IBTIHAL HAUSA NOVELS PDF COMPLETE BY MISS HAJO.docx

Author :  Miss Hajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 13

15K to 18K   out of 36.4K words

da surukarsu hankali,

Watan Aishatou biyuu ta samu ciki farimciki a wajen Marzouq ba ya musaltuwa haka hajiya hajara har kukan farinciki saida ta yi cikin na da wata ukku ya zube sunyi matuƙar damuwa kafin a ƙarshe su barwa Allah akan ya basu wani me Amfani.

wasa wasa aishato ta ƙara samun ciki wata biyu ya zube wani ma kafin yakai wata guda ya zube a shekara biyu da aurensu da Marzouq Saida Ciki goma Sha Ɗaya ya zube a jikinta kuma duk wani bincike anyi babu wata matsala daga gare ta ko daga gareshi Ayshatou kullum cikin kuka ta ke mariya na tayata yanda ta ke nuna damuwa sai ka rantse har ranta hakan ya sa babu wanda ya sa zargi a kanta tunda likitoci sun tabbatar da zubewar cikin daga Allah ne babu wani alamun zubar dashi ake,

Ayshatou ta ɗauki wani cikin wanda mahaifiyarta ta sanyata ɓoyewa hakan ga kowa matsalar irin matan nan ne masu masifar laulayi wanda dole saida mariya ta gano cikin na da wata huɗu shima ta yi ɓarinsa wanda a nan ne jini ya ɓalle mata rai ya yi halinsa ta koma ga mahaliccinta,

Mutuwar tayi masifar girgiza Marzouq domin har ga Allah ya so Aishato domin macece mai tsananin tarbiya ga kulawa da nuna masa ƙauna ba ruwanta da dukiyarsa saɓanin mariya da take harin dukiyarsa ya zuba mata ido kamar baisan me ta ke ba sata kawai take masa ta na sayan kadarori.,

Hajiya hajara ma ta ji mutuwar Aishatou ana kwana ukku da rasuwar ne jin shiru mariya ba ta fito ba ta aika Lena akan ta kira mata Mariya ko lafiya ta na niyyar tura ƙofar kenan ta ji ta babbake da dariya tare da cewa.

“Kina wasa da ni ne ƙawata ta isa ta aurar mun miji daga sama na ƙyaleta ai aikin bokan nan ƙarshe ne babu zargin komai mun lalata ƴaƴa goma sha ɗaya mai kankat har uwar an rasa kinga wasa ya ƙare ni ke da nasara kamar yanda likita ya tabbatarmun bazan taɓa haihuwa ba haka shima bazai taɓa samun haihuwa daga wata mace ba saidai mu rayu mu biyu ƙarshe dai ko ya mutu ni ke da nasara saboda sannan ma tsohuwar banzar uwar chan tasa ta mutu daman ba uba garesa ba bare ya gajesa kinga duk wata dukiya da ya mallaka ta zama mallaki na”

Lena na dafe ƙirji ta ruga da gudu ta na haƙi ta faɗa jikin mahaifiyarta tare da sanya kuka ta ce “wlh Ummy Aunty Mariya ce ta dinga zubarwa da aunty Aishatu duka cikinta yanzu ma ita ta kashe ta so take yaya ya mutu ke ma ki mutu wai ta gaji dukiyarsa”

ta ƙarasa faɗa ta na rusa kuka cike da tsoro gami da sangartar da ta taso da ita,

Sosai hankalin duk mutanen da ke wajen ya tashi musamman mahaifiyar Aishato Hajiya haka Hajara ta girgiza ta ce “Mamana kin tabbata maganar nan haka take bana son ƙarya”

Ta ce”wallahi ummy da gaske tass komai da taji ta kwashe ta faɗa a wajen duk aka kwashi salati basuyi aune ba sai juyawa sukayi sukaga ba mahaifiyar ayshatou a wajen.

da sauri hajiya hajara duk suka bita samu tayi ta shaƙe Mariya ta na wlh sai ta kashe ta kamar yanda ta kashe mata ƴa saidai itama a kashe ta hankali tashe Ummy ta kira marzouq da ya ke chan part ɗinsa cikin rashin lafiya ya daure ya fito nan ya samu wani sabon tashin hankalin da zuciyarsa ta kusa bugawa daƙyal aka ƙwace mariya da ta suma a hannun Maman Aysha.

