Author : Dijensy Category : Romantic Hausa Novels
ba kamar Ikram take ba,taimakon rayuwarta zanyi ita bata san kanta ba ita so ya rufe mata ido bazan zuba ido ta sake samun cikin na biyu ba gara tun wuri na dakatar dama rabon 'yace ya had'asu".Mommy ta fad'a.
"Maryam kenan ,toh Allah ya saww'ake deh". Anty ta fad'a.
" Yanzu Toh yaushe zaki fad'a ma Reyhana d'in?" Ta tambaya.
"Nan bada jimawa ba". Mommy ta fad'a.
Daga nan suka tsindima wata hirar ta daban.
Reyhana kuwa a gida tana ta fama da Nasreen dan ta'ki komawa bacci gashi ta barta a d'aki ita d'ai tasa ihu Ikram bata dawo ba balle ta taya ta ,inno kuma ta fita.
Ahmad daga wajen aiki ya tashi da wuri,wajen 4pm yazo gidansu Reyhana. Har lokacin Mommy bata dawo ba ,kiranta yayi a waya ya fad'a mata yana haraba tace ya shigo.
A parlour ya zauna chan ba dad'ewa ta fito Nasreen a hannunta.
Murmushi ya sakar mata me 'kayatarwa itama ta mayar masa,be jira ta zauna ba ya mi'ke domin kar'bar Nasreen.
" Ummu Nasreen irin wannan kyau haka".Ahmad ya fad'a.
Kuma powder ne da lipstick kawai ko kwalli bata sa ba,tayi kyau sosai cikin green d'in atamfar.
"Babyna ta gane ni kinga tana mini murmushi". Ahmad ya fad'a yana 'ko'karin zama.
Itama Reyhana zama tayi a kujerar dayake three seater ce.
" Watoh har ta fara gane ka?"Cewar Reyhana.
"Ehmana baki gani ba taga mey kama da ita". Ya fad'a.
" Sonkai koh".Ta fad'a.
"Mommy bata nan?" Ya tamabaya.
"Ta fita d'azu". Ta amsa.
" Yau ke aka bari da babyn tamu,karfa kice zaki mata wanka karki sa mata ruwa a hanci".Ahmad ya fad'a.
"Aiko na iya". Reyhana ta fad'a.
" No sekun dawo zaki dinga yi mata".Ya fad'a.
"Kin fara had'a muku kayan ku de koh?"
"Wane kaya ana zaune lau,sekace gobe zamu komo". Reyhana ta fad'a.
" Lalle just kwanaki ne fah,gara ma ki fara shiri dan kun kusa komo wa keda baby Nasreen ".
Tashi tayi ta tafi kitchen ta had'o masa abunsha da snacks ta kawo masa.Hira sosai sukai tayi har Ikram ta dawo Nasreen tayi bacci ta kaita d'aki,se kusan maghrib ya tafi har lokacin Mommy bata dawo ba.
Se to 8pm tukun ,ba dad'ewa Abba ya dawo.Mommy se lokacin akai wa Nasreen wanka,Reyhana kuwa bayan tafiyar Ahmad.
Mommy maganar tana cinta amma ta kasa fad'a wa Abba,a kwana a tashi Reyhana sunyi kwana 37 Mommy bata yi wa Reyhana maganar komawa ba.
Shikuwa Ahmad kullum cikin lissafi dan yanzu a tunaninsa baza suyi 5days basu dawo ba,dan har siyayyar 'yan kayan stuffs yayi musu jiran dawowarsu kawai yake.
Mommy yau de ta d'au alwashin fad'a wa Abba duk abinda ke ranta,around 8:32pm bayan sun gama dinner ta shiga d'akinsa lokacin yana 'yan danne-danne a phone d'insa.
" Abban Reyhana ina so zami magana ne".Mommy ta fad'a tana tsaye.
"Toh shigo ina jinki". Ya fad'a tare da ajje wayar gefe.
Mommy waje ta samu ta zauna a kan gadon tana tunanin ta inda zata fara.
" Dama akan Reyhana ne,ina nufin komawarta".Mommy ta fad'a.
