IBTIHAL HAUSA NOVELS PDF COMPLETE BY MISS HAJO.docx

Author :  Miss Hajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 13

27K to 30K   out of 36.4K words

masa akan haka ya na matuƙar ƙaunar ƴan uwansa kuma kullum maganarsa suyi musu biyayya tamkar yanda zasuyi mashi ko ma fiye da haka ya fice aunty Aisha ta ja Dogon Tsaki kafin ta ɗauki Afren da ke kuka ta kalli Safa ta ce”saki biyeta ku dinga kukan marar amfani”

Ta fice da Afren da ke kuka”

Lena ta bita da kallon birgewa don Wlh abunda tayi ya matuƙar burgeta saboda ita kanta ji tayi kamar ta shaƙosa ta wanka masa mari don Haushi,

Daƙyal Safa ta lallasheta suka bar kukan Ibtihal na hawaye ta ce “me ya sa Na rayu Safa wlh nafi buƙatar mutuwa da rayuwarnan”

Dasauri Safa ta rufe mata baki ta ce” ina imaninki wai ya tafi ibtihal Meyasa kike faɗar irin haka wasu sun shiga fiye da halin da kika shiga a rayuwa kuma sunyi haƙuri sun cinye A ƙarshe sunyi nasara meyasa ke bazakiyi haƙuri ba ki cinye jarabawarki Allah ba ya jarbtar bawa da abunda bazai iya ba kisa a ranki ko wanda ya fi wannan zaki iya sai mumunin ƙwarai Allah ke jarabta Alllah shi ha haliccemu kuma Yafi kowa sonmu da ƙaunarmu dukkan abunda ya mana me kyau ne ki sama ranki ƙwarin gwuiwar tunkarar kowata irin matsla”

Ibtihal ta ce”Amma Safa nawa sunyi tsauri “Ta ce “mata shittt kafin ta goge mata hawaaye ta na miƙar da ita ta ce”bana son ki ƙara cewa komai don Allah kin gama sallar”

Ta gyaɗa mata Kai”

Ta ce “To za ki iya tashi ko na taimaka maki”

Cikin siririyar muryarta mai matuƙar daɗin saurara ta ce”zan iya”Ta miƙe da kanta ta nufi gadon sai lokacin ta kalli Lena da ke kan chairs ɗin ƴan dubiya saikuma ta kalli safa ganin baƙuwar Fuska Safa na zama gefen Lena ta kalli Ibtihal ta ce”she’s my best Friend Her name is Lena jiya ma ta zo duba ki”

Ibtihal ta sakar mata sanyayyen murmushi idanunta kumbure sakamakon kukan da ta sha ta ce “Sannu Nagode”

Itama Lena na sakar mata murmushi ta ce”Ya Ƙarfin Jiki”

Ta ce “Alhmdulilla”

Ta ce”Allah ya Ƙara sauƙi “Ibtihal ta ce “Ameen Thanks you”

Lena ta Aje mata Ledar da tayi mata shopping lafin ta kalli Safa ta ce “Besty zan wuce na ga ummy na yimun kira kinsan daga school muka nufo nan shysa zataga na daɗe Allah sauwaƙe”

Safa ta ce “To muje na rakaki Ibtihal ta ce “Nagode”kafin ta kwanta tare da lumshe ido”

Safa ta ce “sis zan rakata na dawo”

Ta gyaɗa mata kai idanunta lumshe”

Ko da suka Fito sallama tayi da su mom bataga Afren ba kamar wani wajen sukayi,

Sukayi sallama Suka fice da safa domin ta rakata Motar ta Da damuwa a fuskar Lena ta ce “Wlh Besty Haka kawai nake jin ƙaunar Cousin ɗin nan taki a raina Please wai me ya sanyata a halin nan da take ciki Na ga dai ta na da full gata sannan ga ta kyakyawa to me zai haifar mata da ciwon zuciya”