a take marzouq ya kira hukumar DSS akayi musu bayanin abunda ke faruwa an samu mariya ta farfaɗo sai kuka ta ke akan sharri akayi mata Marzouq ya umarta a tafi a bincike ta ,

ta na kuka ta na kiran shi zai mata haka daman mahaifiyarsa ba sa ƙaunarta shiyasa suka mata wannan sharrin aka tafi da ita ,

zuwa lokaci zuciyar Marzouq ji yake yake tamkar zata bar gangar jikinsa lurar da mahaifiyarsa tayi bashi lafiya ya sa ta sanya Ashraf ya kaisa asibiti wanda take aka kwantar da shi ganin yanda jininsa yayi mugun hawa ,

kwanansa biyu aka sallamesa bisa tirsasawarsa ba don ya warke ba mahaifiyarsa ta buƙaci da ya dawo gida da zama ita da DR Nazir suka dinga masa nasiha da kwantar masa da hankali gefe guda Ashraf da Yaya Sadeq suma suna bakin ƙoƙarinsu,

Saida mariya tayi sati a ofishin DSS bayan tsananin azaba da bincike da ta sha ta haƙura ta amsa laifinta aka kira marzouq ga shi ga mahaifiyarsa ga mahaifinsa ga mahaifiyar Aishatu da mahaifinta aka maida statement mariya na kuka ta amsa ita tayi asiri duk cikkunan da Aishatu ke samu suna zubewa wani boka ne ƙawarta ta haɗata da shi ana tsafin da cikin ke zubewa domin Aisha macece mai sakaci da Addu’a ta na wasa da azkhar sosai shiyasa har sukaci galaba a kanta amma ita batace a kashe ta ba abun ne ya zo da ajali saboda ta na baƙin cikin wata mata ta haifawa Marzouq yara domin kafin ayi auren su ta yi allurar planing bisa zugar mugayen ƙawaye batare da ya sani ba don su ci amarci sai bayan shekara ukku ta haihu to wannan allurorin ne suka juyar mata da mahaifa likita ya tabbatar da baza ta iya haihuwa ba wanda wannan dalilin ya sa ta kasa haƙuri ganin daga auro Aisha har ta samu ciki shiyasa ta biye zugar ƙawayenta ta faɗa harkar bin bokaye “

Ba ƙaramun girgiza duk mutanen da ke wajen sukayi ba Marzouq ko babu wanda zai iya kwatanta halin da yake ciki sai shi da mahaliccinsa.

“Allah ya isa tsakanina da ke Allah sakamun tun a duniya kije na sakeki saki biyu”iya haka kawai ya iya faɗa ya bar office ɗin .

wanda kafin ya isa motarsa ya yanke jiki ya faɗi Ashraf da ke bin bayansa ya taresa da sauri hankali tashe haka hajiya hajara da ke kuka itama ta nufosa hankali tashe aka nufi dashi asibiti,

Jinya sosai Marzouq ya yi wanda a binciken lafiyarsa da ba wanda ba ayi ba a nan ne likita ya gano ƙwayoyin halittar haihuwarsa dukkaninsu sun ƙare bazai taɓa iya ƙara haihuwa a nan gaba ba.

wannan tashin hankalin saida akabawa hajiya Hajara gado domin jininta yayi mugun hawa saida marzouq ya shafe wata guda ya na jinya asibiti kafin su dawo gida ya ji sauƙi sannan ya rungumi ƙaddara ya barwa Allah dukkan lamarinsa saidai yayiwa kansa aƙawarin bazai ƙara aure ba har abada yayi ƙoƙarin danne komai kodan saboda farincikin mahaifiyarsa da kullum jininta ya ke hawa akan ciwonsa da yanda ta ke kulawa da shi kamar wani yaro domin tuntuni ta aje Aiki shekarun baya Hakan ya sa ya ƙarfafawa kansa gwuiwa ya koma rayuwarsa kamar komai bai faru ba amma ƙasar zuciyarsa shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji .

