ARZIKI RABO Complete Hausa Novels by Dijensy.txt

Author :  Dijensy Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 21

9K to 12K   out of 61.6K words

ta fad'a.

      "Idan na samu sau'ki sena shigo anjima". Reyhana ta fad'a.

       " Toh Allah ya sawwa'ke".Mommy ta fad'a sannan ta katse wayar.

      Reyhana kuwa koda rana tayi bacci ta koma abinta dama Ahmad ze biya gidan Umma daga makaranta.

    Haka aka gama biki bako d'uriyarta ,Ahmad daya dawo ya tamabayeta tace masa ciwonkan be dena ba.

    Mommy dama ta fidda ran zuwanta,akayi dinner ba ita.Washehari ma yini bata jeba haka aka 'kare biki ba ita.

     Ranar sunday da safe Abba yana gida yayi kiran Mommy, ita bata kawo akan Reyhana bane bama.

       "Mommyn Walida me Reyhana tayi miki?" Ya tamabayeta bayan ta zauna.

      "Bangane ba". Mommy ta fad'a tana neman 'karin bayani.

       " A biki mana an fad'amin kun saka tayi kuka a dalilin mey?"

       "Ita Reyhanan ce kenan ta fad'a maka ,amma meyasa bata fad'a maka dalili ba?" Cewar Mommy.

       "Sam ba ita bace and tambayarki nayi ba canayi ki tambayan ba". Abba ya fad'a ba watsa cikin lamarin.

    D'an  gyara murya tayi Mommy kafin tace." Fad'a ne bata so,dan me zata zo biki kusan to 6 kowa yana tambayarta amma shiru abinda tutuni an fad'a mata".

     "Yanzu akan bikin shine kuka rifeta da fad'a? Yayi kyau Maryam kece da ita ko mijinta idan yayi niyyar hanata zuwa ya zakiyi? Dole fa ki ha'kura wannan yaran mijinta ne ko ki yarda ko karki yadda ,kuma bana so haka ya sake faruwa idan ba haka ba rai ze 'baci walhy". Abba ya fad'a cikin fushi.

    Mommy da ta gama 'kuluwa yana gama maganar ta tashi ta fita bako bada ha'kuri.

     Ai d'akin Ikram ta wuce direct,bacci ma take taji ana d'ala mata duka a cinya.

      " Tashi zaune nace!" Mommy ta fad'a.

     A zabure ta mi'ke dan dukan ya shigeta"Mommy !"Ta kira kamar zatai kuka.

       "Kece kika fad'a wa Abbanku nayi wa Reyhana fad'a a gidan biki?" Mommy ta tambaya.

     "A'a bani bace". Ta amsa.

      " Waye idan bake ba?"

       "Sede Walida". Ikram ta fad'a.

      Mommy kai ta kad'a ta wuce d'akin Walida,itama tana bacci ta tasheta.

      " Kece kika fad'a wa Abbanki nayi wa yayarki fad'a koh?"

      "A'a canai tayi kuka de". Walida ta amsa tana murza ido.

     Rankwashi taji akanta wanda batayi tsammani ba,da sauri ta dafe gun tana shirin kuka taji dundu a bayanta 'kwarara uku.
 
     " Sarkin surutu manya suna magana kina zuba musu ido shashasha na sake ji kin fad'a masa wani abun".Mommy ta fad'a ta dungure mata kai ta fita.

     Walida kuwa kai ta cusa cikin fulo ta fara rera kuka wanda baza a jiyota ba.

             ****
    Reyhana yau baccinsu suka sha se wajen 10 am suka tashi ,nan tayi musu abincin breakfast bayan sunci sukai wanka.

      Kayan wankinsu ya taru saboda haka koda Ahmad yace ze kai mata nata tunda shi dama baya kai wanki da kansa yake yi.Reyhana tace ya bari kawai sayi wankin tare yau tunda yana gida sesiyi ba yadda be da ita ba tace a'a dole ya ha'kura.Ganin baida isassun kud'i yasata yin haka dan kusan duka salary d'in a abinci ya 'kare.
   
