IBTIHAL HAUSA NOVELS PDF COMPLETE BY MISS HAJO.docx

Author :  Miss Hajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 36.4K words

ya so ya raba Mom da Turai don haka kawai ba su kwanta masa arai ba amma ranar har faɗa sukayi da mom ta sanya kuka wai baya son ta na mu’amula da mutane haka zata zauna a gari bata da kowa kamar mayya kullum ta na gida yarinyarta harta fara sakewa sakamakon fara alaƙarta da gidan Sam dad baya son Ɓacin ran mom sannan ya na son Farincikinta hakan ya sa ta ƙyaleta har takai ya yafe mata idan zata gidan ba sai ta tambayesa ba,

Turai zuwanta Gidan mom biyu kachal saika ɗauka irin kamammun dattijawan wannan ne hauwa’u ce kullum ta na gidan Sosai mom keyi musu alkhairi Abinci kullum ta dafa sai ta zuba a kula an kai gida Haka sukaci gaba da mu’amula kamar ƴan uwa gefe guda rashin sake samun cikin mom na ta damunsu ita da dad mom ta nemu alfarmar ya sanya Jamila makaranta domin ta na tausaya mata yanda turai ta bata labarin da cikinta Allah yayiwa mijinta mahaifinsu Rasuwa Ɗanta na Farko *SHAREF* halin rayuwa ya sa ta turasa neman kuɗi Lagos da ƙarancin shekaru sai Hauwa’u dukda lokacin budurwa ce da ke tuyar awara don su rufawa junansu asiri sai autarta jamila,

bai musa ba ya sanyata makaramtar da Ibtihal ke ciki amma ibtihal ta fi ta aji sosai don ibtihal na da 9years ta gama primary lokacin ne Mom ta fara laulayin ciki zo kuga murna wajen dad Kullum fatansu Allah ya bar musu cikin ya sauketa lafiya lokacin ne mpm ta ƙara ƙauna da awarar Mama turai kullum ita ta zame mata abinci Tun da na mata faɗan tafiya cin awarar har ya ƙyaleta ya zuba mata ido har Allah ya sauketa lfy ta haifo santalelen baby boy ɗinta mai kama da babanshi sai hasken fatarta da ya ɗauko anan kano akayi suna wanda lokacin su turai ne a tsaye akan komai kowa ya na yabawa da jin daɗin mom ta haɗu da maƙota nagari domin har haihuwa asibiti turai ta kai mom daidai da wankin jini da komai ita tayi,ranar suna yaro ya ci Suna Adam ana ce masa Jinour sosai ke ƙaunar jinour haka Ibtihal na son ƙaninta sai suka taso cikin tsananin ƙaunar juna,

Jiniour na da 6months Allah yayiwa Dadyn su Mom Rasuwa Alhaji Dikko ashe daman ya fi shekara ya na jinya a tsaitsaye amma ko matarsa bai faɗawa ba saboda bayason ya ɗaga musu hankali mutuwar da ta matuƙar girgiza ahalinsa don aunty aisha lokaci da ƙaramin cikinta tashin hankali ya zubar dashi sunyi kuka sunji mutuwar ba kaɗan ba kafin daga baya su haƙura domin daman dukkan mai rai mamaci ne,

Bayan gama takabar Hajiya Nan fa Abba bashir ya ce zai mayar da ita gidansa Abuja Har ya Mata Gini domin Lokacin Abba Bashir ya kama Ƙasa Ɗan majalissar tarayya ne na Ƙasa mai wakiltar Bama har ya ci shekara huɗu aikin aikhairansa da ya yi ya sa suka sake zaɓansa a karo na Biyu fir hajiya taƙiya ta ce ita bazatabar mahaifarta ba nan duka ƴaƴan suka mata cha Shima Adam ya ce ta dawo wajensa kano duka ta ce bata so tabbas bazasu iya bariin mahaifiyarsu ita kaɗai a Bama ba domin duka yaranta Alkah ya jefa mata su Auren nesa Hakan ya sa sukayi metting sukace to tunda bazata koma abuja ba kusa da Abba Bashir to suma dukansu zasu dawo nan wajenta har masu auren sun haƙura da auren tunda tsufa ya kama kamata shima Adam ya haƙura da kasuwancin sa Haka Abba bashir ya haƙura da muƙaminsa ,

