Author : Miss Hajo Category : Romantic Hausa Novels
karatu da kuma abunda take so ya sanya mahaifinsu aminta ya turata karatu a A B U zaria ,
nan fa cheche kuce ya ƙaru a kanta aka dinga ƙananun maganganu akan malam mutari ya tura ƴarsa karuwaci maganganu kala-kala wanda daga shi har ƴar sa suka toshe kunnansu domin sunsan ba haka ba ne.
Lokacin da Hajara ta gama karatun degiri ɗinta a zaria ranar mahaifinta ya yi farinciki matuƙa adduo’i da fatan nasara da albarka ko ba irin wanda baiyi mata ba.
A lokacin ne wani Aminininsa wanda hulɗar kasuwanci ta hana su ya na sayan kayan nomansa idan ya girbe sunkai shekaru Ashirin suna tare mai suna Alhaji MARZOUQ ya nemawa ɗansa auren Hajara Ba musu malam mutari ya amsa masa da ya ba ɗansa MALEK Auren Hajara amma sai ya tuntuɓeta idan ta amince domin ba zai mata dole ba.
Lokacin da mahaifinta ya zo mata da batun ta ji ba daɗi a ranta domin akwai saurayinta Nazir da sukayi soyayya da shi ya ke matuƙar ƙaunarta ita ma ta ke tsananin sonsa domin ya shafe kusan shekara biyu ya na magiyar ta so shi wanda daƙyal a ƙarshe itama ta faɗa soyayyarsa ba tare da ta shiryawa hakan ba ,
Wanda kafin su rabu ta kwatanta masa har gidansu saboda lokacin babu waya wanda sunyi alƙawarin idan ta koma da sati ukku su zo neman aurenta sannan za ta sanar da mahaifinta game da shi ,
asalinsa lecturer dinsu ne ɗan asalin Kaduna ne dukda son da take yiwa nazir haka ta haƙura ta kasa furtawa domin tayiwa mahaifinta biyayya ,
Abun yazo da gaggawa domin a satin aka Ɗaura musu aure da Malek wanda basu taɓa ganin juna ba ko da a hoto Wanda baƙinciki kamar ya kashe ƴan ubansu da kishiyoyi domin abu ne da ya zo musu a bazata domin a kaf ƴaƴansu babu wanda ya auri kamar ɗan gidan alhaji Marzouq saboda dukkaninsu kusan auren wahala da ci da kai sukayi duk sun jeme sun lalace hakan ya ƙara wutar ƙiyayyar hajara da malam mutari a ransu akan cewa daman yafi son hajara akan duka sauran ƴaƴan su shiyasa bai haɗa kowa da attajiri ba sai ita wanda yayi kamar ma baisan me suke ba,,
An kai hajara gidan mijinta da ke Taraunin Jahar Kanon dabo bisa rakiyar Dangin uwa da na uba don dangin mahaifiyarta na raɗɗa duk an aika musu kuma sunzo sai shafa’atu ƙanwarta kaɗai domin kaf gidan babu wanda ya rakata ta sha matuƙar kukan rabuwa da babanta ta na kuka haka kowa ya tafi ya barta ta sha kuka ta gaji kafin ta haƙura,
Gida ne aka kaita daidai wadaidar mai rufin asiri ɗaki ciki da falo sai baranda da kitchen da banɗaki dukkanin gidan shafe da sumunti wanda lokacin sai wane da wane.
Mahaifinta yayi matuƙar ƙoƙari domin ba abunda bai zuba mata ba na ƴaƴan gata a lokaci,
Tsoro ne ya kamata ganin dare ya tsala ita kaɗai a gida ba alamar shigowar Ango haka ɓarawon bacci ya saceta ba tare da ta shiryawa hakan ba ,
Washegari wasu daga cikin danginsa suka zo wanda ta kula da kallon ƙiyayya da ƙasƙancin da suke mata dukda tasan ta fi su komai kyau wayewa ilimi yawan dukiya kawai zasu gwada mata dukda daidai rufin asiri Allah yayi musu suma saidai su nuna musu su a birni suke dukda suma garin su ba ƙauye ba ne,
Saida Hajara ta yi sati babu Malek ba labarin sa tun ta na tsoro da fargaba har ta haƙura ita kaɗai ta ke kwana abincin gara da komai na buƙata daman mahaifinta ya haɗo ta da su kuma da sadakinta da ya damƙa mata a hannu hakan ya sa ba ta sha wata wahala ba ,gashi ba laifi maƙwabciyarta da suke katanga ɗaya mai suna Farida ta na leƙota akai akai ta kula ba ta da matsala ko kaɗan ga su kuma sa’anni hakan yasa lokaci kaɗan sukayi sabo.
