IBTIHAL HAUSA NOVELS PDF COMPLETE BY MISS HAJO.docx

Author :  Miss Hajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 13

36K to 36.4K   out of 36.4K words

uba na hausa tun wata rana da na taɓa ɗura mata maganin zafi da aka bani kwana a gaba ya tasheta ta dunga amai da zawo tun dagashi na ce na haƙura “

Aunty Aisha ta ce “amma ai wannan daban da wancen Amfanin kan ta ne fa haka za a kaita gidan mijin ba wani gyara ai bazaiyu ba sai ta sha”

Ibtihal na jin haka ta ƙara sanya kuka Aunty salma ta ce”Mun shiga ukku saikace wacce za ayiwa Auren Dole Ke daman har yanzu baki girma ba kin bar wannan sangantar to don ubanki haka kike so a kaiki gidan miji Ba daraja saikace ba jinin Shuwa ba “

Mom duk ta ruɗe ta ce”Don Allah aunty Tunda bata sha a ƙyaleta a mata gyaran jiki kawai”

Ibtihal na kuka ta ce “Ni duka ba na so”

Aunty Aisha da ta zuba mata ido ta tashi tare da kama hannunta suka shiga Cikin Ɗaki banda Faɗuwa babu abunda Gaban Mom Ke yi lokaci guda zufa ta keto mata,

Suna shiga ciki aunty Aisha ta rufe ɗakin ta na Kama hannunta suka zauna Bakin gado zuba mata idanu sosai ta yi ta na kallonta ta na kuka saida ta yi mai isarta Kafin ta fara sauke ajiyar Zuciya Aunty Aisha na kamo Haɓarta ta ce “Ibtihal”

Cikin shasheƙa ta ce”Aunty”

Ta ce “Bakya son Auren nan ko ki faɗamun gaskiya bana son ki Ɓoyemun komai wa ya tilasta miki Auren nan…….. ✍🏽

*Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen free page na wannan littafin domin samum daman cigaba da karatunsa ki biya 500 kachal ki karanta har ƙarshe cikin kwanciyar hankali domin tura kuɗin kai tsaye ga account number 7026166536 Opay Hajara Abubakar Lawal tare da shaidar biya ta wannan number 07026166536 wannan karin babu Promo*

*Hmm wasa farin girki idan nace muku bamu fara komai a littafin Ibtihal ba zakuyi matuƙar mamaki Sabuwar tafiya mai ɗauke da sabon salo mabanbanta natabbata ko nawa kika biya kika karanta Ibtihal ƴar uwa baki faɗi ba Ki saya ki karanta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa karki bari sai an fitar ki karanta ba girmanki ba ne hajiya sannan idan kinsan don ki saya ki fitar mun na yafe maki saya please mu riƙewa juna amana*



*_Miss Hajo ce*_🤙🏿

13 / 13