IBTIHAL HAUSA NOVELS PDF COMPLETE BY MISS HAJO.docx

Author :  Miss Hajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 36.4K words

na cigaba da kuka”

“Kiyi haƙuri My love kuka bai dace da kyakyawar fuskarki ba “

Cikin kuka ta ce “ka ficemum a ɗaki wlh ko nayi maka ihu sannan ka bani makulli na”

Ya na miƙewa ya ce “mu kwana lafiya”

Ya fice ba tare da ya bata makullin ba ta haɗe kai ta gwuiwa ta na cigaba da kuka ta kai 1:30 kafin ta lallaɓa ta yi alwala ta yi sallah ta na addu’ar Allah mata maganin wannan masifar ta yaya yusuf meyasa su maza gabaki ɗayansu matsala ne”

“Ya Allah ka ciremunsu daga rayuwata har abada”ta faɗa ta na hawaye itafa wallah muddin za a tilasta mata akan aure ta gwammace ta gudu tabar ƙasar ta tafiyarta ma ƙarin wani karatun ba tare da kowa ya sani ba.

Ranar Monday ta koma bakin Aiki lectures ta ke amma rabin hankalinta na a kotu da aka sanar mata a waya an shiga yanxu ,

Yanayin yanda take koyawar cikin zallar ƙwarewar turanci da kamewa kaɗai ya isa kasan yarinyar classic ce ajin ƙarshe sosai tayi kyau cikin shigar lafaya ta suturta jikinta cikin mutunci idanunta sanye da glass da yayi mugun ƙawata fuskarta.

Awa Ɗaya da rabi ta ɗauka ta na lectures kafin ta bar class ɗin ta na fita matasa suka hau cece kuce akan wannan kyakyawar budurwar fa gaskiya duk ta tafi da imaninsu ba mazan ba har matan domin tayi masifar burgesu ga kamewa ba ta dariya duk iskancinka ba ka isa ka kai mata wargi ba.,

Ba ta koma office ba kasantuwar ta na da metting da sauran malamai da shuwagabannin makaranta wanda a wajen metting ɗinma rabin hankalin wasu daga cikin mazan Shuwagabannin na a kanta wanda hakan ya sa ta ƙara kame kanta.

ƙarfe biyu ta samu kanta sallah ta gabatar a office ɗinta kafin ta ɗauki tarkacenta ta fice ta na nufar mota domin azumi take ba ta buƙatar komai.

Allah-Allah take ta je gidan aunty salma ta ji halin da ake ciki,

Sosai labarin da ta samu daga wajen aunty salma ya masifar kwantar mata da hankali domin karin farko sukayi nasara sa’annan kotu ta ci Sharef tarar kuɗaɗe na ɓata musu suna da yayi ƙarshe dai reshe ya juye da mujiya don daƙyal sharef ya kuɓuta bayan kotu ta kori ƙarar”

Hamdala Ibtihal ta yi ba iyaka domin bata taɓa tunanin lamarin zai zo da sauƙi haka ba a nan ta sha ruwa Safa na magiyar ta kwana ta ce “ba yau ba hakan ya sa ta yi fushi ta ce “itama bazata ƙara zuwa gidan Hajiya ta kwana ba”

Ibtihal ta yi murmushi ta ce”kinma Huce student ɗin Nile”

Ta na harararta tare da tura baki ta ce “to faɗamun magana sannu Malama”

Ibtihal ta ce faɗa ki ƙara ai da school ɗinku nake lecturing kuma class ɗinku da na sauke miki rawan kan nan naki don in ba da ƙatuwar hijab ba bazakiyi lectures ba sannan atteders ɗaya kika rasa kinsamu Carry over”

Safa ta kwashe da dariya ta ce “tab kinma isa ai bama zaki fara ba Ni da Besty Lena Kaɗai ma mun ishe ki don kullum saidai ki koma a Box tayar motarki zamu dinga sace miki”

Ibtihal zata kai mata danƙwashi ta ruga ta na dariya tare da mata gwalo ta ce “Bye ƴar ƙanwata “

Ibtihal ta shige mota ta na murmushi tare da tayarwa saida ta biya ta sayawa Hajiya Fruits kafin ta wuce gida.