Safa ta ce”Hmmm bazaki gane ba Besty Ta shiga Jarabawar da tabbas ko nice zuciyata za ta iya bugawa tuntuni Da zan baki Tarihin Rayuwar Ibtihal da irin gatan da soyayyar da ta samu daga ɓangarori biyu na iyayenta Uwa da uba Da zaki sha mamakin me ma zai sanya ta a damuwa sam a da rayuwarta bata san ma meye damuwa ba komai take so shi iyayenta ke so ƴar gata ce ta ƙarshe saidai kash lokaci guda ƙaddara ta ruguza mata wani ɓangare na wannan Gata kuma duk a kan Tuggun Makirci Jinsi biyu Domin baza’akira sa da tuggun Namiji ba saidai a kirashi Da tuggun Mace da Namiji idan zan baki labarinta za mu iya kwana ba mu Ƙarasa ba cike yake da sarƙaƙiya mafi ƙarfin Abun kuma a kirasa da zazzafar yaudara da Cin Amana “

Lena ta ce “Please zan zo ki bani Labarin domin har naji na kwaɗaitu da son sanin abunda ya faru da ita”

Safa ta ce “Zan baki labarin Duka Rayuwar *IBTIHAL* amma ba yanzu ba sai mun samu free Time “

Ta ce “Gobe ya yi ?

Safa ta ce”A a Gaskiya Mu bari sai zuwa Jibi a school kinga ranar ne muke da lecturea ɗaya ta one hour kinga zamu fi samun isashen Time”

lena ta ce “to Allah ya kaimu jibin karkiga yanda na ƙagara jibin ta yi”

Safa ta ce “Uhmm Aku ta ji Labari “

Ta yi dariya ta ce”Eh naji kima kirani da abunda ya fi aku “

Sukayi dariya ta rakata har mota saida har ta tada motar kafin ta juya da niyyar komawa cikin Asibitin ta ga Motar Marwan ta yi parking sun buɗe Sajida na shirin fitowa ya dakatar da ita ta hanyar riƙe mata hannu ta hararesa ya yi murmushi Safa ta Nufi motar cike da tsokana ta ce “Mudai gaskiya a maza azo ayi auren nan Tunda na ga duk kun ƙosa baƙincikin Dinner da zamu sha Kawai na kula ake mana”

Marwan ya ce “me kike ci nabaka na zuba Autar Fam Ai bazata bar Ƙasar nan ba saida igiya ukku na masu nauyi a kanta ta ƙarasa karatun da Aure na”

Ta na narke masa kamar zatasa kuka ta ce “Haba Babe Duka 3Months fa ya rage please karkamun haka”

Ya ce”Ai bazaiyu ba gaskiya haƙurina ya na gab da ƙarewa ko so kike nayi abun kunya tun kafin a kawomunke Baki tausayamun ne Babe”

Da sauri Sajida ta kama Hannu Safa har haɗawa take da gudu wajen barin wajen safa ta tuntsure da Dariya Hada riƙe ciki ta ce “Ah ina Bayan Yayanmu kar mu samu Ɗan daga Jinya Ah to na ga Liƙe-liƙen nan naku yayi yawa”

Sajida Ta kai mata mintsini ta ce “Shegiya Ƴar Iska”

Ta ce “Ah ga dai Babban Ɗan iska Mijinki “

Ta kai mata Dundu a baya ta ruga ta na dariya Sajida ta yi ƙwafa ta ce “da mana ki tsaya ƴar ƙaryar rashin kunya”

Aunty salma ta kallesu yanda suka shigo ta ce”Ku fa kamar an jefo ku haka me ya faru”

Safa ta ce”Mom daga fa yaya Marwan ne ya ce “na faɗa muku shi dai….Dasauri sajida ta rugo tare da rufe mata baki Har Hawaye ta ke ta ce “Haba sis Daman har yanzu baki da wayau don Allah bar maganar”

Safa ta ce”To meyasa kika dakeni”

Ta ce”wasa ne kinga muje ciki akwai labari”Aunty Aisha ta ce “Allah shiryeku iyayen shiririta girma kuke ba nutsuwa “

Mom ta ce “ni na saki baki zan sha Labari tayi mana buƙulu Shalelena Autata Ai zamusa Labulai “

Ta faɗa ta na kallon safa Sajida ta ce “Haba Aunty ni da ke fa Ba ma Haka”

Ta na harararta ta ce “yau zamu fara”

Safa ta ce “karkiji komai Aunty komai sai na baki Labari”

Sajida ta harareta ta na jan hannunta suka nufi Ɗakin Ibtihal da lokacin ta ke zaune Suna Game da Afren a saman Gado sai murmushi ta ke ganin yanda Afren ɗin ke mata dariya idan ta wuce ta,