     Turyan turyan suka fara kusan shine 'karfin wankin daga baya jagab sukai da ruwa dukansu wannan ya she'kawa wannan haka sukayi tayi har suka 'kare wankin.

              'Bagaren Mommy kuwa koda suka fito breakfast dinning table, Abba ya lura da jan da kumbura da idanuwan Walida sukai.

     "Walida meya sami idanki? Ko kuka kikai?" Abba ya tamabayeta.

     Kowa kallonsa ya dawo kanta bare Mommy da take jira taji me zata ce.Wuri-wuri tayi da ido tana tsoron Mommy karta fad'a ta sake dukanta idan ta kalli Abba seta kalli Mommy ta rasa ya zatai.

      "Fad'a min kinji meya sami idon?" Abba ya sake tambaya.

AR²💖
   
*Please comment,vote and share, love you all💕*

Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 0⃣6⃣

Walida da ganin irin kallon da Mommy keyi mata yasa tace"Abune ya shigemin idon shine na sosa yayi ja".

"Ayya ya fita yanzu?" Abba ya tamabaya.

"Eh". Ta amsa.

Mommy kallonta tayi alamar kin ceci kanki d'innan.

***
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa yau da dad'i gobe babu.

Reyhana tana d'aki tana nikke jera kayan data goge a wardrobe. Sallamar yaya Ahmad yasa ta fitowa dan wataran dama yana fita da key idan ya dawo ya bud'e base yayi knocking ba.

A sanyaye ya 'karaso d'akin." Sannu da dawowa".Reyhana ta fad'a.

"Yawwa". Ya amsa a sanyaye.

"Yaya wani abune?" Reyhana ta tambaya.

"Ahnn...kainane yake ciwo". Ya amsa.

" Ayya sannu kayi wanka sena zubo maka abinci kasha magani".Ta fad'a.

Tashi yayi ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet,Reyhana kuma ta fita had'o abinci.

Sitting room d'in ya zauna yaci abincin kad'an -kad'an yake amsata.Paracetamol ta 'ballo masa ta bashi ya watsa,kan kujera ya samu ya haye yayi rigingine hannunsa ya d'ora kan goshi kamar me bacci amma ba baccin yake ba.

Reyhana kuwa bayan data kwashe kwanikan d'aki ta koma ta cigaba da abinda take dan tana tunanin ko gajiya ce tasa shiyasa ta bashi space.

Shikuwa ba abinda yake tunani se ta yadda ze 'bullo mata da wannan al'amari daya faru dashi.

Da asr ya tashi yaje masallaci bayan ya dawo kuma ya tarar tana kitchen had'a abincin dare saboda haka ya koma d'aki yana jiran anjima ya sanar mata.

Se bayan da suka kammala cin abincin dare sannan ya zauna da ita.

"Reyhana bansan ya zaki d'auki wannan abun da zan fad'a maki ba,ina me baki ha'kuri". Ahmad ya fad'a.

" Yaya mene ka fad'amin du na tsorata".Ta fad'a.

"Reyhana.. aa..an sallameni daga makarantar da nake teaching". Ya fad'a da 'kyar.

"Subhanallahi yaya meya faru? Meyasa?" Reyhana ta fad'a hankalinta a tashe.

"Director na school d'in ya fad'a mana cewa malaman school d'in sunyi masa yawa kuma biyan salary yana nema ya gagareshi and kuma yanzu sunfi son masu degree certificate".

Shiru tayi Reyhana hannunsa biyu ta ru'ko." Yaya addu'a kawai itace mafita ba damuwa ba jarabawace garemu,Allah ya musayya maka da wanda yafi wannan Yaya".

"Ameen". Ya amsa.

Sosai ta damu amma ta danne irin damuwar data shiga,ranar kusan dukansu basi cikakken bacci ba musamman Ahmad.