Saida ta cika sati ukku wani Dare har ta fara bacci ta ji mutum na bugun tashinta da ƙarfi da mugun tsorace ta tashi ta na Dunƙulewa waje guda tare da fara salati ta na sanya kuka don a tunaninta ɓarawo ne,
Da Torchlight ɗin da ke hannunsa ya dalleta kafin ya zaro idanu sosai ya na ƙara haskata cikin magana mai kama da ta ƴan maye ya ce”kaii daman wannan kyakyawar BaBa ya auramun “
Sosai tsoro ya kama Hajara kar dai wannan ne mijinta yana magana ya na tangaɗi banda warin giya ba abunda ya ke .
Tsorata ya sanyata tashi za ta ruga ya chafko ta daren ranar ta ƙarfi ya mayar da hajara cikakkiyar matarsa cike da zalunci da mugunta domin ba ya a hayyacinsa ya aikata hakan wanda daga lokacin wani dogon bacci ya kwashe sa wanda ita kuma suma ne ta yi.
Sai ƙarfe takwas na safe ya farka ya na mamakin me ya kawo sa gidan ya dai tuna ya na gidan Club din su sungama shan giya mahaifinsa ya samesa a wajen ya mammaresa tare da tisasa a mota daga nan bai ƙara tuna komai ba sai yanzu da ya buɗe ido ya gansa a wani gida kwance saman gado .,
Jikinsa duk ya masa nauyi ya miƙe idanu ya zubawa kyakyawar budurwar da ke bacci a gefensa ta yi share-share fuskarta hawaye duk sun bushe zuba mata idanu ya yi kafin ya ja dogon tsaki uban me ma ya kaisa kwana gado Ɗaya da matar nan ai yanda ya ɗauki alƙawarin bazai amsa auren dolen nan da mahaifinsa ya yi masa ba domin ya na da wacce yake so haka bazai taɓa haɗa shimfiɗa da wacce ya auro masar ba kai ganinsa ma bazata ƙarayi ba ,
ɗauke idanunsa ya yi ba tare da ya gane koda kamanninta ba ya fice wanka ya yi tare da mayar da kayan jikinsa ba tare da ya ƙara koda kallon Hajara ba ya fice a gida daga nan club dinsu ya wuce ya na ɗaukar motarsa da jiya ya bari a wajen cike da jin zafin abunda mahifinsa ya yi masa na ƙin aura masa budurwarsa Rafaida da baiyi ba ya fice da motarsa ya bar garin kano gaba ɗaya.,
Hajara ba ta tashi farkawa a sumar da tayi ba sai ƙarfe sha ɗaya na safe da rarrafe da kuka ta fito tsakar gida ta na kuka ta hau ƙwalawa maƙwabciyarta Farida kira sosai hankalin Farida ya tashi halin da ta samu hajara a ciki sosai ta jinjina rashin imani na mijinta ita ta taimaka mata ta gyara jikinta tare da mata gashi me kyau ta taimaka mata suka je asibiti aka duba ta bayan an bata magunguna da shawarwarin yanda zata kula da kanta har ta warke kafin su dawo gida saida hajara ta yi jinyar sati biyu da taimakon makwabciyarta farida mutuniyar kirki,
A lokacin ne mahaifinsa ya zo ganinta ko da ya tambayeta lafiya Amsa masa tayi da lafiya qlau ba tare da ta sanar masa komai game da ɗansa ba ya yi mata alkairi ya bar gidan,
Sosai take kewar mahaifinta ga babu waya a wajenta don har lokacin wayarma babu saidai telephone da ba kowa ke samunta ba,
Haka rayuwa ta dinga tafar mata saida ta yi wata ukku kafin mahaifinta ya zo ganinta wanda daƙyal ya cire kara da kunya ya zo gidan ganin ƴarsa don fulani akwai kunya.