Washe gari Abba ya dawo bayan magrib ya na ɓangaren Hajiya jin shiru baiga Ibtihal ba ya ce “Hajiya ya banji motsin ƴata ba “

Hajiya ta ce”wannan uwar zaman ɗakin ta na ciki na rasa ubanme ta aje a ɗakin yarinya ko hira ba ka isa ta zauna kuyi doguwa ta ita ba ta shige ɗaki kullum ta na gado ai ba ƙaramun kewar Marwan nayi ba don shine zai zauna kuyi hirar arziki da shi amma Waccen da yusufa ai basu da hali sam“

Abba ya yi murmushi ya ce “akwai gajiya ne har yanzu hajiya tattare da ita shiyasa”

Marwan da ke gefen Hajiya ya yi dariya ya ce “To hajiya ko dai mukaita ayi mata ruƙiya Kinsan mutanen Ɓoye suna haka”

Hajiya ta ce “Allah maka Albarka Marwan Nima abunda nake ta saƙawa a raina lamarin nata dole akwai mutanen ɓoye a ciki yanzu ka ganta mutum anjima wani abu daban”

Lokacin Ibtihal na fitowa ta yafa gyale samar doguwar rigar jikinta harara ta ɓallawa Marwan ya waro ido ya na dariya ya ce.

“Tuba nake Shalelen Abba Ni da wasa na ke fa amma fa ba ƙaramun ƙara miki kyau japan ɗinnan tayi ba ƙanwata”

Ta na zama ba tare da ta ƙara kallonsa ba ta duƙursa ta gaishe da Abba cike da soyayya ya amsa ya na tambayarta ya aka gama karatu ta amsa “da Alhamdulillahi Abba ya hanya ai lokacin da nadawo akace baka nan sai naji dama ban dawo ba sai na jira lokacin dawowarka mu dawo tare”

Abba ya yi murmushi ya ce “ai ni kaina ƴata da nasan Ranar zaki dawo da babu inda zanje na ɗaga tafiyar don na taryo shalelena”

Hajiya ta ce “to ai duk sai ku tashi ku koma”

Duk akayi dariya kafin Ibtihal ta ɗan sake suka fara hira da Marwan wanda rabin hirar zolaya ne don marwan akwai zolaya suna ɗasawa sosai da Ibtihal,

sai 10 na dare suka bar part ɗin ga mamaki na washegari sai ga Hajiya Lubna tare da Abba sunzo gaishe da Hajiya yanda hajiya Lubna keyiwa Hajiya zaka rantse ta fi kowa kulawa da ita da ƙaunarta a gidan har da mata tausa wanda wannan shine babban abunda yake sa take ƙara daraja a idon Abba ya ke ƙaunarta saboda yanda ta ke kula masa da mahaifiyarsa da yanda take basa labarin kulawar da takeyiwa hajiya fiye ma da sanda yake nan ita dai Hajiya saidai ta kalleta amma bata taɓa nunawa ɗan nata ba haka ba ne ba ruwanta kowa yayi nagari kansa tunda dai a zage bata zaguwa haka a dake bata dakuwa ballantana baƙar magana chan taje ta yi shiriritarta ita taga za ta iya (Wlh hajiya kin huta🏃🏼‍♀️😂)

Kwanan Abba huɗu da dawowa ya kira Ibtihal ta samesa a palourn sa sosai tayi mamakin ganin yusuf gefensa “matso ƴata”Abba ya faɗa ya na ganin yanda ta yi shock bayan shigowarta.

Matsawa tayi inda ya umarta ta zauna bayan ta gaishe shi ya amsa tare da ɗorawa da cewa”daman wata magana yusuf ya zo mun da ita kan cewar kun sasunta kanku kin amince zakuyi aure shi ne nace bazanyi amfani da maganarsa ba dole sai naji daga bakinki Haka maganar ta ke”?

Abba ya faɗa ya na zuba mata idanu wanda da sauri ta ɗago ta na kallon Abba kafin tayi saurin janye idanunta ta maida ga Yusuf wlh a tunaninta da wasa ya ke kenan da gaske ne Abunda ya faɗa mata zai aikata.

