ARZIKI RABO Complete Hausa Novels by Dijensy.txt

Author :  Dijensy Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 21

18K to 21K   out of 61.6K words

samu admission.

     " Abinda nake fad'a mata kenan ai".Cewar Abba.

    "Gara ma yarinya ki soma 'koluwa kyaji yadda nake ji". Sageer ya fad'a.

     Dariya sukai ,ita kuwa harara ta watsa masa.

    " Toh kai ai dole kasha wuya tunda kake namiji ita ai mace koh".Mommy ta fad'a dan ta kare ta.

      "Atoh kuma dole a kaini school". Ikram ta fad'a tana masa gwalo.

     Shikuwa sageer baki ya ta'be ya cigaba da cin abinci,Walida kuwa ana d'aki ana bacci.

         ***

Da asr sega su Anty Asma'u da sauran sisters na Mommy ,Reyhana tana parlour tajiyo muryarsu kuma dama taji inno tana musu sannu da zuwa a waje.
 
     Da sauri Reyhana ta bar parlourn wai kunya take ji kar su ganta.

      Aikam basu dad'e da shigowar ba suka tambayeta.

     " Ai tana jin muryarku ta ruga d'aki wai kunyar ku ganta take".Mommy ta fad'a.

     Reyhana da take d'aki ta kasa kunne ta jiyo Mommy ta fad'i haka ji tayi dama tuntuni ta fita kafin ta fallasa ta.

     Gabad'ayansu dariya suka sa, Anty ummi (autar su Mommy) tace "Aiko ki dena kika sani ko mu zami kar'bi haihuwar".

     Nan ma dariyar sukai mata ,Reyhana jitake kamar ta nuste.

     Seda ta gama 'bata lokaci ta shiga d'akin Walida da tun d'azu ta tashi amma bata sakko 'kasa ba.Lalla'bata tayi suka fito tare banda hijab d'inda ta zinbila tasa ta a gaba wai ta kare cikin.

       " Ina yini ta gaidasu".Tana daga gefe-gefe se wani raku'bewa take.

     "Lafiya lao". Suka amsa.

     " Maman boy ce ko maman girl?"Anty ummi ta fad'a.

     Shiru tayi bata ce komai ba,sede idan kai magana ta amsa da eh ko aa,daga baya ma sulalewa tayi ta koma d'aki.

       Wayarta ta d'auka ta kira Ahmad suka sha hirarsu ba jimawa sega kiran umma itama ta kira taji ya take.

       Seda za su tafi tukun ta koma sukai sallama,itama ba jimawa suka itada Ikram tattaki.

                ***

    Idan kuwa su Mommy duka zasi je unguwa ita kad'ai suke bari dukda de ma yanzu Mommy ta rage fita d'in saboda tsaro...

      Ahmad a week d'innan ma ya sake zuwa amma baya dad'ewa idan yazo dan yawanci bayan maghrib yake zuwa.

       A kwana a tashi Reyhana cikinta ya shiga 9month,Abba ya 'kara mata wasu siya-siyen akan na Ahmad haihuwa yanzu ake jira yau ko gobe.

       Ahmad daga wajen aiki gidan Umma ya wuce koda suka gaisa ya fita majalissarsu ,Sadiq(kusan shine babban abokinsa ,beyi aure ba) se tsokanarsa yake wai ya zama gauro.

       "Aiko 'karyarka ka kirani da gauro ko ba komai nasan ina da mata kaikuwa fa babu baka ma tunanin yin auren". Ahmad ya fad'a.

      " Zaka sha mamaki lokaci guda sede ka ganni nazo gidanka da matata".Sadiq ya fad'a.

       "Haka de kace dan banga alama ba".

      " Ka zuba ido kawai".Cewar Sadiq.

      Suna cikin hira sega kiran Reyhana, ganin haka Ahmad ya matsa daga gun.

       "Maman biyu". Ya kirata.

       " Niba maman biyu bace".Reyhana ta fad'a.

       "Au bakyaso?"

       "Chabb! Kana so nasha wuya kenan".Ta fad'a.

       " A'a ai kullum ina yi miki addu'a".

      "D'ayan de a yanzu is enough". Ta fad'a.
   