Bayan abubuwa sun lafa lokacin da zaɓe ke gabatowa kuma Manyan Kaduna a fannin siyasa lura da irin taimakon talakawan da marayu da marzouq ke yi hankalinsu ya ja su akan suna buƙatar ya fito musu takarar gwamna fir marzouq ya ƙiya saboda sam shi bashi da ra’ayin siyasa hasalima siyasa bata taɓa burgesa ba ba irin magiyar da basuyi ba yace shi bazai fito ba suka koma lallaɓawa akan ya fito sanata,

mahaifiyarsa ma tace ita bazata tursasa masa ba dukda kuwa yanda ake bi ta kanta akan mahimmancin Irin su Marzouq a siyasar ƙasar nan Dr Nazir dai ya goyi bayan hakan ɗari bisa ɗari.

jita-jita ta fara yawo akan takarar wanda talakawa suka dinga shiga gidajen radio da media akan roƙonsu na Marzouq ya taimaka ya tsaya takarar sanatan yankin jahar ba ason ransa ba saidan ganin yanda har wasu tsofaffi aka nuno na kuka na magiyar akan ya taimaka ya fito takarar domin shi idan ba shi ya fito ba to fa kowaye bazasu zaɓe sa haka ba a son ransa ba Marzouq ya faɗa harkar siyasa wanda karon farko ya kayar da abokin hamayyarsa kadi mai tazarar gaske.

murnar da mutanen jahar kaduna sukayi akan hakan ba ƙarami ba ne wanda shikam ranar bai iya bacci ba saboda tsoron nauyin shugabancin da ya hau kansa alhalin bai shiryawa hakan ba.

kwana ya yi ya na adduar Allah ya basa ikon adalci Allah ya hanesa da cin haram ko zalunci yayiwa kansa addua sosai kafin zuwa safiya ya ji sanyi a ransa yinin ranar gidan su na kaduna cika yayi da mutane ƴan taya murna da sanya alkhairi gari sai wasanni ake na murna,

Shekarar Marzouq guda a mulki amma mutane sun shaida domin da aljihunsa wasu abubuwan yakeyi ya tallafi marasa ƙarfi da dama,

yaran da ya ɗauki nauyin karatunsu har su gama kuwa basu da iyaka ,

tallafin kayan sana’a da ya rabawa mararsa ƙarfi basu da iyaka ya ƙara samar da wadatattun famfunan ruwan sha, ya gina gidan marayu irin wannan komai da komai a kaduna ya yi abubuwan alkhairi da dama har yanzu da ya cika shekaru ukku da hawan mulki sam babu mata ko maganar aure a ransa dukda harin da dubunannan mata ke kai masa ganin kyakyawan ɗan siyasa mai jini a jika.

Rashin kula matan ya damu mahaifiyar sa amma tace ba zata ƙara tilastasa akan aure ba tunda dole zai mata biyayya sannan ya ce ta zaɓa masa wanda tayiwa kanta alƙawarin bazata sake zaɓa masa mata ba ta na masa dai adduar da fatan Allah haɗa ɗan nata da macen da tayi daidai da ra ayinsa ya ji da kansa tayi masa ya na sonta ya na ƙaunarta ta kwanta masa rai ta na fatan ɗan nata ya san meye soyayya da kansa dukda ta ga soyayyar Marigayiya Aishatu a ransa amma itama bawai masifar so ya ke mata ba ta na fatan ya auri macen da zasu rayu har ƙarshen numfashinsu macen da zai so kamar ransa dukda likita ya tabbatar da bazai sake haihuwa ba a ganinta ba kowace mace ba ce zata aure sa tsakani da Allah da wannan larurar tattare dashi hakan ya sa ta miƙa lamarin marzouq gaba ɗaya zuwa ga Allah akan Allah masa zaɓi mafi alkhairi a garesu baki ɗaya ,

dukda rashin auren nasa a yanxu na damunta domin ya tafi shekaru Arba’in da biyu da haihuwa yanzu a duniya sannan ta sanarmun sau biyu ta na zuwa kano domin neman Kakansa Alhaji Marzouq amma sam bata samu ko wanda