Ko washegari daya tashi yana d'aki ko breakfast d'in arzi'ki beba ya kwanta yana tunane-tunane.Reyhana ce ma take d'an kwantar masa da hankali da taga yana tunani seta zauna ta fara yi masa hirarraki kota kunna masu kallo da rana,haka da daddare dukansu tashi sike sallah.

Ko Umma be fad'a mata ba bayaso ta shiga damuwa,yanzu fafutukar neman abinyi ya tsindima.A rana seya fita yafi so uku,a haka har ya samu wajen aiki,sunayin sliding window.

A kullum ake biyansa kud'in ba masu yawa bana sede addu'a kawai.

Yau bayan fitarsa wajen 9am ko karyawa beba dan tashi sukai gas d'inma ya 'kare gashi ba kud'in refilling danma Allah yasa da 'yan wasu kud'i a hannunsa da Abba ya aiko mata sanda Sageer yazo.

Ragowar 3k ne dan haka da kanta ta fita bata da me aike.Ganin kayan abincin su sun 'ka'kkare ta sissiyo wasu abubuwan se ragowar ta d'uro gas.

Ahmad ba shi ya dawo ba se 3pm,bayan watsa ruwa ya fito sitting room be ganta ba dan haka ya le'ka kitchen.

"Azizaty ina kika samu kud'in gas?" Ya tambaya.

"Hmm karka damu akwai wasu 'yan kud'ine a guna shine nayi amfani dasu nayi siyayya". Reyhana ta amsa.

" Meyasa kikai haka Reyhana? Kud'inki ne na amfanin kanki kuma shine..."

"Is ok wannan ba wani abu bane me zanyi dasu idan banyi hakan ba?karka damu mana".

Shiru yayi yana kallonta a ransa yana jin sonta na sake ha'baka a zuciyarsa,ta wani side d'in kuma tausayinta dan bata taso cikin irin wannan rayuwarba.

***
Mommy kuwa batasan halin da Reyhana ke ciki ba dan bata fad'awa Mommy ba.

Gobe zasije wata dubiya dan haka tasa Ikram ta sanar wa Reyhana.

Ahmad yana zaune ta amsa kiran Ikram d'in saboda haka bayan ta gama wayar ta sanar masa.

Washegari around 2pm ta isa gida,Walida da gudu ta tarota dan ta hango shigowarta.

" Yaya oyoyo!" Ta fad'a .

"Walidandan 'yan matan Mommy".Reyhana ta fad'a tare da rugumota.

Hannunta a nata suka 'karasa ciki ,Mommy tana d'aki ta fito.

" Mommy ina yini ".Reyhana ta gaisheta.

" Lafiya lau".Ta amsa.

Yau ba kamar rannan ba fuskarta a sake take ko dan ganin ba Ahmad..

"Ina Ikram da Bassam?" Ta tambaya.

"Suna d'aki". Mommy ta amsa.

" Walida maza jeki ce inno ta kawo mata masa(wainar shinkafa)".Mommy ta fad'a.

Tashi tayi kamar yadda Mommy ta umarta,inno ta kawo mata wainar Walida ta taho da juice.

Kad'an taci wainar tace ta 'koshi,bayan sunyi sallar asr suka fita,Mommy ce da kanta ta jasu a motarta.

Kasancewar dubiyane basu dad'e ba sosai,Mommy ta biya dasu gidan Anty Asma'u.Reyhana sam bata so zuwansu chan ba dan tasan halin Anty Asma'u gashi Ahmad's besan da wani biyawa gidan Anty Asma'u ba ,tana kallo har suka isa bata iya cewa komai ba.

"Ahh! Yau harda Reyhana lalle irin wannan ba zatan". Cewar Anty Asma'u.

D'akinta ta jasu kamar yadda suka saba da hakan,ita de Reyhana jikinta a sanyaye.