       " Azizaty kidena tsoro fah,inshaAllah komai zezo da sau'ki".

        "Ameen". Ta amsa.

     Hira kad'an suka ta'ba sannan sukai sallama.

       Walida ta samu sau'ki har ta koma makaranta,Ikram ma satinta biyu da fara zuwa school amma har an fara rigima da Sageer wai shi tana makarar dashi a tafiya kenan,a dawowa kuwa wataran har tahowarsa yake ya barta sede ta hau d'an sahu.

       Yau wajen7:43am ita Ikram tana da lecture na safe shikuma bashida ,da'kyar seda Mommy ta taso shi ya fito ko wanka beba kayan jikinsa ma wandan kawai ya sauya rigar kuwa T shirt d'in jiyace.

      A cukule ya fito fuskarsa ba annuri ,Ikram kuwa tun-tuni ta gama shiryawa shi take jira,ada taso yi masa tsiwa amma ganin yanayin annurinsa tayi shiru.

     Bayansa tabi tana masa gwalo har seda suka shiga mota ta nutsu.

      Koda suka hau titi Sageer ya fara wani tu'kin wula'kanci ,motar kamar bata tafiya se horn ake musu kowace mota sede tayi overtaken. Ikram kamar ta rusa ihu.

     " Wai matsala ta samu ne motar?" Ta tambaya.

      "Bansaniba kuma yarinya zaki dakinsani". Ya fad'a tare da makirin murmushi.

      Kafin tayi magana taji ya zugi motar kamar wani mey gudun race.

        " Wayyo dan Allah ka bari rannan d'aya garemu".Ikram ta fad'a a rikice.

       Kamar ma zigashi tayi  haka ya sake fyallarsu kafin a shiga school fuskarta ta cika da hawaye.

       "Gobe ki sake taso ni, kuma ki fad'a wa Abba kiga". Ya fad'a lokacin da yayi parking a cikin school.

      Abinda ya guda shi ya faru,'yan click d'insu ya gani sun nufo inda yake,gashi Ikram bata fita ba dole suka taddashi.

      Yana zuge glass d'in suka fara." Wanka(sunan da ake kiransa dashi) yane da matsalane muka ganka haka".

     Se yanzu ya sake kallon rigarsa da yayi bacci da ita,haushi ya kamasa.Sageer akwai son gayu,haka yasa aka sa masa wanka.

       "Nayi dropping yarinyarnan ne se anjima zan shigo lecture". Ya fad'a.

       Fitowa tayi ta wuce ko kallan inda suke batai ba.

      " A haba kazo mu zagaya makarantar mana".D'aya daga cikinsu ya fad'a.

      "No se anjima". Ya fad'a .

     Ba yadda basi dashi ba ya tsaya amma ya'ki ,shikuwa baya so 'yan mata su ganshi a haka su raina sa.

           ***

   Wajajen 5:27pm Reyhana suka dawo daga waje ita da Walida.

       Koda suka dawo d'aki ta shige tayi zamanta dan bata jin normal cikinta se hautsinawa yake kad'an-kad'an tana jin suka.

      Shiru tayi bata tafiya wa Mommy ba har aka bayan sallar maghrib ,koda aka zubo abinci ma kad'an taci.

     Suna parlour dukansu banda ita da tana d'aki tsoro ya kamata kuma ta'ki fad'a wa Mommy, kuma ita Mommy tayi zatan ko waya take shiyasa bata nemeta ba.

      Ahmad kuwa around 6 ya koma gida koda jona phone d'insa a charge se ta 'ki hawa,da alama ko charging point ne.

        Hakannan ya fita masjid amma yana ta tunanin Reyhana dan yau tun safe basi sake waya ba wayarsa ta mutu.

      Reyhana kam har da Mommy ta shigo d'akinta data tambayeta lafiya bata sakko 'kasa ba tace ba komai.

      Mommy ganin haka tai wucewarta d'aki,kowa ya koma d'akinsa.10:24pm kuma tana trying number na Ahmad a kashe,abi gaba yake 'karayi ciwo se 'karuwa yake.

      Tun tana daurewa ganin yin hakan ba mafita bane ta d'auki wayarta ta kira Mommy.