yasan sunansa ba gashi garin duk ya sauya mata don rabonta da kano tun lokacin daƙyal ta gano gidan da ta taɓa rayuwa domin a matse ta ke da Allah ya sake haɗata da farida amma tace ta samu gidajenma duka biyun anyi wata makarantar kuɗi da su sannan duk wanda ta tambaya a layin sai suce gaskiya basusan farida ba a haka ta haƙura ta dawo ta na fatan Allah ya haɗata da farida a gaba tare da kakansa Marzouq domin ta kasa manta halaccin Bawan Allahn gareta ita kuma Mariya Kotu ce ta yanke mata hukuncin zaman gidan yari na rai da rai ta na chan ta na fara girbar abunda ta shuka domin uwar ruƙonta ma abun yayi mata zafi ta ce babu ita ba ita har abada mahaifinta kuwa wannan yayi sanadin ajalin mutuwarsa saboda baƙinciki abunda ta aikata ɗa ne ka haifa ba ka haifi halin sa ba ,

ƙawayenta kuma duka sun gudu don tunda suka samu labarin ta na hannun hukuma suka gudu to daman ashe masu yawon banza ne ba asan ma iyayensu ba bare garinsu ba shi kanshi bokan da yayi musu aikin anje da ita domin ta nuna wajen amma ba a samesa ba lamarin dai yayi kama da kamar ƙungiyar wasu matsafa ce suka shiga Allah dai masani ko me mutum ya shuka shi zai girba walau alkhairi walau sharri.

To fa jikata kinji asalim Tarihin *MARZOUQ MALEK MARZOQ* ban ɓoye miki komai daga abunda na sani dangane da rayuwarsa ba jikata ban taɓa zaunawa na ba wani wannan labarin ba sai ke kema kawai don ina jinki ne tamkar jikata yanzu wannan ba abun a tausaya masa ba ne”

Mama salame ta ƙarasa faɗa ta na kallon Ibtihal”

Batayi mamaki ba ganin Hawaye a fuskar Ibtihal ta ɗanyi murmushin yaƙe tare da cewa “ai nasan kema dole ki zubar masa da hawaye Jikata domin duk wani mai imani yaji labarin Marzouq sai ya tausaya masa saidai muna masa fatan Nasara a gaba kamar yanda Mahaifiyarsa ta yi nasara bayan ƙalubalen rayuwar da ta fuskanta kala-kala a baya”

Ibtihal na sauke ajiyar zuciya tare da goge hawayen da suka zubo mata ta kalli mama salame ta ce “tabbas akwai tausayawa a labarinsa ina masa Fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya haɗasa da mata ta gari a gaba sannan ya basa haihuwar da ya ke buri me Albarka”……………..✍🏽

https://chat.whatsapp.com/JYPWPtF78zlIr2kJcbp6ms?mode=gi_t

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~

*HAJARA L SADEQ*

(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼

Auren wata tara

Ni da yaya arman

Matar uncle

Najmat abiy

Komai mukaddari ne

Khadijatul Sabren

Ribar so

Mata ta ce

*And now*

*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*8*

Mama salame ta amsa da “Ameen jikata kema Allah ya yaye miki abunda ya ke damunki idan kina da aure ya ƙara miki zaman lafiya da mijinki tare da baku zuriya ta gari idan kuma baki da aure ya baki miji na gari”

Ibtihal ba ason ranta ta amsa da “amen ba saidai kawai ba daɗi mutum yayi mata addua ka ƙyalesa amma a ranta tasan ita ta gama aure har abada ta gwammace ta ƙare rayuwarta a haka,

Tayiwa mama salame alkhairi sosai sai ƙarfe 1:30 ta bar gidan marayun zuciyarta cike da tunanin labarin nan da mama salame ta bata har ta isa gida abun ya na ranta ,

Ga mamakinta duk yanda ta so ta manta da batun *MARZOUQ MALEK* hakan ya gagara bacci tazo yi amma hakan ya gagara tiryan-tiryan labaran suke dawo mata tamkar a film ta rumtse ido bacci ya ɗauke ta yafi a ƙirga amma hakan ya gagara,

sosai mamaki ya kamata akan meyasa labarin bawan Alllah nan ya tsaya mata a rai,

bacci bai ɗauke ta ba sai bayan Asuba shima bayan ta gama salla ta fara karatun alƙur’ani sai taji damuwarta ta ragu a haka ɓarawon bacci ya sace ta.