Nan fa hankalin hajiya ya tashi taga da gaske suke duka sunyi zaune har sati biyu sunƙi tafiya haka ya sa ta ce ta haƙura ta bisu mafarin dawowar Hajiya Abuja Wanda Hakan sosai yayiwa Abba Bashir da Momy na daɗi tunda suke mazauna Abuja,

Rayuwa ci gaba da tafiya wasa-wasa mama turai sai yazama sai abunda tacewa mom takeji ta daina shawarar komai da ƴan uwanta sai ita Tunda mom take daidai da maganin sammu bata taɓa wankawa ba mahaifiyarta bata taɓa bata ba saidai tace su dage da sallar dare Azkhar suji tsoron Allah sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci Turai ta juyawa da mom tunani itace yau ta bata wannan magani na mallaka wancen na sammu wancen na kaza kuma bata iya musa mata haka zata Amsa sai ta kai mom har Magani a abinci ta ke zubawa Dad matsayin na mallaka ji wata toshewar basira tsakani da Allah wata mallaka ta wuce wacce Allah ya mallaka mata zuciyar Adam wata irin soyayya take nema da tafi wannan to in akace miki magana da sihiri sai a hankali domin saida turai ta gama mallake mom gaba ɗaya wanda bata iya musa mata komai tsananin tsoronta da shakkunta take Ibtihal na da shekara Sha tara ta gama Degree Ɗinta Haɗe da Mastera a nan Maryam Abatcha Kano,

Lokacin mu ko Level one bamu tafi ba “

Wanda lokacin ne Ibtihal ta janye abotarta da Jamila saboda ta fahimta sam bata da kamun kai ga biye-biyen maza tun ta na ƙarama tun ibtihal na mata nasiha har ta koma mata faɗa a ƙarshe ta ce to babu ita ba ita sai ibtihal ta ji tsanar Gidansu Jamila a ranta don ta fahimci Ta fara gurɓatawa mom tunani da Amfani da magungunan Tsubbu saikaga Laya,Rubutu,da sauransu wanda sam ta san ba halayayyar mom ɗin ba ne,

Akwai ranar da Ibtihal ta kama mom na zubawa Dad Magani a abinci ta ce “Gaskiya mom Wlh zanfaɗawa Dad haba kowata Ƙazanta tsakani da Allah sai a baki ki zubawa dad a abinci wannan wlh shirka ce mom nidai zan faɗa masa”

Ranar mom ta shaƙe Ibtihal tayi mata dukan da bata taɓa mata ba tunda ta haifeta ta ce “ki faɗa masa ɗin don ubanki marar kunya dama na daɗe da sanin kinfison mahaifinki a kaina don uwarki idan ban mallakesa ba so kike ya auromun wata ta zo mu jera matsayin kishiyoyi banza sakarya da bata kishin uwarta”

Ibtihal ta ci kukanta ta gaji tun daga ranar suka fara takun saƙa da mom Ita Ibtihal kafiya da taurin kai Ita kuma mom zuciya abu kaɗan ta hauta da duka,

Duk yanda Ibtihal ta so raba mom da su Turai abun ya gagara ta riga ta gano sun gama gamawa da mom ɗin baki ɗaya,

Ganewa da mom ta yi Ibtihal na sauyawa Dad Abinci hakan ya sa mom ke kasawa ta tsare dole sai dad ya ci wanda Ibtihal dole ta haƙura ta bi mom ɗin kawai da Addua don gaba ɗaya a firgice ta ke,

A lokacin ne Babban ɗan turai ya dawo daga lagos ashe shiri sukayi da mahaifiyarsa da yayi ɓadda kama tantiririne sai gashi ya zama kamar ba shi ba Ya koma kamili cikin shigar Mutunci shine sahun farko a masallacin anguwar ga ladabi da biyayya idan zai gaishe da mutum har sai ya duƙa lokacin ne turai tajewa da mom da batun Ta na son Mijinta ya samawa Sharef Aiki ko dako ne a shagunansa ta samu yadawo garin daƙyal chan lagos ɗin ma ba abunda ya samo,

