Author : Dijensy Category : Romantic Hausa Novels
ba ko na 'kuntata maki".
"Kuma wayata ba charge d'azu da kika kirani ,sanda naga missed call d'inki zanyi calling back wayar ta mutu please kiyi ha'kuri".
Shiru Reyhana tayi bata sake cewa komai ba amma ta tsagaita da kukan.
" Azizaty".Ya kira sunanta.
Reyhana bata amsa ba ,jin tayi shiru ya sake kira.
"Azizaty".
" Uhmm".Ta amsa a ciki.
"Kin ha'kura yanzu?" Ya tambayeta.
Kai ta kad'a ba tare da tace komai ba.
"Toh kinci abinci ?"
Nan ma kai ta kad'a,hannu yasa ya d'ago ta a hankali.Fuskarta tayi sha'be-sha'be da hawaye.
Idanta ta sauke 'kasa ,hannunsa yasa ya goge mata hawayen ya d'ago da ha'barta.
"Please look at me". Ya fad'a.
A hankali ta kallesa sannan ta sake sauke idanuwanta.
" Am sorry kinji".Ya sake fad'a.
A hankali ta kad'a kai alamar ta ha'kura.
"Ok smile".Ya fad'a.
D'an guntun murmushi ta saki ba tare da ta kallesa ba.
" Maman Baby saura na baby baki masa murmishi ba ko bakisan tana kallonki ba duk abinda kike"?"
Jin ya ambaci haka ta d'ago da sauri "Tana kallona kuma? Yana de kallo na".
" Auu! Naki choice d'in kenan ? Nide itace ba shi ba".Ahmad ya fad'a.
"Toh nikuma ba haka ba ". Cewar Reyhana.
"Ok then we shall see ,nan bada dad'ewa ba". Ahmad ya fad'a tare da jawota jikinsa yana shafa bayanta.
Nan take suka mance da fad'an kamar basu ne ba.
***
Mommy sautin muryarta ne yake tashi a part d'inta kana doso wajen zaka jiyo muryarta.
Waya take da Anty Asma'u kuma hira duk bata wuce ta Reyhana ba.
" Yanzu wayar tata ta siyar ta bashi kud'in kenan?" Cewar Anty Asma'u bayan da Mommy ta labarta mata komai.
"Eyyi taga zata iya se tai tayi". Mommy ta fad'a.
" Ni yarinyarnan ma gani nake ciki gareta ".Mommy ta fad'a.
" Ahaf ai na ayyana ,yanzu a wannan 'kuntacaccen gidan zata bari ta samu ciki".Cewar Anty Asma'u.
"Eyyi bata da tunani ai ,ni naga d'an 'beran da za'a haifa gafa yadda take d'ura abincin lami a cikinta ko kifi babu a abinci ya kike tunani yaro ze kasance". Mommy ta fad'a tana kumfar baki.
" Hmm Allah de ya sawwa'ke ,amma fa baza ki barta ta haihu a gidanta ba" Anty Asma'u ta fad'a.
"Ahh dama yaushe ai dolensa ta dawo gida idan ba so yake jininta ya 'kafe ba kuma". Cewar Mommy.
Sageer tun shigowarsa yake jin d'aga muryar Mommy ,kan wata kujerar d'akin ya zauna zaman jira ta gama wayar.
" Mommy ku baku da zance se maganar Reyhana koyaushe Reyhana kubarta mana"Sageer ya fad'a bayan data gama wayar.
"Dalla rufen baki, kai haryau yarone baza ka gane mey muke nufi ba daga kai har Reyhana d'in". Mommy ta fad'a.
" Kuka san gaba mey ze faru".Sageer ya fad'a.
"Koh? A hakan da certificate d'in diplomar zeyi arzi'ki?" Cewar Mommy.
"ARZI'KI RABO de". Ya fad'a.
" Kai kasani nide ina sa'kona dana aikeka idan bashi ya kawo ka ba ka iya bani space".Mommy ta fad'a.
"Gashi". Ya mi'ka mata kud'in daya ciro mata a ATM.
