Author : Miss Hajo Category : Romantic Hausa Novels
akan tayi haƙuri ta ɗauki ƙaddara wanda da zai tafi da kuka suka rabu da jikan nasa saboda kusan duk sati biyu daman sai ya zo ganinsa shi da malam mutari hakan ya sa ya saba dashi dukda yaron ya taso ba ba me son magana ba,
Ranar da malam ya cika kwana bakwai da mutuwa sukace a raba gado kowa ya kama gabansa a washegari ne abun mamaki saiga Malek ya zo musu ta’aziya wanda hajara ta tabbatar tirsasawar mahaifinsa ne,
Tunda ya zo idonsa akan yaron amma ya kasa cewa komai da zai tafi ya miƙawa hajara takarda tare da tafiya abunsa wamda ta na buɗewa ta ga takardar saki ukku ce ta ji ba daɗi amma ta wani ɓangaren taji daɗin hakan ko ba komai ya raba ta da nauyin auren sa da bata san matsayinsa ba,
An raba gado anba kowa nasa wanda manyan mazan ƴaƴan haule duk suka handame gonaki da sauran kadarorin malam bisa zalunci wanda hakan ya haifar da gagarumin tashin hankali tsakaninsu don marariya da ƴaƴanta sukace basu yarda ba nan aka dinga rigimgimu a ƙarshe dai ba yanda suka iya dole suka haƙura ita daman hajara ƴar kallo ce domin raɗaɗin mutuwar mahaifinta ce kawai a ranta ta ƙara zama shiru-shiru akan da an raba gado wanda ita saidai ma tace an sammata wani fegi ƙwara ɗaya aka bata wanda ita kanta tasan manya manyan gonakin malam sunfi Ashirin banda gidaje da feguna da rumbunan kayayyakin gona batace komai ba domin ba dukiya ba ce a gabanta,.
Nan fa sukace dole zata bar musu gida domin bata da gado a gidan ranar hajara ta yi kukan da bata taɓa irin sa ba ranar ta san yanda rayuwar maraici take ta na ji ta na gani aka rabata da gidan ubanta korar wulaƙanci da ƙasƙanci da ita da yaronta a ranar rasa wajen kwana tayi ƴan uwanta aurarru a gari dukkaninsu ta je gidansu akan su taimaketa da wajen kwana na yau ɗaya kafin gobe tayi shawarar wajen zuwa amma suka hanata ranar sai a tashar mota ta kwana washegari sanin bata da mafita ga ba kuɗi hannunta hakan ya sanya ta je ta nemu dillalai ta sayar da ƙaramun fegin gadon ta ganin a gaggauce take akayi mata cinikin wulaƙanci ta na buƙatar kuɗi hakan ya sa dole ta haƙura ta sayar ta amsa kuɗin.
tunanin wajen zuwa ta ke kawai hakanan zuciyar ta bata da ta tafi Kaduna domin lokacin da tayi karatu a zaria suna ɗan zuwa kaduna haka nan tsarin garin da yanda mutanen garin ke mu’amulansu ya matuƙar burgeta domin bata da mafitar da ya wuce haka indai ta na neman rufin asirinta da na ɗanta ranar sai sha ɗayan dare ta isa garin Kaduna,
A ranar ma a tashar mota ta kwana in taƙaita miki labarin ƴata domin ya na da yawa hajara ta yi mabanbanta sana’oi anan Kaduna domin rufawa kanta asiri Dukda ta sha fama saboda kyawunta amma haka ta tsare mutuncinta da na ɗanta aikatau ne a gida je kawai batayi ba amma sana’a wankau ,guga ,Ba irin sana’ar da batayi ba domin a ƙuɗaɗen da tazo da shi ta kama hayar ɗaki ɗaya a wani gida su bakwai sauran kuɗin kuma ta fara juyawa,
rayuwa na tafiya da daɗi ba daɗi kullum cikin faɗi tashin neman halak take dukda irin gidan da take amma bata shiga harkar kowa haka shima Marzouq ya taso da ƙwazo tun ya na shekara Shida ya san neman na kansa tun hajara na masa faɗa har ta haƙura shi ne sayar da bread,Sayar da pure water tashar mota duk don ya taimakawa mahaifiyarsa domin duk lokacin da yaga ta na wahalar nan ya najin Ɗaci a cikin ransa .