tayi matuƙar jin daɗi da farincikin hakan wanda malam mutari dukda namiji ne ya lura da shigar cikin da ke jikin ƴarsa sosai ya ji farincikin haka Alhaji Marzouq Watau Mahaifin Maleek shima hakan ba ƙaramun daɗi ya yi masa ba domin hakan ya nuna masa Malek ya amsa Hajara hannu biyu kenan fushin hanasa auren Rufaida yarinyar da kowa ya san bata da tarbiya hakan ne ya sanyasa yin fushi ya daina zuwa inda yake a ransa ya ce ,
“ai daman nasan dole zaka so Hajara Daman don ganinta ne bakayi ba shiyasa amma yarinya kyakyawa kamar wannan a aurawa mutum ya ce baya so ai sai mahaukaci Wanda tarbiyar yarinyar da nagartar Malam mutari ya ja ra’ayinsa na kwaɗayin son haɗa zuri’a da su dukda ya sa ya yi laifin ɓoyewa mahaifinta halayar Malek na shaye-shaye domin ya san muddin ya san da halayyar nasa ba zai aura masa ƴarsa ba ko shi yafi kowa komai a duniya,shiyasa ya ke Adduar kullum akan Allah ya shirya masa malek ya bar shaye-Shayen shi kaɗai ne ɗansa namiji mafi soyuwa a cikin ransa sauran yaransa ukku duk mata ne gashi Allah ya jarabce shi da son malek fiye da kowa a cikin yaransa yasan hada tausayin maraicin da ya taso cikinsa dukda ya san matar sa Hajiya Habasiya ba ta taɓa nuna ba ita ta haifi malek ba amma ya san da soyayyar mahaifiyarsa Maryam da ta rasu bayan ta haifa masa Malek da kwana ukku ta koma ga Allah”,
Sai yamma Baba Mutari da mahaifin malek suka bar gidan wanda hajara ta sha kuka kamar ranta zai fita gashi ta kasa sanarwa da kowa halin da take ciki ta rasa ta inda zata fara ga zazzaɓi da kasala ,amai da take ta yawan fama dashi a watannin nan domin ko aka ba ta kawo ciki ne gare ta ba saida ya kai kimanin wata shida shima a bakin farida ta fara ji tun bata yarda ba har ta yarda bayan ta je likita ya tabbatar mata da hakan,
Hakanan Allah ya jarabceta da son Cikin dukda ƙiyayyar mahaifin cikin da take ji a cikin ranta da taimakon Allah da taimakon Farida tare da mahaifin malek da ya ke ziyartar ta akai akai tare da aiko mata da saƙo duk wani abun maƙulashe da mai ciki za ta buƙata sai ya aika mata har Allah ya sauke ta lafiya Ranar wata Juma’a da taimakon nurse da farida ta kira lokacin da ta fara naƙuda ta sha wahala sosai kafin ta haifo santalelen ɗanta kyakyawa ajin ƙarshe mai matsanancin kama da ita sai ma ya ninka ta a kyawu saɓanin Haske da nashi bai kai nata ba,
Masha Allah tun a lokacin nurse din da farida suka dinga Yaba kyawun yaron wanda lokacin ko gama gyara hajara ba ayi ba ta ɗauki yaron ta na hawaye ta sumbacesa tare da sanya masa albarka ta na jin tsanantar soyayyarsa da Tausayinsa a cikin ranta.