      Seda ta kira kusan 3× Mommy ta farka ganin Reyhana yasa da sauri ta mi'ke.

     D'akinta ta shiga ta ganta se mur'kususu take.

       "Reyhana jikinne? "

         "Cikina washh! Mommy". Abinda take fad'a kenan.

       Agogon d'akin ta kalla taga 12:05am." Tun d'azu Reyhana na tambayeki kika ce ba komai, bari na fad'a wa Abbanki".Mommy ta fad'a tare da fita.

      Mommy ce ta taimaka mata suka sakko ,Abba ya fito da mota aka sata a ciki Mommy ta d'akko kayan da za'a bu'kata.

      Inno Mommy ta tasa tace ta lura da yaran ,su Ikram baccinsu ma suke.

        Suna isa nurses suka shiga da ita d'akin haihuwa koda suka dubata suka ce da saura,amma de zasu iya zama  a asibitin.

       Wayar Reyhana Mommy ta d'auka ta lalubo number na Ahmad. Koda ta kira aka she taji tsaki tayi,instead ta kira na umma ta'ki.

      "Ya kin kira Ahmad d'in?" Abba ya tambaya.

    "Gashi na kira switched off". Mommy ta fad'a ranta a 'bace.

        Reyhana tana ciki se mur'kususu." Ku kirawon Mommy ". Ta fad'a ma nurses d'in.

       " Hajiya kizo yarinyarki tana kiranki". D'ayan nurse ta fad'a wa Mommy.

      Mommy a tsorace ta shiga ciki dan tausayin 'yartata ya kamata.

      "Sannu kinji". Ta fad'a.

      Kai kawai take kad'awa bakinta ya bushe.

      Idan ta fara salati seta koma addu'a kafin ta gama seta kamo wata, Mommy ma addu'ar take taya tayi Abba ma yana daga waje yana yi.

       " Mommy kin sake kiransa?" Ta tambaya murya na rawa
  
     "Na kira a kashe wayar". Ta amsata.

    Kai kawai ta kad'a tana tapping cinya dan azaba.

      " Wayyo Allah Mommy !" Ta kurma ihu har Abba seda ya jiyo.

       "Sannu Reyhana". Abinda Mommy take fad'a kenan.

         (Allah sarki mata😭)

      Daga baya nurses d'in suka fita guda d'aya ce ta tsaya akan Reyhana.

      An d'au  tsahon lokuta ana abu d'aya ,daga baya ya lafa tana maida numfashi hannunta ri'keda Mommy.

      Reyhana har gari ya waye tana na'kuda ta fita daga hayyacinta.

        Yanzu ihun ma ta bari se addu'oi iri-iri ,Mommy da'kyar ta iya barinta tayi sallah ta fito wajen Abba suka gaisa.

          Su Ikram da asubah Inno take fad'a musu,nan da nan jikinsu yayi sanyi ko baccin sun kasa komawa dama lecture d'aya take dashi aiko ta fasa zuwa.

      Koda suka kira Mommy take fad'a musu bata haihu ba.

     Mommy bata dad'e da ajje wayar ba Reyhana ta 'kwala mata kira,da sauri ta koma d'akin.

          Na'kuda ce ta dawo fiya da baya ,gam ta ri'ke Mommy suna haka nurse d'in suka shigo,Mommy jikinta sake sanyi yayi ganin yadda Reyhana tayi firkai firkai ,Mommy bata doguwar na'kuda shiyasa ta tsorata.

       Mommy fita tayi daga d'akin tabar nurses d'in akan Reyhana.

         Mommy ta kasa zama Abba ma yana tsaye."Addu'a kawai zami mata Mommyn Walida ". Abba ya fad'a.

         Lokaci guda suka jiyo ta kwalla 'kara daga bisani tayi shiru sega kukan baby daya biyo baya.

       " Kaji kamar kukan baby nake ji". Mommy ta fad'a tana sake kasa kunne.

      "Eyyi nima de.." Be 'kare ba nurse ta fito.

       "Hajiya congratulation ta haihu yarinyarki..."