"Toh ina sauraro". Ya fad'a yana 'kara tattaro hankalinsa gareta.
" A gaskiya nifa bazan yadda yarinyar nan ta koma gidanta ba".Mommy ta fad'a.
Kuma yadda take maganar zaka gane da gaske take.Abba zama ya gyara yana kallon ikon Allah.
"Toh bazata koma ba a gidanki zata cigaba da zaman auren kokuwa mey kike nufi?" Abba ya tambaya.
"Ina nufin Ahmad ya sawwa'ke mata". Ta amsa ba tare da ta nuna alamar damuwa ba.
" What!" Abba yayi exclaiming cikeda nuna damuwa.
AR²💖
*Oh! ni Dijensy mey yake shirin faruwa neh??*
*Readers your comment is what will keep this story survive remember your vote,comment are needed.Love you all, sis feezoh😘*
Jasko💕
*ARZI'KI RABO*
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD @dijensy*
🅿 1⃣4⃣
Sis feezoh tnx for ur concern, Allah ya bar zumunci we are always together😘
Mommy da ganin yanayin reaction na Abba yasa ta sake zage dantse.
"Eh sakinta zeyi".Ta fad'a babu alamar damuwa tare da ita.
" Kina da hankali kuwa Maryam? Ina tunaninki? Ina iliminkii ? Kina abu kamar wata 'karamar yarinya wannan ai shirmene!"Abba ya 'kare maganar cikin d'aga murya dan ransa ya 'baci.
"Ba zancen rashin hankali,nide da raina bazan bari 'yata tashiga wani hali na rayuwa ba,wannan yaran baze iya ciyar da Reyhana ba balle bata sittira kana gani wani nauyin ya sake hawa kansa".
" Maryam arz'ikinnan kece mey bayarwa neh? Kada ki manta bada arzi'kina kika aureni ba".Abba ya fad'a.
"Da daban yanzu daban,shikenan kafiso kadinga ciyar da ita tana gidan auren nata ? Haka ake rayuwa?"
"Maryam bana son sakarci fah,ke yanzu ba abun kunya bane a gareki ace d'iyarki daga zuwa wanka gida aure ya mutu yaran da koh shekara biyu da aure basi ba".Cewar Abba.
" Du kai ka janyo mah yarinyarnan ta aureshi tun farko seda nace maka kada ayi ka'ki jina, yanzu kaga irin halin 'yarka data shiga kuma wai a haka kake so ta cigaba da rayuwa,kafiso sede kullum ka dinga yafita mata kud'i tana cida kanta da mijin koh? "
"Maryam ke meyasa bakya jin magana neh a rayuwarki?" Abba y fad'a tare da mi'kewa tsaye.
Itama Mommy tashi tayi daga zaunen."Kasan Allah bazan ziba ido Reyhana ta shiga cikin rayuwar 'kunci ba ,yarinyar da bata taso a wahala ba kawai rana d'aya ta shiga 'kuncin rayuwar da bata san ranar barinta ba".Mommy ta fad'a.
"Baza a raba masu aure ba na fad'a maki ,wannan haukar baza ayi dani ba". Abba ya fad'a.
" Shikenan idan kai bazaka d'au mataki ba ni zan d'auka".Mommy ta fad'a.
Ba tare da ta jira Abba ya sake magana ba ta fita daga d'akin fuuuu.Yana kiranta amma tayi banza dashi ta koma d'akinta.
Daga yara har Reyhana ba wanda yasan meyake faruwa sede sunji ba Mommy a parlor ba Abba dan ko alamar su babu ,dukansu kowa d'akinsa ya koma Reyhana itama haka.
Tunanin komawarta gidanta ta shiga yi ,sede kuma abin da yake bata mamaki shine haryanzu Mommy bata yi mata maganar hakan ba.
Tana cikin wannan batunne kiran Ahmad ya shigo.
"Ummu Nasreen". Ya kira sunanta.
Bayan sun gaisa yake tamabayarta ya batin dawowarsu.
" Azizaty ana ta shiri?"Ya tamabaya.
"Uhmm".Ta amsa.
