Author : Miss Hajo Category : Romantic Hausa Novels
wanda muryar mahaifiyarta ta daki dodon kunnanta da cewa”Ina kika saka wayarki tun jiya ba ta shiga “
Jiki sanyaye ta ce “momy sim ɗin ce ya lalace amma na sayo wani zan kiraki da shi”
Ta ce “karye-karyen sim ɗin naki na masifa dai zakice kinyi zanga idan Nin ɗinki ya daina miki register layi yanda zakiyi ashe kuma haka wannan ƴan iskan suka ɓullo to abunda nake so da ke ki kwantar da hankalinki bana son ko da wasa ki ɗaga hankalinki abunda yake so kenan daman baya son kwanciyar hankalinki insha Allah ba abunda zai faru sai alkhairi ko Court ɗinma ba za a shiga da ke ba Lawyer kawai zamu ɗauka don yanda kika firgitar nan sai ki ɓata mana shiri ki ci gaba da harkokinki ki manta da su kinji”
Ba don ta gamsu ba ta ce “Toh momy amma wata shaida zamu bayar da zata tabbatar da cikin ya fita”
Ta ce “Salma ta ji da komai zatayi magana da wata ƙawarta Aunty Aisha da ke da asibiti mallakinta ne sannan yanzu zanje gidan aunty Aisha mu tattauna za a bada shaidar da date ɗin da komai sai ma mun kullesa akan ɓacin sunan da yake shirin mana bayan munci nasara”
Ta na sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta ce”Momy don Allah ku ƙyalesa kawai Ni dai a tsorace nake ba sai kun kullesa ba kawai a rabu lafiya”ta ce “to naji amma kiyimun alƙawari kin daina kuka akan batun daga yanzu”
Kamar ta na gabanta ta gyaɗa mata kai tare da cewa momy sai yaushe to zakuzo”
Ta ce”insha Allah ba da jimawa ba Afren na gaishe ki dukda bakya nemanta”jiki sanyaye ta ce “ina ansawa momy ki gaishe ta “
Ta ce “ga ta ma ku gaisa shiru ta yi ta na saurare chan momy ta ce”kinga ta maƙe kafaɗa wai ba ta Amsa fushi take da ke bakya nemanta “
Ta ɗan saki murmushi ta ce”anjima zan kira Video call sai na bada hakuri”
Momy ta ce “haka ya kamata ba Salma wayar”
Ta miƙawa Aunty salma wayar ta na jin sanyi a ranta,
Aunty salma ta fita da wayar a kunnanta suna cigaba da tattaunawa.
Safa na kallon Ibtihal da tayi tagumi ta dinga janta da hira har ta samu ta sake suka ci abinci tare sai shida na yamma ta bar gidan ta na jin damuwarta ta ragu ,
ko hajiya batayiwa bayanin abunda ke faruwa saima ta ɗan saki suna hira da hajiya dukda rabin hirar hajiya ce me yi .
8:30 Sukaji bugowar ƙofa Ibtihal ta bi ƙofar da kallo ganin me shigowar ne ya sanyata tashi ta shige bedroom hajiya ta gorgiza kai ta na maida kallonta ga farin matashin da a ƙalla zaikai 33yrs dogo mai ɗan garin jiki kaɗan ta ce.
“Yau Yusufa ne a gidan nawa lallai Ibtihal ta dawo kusan sati biyu fa rabon da ka taka ƙafar ka gidan nan”
Ya na zama tare da cewa”zaki fara mitar tsohuwar nan toh ba na garin tafiya na yi shiyasa “
Ta ce “haka dai baku da aiki sai gantali a jirgi daga kai har uban naka”
Ya na taɓe baki ya ce”Ita kuma waccen fa yaushe ta dawo”
Ta na harararsa ta ce “ka shiga ka tambayeta munafuki saikace bai san da zuwan nata ba ko ba saboda ita ka shigo ba”
Ba tare da ya bata amsa ba ya miƙe tare da nufar ɗakin na ta “
Hajiya ta taɓa hannu ta ce “Eyye da gaske kuma shigar zakayi zo ka wuce don ubanka karka sake ka shigar mata ɗaki bana son taɓara ƙaton baligi dakai ka faɗa ɗakin yarinya”
Ko waiwayowa baiyi ba bare ta sa ran amsa.