Yana bata ya fita ya koma sashensa...
AR²💖
Please Read,comment and vote. Luv u all😘😘
Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD @dijensy*
🅿 0⃣9⃣
Yau Reyhana tun 10:30am ta gama komai dan yau gida zata da wuri Ahmad dama yau alhamis yana azimi shiyasa ko girkin rana batayi ba wajen 11:37am ta gama shiryawa.
Sanda ta shiga gida Abba ze fita nan ya tsaya suka gaisa tukun ya fita.
Tana shiga ciki inno ta gani tana goge-gige a parlour.
"Ina kwana inno".Reyhana ta gaidata.
" Reyhana kece a gidan? Lafiya lau ".Ta amsa.
" Su Mommy suna d'aki ne?" Ta tambaya dan taga bakowa a parlourn.
"Eh Walida ce bata da lafiya suna d'akinta dan basu jima da dawowa daga aibiti ba". Inno ta fad'a.
" Tohh! Allah ya sawwa'ke bara na hau saman".Reyhana ta fad'a.
A kwance ta isketa a gado se fad'a ake da ita wajen shan magani.
Tana ganin Reyhana ta fara 'ko'karin tashi zaune.
"Yi zamanki keda bakida lafiya". Reyhana ta fad'a.
" Mommy ina kwana".Reyhana ta gaisheta bayan ta zauna a wata kujera dake d'akin.
"Lafiya ". Mommy ta amsa.
" Ya jikinnata ?"Reyhana ta tambaya.
"Da sau'ki,tashi tayi da zazza'bi seda aka kaita asibiti". Cewar Mommy.
Su Ikram da Sageer ma suka gaisa da ita.
Bassam kuwa yana makaranta." Walida kisha magani kinji koh bakya so ki warke?" Reyhana ta fad'a.
Kai ta girgiza alamar "A'a".
" Toh maza tashi kisha".Ta fad'a.
Da 'kyar aka samu tasha maganin sannan ta samu ta sake shan tea daga baya tayi bacci.Se lokacin ta barsu suka sarara dan Walida bade raki ba.
Sageer ya wuce d'akinsa haka Ikram ma.Reyhana kuma d'akin Mommy.
"Reyhana meyasa kike cutar rayuwarki?" Mommy ta fad'a .
"Yanzu har takai ga kin fara sayar da abubuwanki ,wannan shine rayuwar da kika za'bawa kanki?" Cewar Mommy ranta a 'bace.
"Mommy fa daman ta fara bani matsala wayar". Reyhana ta fad'a.
" Bawani nan 'karya kike,nasan mijinki kika bawa kud'in".Mommy ta fad'a.
Reyhana shiru tayi ta sunkuyar da kai dan ta rasa abin fad'a.
"Ke bazaki ta'ba gane mey nake nufi ba ,ki duba kiga tun ba aje ko ina ba kun fara shiga cikin wannan halin ina ga kun fara yara,Ahmad sam ba tsaran aurenki bane baki dace dashi ba baze iya ciyar dake ba a haka kuma kike tunanin kuyi 'ya'ya dashi".
Reyhana kwallar da take ma'kale take ta zubo kalaman Mommy suna tsorata ta.
" Mommy umma ce fa bata da lafiya shine na siyar dan akaita asibiti".Reyhana ta fad'a murya na rawa.
"Ummansa ce ba lafiya? Yanzu kinzamo kece mijin kenan". Cewar Mommy.
" Reyhana ina tausaya maki amma ke gani kike kamar na matsawa rayuwarki ki".
Sallamar Ikram ce tasa suka katse maganar da suke ,da sauri Reyhana ta goge hawayen idanuwanta.
Mommy tashi tayi ta bassu suna ta hirarsu.Daga bisani suka shiga kitchen Ikram da Reyhana suka soya wainar flour dama gashi Walida tana so.
Kasancewar Ahmad yana azumi yasa ta koma gida wajen 4pm saboda had'a masa abin shan ruwa.