" Kin jiki ,gara ma ki bud'e baki ki magana kin shagwa'be da zaman gida koh toh aiko ki shirya ina nan ina jiranku".Ahmad ya fad'a.
"Se mun 'kara sati biyu".Ta fad'a cikin zolaya.
" No shekara".Yayi gatse.
Haka suka sha hirarsu lokaci har yaja ta fara jin bacci dan haka sukai sallama ta kwanta.
***
Washegari da safe koda Reyhana ta tashi taga Mommy bata ma shigo ba,Nasreen ta lura taga itama ta tashi dan haka ta d'auketa.
Tana bata mama sega Walida ta shigo d'akin dama yau Saturday.
"Mommyn Nasreen ina kwana". Walida ta gaisheta.
" Au yau kuma sunan da aka samun kenan".Reyhana ta fad'a bayan ta amsa.
"Mommy bata fito ba?" Reyhana ta tamabaya.
"Eh nima ban ganta ba". Ta amsa tare da zama kusa da Reyhana tana shafa gashin Nasreen.
Abba around 8:30am ya sakko 'kasa, Walida ya tarar da Ikram a 'kasa yake tambayarsu Mommy suka ce bata sakko ba.
Abba kai kawai ya kad'a ya koma sama dan yasan dalilinta na 'kin fitowa.Koda yaje a bakin d'akinta ya tsaya yana knocking tare da kiran sunanta amma tayi burus.
" Maryam ki fito na fad'a maki".
"Na fito na muku mey?" Mommy ta fad'a.
"A'a kamarya ? Da haka kike yi ga yara nan suna jiranki a 'kasa,ki fito kiyi breakfast".Abba ya fad'a cikin sanyin murya.
Haka ya rabi da ita ya sakko daga shi se yaran sukai breakfast ,Reyhana ma se daga baya tayi nata breakfast d'in.
Abin ya fara damun yaran dan Mommy bata saba haka ba.Suna cikin wannan batun ta sakko.
" Mommy ina kwana ".A tare suka gaidata.
Sun lura mood d'in Mommy hakan yasa suka d'an yi shiru.
" Lafiya".Ta amsa muryarta a ciki-ciki.
Kitchen ta nufa ba tare da ta sake cewa komai ba.
Abba kuwa yana d'akinsa,Reyhana tana d'aki itama basu jima da yin waya da Ahmad ba.
Mommy a kitchen tayi breakfast d'inta ta shiga d'akin Reyhana.
"Mommy ina kwana". Ta gaidata
" Lafiya".Ta amsa.
"Reyhana".Mommy ta kira sunanta cikin wata murya lokacinda ta zauna.
"Na'am". Reyhana ta amsa gwiwarta ba 'kwari.
"Kinsan ni mahaifiyarki ce kuma bazan yi wani abu dan cutar dake ba koh?" Mommy ta tambayeta.
Kai kawai Reyhana ta kad'a alamar "eh" ba tare da tace komai ba.
"A gaskiya ni ban amince da komawarki gidan Ahmad ba,bazan amince ki cigaba da zama a irin wannan rayuwar ba". Mommy ta fad'a.
Wani irin fad'uwar gaba taji ,a take zuciyarta saurin bugunta ya 'karu.
"Reyhana a kullum ina fad'a maki ke ba tsarar Ahmad ba ce,ki duba kiga aikin dayake baze iya ri'keku ba kuma yanzu nauyi ya 'karu idan yau Abbanki ya baki kud'i gobe wa ze baki idan matsala ta faru? Wannan abubuwan nake guje maki shiyasa tun farko na'ki amincewa da aurenki dashi,dan haka tun ba'ai nisa ba gara a yanke ala'kar aurenku ,gatanan dama Allah yayi itace rabon auren". Mommy ta fad'a tare da kallon Nasreen.
Reyhana jinta take kamar wata kurma ,kwalla ta cika taf a idanuwanta a take ma'koshinta ya bushe.
" Mommy? " Reyhana ta fad'a lokaci guda kuma hawaye ya gangaro a idanuwanta.
"Reyhana nasan hakan baze zo maki da sau'ki ba amma ki sani dan farincikinki nake komeh da kika gani".