Ibtihal na shiga ta ja dogon tsaki bacci ma takeji gwara ta kwanta ta huta da wuri hakan ya sanyata cire kayan jikinta tare da ɗaura Towel ta na niyyar juyawa ta nufi Bathroom ta ji an Banko ƙofar,
a matuƙar firgice ta waiga ganin mai shigowar ne ya sanya gabanta tsananta faɗuwa ran ta na tsananin ɓaci ta juya da sauri zata wuce toilet don gaba ɗaya ta duburce ta ji an kamo hannunta cikin sauri ta waigo sukayi ido huɗu dashi ta rumtse ido da ƙarfi ta na jin tamkar ta ɗauke sa da mari ta ce ……….✍🏽
https://chat.whatsapp.com/JYPWPtF78zlIr2kJcbp6ms?mode=gi_t
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
🪅*IBTIHAL*🪅
~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)
MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*
*DEDICATED TO MY HUSBAND*
🅿️…………………………..*03*
Ta ce “Ba ka da hankali ne yaya Yusuf za ka shigo mun ɗaki ba neman izini ka sakemun hannu kar nayi maka abunda duk bazamuji daɗi ba”
Ba tare da ya sakar mata hannu ba ya ce
“meye zakimun duka na zakiyi ko zagi na watau da sabuwar rashin kunya kika dawo ko meye a ciki don na shigo ɗakin ki ba izini kin manta matsayina a wajenki yaya kuma miji nan gaba kaɗan gaba ɗaya ma abunda kike ɓoyewar bakya son na gani zai zama mallaki na “
Haushi ,Takaici gami da kunya ne suka lulluɓeta wani ɓacin rai takejin na taso mata ba tare da zato ba ta ji ya saki hannunta ya na taɓe baki ya ce idan kin gama wankan ki sameni a falo idan ba haka ba Allah na sake shigowa bazakiji da daɗi ba”
Ya na gama faɗar haka ya fice tare da zare makullin ɗakin ta bi sa da kallo saida ta ga ficewarsa kafin ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta na jan dogon tsaki tare da nufar Toilet ba ta wani ɓata lokaci sosai ba wajen wankan ta fito shiri tayi cikin kayan bacci silver masu masifar kyau riga da wando yalwaltaccen gashin kanta da ke ta sheƙi da ɗaukar ido ta tace da mataci wanda ni kaina tsawon gashin da sulɓin saida ya masifar burgeni turaruka masu sanyin ƙamshi ta fesa tare da gabatar da sallah don har wankan tsarki ta yi kasancewar perioud ɗinta ya ɗauke.
Ta na shirin kwanciya ta tuna Wancen mutumin ya cire key ya tafi da shi kuma ba kunya ta ishe sa ba zai iya dawowa tunda komai yayi mata ba dukansa ko zaginsa zatayi ba a ranta takejin tsanantar jin haushinsa,
Hijab blue black mai girma ta ɗora saman kayan baccin tare da fita ta na harhaɗe
Fuska,
Tunda ta fito idanunsa a kanta baisan sanda ya furta kalmar “Wow “ba “ ita komai ta saka sai ya mata kyau ne?”