Ba musu mom tayiwa Dad magana da farko musawa yayi kafin daƙyal ta shawo kansa ya amince shima don ya kula da nutsuqar yaron domin suna yawan haɗuwa a masallaci,

Ya fara zuwa shago Dad na ƙara aminta da amanarsa da nutsuwarsa ita daman Ibtihal Tunda ta gansa sau ɗaya bai kwanta mata a rai ba sanin bata da alaƙa dashi ya sanya ta watsar da batunsa kamar wasa Sharef ya fara biɗar soyayyar Ibtihal wanda sam ta nuna bata sonsa Tsananin soyayya ya ke nuna mata Magiya kuka Gabanta ya sha yi ba adadi akan idan ya rasata zai iya rasa ransa amma da yake Ibtihal kafiya ne da ita ta ce “bata sonsa dukda lokacin halayyartace sam maza ba sa gabanta Ko a sch ba irin samarin da basa bibiyarta amma bata taɓa bawa namiji number ta Yaya yusuf babban Ɗan Abba Bishir shima daga gwada ya na sonta ƙarshe ta yi blocking nasa gaisawar zumuncin ma suka daina Lokacin da mama turai tajewa da mom batun Sharef na son Ƴarta Da farko tayi jim kamar ba ta amince aiko cikin kwana ukku sukaje suka ƙara shiri saigashi mom ita taje musu da batun a karo na biyu,Nan fa mom ta samu Ibtihal da batun ta ce “wlh bata sonsa “

Mom ta ce “Wallahi sai kin aure sa saidai idan ba na Raye “

Ibtihal ta sa kuka ta ce “Ni wlh bazan aure sa ba”

Mom ta ce”Da ko na tsine miki kin lalace akan dai ki ce bazaki Auri Ɗan Mama Turai ba “

Ibtihal ta sanya kuka ta na rugawa jikin Dad ɗinta lokacin da ya shigo cike da taɓara ta ce “Wlh Dad ba na sonsa don Allah karka Yarda “

Dad na shafa bayanta ya ce”Calm down daugher kinsan ba abunda na tsana Sama da fushinki akanme kike magana”

Cikin kuka ta ce”Dad wai mom ce dole sai na Auri Yaron Mama turai nikuma bana sonsa dad wlh sam baya burgeni”

Dad na haɗe fuska ya harari mom da ke huci ya ce”Nafisa”!

Ta ce”Adam”…………….✍🏽

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~

*HAJARA L SADEQ*

(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼

Auren wata tara

Ni da yaya arman

Matar uncle

Najmat abiy

Komai mukaddari ne

Khadijatul Sabren

Ribar so

Mata ta ce

*And now*

*IBTIHAL*

*Last Free page*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*15*

Ta ce “Adam”

Dad ya zuba mata idanu tunda ya ke da ita bata taɓa faɗar sunansa ba gatsal sai ranar ya ce “Nafisa ke ce da faɗin sunana yau gatsal?

Ta ce “ka na da wani sunan ne to bayan wannan “

Ya ce “Babu Zanyi miki warning karki ƙara takurawa ƴata muddin kina son Mu shirya da ke a gidannan “

Mom ta ja tsaki ta ce “Ƴarmu zakace dai ai ba kai kaɗai kake da iko da ita ba “

Ya ce “hmmm aiko zaki sha mamaki muddin kikace zaki takurawa Ibtihal a gidan nan ke har kin isa ki tilasta mata Auren wanda Bata so Ƴata ni Adam Za ayiwa auren dole anya ma kina cikin hayyacinki kuwa ke ko kina hauka akace miki zanyiwa ƴata auren dole zaki yarda”?