" Anty ina yini". Ta gaisheta bayan sun zauna.

"Lafiya lau Reyhana yau an samu de an fito". Ta fad'a.

" Atoh na tusota a gaba da baza ki ganta ba". Mommy ta fad'a.

Yaran Anty Asma'u ne suka shigo suma suka gaggaisa dasu,a ciki akwai 'yan mata biyu kusan sa'annin Reyhana ne shine suka soma d'an hira.

Me aiki tasa ta kawo musu abinsha,suna zaune har maghrib ita de Reyhana hankalinta ya fara yin gida.

Gashi tana tsoro tayi wa Mommy magana tace ta fiya zumud'in gidan miji dan haka tayi shiru.

"Reyhana de ta gaji naga tayi shiru". Cewar Anty Asma'u.

" Toh ai nima yanzun nake so mu tafi".Mommy ta fad'a.

Seda sukai sallah tukunnan lokacin har 7:25pm tukun suka fito ,har bakin gate ta rakosu sukai sallama.

A mota suna tafiya sega kiran Ahmad.

"Hello yaya". Reyhana ta fad'a bayan data d'aga.

" Azizaty naji ki shiru".Cewar Ahmad.

"Gani ina hanya ba dad'ewa zan 'karaso". Ta fad'a.

" Toh sekin dawo"

Yana katse wayar ta kalli Mommy a ranta tana fad'in Allah yasa ba gidan Mommy zasi wuce ba.

Tana wannan tunanin taji Mommy tace "chan zami koh?"

"Eh". Ta amsa da saurinta.

Mommy har 'kofar gida ta kaita,tana fita daga motar sega Ahmad yana fitowa daga gida zaije masjid.

Reyhana ce ta fad'a masa Mommy ce ta kawota.'Karasawa yayi har k'ofar mota Mommy ta sauke glass d'in motar ya gaisheta cikin rissinawa.

Mommy tana tafiya ya wuce majid karya makara Reyhana ta shiga gida.

Reyhana wani dad'i taji lokacin da ta le'ka kitchen taga ya siyo gurasa saboda haka miya kawai zatayi.

Tana dire bag d'inta da mayafi ta shiga kitchen had'a miyar a d'an 'kan'kanin lokaci ta kusan kammalawa.

Ahmad daya shigo ya tarar da ita a kitchen.

" Uwargida daga dawowa se girki kuma".

Murmushi tayi tare dayi masa sannu da zuwa.

"Ai naga ka siyo gurasa kaga miyace kawai zanyi nama kusa gamawa". Ta fad'a.

" Toh sannu da aiki".Ya fad'a.

"Yawwa". Ta amsa.

Tana gama miyar ta turara gurasan ta sako musu.

" Azizaty ai baki ci dayawa ba". Ya fad'a.

"Ya isheni naci waina a gida". Ta fad'a.

" Mun biya gidan Anty Asma'u fah".Reyhana ta fad'a dan bata so ta kasance me 'boye-'boye.

"Haba,daga gidan dubiyar kuka biya?"

"Eh". Ta amsa.

" Toh ya suke?"Ya tamabya ba tare da ya nuna komai ba.

"Lafiya lau". Ta amsa.

Haka suka cigaba da hirarrakinsu kafin lokacin kwanciya yayi suka kwanta.

***
Washgari Reyhana ta farka jikinta li'kis dan zazza'bi daya rufeta da'kyar tayi sallah.

" Azizaty ko asibiti zamu?"Ahmad ya tambayeta.

"A'a mu bari ze sauka".Ta fad'a.

Goshinta ya ta'ba yaji da zafi amma ba kamar da asuba ba.

Da kanshi ya had'a mata breakfast ya kawo mata.

" Azizaty ki daure ki sha tea seki sha magani".Ahmad ya fad'a.

Da taimakonsa ta mi'ke daga kwance,tea d'in ta d'an kur'ba.

"Kici doyan ko kad'anne". Ahmad ya fad'a.