ya tambaya kansa ya shagala da kallonta wanda har baisan ta zauna ɗaya daga cikin kujerun nesa da shi ba saida zazzaƙar muryarta ta doshi dodon kunnansa ya dawo cikin hayyacinsa ya na sauke ajiyar zuciya tare da amsa gaisuwar da tayi masa ya ɗora da cewa”ya aka gama karatun dukda baki faɗa mana dawowar ba bare mu shirya miki partyn graduation”
Hankalinta akan t v ba tare da ta kallesa ba ta ce”Alhmdulillah”ba tare da ta basa waccen amsar ba
Tashi ya yi daga kujerar da ya ke ya na komawa wacce take zaune 2sitter da sauri ta matsa ganin yanda Yake shirin shige mata harga Allah shiyasa bata so ba ganin ba hajiya a ɗakin don ta riga ta shige ciki ana isha’i dama ta ke kwantawa abinta,
Ƙara matsawa tayi murya ba wasa ta ce”meye haka yaya Yusuf”
Ya ce “Soyayya ce”
“Amma dai kasan babu kyau abunda kakeyi”
Ya na wani lumshe ido ya ce “meye marar kyawun “
Rasa da me zata amsa kawai tayi sai tsaki da ta ja a cikin ranta”
“Ya maganar Auren mu “
Ta tsinta muryarsa,
Ba tare da ta kallesa ba har lokacin idonta na kan tv dukda tana jin kusancin na su ya yi yawa ta ce”Daman munyi alƙawarin aure ne da kai?
“Hmmmm har yanzu ba ki janye kalamanki ba kenan amma kinsan a gobe na ga damar a ɗaura mana aure sai an ɗaura bana son ne na tilastaki shiyasa ko a baya na ƙyale har kika tafi ƙarin karatu”
Banza tayi ta ƙyalesa ta na jinjina Gadara da nuna iko na Yaya yusuf na daga dalilin da yasa kwata-kwata daman chan ba sa jituwa”
“Hmmm na kula kin dawo da sabon wulaƙanci karatun nan da kika dawo ko don kina ganin Kina Da PHD ina da Masters ko yanzu na ga daman zama DR ma zan zama don kar ki ga kamar kin fini ajin karatu ki rainani gaba nake dake a komai tunda Allah ma da kansa ya bamu wannan girman a kanku ko primary gareni ki sani gaba nake da ke don Haka ki aje girman kai mu fuskanci juna da bakya nan idan na daure yanzu bazan iya daurewa ba komai zai iya faruwa don haka ki bani hankalinki mu fuskanci juna”
Ba tare da ta basa amsar waccen tambayar ba ta miƙe tare da cewa” makullin ƙofar ta fa”
“Hmmm haka ma kawai zakice”
Ta ce “eh”
Ya na zare ɗaya daga cikin makullan ƙofar ya ce “Ga shi”
Ta na mamakin me zaiyi da makulli ta kallesa ta ce “ka mayar mun makulli na me zakayi dashi kuma “?
Ba tare da ya ba ta amsa ba ya miƙe tare da damƙa mata makullin a hannu ya na damƙar hannun kamar gaisuwa ya ce “Have a nice dream my beautiful wife”
tare da sumbatar hannun ya fice ta bishi da kallo sakaka tamkar sakarai kafin ta kalli hannunta da ya sumbata ta na jin takaici wasu hawayen takaici ta ji ya zubo mata ta wuce bedroom ta na hawaye zuciyarta chunkushe duk ba daɗi har ga Allah ba ta ƙaunar takurar nan da yaya faruq ke mata ita gaskiya ma sai ta bar gidan ma indai haka zaici gaba da mata”
“to ki bar gidan ki je ina kin manta mahaifinki ya muku iyaka da shi ko a waya ballantana gidansa da yayi muku korar kare”
“Innalillahi wa inna ilaihiraju’un wata Kewar Mahaifinta take ji har ƙasar zuciyarta dukda abunda yayi musu amma batajin tsanarsa ko kaɗan a cikin ranta”
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta na duba lokaci ta ga 10:30 tasan chan yanzu kusan 12 ma ta wuce kuma yanzu ta na tare da mijinta bai dace ta kirata a daidai wannan lokacin ba “Jiniour nasan yanzu baiyi bacci ba”
Ta faɗa ta na lalubo number sa saida ta kusan katsewa kafin ya ɗauka cikin muryar wanda ya fara bacci ya ce “Waye”
Ta ce “Sabuwar budurwarka da muka haɗu rannan”