Ibtihal na kallon Sajida ta harareta ta ce “daga minti biyar yanzu zan dawo Shine har 5hours”

Safa na zaro ido ta ce”Kaiii 5hours fa tab aiko ta na chan ta na Soyewa da yaya Marwan ba ma sa asibitin yanzunnan ya maido ta”

Sajida ta ce “na shiga ukku da tonon asiri yau wai meyasa Safa ke baki da sirri sam to uwarme kike tunanin munyi da ya Ɗaukeni Yawo ne fa kawai ya kakkaini na faɗa masa Nayi missing Abuja “

Safa na dariya ta ce “Ah faɗa Gaskiya dai yawon 5hours saikace wanda suka bar gari”

Sajida na jan Tsaki ta ce “ hotel mukaje Ƙarewar Iskanci stupid girl kawai kuma wlh zakisan ni kikewa iskancin nan ko dan kinga ina sake miki fuska Watau ma ni sa’arki ce”

Safa ta ce “to fa Batun Girma ya tashi Dalla One year har wata Tsiya ce Wlh a fuska ma daga ke har Ibtihal ɗin da kuke tutiyar kun girmeni Nafiku Girman jiki”

Sajida ta ja tsaki ta ce “Girma ba wayau ko”

Ta ce”Anji”

Kafin sajida ta kalli Ibtihal ta ce “Sis ya jikin fatan yanzu bakyajin komai”

Ta harareta ta ce”bansani ba”

Ta taso tare da hugging ɗinta ta ce “sorry Fav sis bazan sake zuwa ko nan da nan ba i promise”

Afren ta ce “Aunty Sajida “

Ta kalleta ta ce “Yesss My princess”

Ta ce “Yanzu Friend ɗin Aunty Safa ta tafi i love her We will go to their house tomorrow zaki kai ni”

Sajida ta ce “to Afren ai Aunty Safa za ta kaiki ba ni ba ni da ba ƙawata ba”

Ta kalli aunty safa ta tura baki alamun fushi take da ita”

Safa ta ce “Ohh baki huce ba to ai ko bazan kaiki ba”

Da sauri ta ce “Sorry Aunty please i want see her Tomorrow I didn't know she was gone”

Safa ta ce “to zan kaiki but not tomorrow”

Ta na shagwabe fuska ta ce “Aunty please”

Ta mata shitt da baki ta ce “kika sake begging ɗina zan fasa kaiki ki bari zan kaiki wataran”

Ta jinjina mata kai ta na Direwa daga jikin Ibtihal ta yi hugging hannunta ta ce “i,am goin to mom take cake Aunty”

Ta fice da gudu”

Ibtihal za ta juya ta kwanta Sajida ta ce “Wai bakya gajiya da kwanciya Ni wlh magana ma nake so muyi sis don Allah wai me ke damunki nasan Akwai wani sabon abu da yake damunki kin kasa faɗa a tunani na ko zaki ɓoyewa kowa ai bai kamata ki ɓoye mana ba”

Ta na kwanciya Tare da lumshe ido ta ce “Bakomai”

Safa ta ce “Hmmm ni fa wlh na so na Ɗauko Haske kamar maganar Auren yaya yusuf ne bakya so saboda ranar naji Abba ya kira mom ya ke sanar mata za a tsaida rana dukka kun amince kuma washegari wannan Al’amarin ya faru kuma nasan ai bakya son yaya yusuf”

Da sauri Ibtihal ta buɗe ido ta na kallon safa tare da haɗe fuska ta ce “ni na faɗa maki haka?

Ta ce”a a amma nasan hakan ne”

Ta ce “To ba haka ba ne kuma naji maganarnan a wajen su mom bazan taɓa yafe miki ba “

Sajida ta ce “Haba Ibtihal”

Safa ta ce “ƙyaleta za ta cuci kanta da kanta ni wlh bantaɓa sanin haka yaya Yusif yake ba sai Ɗazu kinga maganganu masu ciwon da ya faɗa mata wanda wlh da nasan haka yake ko ni da bazan goya masa bayan son ya aureta ba a baya “ibtihal ta yi banza ta ƙyaleta ta na kallon gefe guda ta na durmiya duniyar tunani,