“innalillahi wa inna ilaihiraji’un wannan wani irin tsaka mai wuya ne ta ya zata iya kallon idon Abba ta ce bata son ɗansa mutumin da ya so ta kamar ƴar cikinsa ya tallafe su ita da ɗan uwanta lokacin da nasu mahaifin ya koresu ya sama Mata Aiki ,ya saya mata Mota,Ya Biya mata maƙudan kuɗaɗe ta tafi Ƙarin karatu da dukiyarsa har ta gama da wani ido za ta kallesa ta ce bata son Ɗan sa ta ya zata fara wata zufa ce ta karyo mata ba shiri Abba na lura da ita jin shiru ba ta ce komai ba ya sa shi cewa.

“ƴata ke nake saurara”Saida ta ja numfashi mai ƙarfi kafin ta ce…………✍🏽



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~

*HAJARA L SADEQ*

(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼

Auren wata tara

Ni da yaya arman

Matar uncle

Najmat abiy

Komai mukaddari ne

Khadijatul Sabren

Ribar so

Mata ta ce

*And now*

*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

*Page ɗinnan naki ne Uwar Faredaƴar Amanata Alkhairin Allah ya cigaba da baibaye rayuwarki ya muna mana Auren Quen muzo jos mu raƙashe*😘

🅿️…………………………..*09*

Ta ce”Amma Abba ya na saurayi bai kamata ya aure ni ba matsayi na na wacce ta taɓa Aure har…….”

Rai ɓace Abba ya Ɗaga mata hannu ya ce “kull kar na sake jin wannan maganar daga bakinki Ai yasan da hakan ya ce ya na sonki amsa kawai nake so ki bayar kina son sa”

Da zuciyar Ibtihal za ta fito Allah kaɗai yasan irin halin da take ciki rumtse ido tayi da ƙarfi ta na jin zuciyarta na tsananta bugawa.

“Abba ya ce”ina sauraronki ƴata babu kunya a tsakaninmu ki faɗamun gaskiya kina son Haɗin Aurenki da ɗan uwanki yusuf”

Ba zato yusuf ya ga ta gyaɗa kai ,

Daga yusuf har Abba wata irin nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke Wannan na daga cikin babban burin Abba na son haɗa Aure tsakanin Ibtihal da jininsa Kamar yanda tun ta na budurwa ya so hakan Allah dai bai nufa ba,

Wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyar Yusuf baisan sanda ya furta kalmar “Thnks you my Love i love you morethan everything”

Abba ya yi murmushi ya ce “to kodai na baku wuri yusuf”

Yusuf ya sosa kai ya na ɗan jin kunya Abba ya maida kallonsa ga Ibtihal ya ce “tashi kije ƴata Allah yayi miki Albarka Gobe insha Allah zanje da kaina har kano muyi magana da mahaifinki”.

Ibtihal ta miƙe ta na jan ƙafafunta da takejin tamkar ba a jikinta ba Ta na ficewa daga part ɗin Abba hawayen da take ɓoyewa suka fara zuro mata ta kasa kwatanta halin da take ciki ji take anya ba mafarki ba ne daƙyal ta kai kanta ɓangaren Hajiya Wanda bata kai ga ƙarasa shiga part ɗin ba ta ɗuƙursa ƙasar bishiyar mangwaron da ke farfajiyar gidan tare da rusa kuka tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwar Mahaifiyarta kuka take tamkar ranta zai fita ta kai minti Hamsin a wajen ta na kuka babu alamar tsayawa .

“Ƙanwata”

Marwan ya faɗa da mamaki ya na ƙarasowa inda take wanda da sauri ta ɗago kanta tare da fara pretending goge hawayen hakan ya gagara ai ko

Yaro ya kalleta ya san ta ci kuka”

Tsaye ya yi ya na kallonta da mamaki ya ce “Ibtihal kukan me kike me yake faruwa”

Shiru ta yi ta na ɗasa da kanta ta na mayar da mahawayen da yake ƙara ziraro mata.