watarana kwatsam hajara ta ji sanarwa a gidan radio akan ana neman masu takardun karatu tundaga masu sakandire har zuwa ,Digiri duk wani mai takardun ya zo ana nemansa a sakateriya ranar litinin”
Ba tare da tunanin zata samu ba haka nan dai ta je ta kai takardunta domin daman suna tare da ita sam wahala ta ma mantar da ita tayi wani karatu,
Allah mai iko sai gashi fitowar farko ta samu aiki domin lokacin masu irin takardunsu ake nema basu da yawa bare ita da takardarta tayi mugun kyau,
Ranar da ta amsa offer ɗinta a hannu tayi matuƙar murna da farinciki ta godewa Allah babu iyaka ,
Ta fara aikinta cikin nasara da kwarewa a wata makarantar sakandire,
Mace ce mai kwazo da ta saba da nema ko da ta samu aiki sai sana’arta ta ƙara bunƙasa ta dinga sarin atamfofi,shaddoji,Takalma,yadika,ta na rabawa sauran ma’aikata da anyi albashi su haɗa mata kuɗinta gefe guda ta na kula da karatun ɗanta da ta sauya masa makaranta ta maida sa ta kuɗi mai kyau.
Lokacin da Marzouq ya gama sakandire Hajara ba ƙaramun cigaba ta samu ba ta saya gida ta saya mota hakan ya sa ta buɗewa Marzouq shagon atamfofi da shaddoji da yadika ganin ya zama saurayi kafin Result ɗinsu ya fito ta sama masa Addmission ya fara sana’a ,
dukda yanda ƴan mata suka masa chaaa saboda ganin kyakyawan saurayi ɗan ƙwalisa ba ya kula kowa kamar yanda ya ke shiru shiru in kaga dariyarsa da fara’arsa ko maganarsa doguwa to da mahaifiyarsa ne Kallo ɗaya zakayi masa kasan akwai abu a ransa domin mahaifiyarsa ba ta ɓoye masa komai ba game da tarihinsa da nata baice komai ba amma tana ganin tsananin tsanar mahaifinsa a ransa ba irin yanda batayi ba akan ya shirya ta kaisa wajen Kakansa saboda halin rayuwa idan itace yau ba itace gobe ba amma fir ya ƙiya hakanan ta haƙura domin ita ɗinma kanta bazatace ga inda gidan kakan nasa yake ba domin duk zaman da tayi bata taɓa zuwa koda sau ɗaya ba ta aje batun a gefe dukda a ranta ba ta manta halaccin Alhaji Marzouq a garesu ba.
*MARZOUQ MALEK*
Shine sunan da ake kiransa a makaranta dukda baya son haɗa sunansa da malek da ake haɗasa ya so sunan kakansa na wajen uwa aka sanya masa amma fir hajara ta ƙiya saboda darajar kakansa ,
Sosai take samun cigaba a wajen aiki gefe guda marzouq na kula da shagon da ta buɗe masa,
A haka jarabawarsu tayi kyau haka Jamb Ɗinsa yayi mugun cin da saida aka gayyacesa interview bayan angama masa aka tabbatar da eh yaron da gaske shi ya ci yaro ne mai matuƙar ƙwazo a cikin wanda sukayi masa interview din akwai wani DR NAZIR wanda tunda ya ɗora idonsa akan yaron ya ji ya matuƙar burgesa sannan ya na ganin kamar akwai Kamannin Hajara a fuskar yaron wanda ya kasa mantata har yanzu……..✍🏽
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
🪅*IBTIHAL*🪅
~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)
MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI 07026166536*
*DEAZATOH Tawa ƴar amana shafin nan naki ne kyauta Alkhairin Allah ya kai maki har gadon baccinki nasara ta lulluɓe rayuwarki yakawo mana twins mu zo Kd shan suna*😘😘😘😘
*DEDICATED TO MY HUSBAND*
🅿️…………………………..*07*
A lokacin Dr Nazir ya basa number sa saboda lokacin waya ta zo har ta ɗan fara wadata akan in yana buƙatar wani taimako ya tuntuɓesa zai taimaka masa sosai insha Allah shima ya amsa number sa,
A hankali shaƙuwa ta shiga tsakaninsa da DR Nazir ya zame masa tamkar uba mai basa shawara zuwa lokacin Hajara ba ta taɓa haɗuwa da DR nazir ba ta na jin dai labarinsa a wajen ɗanta da yanda ya ke basa shawarwari akan karatunsa.