Ibtihal ba ta tashi ba sai ƙarfe sha biyu na rana ta ji daɗin ramuwar baccin da tayi dukda batayi tunanim zata kai haka ba,

Yinin ranar sukuku ta yini tamkar mara lafiya don sai azahar ta karya Hajiya na kula da ita sai ta ɗauka ƴan miskilancin ne suka tashi,

Daren ranar ma sosai ta dulmiya duniyar tunani ƙarfe sha biyu ta yi kwance ta na kallon POP donma sun jima suna waya da mom ta na ƙarfafa mata gwiwar akan kar ta damu game da shiga kotu insha Allah su ke da nasara don ganin yanda tayi sanyi kamar bata lafiya ta ɗauka duk damuwar shiga kotun ce.

Jin murza key tare da buɗe ƙofar ne ya sanyata zubawa ƙofar ido ta yi mamakin ganin yusuf sanye cikin kayan bacci da zallar mamaki ta miƙe zaune ta na rufe jikinta da blanket don kayan bacci ne jikinta hankali tashe ta ce.

“meye haka yaya yusuf ya kake abu kamar baka da hankali ƙarfe sha biyu ka shigo mun ɗaki a haka me kake nufi”

Ya na nufo gadon ta ƙara matsawa chan ƙarshen gado hawaye na zubowa daga idamunta ,

gadon ya zauna tare da cewa”Zaɓi na zo na baki Ranar Talata Abba zai dawo zai miki magana domin na faɗa masa mun riga mungama sasinta kanmu jiran dawowarsa kawai muke mu tsaida ranar aure don Allah idan ya tambayeki kar bakinmu ya banbanta idan ba haka ba hmmm”

ya gama faɗa ya na wani ciza lips

“Idan na ƙi faɗa masa hakan me ka isa kayi ko an faɗa maka tsoranka nake yaya yusuf kai bakasan kawaici ba to bazan faɗa hakan ba bazan aure ka ba ko ni kaɗai ce mace a duniya gasunan dayawa kaje ka auri wata mana ko dole sai ni”

Ransa na ɓaci a zafafe ya ce “Eh sai ke ke kaɗai kika rage mace a idanuna bazan auri kowa idan ba ke ba kuma ki ƙi faɗawa Abban ki ga abunda zan miki wlh sai na ja mana abun kunyar da dole sai an ɗaura mana Aure idan nayi miki ciki kika haihu ai magana ta ƙare tunda na kula kinfiso sai ta tsiya-tsiya zan mallakeki”

Yagama faɗa cike da masifa ,

Hawaye na zuba a idon Ibtihal ta ce “

“bazan aure ka ba sannan wlh baka isa kayi lalata dani ba kodan ka na ganin ina gidanku shiyasa duk wani iskancinka ya ke ƙarewa a kai na meyasa bakayiwa Safa haka ba ko don ita ta na gidan mahaifinta sannan meyasa bakace zakayiwa Sajida haka ba me ya sa sai ni watau ni ce marar galihu ko”

Ta ƙarasa faɗa ta na sanya kuka,Jikinsa ne gaba ɗaya yayi sanyi duƙursawa ya yi ya ce .

“kamar yanda nake da iko da nan gidan Mahaifina ne Ibtihal haka kema nan gidan mahaifinki Abba ya na sonki kamar yanda yake sonmu meyasa zakice haka wallahi soyayyarki ce tayimun kamun da bazan iya control ɗinta ba kinƙi ki gane Ibtihal ina sonki ina ƙaunarki bazan iya rasaki ba ke kuma kin kasa fahimta me yasa bazaki aure ni ba me ye aibuna me sauran maza suka fini da shi’?

Ya ƙarasa faɗa ya na nuna kansa”

Ibtihal batace da shi komai ba illah haɗe kanta da gwuiwa da ta yi ta

6 / 13