Ya na zama gefenta tare da miƙa mata handkchiep ya ce “a tunani na ko zaki ɓoyewa kowa damuwarki bai dace a ce har ni kin ɓoye mawa ba Ibtihal me ke damunki”

A hankali cikin shashsheƙa ta ce “bakomai”

Ya na zama gefenta ya ce “ki faɗamun me ke damunki ƙanwata ko da kina ganin babu abunda zanyi miki sai na taimake ki da shawara”

Daidai lokacin yusuf da ya biyo bayanta ya tunkaro wajen fuskarsa ba alamar annuri ya watsawa Marwan wani kallo tare da cewa”Ubanme kake a nan zaune da matata”

Marwan ya ja tsaki tare da miƙewa ya bar wajen,

Itama ibtihal da sauri ta ruga ta wuce ciki ta na kuka Yusuf yayi ƙwafa tare da bin bayan marwan zai fice ya shaƙosa ya ce “don ubanka uban me ka ce mata”

Ya na masa wani kallo ya ce”ka sakeni kasan dai ba ƙarfina kafi ba da Allah malam “yusuf ya ce “to ko zaka gwada dukan nawa marar kunya ai nariga na gano sonta kake kuma wallahi ƙwalelenka na haramta maka ita har abada domin yanzu haka batun aurenmu ake don haka kar na ƙara ganinka kusa da matata ta”

Marwan ya ja dogon tsaki ya na fincike shaƙarsa da yayi tare da cewa”saika tambaye ta idan na taɓa cewa ina sonta kuma baka isa ba ƙanwata ce dole zanyi mu’amula da ita har abada ko wani ta Aura ba kai ba”

Ya na gama faɗar haka ya fice ya barsa salalo wanda cikin zafin nama ya nufi ɓangaren hajiya ko hajiya da ke masa magana bai kula ba ya nufi ɗakin Ibtihal kwance ya sameta rubda ciki sai rubza kuka ta ce rai ɓace ya ce.

“Ba kuka ba kiyi kukan jini mtswww saikace za a aura mata dodo yanda mata ke nacemun ina wulaƙantasu shine don kin sameni a bulus zaki rainawa kanki wayau ki rainamun kashedi na zo nayi miki daga yau karna ƙara ganinki tare da Marwan ko gaisuwa bance ta ƙara haɗaku ba idan ba haka ba zakiga yanda daga shi har ke ranku zai ɓaci”

Ya na gama faɗar haka ya wulla mata Key ɗin tare da cewa”kin fanshi kanki a wajena Bari naje na samo miki maganin ciwon kai idan kingama koke-koken aure ne dai babu fashi ki sa a ranki kamar har an ɗaura an kai mun ke”

Ya na gama faɗar haka ya fice Ibtihal ta Ƙara sanya kuka Kamar ranta zai fita ita wallahi a yanda takeji muddin da zata samu aljanna ta na fatan Allah ya ɗauki rayuwarta saboda bata tunanin zata iya rayuwar Aure da yusuf shi kansa ba shi da hali ballanta mahaifiyarsa meyasa ƙaddara take zo mata a haka?

ita haka zata ƙare rayuwarta ba ƴanci?meyasa rayuwarta bata da sa’a ne wai?idan ance Aurenta da SHAREF Ƙaddara ne to shikuma Yusuf da me za’a kirasa GANGANCI Ɗayar zuciyarta ta bata amsa domin tabbas ta sake ta auri yusuf ta yi ganganci mafi hatsari a rayuwarta domin yanda take ganin ƙiyayyar ta a idon mahaifiyarsa komai zata iyayi “innalilllahi wa inna ilaihiraji’un ya Allah ka kawomun mafitar kaucewa ƙaddarar nan da ke tunkaro ni Allah idan nayi maka wani laifi na tuba ka yafemun”

Washegari da azababben zazzaɓi da ciwon kai ta tashi ga zuciyarta da takejin ta na mata mugun ciwo ta na harbawa da ƙarfi a ƙarshe dai bata ƙara sanin inda kanta yake ba ko da hajiya ta sameta a haka hankali

tashe ta kira Abba ta sanar dashi da kansa tare da taimakon marwan da yusuf aka kaita asibiti wanda karon farko aka bata gado bayan duk wasu gwaje-gwaje da bincike likita ya tabbatarwa da su Abba ta na Stage ɗin farko na Kamuwa da ciwon zuciya daman tun a wancen lokacin ya faɗa musu ta na gab da kamuwa da ciwon zuciya ayi mata duk abunda zai sanyata farinciki to gashi abunda ba’a son ya faru.