Cike da jin haushi Sajida ta ce “meyasa ke wai kike da zurfin ciki Sis wlh bakya son Yusuf me ya sa zaki amince a aura miki shi alhalin zaki chutu ki fito ki faɗa bakya sonsa a wuce wajen tunda ba Auren dole za ayi miki mi daman chan bana son Aurenki da shi wannan zafin zuciyar tasa da masifa ga faɗin baƙaƙen maganganu”

Ibtihal na miƙewa zaune cike da Ɓacin rai ta ce “babu ruwanku rayuwata ce ba taku ba Zan Aure sa Koda hakan shi zai zama silar mutuwa ta kuma wlh Duk wanda ya faɗawa Iyayenmu maganar nan bazan taɓa Yafe masa ba”

Safa ta ce “me yayi zafi Allah huci zuciyarki “

Ta ce “Amen “

Ta na komawa ta kwanta”

sajida ta ja tsaki ta fice cike da jin haushi wannan tsinannen zurfin cikin na Ibtihal da babu abunda ya ke ƙwarar rayuwarta ko a baya kamar shi,

Washegarin ranar da Sassafe aka sallame su da Asibiti bayan magunguna da shawarwari da Dr ya bayar,

Sakamakon allurorin baccin da aka mata yasa yinin ranar kusan yini ta yi a kwace,

Dukkaninsu Zaune Suke a Palour suna Hira Tundaga Kan Abba,Aunty Aisha,Momyn Ibtihal,Aunty salma, sai hira suke gwanin sha’awa da burgewa kallo ɗaya zaka musu kasan akwai shaƙuwa mai ƙarfi da soyayya a tsakaninsu,

Aunty salma ta so kwana a nan amma Hajja ta Tisata ta bi mijinta da ya zo ɗaukarta daman ya je duba Ibtihal Asibiti sau biyu daman Safa ta Ƙi binsu saboda Sajida a nan suka gama tattaunawa akan Batun Auren Ibtihal Da Yusuf Tare da na Sajida Da Marwan da dama a sanye ya ke wata Ukku da sati biyu ya rage wanda yayi daidai da lokacin ta gama Masters ɗinta Sun tsaida magana akan za a haɗe bikin tare da na Ibtihal,Bayan ya je sun gana da mahaifinta za su tsaida Ranar a chan”

Momy lokaci guda fuskarta ta sauya ta ce “ba na buƙatar sako Mahaifinta a batun nan Yaya Don Allah “

Ya ce “a a Nafisa baza’ayi haka ba shi ya ke da haƙƙi akan ƴarsa dole zamu basa Haƙƙinsa”

Aunty Aisha ta ce “haba Yaya Bashir wani kuma haƙƙi yaran da ya wulakanta ya musu Allah ya isa suka Ƙara taka gidansa ko kiransa a waya ko nemansa ma ya ce ba ya buƙatarsu a cikin rayuwarsa har abada su nemu sabon uba shi ya yafe su shine har kake maganar tunkaransa da batun yaran saikace bamu da zuciya a ƙirjinmu ai gaskiyar Nafisa Kai ma Uba ne Ka yanke duk wani hukunci akan Ibtihal amma ba ma buƙatar Adam a batun nan”

Abba ya ce “ku mata ne mu kuma maza ne akwai banbancin tunani tsakaninmu tunda nace hakan kawai ku ƙyaleni”

Hajja ta ce “Hakane sannan Ni har yanzu ban yarda ba Ɗana Adam ba a hayyacinsa ya ke ba kuma har yau har gobe bazan daina masa Addu’a ba Allah kuɓutar dashi”

Abba ya ce “Amen Hajiya”

Ta ce “idan ka je goben ka ce ina gaishe sa “ya ce “Insha Allah Hajiya”

Aunty Aisha da mom ba su ƙaracewa komai ba amma tsananin haushin hakan suke ji,

Washegari misalin takwas na safe Ibtihal ta farka bayan ta yi wanka ta shirya cikin kaya mararsa nauyi Safa da ke shirin tafiya school ta kalleta ta ce”don Allah kafin ki wuce kisa Saratu(mai aikinsu)

Ta haɗomin Tea Ba madara da milo zallarsa kawai banda bread”

Safa na Gama roalling gyale ta ce “toh amma ai da abu me nauyi kika ci zafikijin ƙwarin jikinki amma fa tun a asibiti daga Fruits sai Tea kike ta sha kinga yanda kika rame”