'Kwaya d'aya tasa a baki da'kyar ta iya had'iyewa ta kora da tea.

Sede tunda ta had'iye ta kasa sukuni saboda tashin zuciya da ya tunkaro mata.

Ahmad yana mata sannu kai kawai take kad'awa ta kasa ko magana.

" Azizaty ki 'kara ci ko kad'an ne".

Kai ta girgiza masa alamar a'a.

"Azizaty ki...." Be 'kare maganar ba yaga ta tashi da hanzari ta nufi toilet.

Seda ta amayar da abunda ke cikinta kaf,Ahmad ne ya wanke wurin ya taimaka ta koma d'aki.

Kan gadon ta zauna ta jingina Ahmad yana mata sannu.Daya ta'ba goshinta yaji ba zafin.

"Kin dena jin sanyin?" Ya tambayeta.

"Eh". Ta amsasa.

Kwanto da kanta jikinsa yayi yana shafa bayanta,a haka bacci yayi gaba da ita.

AR²💖

*Need your comments, votes and share.Love u all😘*

Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 0⃣7⃣        Ranar Reyhana wuni tayi a kwance ,Ahmad se ha'kura yayi da fita. Jollof taliya ya dafa musu taci kad'an ,shima be iya yaci dayawa ba.

Washegari da safe ya taimaka mata tayi wanka ta shirya.

"Reyhana tashi fa zaki mu tafi asibiti". Ahmad ya fad'a.

" Mu bari ze fa sauka zazza'bin".Reyhana ta fad'a murya tana rawa.

"Ba shawararki fa nake nema ba tashi zaki nace mu tafi yanzu". Ahmad ya fad'a in serious turn.

Tana turo baki ta tashi ta zira hijab da takalmi.A hanya yana mata hira ta'ki ko tanka sa.

Reyhana ba wani abu yasa bata son asibiti ba sedan tana tsoron allura(kamar ni😂).

Suna isa asibitin zuciyarta na sake tsorata a sanyaye ta shiga gun likita.

Koda ta gama zayyane masa abunda yake damunta test na mp da PT ya rubuta mata.

Data fito Ahmad yana tamabayarta takardar kawai ta mi'ka masa, nan suka tafi laboratory. Wajen blood collection da'kyar ta yarda aka d'auka jininta tund PT d'in serum ne.

Bayan kamar 20min aka bata result tana fitowa ko ta kansa bata bi ba.Yana mata magana amma ta'ki kula sa illa hannunta data ri'ke kamar wacce ta karye. Hakan yasa kamar yayi dariya amma dan kar ya had'a mata zafi biyu ya maze kawai.

Koda ta bawa doctor result d'in daya duba wasu 'yan magungunan ya rubuta kad'an sannan yace.

" Congratulation".

Kallonsa ta soma yi cikeda rashin fahimta.

"Kina d'auke da juna biyu,zaki je yanzu wajen scanning ga wasu maguguna da na rubuta maki Allah ya 'kara lafiya". Doctor d'in ya fad'a.

      " Ameen nagode".Reyhana ta fad'a bayan ta kar'bi katin.
   
    Lokaci guda tsoro da farinciki ya ziyarce ta,tana fitowa Ahmad ya 'karaso inda take "Azizaty me doc yace?"

       Mi'ka masa katin tayi ba tare da tace komai ba.

       "Azizaty wannan kike 'boyewa daman?" Ahmad ya fad'a fuskarsa d'auke da murmushi hatta ha'koransa seda suka fito.

     D'an waigar da fuska tayi tace"Nima ai d'azun ban duba ba ".

       " Maman baby me tsoro".Ahmad ya fad'a.

      Tafin hannunta ta d'ora a bakinta tana murmushi amma har lokacin bata waigo ba.

      Wajen scanning d'in suka 'karasa ba dad'ewa akai mata ya nuna 5weeks.