kwatsam rana ɗaya DR nazir ya kira Marzouq akan ya sama masa Schoolership a Ƙasar Switzerland koda Marzouq ya zowa da hajara da labarin rumgumesa ta yi ta na masa kukan farinciki shi a ransa baya son tafiyar domin baya son abunda zaiyi nisa da shi da mahaifiyarsa amma ganin yanda ta nuna farincikin ta akan hakan sai yaji ƙwarin gwuiwar hakan.
Dole hajara ta buƙaci da ya kaita har gidan DR Nazir ɗinnan dai yau tayi masa godiya ,
ya rakata har gidan wanda lokacin da sukayi ido da juna ba ƙaramun mamaki ne ya kama su ba ganin juna Hajara ta nuna sa ta ce Nazir shima ya na nunata da zallar mamaki ya ce Hajara Daman zan sake ganinki ,
sai gani sukayi suna hawaye Marzouq ya tsaya kallon ikon Allah ya na mamakin sanda suka san juna ,
Hajara kuka ta sa domin bata taɓa tunanin sake ganin Nazir a rayuwarta ba dukda duk shekarun nan bata manta da shi ba da irin soyayyar da sukayi a lokacin ne ya ke sanar mata kamar yanda suka tsara kafin ta bar makaranta don tun lokacin bayan sati ukku ya je tare da iyayensa har wajen mahaifinta kamar yanda ta kwatanta masa aka shaida musu ta yi aure ranar ya yi kukan da baitaba irinsa ba ya yi jinyar watanni kafin mahaifinsa ya basa haƙuri ya haɗasa Aure da ƴar uwarsa daman kuma ta na sonsa shima kuma ya haƙura ya amsheta hannu bibbiyu ta haifa masa yara biyu duk Maza Ashraf da Sadeq kafin shekara ukku baya Allah yayi mata rasuwa sanadin ciwon Hanta,
Itama hajara ba ta ɓoye masa komai ba da ya shafi rayuwarta da ɗanta ya matuƙar tausaya mata kafin a ƙarshe ya nemu buƙatar aurenta daƙyal ya sha wahala kafin ta amince dukda itama hada jan aji da tsoron abunda ya faru da ita a baya kafin ta amince bayan sunje Haɗeja ta nema wasu daga cikin dangin mahaifinta suka ɗaura musu aure wanda lokacin sosai tayi mamakin halin da ta samu matan babanta da ƴan uwanta nan take samun labarin shafa tayi aure a katsina ta so ta taimaka musu amma hassada ta hanasu karɓa dukda suna buƙata domin sunyi mamakin yanda suka ganta a tunaninsu zuwa yanzu ta gama lalacewa domin a tunaninsu yanda suka koreta bata da wajen zuwa zuwa yanzu ta zama magajiyar karuwai Sai suka ga saɓanin haka,
Sai a lokacin ne Hajara ta san ta yi Aure domin Kulawa tattali soyayya kawai take samu daga wajen mijinta har mantawa suke da shekarunsu kamar su cinye juna don ƙauna to daman ba wasu yara gare su ba Sadeq ya na Karatu a india domin tsakaninsa da Ashraf shekara biyu ne Ashraf ya basa saika ɗauka ma ƴan biyu ne don sadeq ya fi Ashraf girman jiki hakan yasa ajinsu ɗaya a karatu don sadeq ya ma rigasa tafiya india da wata ukku.