Ta ce “bana son cin abincin ne”

Ta ce “haka dai zaki daure”

Ta yi shiru batace komai ba”

Safa ta buga ƙafar Sajida da ke bacci ta na daga kwance cikin gigin bacci ta ce”meye”safa ta ce “ba fa kiyi salla ba Dukda gaba Ɗaya muka makara amma kiduba 7:30 fa”

Ta na juyawa tare da komawa bacci ta ce “banayi”

Jin haka ya safa Ƙyaleta ta na ficewa maimakon maid ta haɗo wa Ibtihal da kanta ta haɗa mata kafin ta wuce school a motar Ibtihal ɗin domin ta ta ta na gida,

A parking space suka haɗu da Lena kamar yanda suka saba haɗuwa kullum domin duk inda zasu a schook ɗin su biyu za ka gansu tare ba sa Mu’amular abota da kowa sai su biyu sai few mutane da suke gaisawa haka 9:30 suka fito lectures kai tsaye motocinnsu suka nufa suna nufar wani haɗaɗɗen restaurant bayan Sunyi Order abunda zasuci saboda dukkaninsu Basu karya ba suna Tsaka da karyawa Lena ta yi murmushi ta ce “Besty Alƙawari na”Safa na waro ido ta ce”Na meye”ta ce “kinga besty banson jan rai ki bani Labari kawai muna gama breakfast ɗinnan”

Ta ce “Ai yau ban bada labarin nan ba inaga zaman Abuja sai ya gagareni “

Ta ce “ba ma Abuja ba duka Nigeria”

minti Ƙalilan suka gama Kafin Lena ta ce “Oya Ke nake saurara”

Safa na goge bakinta da Tissue ta ce “Asalin kakanninmu wanda suka Haifi Iyayenmu Haifaffun……….✍🏽

*ZAMU KAMMALA FREE PAGES NA WANNAN LITTAFIN A PAGE 15 KUNA DA DAMAR FARA BIYAN KUƊINSA TUN YANZU 500 TA WANNAN ASUSUN BANKIN 7026166536 OPAY HAJARA ABUBAKAR LAWAL TARE DA SHAIDAR BIYA TA 07026166536*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~

*HAJARA L SADEQ*

(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼

Auren wata tara

Ni da yaya arman

Matar uncle

Najmat abiy

Komai mukaddari ne

Khadijatul Sabren

Ribar so

Mata ta ce

*And now*

*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

*Ƙawa ta zama Ƴar uwa💃🏼🎶Roky magaji tawa ƴar amanata wlh jinta nake Ƙasar raina🥹Fatan Alkhairi gareki da dukkan ahalinki Alkhairin Allah yaci gaba da Dabaibaye rayuwarki Allah ya baki miji nagari wanda zai kula mana da ke ya so ki ya ƙaunaceki Allah ya nuna mana ranar Auranki Ranar Zaria ko ba Taya Wollah*

🅿️…………………………..*13*

Asalin kakanninmu wanda suka haifi iyayenmu haifaffun garin Bama Local goverment ne da ke jahar Borno State wanda asalin su Shuwa’arab ɗin Sudan ne,

Kakarmu mai suna Zainab Tare da Kakanmu Alhaji Dikko ƴan uwan juna ne auren zumunci aka musu,

Kakarmu su biyu a gurin iyayensu daga ita sai Ƙanwarta Aisha ,

sun ta so cikin soyayya Da Ƙaunar Juna Wanda kusan tattare akayi aurensu domin shekarar Zainab guda da Aure Akayi auren Aisha lokacin Zainab na da tsohon cikinta na fari wanda Aure ya raba su ita Aisha ya kaita Katsina saɓanin Zainab da aka aje ta a nan Bama saboda lokacin kakanmu Soja ne yana tafiya ya yi watanni ya dawo kafin daga baya ya koma duk inda zaije tare da Ita ya ke tafiya,

Ta haifi Ɗanta na farko Ya ci suna bashir bayan shekara ukku Da haihuwar bashir itama aisha aka kawota gida haihuwa wanda Zainab ta matuƙar kula da ita Har Allah ya sauketa ta haifi ɗanta namiji wanda ta matuƙar jigatuwa bayan haihuwarsa da awa guda Allah ya amsa Ranta bayan ta damƙa amanar

10 / 13