Mommy da hankalinta ya kasa kwanciya da al'amarin Reyhana yasa Abba yana dawowa ta zauna dashi ta zayyane masa komai.
"Toh ke yanzu mey kike so nayi?" Abba ya tambaya.
"Haba Abban Reyhana taya zaka fad'i haka kai da kanka ya kamata ka nemo abun yi". Mommy ta fad'a.
" Nide na fad'a maki ba ruwana a cikin wannan zancen,ki bar yarinya kin'ki ke kullum complain tunda mike da ita bata ta'ba kawomin 'karar yarannan ba suna zaman lafiya kuma sena sa baki".Abba ya fad'a.
"Aikuwa ni ina da abinyi tunda kai baza kace komai akai ba". Mommy ta fad'a.
" Mey kike tunanin yi?" Abba ya tambaya yana jiran amsarta.
"Ya sawwa'ke mata ,bazan bari ina kallo 'yata ta zauna a 'kuntatacciyar rayuwa ba". Mommy ta fad'a.
" Ya sawwa'ke mata fa kika ce? Anya kuwa kina da tunani ?" Cewar Abba yana mamakin kalaman Mommy.
"Toh wani abune? Ai gaskiya na fad'a baze iya ri'ke mana 'ya ba dan haka seya rabu da ita bamu gaji da ita ba".
" Kinga kunnena baze iya d'aukan wannan abun ke iya fita ko kiyi shiru".Abba ya fad'a.
Mommy bata sake cewa komai ba ta mi'ke tai ficewarta.Abba bayanta yabi da kallo kawai ya girgiza kai.
***
Akwai lokacin da Mommy ana wani suna koda aka fad'a wa Reyhana ba ta samu zuwa ba saboda kud'in transport kuma bawai ta fad'a wa Ahmad ba yace baida kud'i,kawai ta san baida isassun kud'i shiyasa batai masa maganar sunan bama.Mommy kuwa tasha haushi nanma haka bata gaji ba seda ta fad'a wa Abba ita a lalle seya d'au action akai.
Tun Abba baya biye zancen har shima abun ya fara damunsa kuma bawai ya fara 'kin Ahmad bane kawai de 'yar tasa ya fara tausayawa amma kuma sam be nuna wa Mommy hakan ba balle Reyhana.
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa da dad'i ba dad'i, Reyhana cikinta ya cika wata 8,zama da 'kyar tashi da 'kyar.Yanzu ta dena cin d'ata, mitimis da albishir ta tusa a gaba.
Mommy kuwa tana kan bakatta na dawowar Reyhana gida,ita kuwa Reyhana ko Ahmad ma batayi wa maganar ba ta san baida ra'ayin mace ta koma gida wanka.
Reyhana tana d'aki tajiyo 'karar wayarta a sitting room, koda taje dubawa taga wanda ke kira taga Mommy ce.Se a karo na biyu ta d'aga kiran.
"Ina yini Mommy". Reyhana ta gaisheta.
" Lafiya lau,bakya kusa da wayar koh?"
"Eh". Reyhana ta amsa.
" Toh ya maganar komowarki ,ko har yanzu baki fad'a masa ba?" Mommy ta tambaya.
"Eh amma yau zan fad'a masa". Reyhana ta amsa.
" Toh kide fad'a masa dan ba ruwana kika haihu a gida dan kinsan ni bani da wacce zan kawo maki atoh".Mommy ta fad'a.
"InshAllah zan fad'a masa". Ta amsa.
Daga haka sukai sallama ,Reyhana tunanin yadda zata 'bullo masa da wannan maganar take.
***
Ahmad kuwa a gurin aiki Umma ta kirasa take fad'a masa ya biyo ta gidanta.
Dama lokacin tashinsa yayi dan haka ya biya gidanta.
Bayan sun gaisa take ce masa Mommy ta kirata d'azu.
" Mommy ce ta kiraki?"
"Ehyi ta fad'a min Reyhana gida zata koma". Umma ta fad'a.
" Gida kuma?" Ya tambaya cikeda mamaki.
"Ehyi a can zata haihu". Ta amsa sa.