Gyara su tsaf akayi ita da kyakyawan jaririnta kasancewar dare ne tare suka kwana sai washegari nurse din ta tafi ta na ta santin jaririn da aka Haifa,
Haka Farida itama sosai Allah ya ɗaura mata son yaron kodan bata taɓa haihuwa ba dukda bata jima da aure ba a lokacin shekararta huɗu da aure dan zatayi sa’annin hajara banbancin hajara tayi karatu shiyasa farida ta fi ta a aure,
Kamar kullum yanda Mahaifin Malek ya ke aikowa da hajara abubuwan buƙata ranar ma ya aiko mata da shi farida ke sanar da ɗan aike saƙon Haihuwar wanda mintuna talatin ba ayi ba saiga Alhaji Marzouq .
sosai ya yi matuƙar farinciki da haihuwar Wanda sau ɗaya ya ɗaura idanunsa akan yaron ya ji tsanantar soyayyarsa a ransa albarka ya sanyawa hajara ba iyaka a nan ne ya ke tambayar ta malek shirun da tayi ya fahimtar da shi akwai matsala me hakan ke nufi?
tambayar duniya mahaifinsa ya mata wanda dakyal ta sanar dashi halin da take ciki tun daga farkon auren ta daure ta cire kunya ta sanar dashi har yanda akayi aka samu cikin yaron da yanda ya shigo cikin maye,
Allah sarki hajara bata taɓa ga hawayen babba namiji ba sai a ranar dakyal ya Daure ya bata hakuri tare da mata alƙawarin insha Allah a yau sai malek ya dawo muddin shi ya haife sa.
A ranar ya bazama bincike ya gano inda malek yake ashe ya na garin katsina driver ya aika tare da ɗansanda aka kamosa don ransa ya yi mugun ɓaci a lokacin da aka kawo masa shi gabansa saida yayi masa mari huɗu saboda jin haushin abunda ya aikata cikin faɗa da jin ciwo Alhaji marzouq ya ce.
“mu aura maka yarinya ka je ka yi shaye-shaye ka Haiƙe mata don rashin imani ka gudu ka barta tsawon wata tara ta na rainon cikinka har ta haihu ba tare da kulawarka ba”
“What Abba Ciki na wlh ni sharri takeyimun ko Al-Qur’ani za aban zan rantse akan ko hannunta ban taɓa riƙewa ba bare har nayi mata ciki ƙarya takeyimun ni ko kamanninta ban sani ba chan ta je ta samu uban cikinta amma ba ni ba,……………✍🏽
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
🪅*IBTIHAL*🪅
~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)
MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*
*DEDICATED TO MY HUSBAND*
🅿️…………………………..*06*
A matuƙar zabure baba kamar yanda suke ce masa ke kallonsa ya na nunasa da yatsa ya ce “kasan me kake faɗa Malek “?
Ya ce “ina sane baba wallahi tallahi ba ciki na ba ne”
“Innalillahi wa inna ilaihiraji’oun”
Baba ya faɗa ya na dafa saitin zuciyarsa tareda zaunawa samar kujera ba shiri”
Hajiya habasiya da ke wajen ta ce “maganar gaskiya a duba batun nan Alhaji daman yarinyar an faɗa idonta a buɗe yake daman a zamanin nan wake barin gaban iyayensa ya tafi har wani gari da sunan karatu yawon karuwanci dai daman kowa ya sai rariya yasan zata zubar da ruwa bakaga yarinya idonta a buɗe karrr ta ga jiya ta ga yau chan ta nemu uban cikinta amma a ɗana ba wallahi”
Da sauri malek ya ce “Yawwa Mama Faɗa masa dai don wlh ni ba ciki na ba ne ni wallahi a hanya ma muka haɗu bazan shaida ta ba”.