    
AR²💖
    
   Please share ,comment and vote. Love u all😘

Jasko💕   



🎍 *ARZI'KI RABO*🎍


*WRITTEN BY DIJENSY*

*WATTPAD @dijensy*

🅿 1⃣1⃣

      *Dayawa suna cewa Ahmad abun yayi masa yawa. I want to remind you this is just the beginning,kude ku cigaba da gashi🔥*

   Mommy da Abba a tare suka furta"Alhamdulillah".

       Bayan an gyaggyara maman baby da babyn kanta su Mommy suka shiga.Su kansu nurses admiring kyan babyn suke, Reyhana kuwa kallonsu kawai take a zuciyarta tana godewa Allah.

     "Mey aka samu?" Mommy ta tambaya.

     "An haifi mace". Suka amsata.

     " Toh mashaAllah ,Reyhana sannu ko".Abba ya fad'a yana kallonta.

     D'an wahalallan murmushi ta saki ta maida kallonta wajen babyn.

     "Sannu koh". Mommy ma ta fad'a".

      Babyn tana hannun Abba Mommy tana daga gefe itama hannunta nakan towel d'in da aka nad'e 'yar.

         " MashaAllah".Mommy ta fad'a.

        Mommy  wayarta ta d'auka ta kira su Ikram take fad'a musu,murna suka shiga yi.

       Bayan ta katse kiran ta kuma kiran Ahmad amma shiru kake ji.Mommy kuwa a ranta tace bazata sake kira ba.

      "Kin sake kiran Ahmad d'in ne?" Abba ya tambaya.

      Kai kawai Mommy ta kad'a fuskarta ta nuna alamar rashin jin dad'i.

      Reyhana tana kallonsu kanta kawai ta kawar ita kanta Ahmad ya bata haushi.

      "Taya za'ai ace ta haihu uban yarinyar ma baya gun? Kuma why not be nemesu ba tun jiya gashi har yanzu" Ta fad'a a ranta.

      Anty Asma'u ma an sanar mata da sauran sisters.

             ***

Shikuwa Ahmad koda gari ya waye da wuri ya shirya ya fita wajen aiki,sunyi da ogansa yau zasu je kasuwa dan haka suka tafi.Amma Reyhana tana ransa dan so yake idan sun dawo ya biya gidan Umma yai waya da ita kafin a gyara wayarsa.

       Wajen 11:00am aka sallamesu daga asibiti,kafin su koma gida dama inno ta d'orawa mey jego ruwa.

       Suna isa Walida ce the first d'in kallon baby har wani rawar jiki take a d'ora mata ita a cinya.

       "Walida baza ki iya ri'keta ba". Abba ya fad'a.

       " A'a zan iya ".

       D'an d'osana mata ita akai kafin Ikram da Sageer su kar'beta suma.

      " Wow! Mommy kalli hancinta da lips d'inta".Ikram ta fad'a.

       "Dani take kama". Cewar Bassam.

      Daga Mommy har Abba seda suka dara,banda Reyhana da tunaninta baya gun ,rashin zuwan Ahmad shi ya tsaya mata a rai.

      " Tabb! Ka cuceta amma ka kalli kanka  ka kalli yarinya  kace kuna kama hhh kade duba(😀 nima nace..).

      Haka suka cigaba da kalleta suna yaba kyanta da farinta (Nide dana kalleta naga copy d'in Ahmad😛).

        Gashinta ma irin nasa ne,kamanninsa sun fito a fuskarta sosai.

         Ruwan wanka Inno ta kai mata toilet,harda hawaye ita wai yayi zafi banda Mommy ta sata a gaba ba da seta surka.

          A cikin atamfofinta ta samu doguwar riga mara nauyi tasa,tea mey kauri Mommy ta had'a mata tasha,se farfesun kaza da inno ta dafo mata taci kad'an.

          Kwanciyarta tayi dan bacci ne a idonta ,babynma bacci take dan haka aka rufo musu d'akin suka fito parlour.

         Ahmad basu suka dawo daga kasuwa ba se 1:20pm dan sunsha yawo a kasuwar shi kanshi ya 'kosa ya komo.Koda suka dawo wajen aikin nasu yana tunanin ko ogan nasu ze barshi ya tafi amma seya bar masa wajen shi ya tafi gida Ahmad kuma ya tsaya akan sauran yaran.Duk haushi ya isheshi ,gashi sam idea d'in ya ari waya be zo masa ba.