" Toh ai ni bata fad'a min ba".Cewar Ahmad ransa a d'an 'bace.
"Toh gashi mahaifiyarta ta fad'a".
" Nifa bana son komawa gidannan fa".Ahmad ya fad'a.
"Toh ai na lokaci ne kuma bayan haihuwar fari ce". Umma ta fad'a.
" Sekace da yanzu fa an dena wannan".
"Toh sekayi ha'kuri da hakan".
" Sede bayan ta haihu".Ya fad'a.
"Toh meye banbancin du d'aya ne fa kwana nawane"
Ahmad badan yaso ba ya ha'kura, ko abincin Umman ma be ciba.
Reyhana a gida tana ta tunanin yadda zata fad'a ma, koda ya shigo gida bayan yaci abinci yayi maghrib suna zaune kawai tunani take.
Ana cikin haka taji yace "Meyasa baki fad'a min ba?"
"Mey?" Ta tambaya.
"Zaki koma gida". Ya amsata.
" Dama yau nake son fad'a maka".Ta fad'a.
"Amma waya fad'a ma?" Ta tambaya a ranta tana Allah yasa ba Mommy bace.
"Umma ce ta fad'a wa Mommy". Ya amsa ta.
" Azizaty haka mukai dake?" Ya tambaya.
"Yaya kaga idan na zauna a gida ba a da wacce zata kawon ta zauna shiyasa zan koma ". Ta fad'a.
" Ni kad'ai kike so ki barni?" Ya fad'a kamar d'an yaro.
"No am always with you forever and where ever you are". Ta fad'a tana murmushi.
" Dad'in baki koh? " Ya fad'a.
"No hakane ai". Reyhana ta fad'a.
" Ok, but zanyi missing d'inku keda baby ".
" Muma".Ta fad'a.
"Yawwa an samo mana sunan?"
"Eyi amma bazan fad'a ba that's surprise". Cewar Reyhana.
" Ko d'an hint?"Ya tambaya.
"Wayo when the time zan fad'a ma".
" Ok we are waiting ".Ahmad ya fad'a yana dariya.
" Yau ba tausa?"Ya tambaya.
"Anjima". Ta amsa.
" Ok Azizaty ".
****
Seda Reyhana ta 'kara kusan 2weeks sannan ta koma gida ,kayan baby da Ahmad ya sayawa baby ta tafi dasu ,su towel ne haka da saitin sauran kayan wanka na baby.Mommy a hakan ma seda ta kushe kayan Reyhana sede kawai ta kawar da kanta.
Yau kwananta uku da komowa Ahmad yazo sau biyu.Tunda ta dawo gida ba wani aiki take ba tana d'aki idan yara sunje makaranta inko suka dawo sesi zauna suyi ta hirarsu da yamma kuma Ikram ko Walida ta raka ta fita waje dan tattakawa.
Mommy kuwa yanzu dad'i take ji Reyhananta a kusa da ita yanzu 'yarta zata ci me kyau(Mommy ta fad'a not me wooo!)
8:12pm,suna zaune yaran harda Reyhana a parlour sun kunna TV suna kallon Bollywood".
" Yaya ni a chanja channel d'innan akai MBC 3" Walida ta fad'a.
"Baza a chanja ba!". Ikram ta fad'a a tsawace.
" Meyai zafi kiyi ha'kuri Ikram ki batta ta kalli cartoon ko d'aya ne".Reyhana ta fad'a.
"Nikuma fa na katse nawa kallon?" Ikram ta fad'a ranta a 'bace.
"Yaya ki rabu da walidannan idan baza ta kalla ba taje ta kwanta". Bassam ya fad'a dama shi kullum kishiyanta ne.
"Dukanku ha'kura za'kwi dan yanzu zan kai wrestling". Sageer ya fad'a.
" Chabb! Lalle kuwa ashe bame kalla".Ikram ta fad'a harda harara.
"Ke! dawa kike?" Sageer ya fad'a yana 'ko'karin mi'kewa.