Ashraf ma tare da Marzouq sun wuce switzerland tare wanda suka zama aminai tamkar uwa ɗaya uba ɗaya domin sa’anni ne haka suka ɗauki hajara tamkar uwa itama ta ɗauke su tamkar ita ta haife su ba ta banbanta su da ɗanta,
Tafiyar Marzouq karatu ba ƙaramun cigaba ta samar musu dashi ba domin overoller ya ke fitowa dashi a result Gefe guda kuma ya fara neman kuɗi wanda kafin ka ce me ya tara arziƙi mai yawan gaske ,
Mechanical engineering ya ke karanta Hakan ya ƙara haɓɓaka kasuwancinsa ya na kammala degree dinsa ya wuce china yo wani course game da koyon ƙera mota da babura da ya fara koya a nan shekara biyu ya yi ya gama iya komai har ma ya fi wanda suka koya masa ƙwarewa saboda Marzouq mutum ne mai kaifin basira .
a switzerland ya buɗe componyn ƙera ababen hawa wanda kafin kace me wajen ya haɓaka sai ya zama shi da nigeria sai dai ya ga iyayensa ya koma Domin Shima DR Nazir ya samu cigaba lokacin ya zama minister ilimi na ƙasa.
a lokacin idan ka kalli Hajara ba ka taɓa cewa ta taɓa shiga damuwa a baya ta zama hamshaƙiyar mace kyawunta da kwarjininta na ƙaruwa .
gefe guda ta na aikinta wanda zuwa lokacin tuni ta samu cigaba da matsayi babba a jahar ta kaduna dawowarsu abuja baisa ta bar aikinta ba domin lokacin Director ce guda a ministry of education da ke jahar ta Kaduna,
Sadeq ya yi Aure don ya riga su Aure dukda sun girmeshi Ashraf ma yana ta so ya yi amma ya ce shi sai tare da Marzouq zaiyi wanda sun sha faɗa da marzouq akan shi ya je ya yi aurensa shi mata ba sa gabansa amma sai ya ce bazaiyi ba saidai suyi tare .
itama mahaifiyarsa sai hankalinta ya karkata akan son ganin sunyi auren duba da yanda zamani ya lalace,Nan fa ake yinta domin Marzouq ba shi da budurwa bai taɓa kula duk ƴan matan da suke bibiyarsa ba Ya ce kawai Ummy ta zaɓa masa duk wacce ta mata zai amsa kasancewar Ummy ya ke ce mata hakan yasa kowa ya tashi da hakan har su Ashraf.
Kafin ya koma Switzerland Mahaifiyarsa ta haɗasa da Mariya a nan garin abuja a ta ke duba da yanayin ladabin yarinyar ƴar maƙotansu ce amma kullum sai ta zo gaishe ta wanda bata san saboda Marzouq ta ke hakan ba daman saboda tsananin son da ta ke masa a tunaninta hakan zai sa mahaifiyarsa ta haɗa su aure sai gashi Allah ya cika mata burinta.
koda mahaifiyarsa ta zo masa da batun ya amshe ta ba don ta kwanta masa a rai ba sai kawai don son ya cikawa mahaifiyarsa burinta sannan bayajin zai iya taɓa bijirewa umarninta har abada.
bayan duk bincike da akayi aka gano yarinyar bata da wata makusa ƴar wani ƙauye ce da ke jahar sokoto iyayenta ba su da ƙarfi suka kawo ta wajen ƴar uwar babanta matsayin riƙo tafi da aikatau.
ta sata ta yi boko da islamiya amma bakinta sakandire lokacin yarinya mai nutsuwa da kawaici lokacin ma ajara ma hajara ta san ba ƴar gidan ba ce .