Ran Baba na tsananta Ɓaci ya Ɗauke malek da mari zai ƙara masa hajiya habasiya ta shiga tsakani ta
Ce”haba Alhaji yaron nan fa na da gaskiya”
Baba ji ya yi kamar ya haɗa har ita ya mara amma ya dake ya daure ya ce su shirya su je su gano jaririn a tunaninsa idan malek ya ga yaron sonshi zai sa ya amshe sa suka shirya har hajiya habasiya suka nufi gidan ,
Nan fa rigima ta ƙara ɓarkewa Malek ya ce “shi wallahi ba yaronsa ba ne dukda lokacin da ya zubawa hajara ido ya ji fargaba domin kyawunta ya matuƙar basa mamaki amma jin haushin abunda ta aikata lokaci guda ya ji tsanarta a ransa domin a rayuwarsa ya tsana zina shi dai iskancinsa a shaye-shaye ya tsaya amma bai taɓa aikata Zina ba,
Hajara na kuka ta na rantsuwa akan ko Qur’ani aka bata zata rantse ba ta taɓa aikata zina ba wallahi ɗan malek ne shima ya na zai iya rantsewa akan ba ɗansa ba ne .
wasa wasa case ya zama babba wanda har mahaifin hajara saida ya zo garin wanda baƙin cikin jin abunda ya ke faruwa daman da sauran tension ɗin da matansa ke guma masa ga wannan sabon baƙin cikin a take ya yanke jiki ya faɗi wanda hankalin hajara ya tsananta tashi itama a take ta yanke jiki ta faɗi hankali tashe Alhaji marzouq ya kaissu asibiti ya na jin tsananin nadamar yaudarar amininsa da ya yi,
Malam Mutari ya riga Hajara farkawa wanda lokacin ba ya iya komai domin likita ya tabbatar da ya samun shanyewar sharen jiki ko da hajara ta farka ta samu wannan labarin ta yi baƙinciki da kuka mai tsanani sosai taji tsanar malek a ranta.
sai washegari aka sallamesu wanda maimakon su koma gidan hajara ta ce bazata koma ba saidai a wuce da ita garinsu wanda alhaji marzouq ba haka ya so ba,
Tashin hankali sabo domin hajiya habasiya da suka rako su ta Gimtsawa matan babanta abunda ke faruwa har da ƙari wanda kafin kace me labari ya baza gari gaba ɗaya .
hajara maida hankalinta tayi wajen kula da jaririnta da shafa’atu ke taimaka mata dukda zagin da take sha wajen mahaifiyarta akan ta na raɓar ɗan shege hakan bai sa ta daina kulawa da jaririn da ya shiga ranta lokaci guda,
Ranar suna Alhaji marzouq ya zo da manya manyan raguna guda ukku da komai na buƙatar uwa da jariri ba abunda bai saya ba wanda a lokacin ne yayiwa yaron Huɗuba Da suna *MARZOUQ*
yayiwa kansa takwara a ranar Ya ƙara neman yafiyar malam Mutari akan ɓoye masa halayar ɗansa da yayi da abubuwan da suka faru ya rantse masa ya shaida masa kan cewar wallahi jaririn nan yasan jikansa ne a ranar malam mutari ya yafe masa,
Hajara ita ta dinga kula da mahaifinta tare da ɗan uwanta ibrahim da ke taimaka mata itakuma shafa’atu na tayata kula da ɗanta da ke ƙara wayau da kyau ko da yaushe domin sauran ƴaƴansa da matansa sunce babu ruwansu da shi ba zasu kula da shi ba chan wacce ta ɗaura masa ciwon ta kula dashi habaici babu kalar wanda hajara bata sha haka ta toshe kunnuwanta,
Mahaifinta kullum cikin sanya mata albarka ya ke tare da mata nasiha kala-kala har ya koma ga Allah ranar wata juma’a wanda lokacin shekarar Marzouq ukku daidai da haihuwa wani irin sabo ya yi da kakansa da halin ciwo bai hanasa nunawa jikan nasa mafi soyuwa a ransa soyayya ba,wanda har zuwa shekarun nan mahaifinsa Malek baitaɓa zuwa ya gansa ba sannan bai aminta ɗansa ba ne.
Mutuwar malam mutari ta matuƙar girgiza Hajara tare da wasu ƙalilan daga cikin ƴaƴansa saɓanin sauran da murnar hakan sukayi tare da mugayen matansa,
Alhaji Marzouq ma yayi matuƙar jin mutuwar aminin nasa saida ya yi kwana ukku duk wani abu da akaci a zaman makokin shi ya ɗauki nauyin komai,ya lallashi Hajara sosai