Sosai hankalin Abba ya tashi haka Hajiya da ta kasa daurewa ta sanya kuka ta ce”yaron nan Tsakaninmu da shi da uwarsa saidai Allah ya isa jikata yarinya ƙarama sun ɗaura mata ciwon Zuciya “

Abba ya lallasheta daƙyal ya samu ta yi shiru Aunty Salma ta kwana da ita wanda har zuwa lokacin ba ta Farka ba Ita kanta Aunty salma Hankalinta a mugun tashe yake da samun wannan sabon Labarin haka Safa don kuka ta dingayi daƙyal ta bi Hajiya da su Abba gida don cewa tayi ita ma nan zata kwana,Yusuf ko ya kasa zaune ya kasa Tsaye.

Wasa-wasa washegari har 1:30 Ibtihal ba ta farfaɗo ba Dukkanin ƴan uwanta hankalinsu a matuƙar tashe yake sanin halin rayuwa ya sanya Abba Kiran mom cikin hikima ya sanar da ita idan babu damuwa ta zo ƙasar ko yau ta samu jirgi ta taho,

Hankalin mom ya matuƙar tashi wanda tun a wayar ta ke tambayar wa ya mutu don Allah kar a Ɓoye mata Abba ya ce ba mutuwa ba ce ya lallashe daƙyal,

Ga mamaki har daren ranar Ibtihal ba ta farfaɗo ba wanda su kansu likitocin abun ya fara tsorata su sai ta kai sun sauya mata waje sun maida ta inda ba a barin kowa shiga saidai leƙe duk an zagayeta da na’ouroori,

Safa da ke gefen Mamanta ta ɗora kanta kafaɗarta ta na hawaye itama aunty salmar daurewa ta ke ta na lallashinta lokacin ne mom ta kira aunty salma ta yi

mamakin ganin number ta ta Nigeria bayan ta ɗauka ta ce,

“salma me ke faruwa munzo gidan Hajiya ba kowa Mai gadi ke sanar mun kuna asibiti wanne asibitin me ya samu Hajiyar innalillahi wa inna ilaihiraji’un”

Aunty salma ta ce “Kinga Aunty Nafisa ki kwantar da hankalinki ga Marwan nan yanzu zaizo ya ɗaukeku ya kawoku asibitin”

Suna gama wayar marwan ya tafi ɗauko su mom cikin mintuna Ashirin sai ga su su ukku Ka na kallon mom zaka san tabbas jinin Ibtihal ce domin kamanninsu sun ɓaci baka taɓa cewa mom ta haifi kamar ibtihal,kyakyawa ƴar gayu mai matsakaicin jiki sai wata Matashiyar kyakyawar budurwa wacce zatayi sa’anni da Ibtihal Ta na Riƙe da wata kyakyawar yarinya da tayi bacci ta kwanta a kafaɗarta daga bayansu kuma wata dattijuwa a ƙalla tayi shekaru hamsin itama fara mai kama da su mom sai yanzu na lura tundaga kan su har Aunty salma kamar su ɗaya haka yaransu duk suna kamannin juna saidai wani yafi wani kyawu,

Kamar mom zatayi gudu ta rigo ba wajen da ta nufa sai hajiya da ke zaune ta yi tagumi ta rungumeta ta na Sauke ajiyar zuciya ta ce “Alhamdulillahi da na sameki Lafiya Hajiyata “

kafin ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya hajiya ta shafa bayanta ta na rungumeta kafin ta tsagaita itama aunty Aisha haka ta zo ta rungume Hajiya duk suna sauke ajiyar zuciya Safa ce ta yi saurin Amsar Afren da har lokacin ta ke sharar baccin gajiya,

nan aka ɗan gaggaisa sama-sama don hankalin kowa ba jikinsa ya ke ba mom ce hankalinta ya yi tsananin tashi ganin ta ga kowa banda ibtihal hankali tashe ta kalli hajiya ta ce”Hajiya wa ye ba lafiya”

Hajiya na kama hannunta cikin sigar lallashi ta ce “bana son ki ɗaga hankalinki kinji Ibtihal ce amma insha Allah za ta samu sauƙi nan

7 / 13