Ta na jin sautin dariyarsa ya ce”Haba Aunty Ibtihal ko a mafarki akace na kasa gane muryarki ai zakice ba Jiniour ɗinki ba ne”
Ta ce “hummm ɗaɗin baki”
Ya ce “gaskiyace aunty na yi ta kiranki nayi miki sannu da zuwa ba ta shiga shine ko ki faɗa mun zaki dawo ƙasar da ko ƙaryar rashin lfy ne sainayi an barni na zo tarbarki”
Ta ce “nasan Exams kake shiyasa Bana son ka samu matsala a karatunka na so ma Zuwa Sch ɗin naku to da naga 10days ya rage ka dawo shiyasa na hakura don kasan nayi missing naka sosai bro”
Cike da zallar ƙauna ya ce”nima nayi matuƙar missing ɗinki aunty har bana son ayi hutu saboda idan nazo nasan bazan iske ki ba aunty ba ke ba momy ba Daddy dukda Shi daddy ba ya ƙaunarmu yanzu amma ai ita momy ta na ƙaunarmu amma itama ta rabu da mu ta zaɓi mijinta a kanmu a shekara sau ɗaya take zuwa ƙasar gwara ke ma kina zuwa inda take amma ni saidai a waya “
Gaɓa ɗaya jikin Ibtihal yayi sanyi ganowar jiniour hawaye ne ya ke itama hawayen takeji amma ta daure don ta kwantar masa da hankali ta ce”Karna ƙarajin kalar maganar nan daga bakinka jiniour jarabawa ce kowa da kalar tasa haka Allah ya zaɓa mana kuma dole mu bi na kiraka domin na ji muryarka naji sanyi a raina Muyi hira shine zaka tayarmun da hankali”
Da sauri ya ce”Kiyi hakuri bazan Sake ba”
Kafin su sake su hau hira sai wajen 11pm suka rabu cike da ƙaunar ƴan uwantaka mafi shaƙuwa.
Washegari kasancewar bazataje office ba tunda ba wani abu take ba sai 10:Am ta fito cikin doguwar riga marar nauyi ta zaman gida da tayi masifar mata kyau,
Breakfast ta je ta yi kafin ta wuce ɗakin hajiya samu tayi ta na walaha saida ta gama kafin ta gaisheta ta amsa da kulawa tare da cewa”meyasa tunda kika dawo bakije sashen Abban ku ba”?
“Hajiya to Abban fa baya nan “
Daƙuwa tayi mata tare da cewa”ja’ira to don baya nan bazakije ki gaishe da matar sa ba”
Ta na tura baki gaba ta ce “to hajiya saikace ke gaishe ki take zuwa tunda nazo banga ta shigo ta gaishe ki ba fa sai Abba na nan ta kafa munafurci da nuna tafi kowa sonki “
Hajiya ta ce “naji dai yanzu tashi kije ki gaisheta shikenan”
Ta miƙe ba har a son ranta ba ta fita Ta cikin part din na Hajiya bayan ta sanyo hijab ta bi wata ƙofa wacce ta sadata da wangamemen ɗayan part ɗin da kallo ɗaya sakayiwa ɓangare kasan mamallakinsa ya mallaki kuɗaɗe ,
Ko da ta shiga palo na farko ba kowa a na biyu ta samu hajiya Lubna baƙar dattijuwa sanye cikin shiga ta alfarma ba kyakyawa ba ce haka ba ta da muni suna haɗa ido ta yi kichin kichin da fuska saida ta ƙarasa har tsakiyar palon bayan sallama har sau biyu da tayi wanda daƙyal ta samu amsa zama tayi saman carpet tare da cewa “ina yini mama munsameku lfy”
A taƙaice ta ce”lfy”
Itadai Ibtihal ba ƙara cewa komai ba,
Hajiya Lubna na gyara zama ta ce ,
“yawwa gwara da Allah ya kawoki daman ina son maki kashe na ƙarshe akan ɗana wallahi tallahi ki fita sabgar ɗana idan ba haka ba zaki shiga mafi munin linkin matsalar da kika shiga a baya wancen nafila ne akan wanda zaki shiga gidan ɗana gwara tun wuri kisan abunda zaki Faɗawa Alhaji idan ya dawo don wallahi tallahi kika kuskura kika aurarmun ɗa hmmmm”
Ta gama faɗa ta na wani cixon yatsa”
Ba tare da IBTIHAL ta ba ta amsar komai ba ta miƙe tare da nufar ƙofa ta fice a binta Hajiya Lubna ta bita da kallo cike da jin haushin ta ta ce “Marar kunya fitsararriya watau ga mahaukaciya ma na magana baki da lokaci na”
Ba ƙaramin tsanar halin nan nata tayi ba na ta datsa mata maganganu tayi kamar ba da ita ta ke ba ta fice,.