Mom ta shaƙu ta ce “Ai wlh baka isa ba ni na haifeta ni nake da iko da ƴata ko kai kayimun naƙudar haihuwarta don haka wanda nake so zata aura idan ba haka ba Wlh sai kunyi mamakin me zanyi”

Dad ya kula kamar ma a zare take hakan ya sa ya ƙyaleta ya lallashi ƴarsa tare da kwantar mata da hankali,

Washegari dad na ficewa mom ta sa ƙafa ta tafi gidan mama turai cikin kuka ta ce “Mama wlh duk mallakar da nakeyiwa Dadyn Ibtihal ta zube yau karkiga rashin mutuncin da yayimun,

Mama turai ta ce “Ai malam ya ce Mijin nan naki da ƴarki halinsu Ɗaya taurin kan tsiya garesu abu ya ci su ya na da haɗarin gaske tsaye suke da ibada Dole ko na rana ɗaya sai an shashantar da su Azkhar kafin a ci nasara a kansu,

Mom ta ce mama ayi hakan ni ko me za ayu indai zasu amince ayi auren nan ayi”

Ta ce “da farko a fara da mahaifinta kafin Yarinyar Da ƙarfe nawa yake Dawowa Cin Abincin rana?

Ta ce “Daga Ƙarfe Ukku sai la’asr ya ke fita”

Ta ce”Yawwa to zaki ja Ra’ayinsa yaƙi komawa shago sallar la’asr ma Karki bari ya fita kija Ra’ayinsa sosai kuyi tarayya kafin nan zan baki maganin Bacci mai ƙarfi wanda kuna gama mu’amula bacci zai ɗauke sa Da Najasa jikinsa nikuma saiki gaggauta kirana idan kin tabbatar hakan ya faru sai na maza naje na samu malam ayi aikin ko abu kika aje Idan ba kince ya ƙetara ba wlh bazai taɓa iya ƙetarawa ba sannan za a shashantar dashi Addini zai dAina ibadoji sallar biyar ma da azumi sai don ta zame masa dole zai dingayi kinga ta nan zamuyi amfani ya amince da batun auren ke kuma Ki mallakesa har abada kinga mun jefa tauntsu biyu da dutse ba ke ba kishiya har gaban Agaba”

Mom tayi shiru Mama turai ta ce “idan kuma bakya so ba dole sai a bari “

Ta ce “a a ayi mama gobe insha Allah zan samu hakan ta faru”

Ta ce “yawwa ko ke fa ƴata ai zansa malam yayi masa aikin da har abada ba ke ba kishiya har abada kallon maza ma zaidinga yiwa duk wata ƴa mace”

A ranar mom ta lallaɓa dad suka shirya ta ce ta janye batun auren suka koma rayuwa kamar da Ibtihal ko ba ta damu kanta ba don tasan yanda Dad ɗinta ke sonta bazai taɓa bari ayi mata auren dole ba ,

Washegari ta aiwatar da duk yanda sukayi da Turai A washegarin ranar komai ya lalace Domin Dad ya goyama Mom baya akan Ibtihal ta Auri Sharef ranar ibtihal ta ci kuka kamar ranta zai fita tsaf gani take an sauya mata dad cikin tsananin tashin hankali taje gidan Turai ta na kuka ta lallaɓeta akan don Allah tayiwa su mom ɗinta Magana su Zanye wlh bata son Sharef bazata aure sa ba “

Mama turai cike da bariki ta kwantar mata da hankali ta ce “karta damu hakan ma bazata yiwu ba”

Mom ta cije Ibtihal ta cije ta kafe wlh bata son sharef “mom ta kalleta ta ce “Wlh Muddin baki Auri sharef ba saidai na Tsine miki ki shiga Duniya Dad ma Da ke shigowa ya ce “ba tsinuwarki kawai za ta samu ba har da tawa domin nima muddin ba ta Auri zaɓinmu ba matsayinmu na iyayenki da muka haifeki muka kula da ke amma Alfarma ɗaya ki kasa mana to fa saidai ki sauya iyaye”

Ibtihal na kuka ta ce”Dad Ni ce Ibtihal ɗinka da ka ke Fifita Farincikina fiye da naka Dad kana Fifita buƙata ta akan ta ka ba ka ƙaunar ganin ɗigon damuwa a raina dad Anya ba chanzamun kai akayi ba”

Ya ce “ni ne ba wani ba Ibtihal kinsan da hakan kika kasa Biya mana tamu buƙatar karo ɗaya Tak”