Bata sake wata maganar ba Abba ya shigo d'akin dan already ya jiyo su da Mommy.
Mommy tana ganin ya shigo ta tashi ta bar d'akin ,hakan yasa Reyhana ta gano sun sami sa'bani da Abba kuma tasan baze wuce akan maganar aurenta ba.
" Ta fad'a maki koh?" Abba ya tambaya.
Kuka Reyhana ta fashe dan bata da wani sauran dauriya a tare da ita.Bece sake cewa komai ba yabi bayan Mommy.
Ita kuwa Reyhana gefe guda ta ajje Nasreen ta shiga rera kuka,a lokacin kuma taji wayarta na ringing koda ta duba taga Dear❤
Seda ta katse ya sake kira tukun ta iya picking, d'an share hawayen tayi tare da sassaita muryarta tai magana.Duk da haka seda yaji yanayin muryar tata ya tamabayeta.
"My Amarya meya faru?"
AR²💖
Please share..
Jasko💕
🎍 *ARZI'KI RABO*🎍
*WRITTEN BY DIJENSY*
*WATTPAD @dijensy*
🅿 1⃣5⃣
"Yaya ba komai ,kawai de kaina ke ciwo". Tayi 'karya.
" Toh! Allah ya sawwa'ke kin sha paracetamol? " Ya tamabaya.
"A'a amma zansha". Ta fad'a.
" Toh ki samu ki sha,ya Nasreen?"
"Tayi bacci". Ta amsa.
" Toh ki shafan min kanta".Ahmad ya fad'a.
"Kema ki samu ki baccin kan ze dena,nima yanzu zan fita".
"Ok,toh seka dawo". Ta fad'a.
Daga haka sukai sallama ta ajje wayar wani sabon hawaye ya sake gangarowa a fuskarta.
Mommy kuwa kafin Abba ya 'karasa d'akinta ta rufo 'kofarta,tana ji yana kiran sunanta amma tayi burus.
Ba 'karamin 'baci ransa yayi ba haka ya koma wajen Reyhana ya tarar da ita tana kuka mey cin rai,rarrahinta yayi yana bata ha'kuri.
***
Sageer ya lura da irin change da aka samu kwana biyu a gidan ,Mommy,Abba,Reyhana ba kamar yadda ya saba ganinsu ba ,kawai de be tanbayi Reyhana bane,abinci ma Mommy ta dena ci tare dasu dinning haka Reyhana ma ko da daddare idan ya dawo d'akinsa yake shigewa dan yason ko meze ce wa Mommy ba sauraransa zatai ba.
Reyhana sun cikake 40 harda kwana biyu akai ,Ahmad har ya soma gajiya dan haka yau yazo gidansu Reyhana.
Sanda ya shiga ya tarar da Sageer dake parlour nan suka gaisa ya hau sama yake fad'a ma Reyhana.
Jiki a sanyaye ta tashi ko Nasreen bata d'auka ba dan bacci take.
Reyhana tana taka step dan ta sau'ka bata 'karasa zuwa parlour ba ta hangi Mommy a palourn.
Ba shiri ta tsaya cak,da alama Mommy bata dad'e da zuwa parlourn ba,lokaci guda bugun zuciyarta ya 'karu.
"Shikenan Mommy zata fad'a masa komai". Ta fad'a a ranta tana ja da baya,da sauri ta koma d'aki ta fad'a gado ta shiga aikin kuka.
A parlour kuwa Mommy bayan sun gama gaisawa da Ahmad ta soma gyaran murya.
" Uh..Ahmad nasan dole wannan maganar da zan fad'a maka zaka ji nauyinta,amma banyi haka dan na ba'kanta muku ba nayi haka ne dan nema muku sau'kin rayuwa".Mommy ta d'iga aya amma bawai ta gama ba.
Jin irin kalaman Mommy yasa Ahmad ya tsinci kansa a irin wani yanayi na daban.
"Ri'kon mace ba abune mey sau'ki ba,kuma musamman ga Reyhana da bata saba da rayuwa irin ta gidanka ba,yanzu kuma idan ka duba zaka ga nauyi ya sake 'karuwa fiye da da wanda ba abune mey sau'ki gareka ba,sana'arka ba mey 'karfi bace da zaka iya ri'ke su dan haka ina neman alafarma daka sawwa'ke wa 'yata Reyhana".