Ibtihal da sauri ta bar part ɗin ta na komawa batare da maganganunta sun wani dame ta ba ta ja tsaki tare da cewa”ɗan nakin ma da kike bambami akansa ni me zanyi da shi mtwss “
Da yamma Aunty Salma tare da Safa suka zo a ɗaki aunty salma tayi mata duk wani bayani kamar yanda suka Tsara sun ɗauki lawyer sannan anyi musu takardar shaidar inda tayi ɓarin harma idan ta Kama Dr ya je ya bayar da shaida akan hakan”
Sosai taji sauƙin damuwarta amma dukda haka a firgice take daɗi ɗaya ta ji da ba zata halarta kotun ba saidai idan abun ya fi ƙarfinsu wanda ba sa fatan hakan so suke suyi abun cikin sirri batare da hajiya ko Abba Bashir sun fahimci halin da ake ciki ba”,
Safa ba ta bar gidan ba saboda daman akwai shaƙuwa me ƙarfi da abuta tsakaninsu dukda iyayin da Ibtihal ke mata akan ita fa yayartace.
Suna shirin bacci Ibtihal ta miƙe tare da Ɗaukar wayarta ta na shiga whats app ta iske missed call ɗin momy video call barkatai mutanen da take chat da su basufi 10 ba wanda sosai hakan ya ban mamaki kiran number momyn tayi Allah ya sa ta na online,
Ba jimawa wata kyakyawar farar matashiya ta bayyana mai matuƙar kama da Ita saɓanin Haske da momyn ta fita amma sak kamar anyi kaki saidai Ibtihal ta fi momyn kyau “hmmm Sai yanzu akaga daman kira hajiya Ibti”
Ta na narke murya ta ce”kiyi hakuri mom jiya zankira naga 10 yayi yau kuma na yi busy”
Ta ce”yayi kyau toh fatan kinji yanda mukayi da salma”
Ta jinjina mata kai”
Ta sakar mata murmushi har dimple ɗinta side na dama na lotsawa tare da cewa”
“inye shiyasa na ga an bar kuka”
Murmushi Ibtihal ta yi ta na rufe fuska tare da sakin murmushin da saida duka dimples ɗinta ƙwara biyu suka lotsa mom ta ce “ga mutuniyar ki lallasheta zanje na kula da mijina ya dawo”
Ibti ta turo baki ta na haɗe fuska itama mom ta bita da hararar wasa tare da miƙewa tabar wajen ta na nufar wani Ɗaki daga wayar na iya hango yanda ɗakin ya gaji da kayan wasan yara,
Daidai fuskar ta na bayyana Ibtihal ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ba ƙaramin kewarta tayi ba a cikin ranta amma a zahiri za ma ka ɗauka ba ta damu da ita ba ,
Wata Kyakkyar farar yarinya ce ta bayyana mai kimanin shekaru ukku ko da bata cika ba kaɗdan ne amma a zahiri zakace ta yi 5 years saboda girman jiki fara ce sol tamkar mom ga gashinta tamkar ba na yarinya ba saika rantse ba ta haɗa jini da hausawa ba saidai ita ba ta kama da mom da Ibti sosai sai waɗansu Abubuwansu da ta ɗauka,
Murmushi ibti ta yi ganin yanda ta tura mata baki ta na maida hankalinta kan ƙatuwar teddy da take wasa”
Cikeda lallashi ibtihal ta ce “wa ya taɓamun Afren ɗin