisawa sukai sannan Umma ta kawo mata ruwan sha da band'ashon gurasa." Sannu da 'ko'kari".Cewar Reyhana kanta a sunkuye tana wasa da yatsunta.

       "Kinga ki sake jikinki se wani ra'bewa kike".Ahmad ya fad'a mata 'kasa-'kasa ba tare da Umma taji me yace ba.

       Bayan 'yan mintina kad'an ya tashi" Umma bara na le'ka waje". Ahmad ya fad'a.

      "Toh seka dawo".Umma ta fad'a.

       Kad'an -kad'an suke hirarsu ,Reyhana ba sabawa tayi da ita ba tunda yau ne karo na farko tazo,sede su gaisa a waya shiyasa ta kasa sakin jikinta.

    " Kici band'ashon mana ai abin marmari ne".Umma ta fad'a.

         Itade Reyhana murmushi tayi sannan ta fara gutsura.

       "Ki saki jikinki nan ai gidane". Umma ta fad'a tana murmushi.

       Reyhana taji dad'in band'ashon kusan biyu da rabi taci(Nima naji dama..😋).

      Umma dama daga ita se d'anta Ahmad data haifa gashi yanzu ita kad'ai shiyasa ma wani d'an saurayin ma'kota yake kwana a shagon gidan na waje.Sunyi sabo da jam'ar unguwar sosai dan a nan aka haifi Ahmad abokanansa dayawa suna nan shiyasa a koda yaushe idan yana gida toh suna majalissarsu yanzun ma can ya tafi.Umma mace me ha'kuri ba sawa ba hanawa dattijuwa ce me son zaman lafiya ba ruwanta da ta'kurawa suruka..

      Har mahrib tayi bai shigo ba,tashi tayi tai sallah danma Allah yasa da wuta 'yar 'karamar TV dake d'akin  Umma ta kunna mata kallo.Haka yasa ta rage zaman shirun,Umma kuma ta koma kan girkinta.

       Ahmad bashi ya dawo ba se bayan isha'i ,a kitchen ya iske Umma.

      " Sannu da aiki girkin ne?" Ya fad'a yana shafa ciki.

       "Baka ci a majalissar ba?"

       "Ai nasan zan kwashi girkin ki shiyasa". Ya fad'a yana d'an dariya.

        " Ni banyi girki dakai ba,daga ni se Raihana". Umma ta fad'a tana kad'a miya.

      "Bafa Raihana ba Rey Reyhana ake cewa". Ya gyara mata.

      Dama tana sani tace Raihana tasan seya gyara mata,ko kafin yayi aure ma haka sike da ita.Reyhana tana jiyosu a d'aki tana dariya yanayin rayuwarsa da mahaifiyarsa yana birgeta.

        " Azizaty ina nawa bad'd'ashon?" Tajiyo maganar Ahmad.

        "Ga d'aya da rabi na rage ma". Ta fad'a tana jiran meze ce.

        " Lalle kinde cinye ,toh aiko tashi zaki mu tafi seki min abincin dare".Ya fad'a.

       "Abincin dare a wannan lokacin?"

        "Ehmana ba kin cinyen na Umma ba". Ya fad'a kamar d'an yaro.

    Dariya ya bata yanda yayi maganar,zata sake magana Umma ta shigo da abinci.

     " Reyhana ga tuwo fah".Umma ta fad'a tare da ajjewa.

      "Toh madallah Umma".Ahmad ya fad'a tare da janyo warmer d'in kusa dashi.

     Reyhana murmushi kawai tayi ta d'auke kai kamar bata gani ba tasani yana sane yayi haka ita kuwa ba kula shi zatai ba balle ma Umma tana wajen.

         " Bakya ci ne?" Ya tambayeta.

         "Niba kai na kawowa ba fah".Umma ta fad'a.

         "Haba Ummana ya dahaka ita d'azu taci band'asho nikuma yanzu se a barni naci tuwo ai koh".Ahmad ya fad'a yana bud'ewa.

      Tuwon dawa ne da miyar kuka ga wani 'kamshin daddawa dayake tashi (Kai wayyo dad'i 😋).

   " Hmmm! nayi missing d'in girkinnan fah". Ya fad'a yana kallon Reyhana. 

        Gani yayi bashi take kallo bama,yana gama zibawa a plate d'in ta faki ido Umma taga bata kallon wajen tayi sauri ta janyo plate d'in wajenta.Kafin ya ankara Umma ta waigo ,basarwa yayi ya sake zuba wani a plate dan yasan ba ci zatai dashi ba.

      Kowa shiru yayi yana sambad'ar tuwonsa har suka kammala.

       "Alhamdulillah se tafiya kuma". Ahmad ya fad'a bayan ya ajje cup d'in ruwa.

      " Ai ka bari abincin ya fad'a kuma".Umma ta fad'a.

        Seda suka 'kara kusan minti 20 suka tafi.

        Koda suka koma gida Ahmad be kwanta da wuri ba dan akwai test na students nashi da be 'karasa marking ba.Ita kuwa tuni tayi bacci bema lura ba dan a zaune yake kan gadon ya juya mata baya.

       Dayai magana yaji bata amsasa ba ya waiga yaga tayi bacci.Murmushi ya saki sannan ya gyara mata kwanciyar ya tofa mata addu'a....
     
    
AR²💖

Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 0⃣4⃣


  Da asuba bayan ya dawo daga masjid Reyhana ta kai masa ruwan wanka toilet.

       Da kanta ta za'ba masa kayan sawa yana fitowa ya gansu ta ajje a kan gado ,T-shirt ce dark blue da ba'kin jeans ,da sauri ya saka ya shirya tsaf tukun ya fito.A kitchen ya taddata tana soya dankali.

      "Ina kwana". Ta gaisheshi.

       " Lafiya,ya bacci Azizaty jiya da wuri haka kika kwanta". Ahmad ya fad'a.
   
        "Eh toh naga kana ta marking". Ta fad'a.

           " Toh me ake dafa wa?" Ya tambaya.

           "Hmm dankali ne". Ta amsa.

           " Sannunki da 'ko'kari".

           "Yawwa dear". Ta amsa.

       Bayan mintina ta kammala ta kawo masa." Azizaty ke ba yanzu zaki ci ba?"

      "Se anjima".Ta amsa.

     Ba jimawa ya gama breakfast d'in,takalmi ta d'akko masa a d'aki yasa sannan ya tafi ,ita kuwa ta koma baccinta.

              ***

     Haka abubuwa suka cigaba da gudana ,Ikram da Walida sunzo sun wuni sageer ma yazo, Abba ne har yanzu daya cewa mommy suje seta ce ba yanzu ba ,sede yana waya da ita.

      Yau aurensu wata uku kenan,Reyhana na kitchen tana girki yau Saudat zata zo.

        " Azizaty 'kawar taki bata karaso ba kenan".Ahmad ya fad'a sanda ya fito tsakar gidan.

        "Minyi waya tace ta taho". Reyhana ta fad'a.

         " OK,bara zan d'an le'ka waje ba dad'ewa zan ba".Ya fad'a yana zira takalma.

         "Toh shikenan seka dawo".

        'Yan mintina 'kalilan ta 'karasa dama couscous da miyan ne se lemon cucumber tun jiya dama tayi mata cake ga exotic guda biyu daya ragu ta had'a mata

2 / 21