Ahmad maganar Mommy yadda ta doki kunnensa ze iya cewa be ta'ba shiga tashin hankali kamar na ranar ba,dan jiyake kamar mafarki.Reyhana matar tasa?Ummu Nasreen Azizatynsa?Tir'kashi!
" Mommy dan girman Allah ki taimaka mini ki dena fad'ar wannan maganar ".Ahmad ya fad'a kamar mey shirin yin kuka.
" Gaskiya ce dole na fad'a Ahmad,kuma babu uwa da zata so 'yarta ta shiga cikin wani yanayin wahala,inde har soyayyar da kake mata ta gaskiya ce toh baza ka bari ta sha wahala a rayuwarta ba".Mommy ta fad'a.
"Mommy kiyi ha'kuri amma rabuwa de Reyhana ba abu ne mey sau'ki ba". Ya fad'a already 'kwalla ta cika idanuwansa.
" Ai nasan da hakan shiyasa nace maka alfarma,kuma nima ba abune mey sau'ki ba na bari 'yata ta shiga wahala".Mommy ta fad'a a lokacin ta fara 'kosawa.
"Mommy ki duba ki tausaya wa rayuwata da halin da zamu shiga nida Reyhana na sani itama bazata so hakan ba". Ya fad'a muryarsa na rawa.
" Ahmad na gama maganar nan bazan chanja ra'ayina ba,kaje ka sake tunani".Mommy ta fad'a tare da barin parlorn.
Ahmad ai zama yayi dirshan hawaye na ziba a fuskarsa ya rasa inda ze saka kansa.Wayarsa ya lalubo a aljihu yai dialing number ta Reyhana.
Ya kirata yafi a 'kirga amma bata d'aga ba,koba a fad'a ba yasan tana cikin wani hali yanzune ya gano dalilin dayasa bata maganar komowarsu sede kullum shi yayi mata.
Mommy kuwa tana hayewa sama d'akinta ta shige ita kanta ta tausaya masu amma ba ta jin zata iya 'kyalesu haka.
Reyhana kuwa tana ganin wayarsa amma ta kasa picking dan tuni tasan aikin gama ya gama,batasan mey zata ce dashi ba.
Ya shafe yafi 30min kafin ya fita daga gidansu Reyhana jiyake kamar yaje d'akin da Reyhana take,haka da'kyar ya iya tafiya direct gidan Umma ya wuce.
Umma ta tsorata ganin yanayinsa ,kuka yasa mata a tsakar parlour kamar d'an yaro ,ta 'kosa taji abinda ya faru ita ta zaci ko wani abunne ya sami Reyhana ko Nasreen.
"Ahmad kukan ya isa nace, ka fad'a mini mey yake faruwa se kayita kuka". Umma ta fad'a.
" UMMA Reyhana,bazan iya rabuwa da ita ba".Ya fad'a cikin kuka.
"Reyhana? Wa yace zaka rabu da ita?" Ta tamabaya a kid'ime.
"Mommy ce Umma ,bazan iya ba Umma dan Allah kije ki bata ha'kuri". Ahmad ya fad'a.
Umma ita kanta batasan sanda hawaye ya zubo a fuskarta ba,take tausayin d'anta ya 'karu a zuciyarta.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'u". Abinda ta furta kenan.
" Ita Mommy da kanta tace ka rabu da 'yarta?" Ta tamabaya.
"Mommy wai na saki Reyhana taya zan iya rabuwa dasu Umma ?"
Umma dafe kanta tayi ta rasa mey yake mata dad'i.An d'an tsahon lokaci a haka ,Ahmad ya bar sheshe'kar kukan sede hawaye gashi idanuwansa yayi ja jijiyoyinsa ma sun tashi fuskarsa tayi jazir.
"Kayi ha'kuri in Allah ya yarda baza ka rabu da ita ba ,addu'a zakai". Umma ta fad'a.
Duba da lokacin yasa bata tafi gidan ba ,8pm tayi.