"A'a Sageer kaifa yaya ne ka cigaba da chat d'inka de". Reyhana ta fad'a.
" Mey yake faruwa neh?" Abba ya tambaya yana 'karasowa inda suke.
"Abba sannu da zuwa". suka fad'a.
" Abba rashin kunya ya Ikram takewa yaya Sageer ".Walida ta fad'a tana kallon idan Ikram taga ya zatai.
" Abba 'karya take".Ikram ta fad'a.
"Toh ya isa". Abba ya fad'a.
Mommy dede lokacin itama se gata ta sakko.
" Abban Reyhana ka dawo kenan".Cewar Mommy.
"Shigowata kenan". Ya amsa.
Abba d'aki ya nufa bayan 'yan mintina daya sakko suka nufi dinning dukansu domin cin abincin dare.Gwanin sha'awa full house ,sunayi suna hira har suka kammala ,daga nan kuma aka zo aka zauna a parlour shan ice cream ana hira.Sun zirfafa suna hira wayar Reyhana tayi ringing Allah yasa tana kusa da ita da bazata jiyo ba.Koda ta duba taga Dear❤ zame jiki tayi tabar musu parlourn ta haye sama amsa wayar habibinta.
Mommy kuwa tana kallon sanda Reyhana ta tashi ,ta'be baki tayi ta cigaba da hirarta.
AR²💖
Hmm! Mommy mey kike nufi? 🙊
Please vote,comment and share,love u all😘
Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD @dijensy*
🅿 1⃣0⃣
"Azizaty kin manta dani". Ahmad ya fad'a.
" Ashe zan iya mantawa da kaina ,kana raina dear ".Reyhana ta fad'a cikin sanyayyar murya.
" Toh ya kike ya babynmu?" Ahmad ya tambaya.
"Lafiya but we miss you much".
" Nima Azizaty tun d'azu ku nake tunani".Ahmad ya fad'a.
"Kaci abinci?" Ta tambayeshi.
"Na kasa ci Azizaty,ba dad'i".
" Ayya! Ka daure kaci kaji".Reyhana ta fad'a.
"Toh zanci amma ba yawa".
" Yafi de ka'ki ci".
Sun d'au tsawon lokaci suna waya kafin daga bisani suyi sallama sannan tayi kwanciyarta dama da wuri take baccinta.
Washegari da asubah kiran Ahmad ne ya tasheta ,bayan sun gaisa ta tashi tayi sallah tayi azkar d'inta.
Da safe kafin ya fita seda ya sake kiranta a waya.
Kamar koyaushe Reyhana ta shiga kitchen ta had'a tea tasha da cake dan yunwa take tashi da ita.
Koda ta koma d'aki jin baccin ya'ki zuwa ta had'a ruwan wanka a kettle,'yan minute kad'an ta shiga tayi wankanta ta zira doguwar riga dan kusan duka rigunanta basa shigarta sede tayi ta fama da dogayen rigunan.
Jin zaman d'akin ya isheta ta fito parlour ta kunnaTV ta soma kallo.Se chan bayan wasu 'yan lokuta suka tashi Mommy ta sakko 'kasa inno kuma tana kitchen ta fara had'a musu abun breakfast.
"Mommy ina kwana". Reyhana ta gaisheta.
" Lafiya lao,ke kuma baki koma baccin bane ?" Mommy ta tambayeta.
"Eh". Ta amsa.
" Toh ki sha tea d'in?" Ta tamabaya.
"Eh nasha". Ta amsa.
" Yawwa ya jikin Walidan ? "Ta tambaya.
" Walida taji sau'ki d'azu ta farka tasha tea sannan aka bata magani".Mommy ta amsa.
"Bari na shiga kitchen na duba inno".Mommy ta fad'a.
" Toh".Reyhana ta amsa ta cigaba da kallonta.
Se around 9:30am suka hallara a dinning dukansu Ikram a haka ma bacci be isheta Reyhana ce ta tasota.
"Yarinya kwanan zaki dena baccin safe". Reyhana ta fad'a dan nan bada dad'ewa ba zata fara zuwa university tunda ta