Ta na kuka ta ce”Auren Sharef shine kawai Abunda zanyi na Sanyaku farinciki “

Ya ce “Tabbas hakan da zakiyi shine Alfarma ɗaya a duniya da zaki mana na darajar haihuwarki da mukayi”

Ta na shafce hawaye ta na jin zuciyarta tamkar za ta bar gangar jikinta ta ce “Na Amince ko da hakan zai zama silar mutuwa ta”

Daga mom har dad ji sukai kamar an sauke musu wani nauyi mom na rungumeta ta ce “Insha Allah hakan saida yazama silar farincikinki ba Baƙincikinki ba “

Dad ma ya ce “Ina matuƙar alfahari da ke ƴata “

Ibtihal ko daga mom har dad tsananin haushinsu take ji a ranta Ko da ta shiga ɗaki kuka ta sanya ta rasa ina zata saka ranta haka Auren Dole ya ke dama?

Irin wannan raɗaɗin Wanda hakan ta faru da su suke ji ,

Ba ta da mai lalllashinta Sam batajin zata iya bijirewa iyayenta har biyu kuma gatanta a karo na farko a rayuwarta saidai me haƙuri da juriya take ƙoƙarin Yi amma hakan ya gagara zuciyarta zafi da tafarfasa takeji Ga bata da ƴar uwa mace da zata rungume ta sanyawa kuka su jajinta Bata da ita cousin Ɗinta da sukayi sabo Safa Da Sajida sunyi mata nisa batajin zata iya ma faɗa musu saboda tasan dole zasu faɗawa Aunty’s ɗinta da hajiya kuma bazasu yarda hakan ta faru ba mom da dad zasuyi fushi da ita kuma Allah ma zaiyi fushi da ita akan bijirewa Iyayenta da tayi bata da mafitar da ta wuce haƙuri da wannan ƙaddarar da ta Tunkaro ta,

Radaɗin rashin ƴar uwa mace take ji jiniour yaro ne ya na ma boarding school Turkish Kaduna kamar yanda mom ta umarta aka Kaishi chan bisa Umarnin Turai tsananin tsanar turai Ibtihal take ji a cikin Ranta,

Wasa-wasa Ibtihal ta zama ƴar kallo domin ta na ji ta na gani mom da dad suka fara shirin bikinta Aka sanya Aure wata Biyu Kachal Ranar Ibtihal ta sha kuka ta na kwance azababben zazzaɓi ya rufeta sajida ta kirata ta na mata tsiyar Ba suji soyayya ba Sai aure kawai haka nima na kirata ina mata tsiyar munafuka ashe ta na gefe ta na soyewa ta ke nuna ita ba ruwanta da maza bata bamu Amsa ba sai kashe wayarta da tayi,

Ranar da Sharef ya zo zance Ibtihal ƙin fita tayi ba yanda mom batayi ba amma fir ta ƙiya ta sanya kuka Ganin haka ya sa ta ƙyaleta ta ce ya yi haƙuri shi da za a kai masa ita ma baki ɗaya,

Ibtihal ta na gefe bata sanin wainar da ake toyawa ta ƙulla alaƙa da zaman ɗaki Damuwa da ƙunci duk sun mamaye zuciyarta su mom kawai suke Bidirinsu,

Kamar yanda Al’adar su Mom Ɗinmu ya ke na Shuwa,Arab Kuma ya haɗo da Maiduguri garin gyara ,

mai gyara ta musamman daga maiduguri a dangin su hajiya su mom ɗinmu suka tafi tare da ita tun ana saura sati Ɗaya biiki domin ta kimtsa Amarya Amma fir Ibtihal ta ƙiya mom ta mata bori ta dinga rafka kuka ita wlh ba abunda za ta sha aka dinga dabi da ita Amma fir taƙiya ganin ta na shirin tona mata asiri domin ba wanda yasan Auren dole za a mata gashi ta ga Aunty Aisha ta fara ankarewa ya sanya mom fusgewa da cewa,

“Wlh Aunty Haka yarinyar nan take tun ta na yarinya bata shan magani ko wani iri ta gwammace a mata allura ko bata lfy uwa

12 / 13