ba ɓata lokaci aka sha shagalin bikinsu tare da Ashraf da budurwarsa Saudat da tun a switzerland suka haɗu a makaranta itakuma ƴar masu kuɗi ce anan Abuja bayan aure Marzouq ya koma da matarsa Switzerland saboda kasuwancinsa duk suna chan ba yabo ba fallasa a zaman su ya na nuna mata kulawa saboda yanda ta ke nuna masa soyayya dole ya haƙura ya amshe ta hannu biyu suka cigaba da rayuwa kamar ko wasu ma’aurata ,
Lokaci kaɗan Marzouq ya zama hamshaƙin attajiri da Ya yi suna A chan ƙasar da ma nan ƙasa nigeria domin ya gina katafaren componyn sayar da motoci a nan Abuja saida ya zama ya na da componynnykan Ababen hawa goma a ƙasashen duniya ya mallaki manyan gidaje da kadarori tare da jiragen sama guda biyu ana masa jigilar ƙasashen duniya ya zama attajiri wanda duk inda ka ce *MARZOUQ MALEK* a Ƙasar nan to fa ɗaiɗaiku ne ba su sansa ba musamman a fannin taimakon al’umma.
lokacin ne mahaifiyarsa ta buƙaci da ya dawo nigeria da zama ta na buƙatarsa a kusa da ita a katafaren gidan sa da ya gina ya sauka lokacin shekararsu biyar da aure ba haihuwa dukda yanda yake tsananin so da buƙatar haihuwar haka ya daure bai furta ba a bayan dawowarsa ne ya gina katafaren gidan marayun nan wanda lokacin ni ina ɗaya daga cikin amintacciyar mai aikin Hajiya Hajara hakan ya sa ta buƙaci da na dawo nan naci gaba da tayasa kula da yaran domin ta aminta da ni kuma duk labaran nan da nake baki ita ta bani su da bakinta,
na manta ban sanar miki ba Hajiya ta haifi ƴa ɗaya da Alhaji Nazir mai suna Rabi’atu ma’ana sunan mahaifiyar hajiya ana ce mata Lena wanda yanzu zakuyi sa’anni yarinyace da ta taso cikin gatan uwa da uba da yayyinta domin ko ƙuda basa so ya taɓa ta musamman Marzouq da ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata,kodan kasancewarta tilon ƴa mace a cikinsu hakan ya sa suke mata soyayya ta musamman suka ɗan sangarta ta da shagwaɓa.
Lokacin ne fa Mariya ta dawo da sabon salon raini ita matar attajiri magana ma daɗyal ta ke ga wulaƙanta na ƙasa da ita amma duk iskancinta batayiwa Hajiya Hajara domin duk hakurinta da kawaici to fa ba ta ɗaukar raini ko ƙadan sannan ta na da kwarjini,.
Suncika shekara takwas da Aure wanda zuwa lokacin Hankalin Hajara ya matuƙar tashi game da rashin haihuwar don lokacin sadeq yaransa ukku Ashraf na da biyu kuma ta na kula da yanda Marzouq ke ƙaunar yaran ta san na daga dalilin son yara ne ya ja shi ga ra’ayin buɗe gidan marayu a nan ne ta ke ba sa shawarar da ta na son ya ƙara aure ba tare da ta faɗa masa dalilinta na hakan ba,
Da farko ya shashantar da maganar wanda a ƙarshe ya amince amma akan ta nema masa kamar yanda ta nema masa a baya haka ko akayi Hajiya hajara tayi matuƙar bincike a wannan karon kafin ta nema masa ƴar gidan wata Aminiyarta Hajiya Bara’atu a nan Abuja gidan dattako da kamala.
Aishatou kallo ɗaya tayiwa Marzouq ta ga ya yi mugun tafiya da imanin ta shima kuma ba laifi yarinyar ta ɗanyi masa akayi aure bayan hauka da mariya ta sha ba irin haukan da batayi ba akan hakan a ƙarshe uwar riƙonta ta lallasheta lafin ta fara aiki da shawarar mugayen sabbin abokan da ta yi .
da farko Hajara ta so a raba musu gida ga mamakinsu na dawowar mariya daidai itace hada bada haƙuri akan borin da ta dingayi zaka ɗauka tubar gaskiya ta yi sai hankakinsu duk ya kwanta akan haɗa musu gida mariya ta danne kishi ta amshi Aishato hannu biyu to ita daman ba mai fitina ba ce hakan ya sa suka zauna lafiya wanda hakan ya kwantarwa da mijinsu