       Dad'i gun Ahmad baze misaltu ba itade Reyhana kawai takardan ta zubawa ido dukda kuma cikin ranta itama farincikinne.

      A hanyar dawowa ya sayi fruit da balangu suka komo gida a napep yana ta mata hira itade uhm da a'a ne amsarta.
    
     Suna shiga gida Ahmad ya sata a gaba seta sha fruit da naman.Kad'an ta samu taci tace ta 'koshi.

       "Kina so ki bar Babynmu da yunwa ne?Ahmad ya fad'a.
 
     " Nafa 'koshi anjima na sake ci".Reyhana ta fad'a.

    "Toh yanzu me kike so?" Ya tamabyeta.

     "Bacci"Ta amsa.

     " Laa! Azizaty yau bacci kike so ba niba".Ahmad ya fad'a dan so dayawa ya saba tamabayarta haka seta ce masa shi.

      "Toh nima shikenan ,babynmu nake so". Cewar Ahmad.

     Reyhana murmushi kawai tayi ,tashi tayi da niyyar tattare kayan gun da sauri Ahmad ya ri'ke hannun.

     " Azizaty rufan asiri mey ta kaikai yin aiki a wannan lokacin kwantawa zaki ki bacci ba abinda zaki ta'ba".Ahmad ya fad'a.

       Hannunta ya ri'ke suka nufi d'aki ,kan gado ya kwantar da ita ya saisaita mata fankar d'akin ,yana zaune gefen gadon har seda tayi bacci tukun ya koma sitting room.

      Kayan wajen ya tattare da kwanukan da suke ba a wanke ba ya d'aurayesu.

       Reyhana baccinta tayi ta 'koshi se wajen 2 ta farka tayi sallah nan ta tarar da abinci shinkafa da miya koda ta tambayeshi shi waya dafa yace ai umma ce ta turo yaro ya kawo.

      "Kenan fad'a mata kai bani da lafiya". Cewar Reyhana.

      " Ehyi ta kira kina bacci ma".Ahmad ya fad'a.

      "Ya babynmu ya tashi?" Ya tambayeta tare da d'ora hannunsa ya shafa cikinta dayake a shafe.

       Dariya tayi tana kallonsa "Taya zansani nikam?" Ta fad'a.

     "Kinjiki tun yaushe ma ni ai yanzu naji tunda ke baki sani ba". Ahmad ya fad'a.

      " Hmm!"Abinda kawai ta fad'a tare da girgiza kai tana murmushi.

       Da kansa yayi ta bata abincin kuma taci da yawa ba kamar jiya ba ,maganin ya 'ballan mata tasha.Zazza'bin ma ya sauka yanzu se kasala de gashi baccinma ba dika ya tafi ba.

               ***

     Se washegari ya koma aikinsa ,itama Reyhana ta samu sau'ki zazza'bin yawanci se da dare takeyi kad'an se bacci ba wuyar tayi bacci.

        A 'yan kwanakinnan haka take daga shingi'da se bacci ya kwasheta ,idan kuwa ya fita tana d'an yin abunda zatai se bacci wani sa'in ko shigowar Ahmad bata ji.

        Umma ma tazo ta duba ta har gida ,su Ikram ma sunzo  lokacin da bata jin dad'i.

         Yau tana zaune bayan tayi wanka ta shirya ,haka kawai taji tana son cin d'ata.

      Da farko tayi tunanin ko ta kira Ahmad idan ze dawo ya taho mata da ita,ganin bazata iya jiran har tsahon wannan lokacin ba ta yafa mayafi wasu 'yan chanjin dake wajenta ta d'auka ta le'ka 'kofar gida Allah yasa ta hangi wani yaron ma'kwafta nan tayi kiransa ta basa kud'in ya sayo mata.

      Bayan 'yan mintina ya dawo Reyhana ana rawar jiki aka amsa ta shige gida nan danan ta d'aureye ta fara gutsurar kayanta.

     Taci kusan uku

4 / 21