       Anty Asma'u wajen 4pm suka zo da sauran sisters, lokacin Reyhana ta tashi daga bacci babynma haka.
  
       "Me jego da babynta mashaAllah Allah ya raya".Suka fad'a.

         Faten dankali Mommy tasa inno ta dafo mata da'kyar taci rabi hakan ma dan su Anty sunsa baki.

        Baby ta fara kukan yunwa gashi mama be zo ba.Reyhana dama ko gwada bata batayi ba ,se dabino ta tauna ta samata a baki ta lasa.

       Da'kyar tayi shiru ta koma bacci.

        Anty Asma'u dasu ka d'an ke'be take tanbayarta Ahmad." Kinsan kuwa besan ta haihu bama?" Cewar Mommy.

     "Kamarya? Baku kirashi bane?" Anty ta tambaya.

     "An kira kusan sau nawa amma a kashe ". Ta amsa.

     " Shine kuma be kira ba har yanzu".

      "Ai yanzu ta fara gani kinga abinda nake fad'a tun ba aje ko ina ba ya fara wula'kantata,ace tun jiya bazaka nemi matarka ba kaji yaya take ciki". Mommy ta fad'a.

     Kai kawai Anty ta kad'a" Aiko shima se an gwanya mashi rabi da d'an banza ai ze nemeta ko ba dad'e ko ba jima lokacin za'a nuna masa kuskuransa".

      "Abbanta ma ai bece komai ba yasan yaran be kyauta ba itama Reyhana haka zata fara gane me nake nufi". Mommy ta fad'a.

    Parlour suka koma suka cigaba da harkarsu,ita kuma Reyhana lokacin ta samu damar kiran friends nata.

      Ahmad se 6pm ya tashi daga gun aiki,gidan umma ya wuce direct kan ya 'karasa maghrib tayi.Suna gaisawa ya tafi masjid se bayan ya dawo ya d'auki wayarta yasa credit tukun yayi dialing numbern Reyhana.

       Number busy yaji, har kusan sau uku number busy.Reyhana lokacin tana waya da sauran family and friends tana sanar musu.

     " Meya sami wayar taka?" Umma ta tambaya.

     "Wajen charging tana ya samu matsala".Ya amsa.

     " Toh bakuyi waya dasu ba kenan?" Umma ta fad'a.

     "Tun jiya fa yau kuma aiki ya mini yawa shiyasa ban biyo nan d'in da wuri ba". Ya fad'a.

      " Yanzu bata d'aga wayar ba ne?"

      "A'a a busy". Ya amsa.

       " Sede ko anjima". Ta fad'a.

       "Eh". Ya amsa.

     Reyhana kuwa koda ta ajje wayar Inno ta kai mata ruwa toilet.Yanzu ma tana kwazazo wai ruwan zafi sukai ta drama a toilet.

       Mommy ta rigata fitowa daga toilet d'in tana kallo wayarta tana haske ana kira ,koda ta duba taga umma.

     Wani murmushin mugunta tayi ta d'auka wayar seda taga kiran ya katse tasa  a black list.

      Ya kirata ba adadi waya  busy har ya damu sosai.Hakannan ya ha'kura ya koma gida yana ta shawarar ko yaje gidan su se kuma ya fasa yace gobe.

         Reyhana tana expecting call nashi amma shiru taga gashi Mommy ta goge kiran umma saboda haka bata gani ba.

         Da daddare Abba ya sake shigowa ya dubasu ita da baby.

                  ***
     Cikin dare baby bata barsu sunyi barci ba tayi ta kuka Reyhana kuwa ta'ki bata mama wai ba komai a ciki.

       Washegari da safe 'yar baby tayi ta bacci abinta jiya bata barsu ba, Reyhana tayi ba itama bacci tayi tayi.

     " Reyhana tashi zaki ga ruwan wanka".Mommy ta fad'a.

     Reyhana a cikin bacci taji muryar Mommy, da'kyar ta tashi.

      "Ance ki bata mama kin'ki ba dole ta hanaki barci ba ,bari kici abinci sekin bata dolenki so kike ki barta da

7 / 21