IBTIHAL HAUSA NOVELS PDF COMPLETE BY MISS HAJO.docx

Author :  Miss Hajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 13

6K to 9K   out of 36.4K words

momy na zanesa”

Ta na turo baki kamar bazatayi magana ba ta ce”is you”

Ta ɗan zaro ido alamun mamaki ta ce “to me nayi”

Ta na ƙara tura baki gaba ta ce “a lot of guilt”ta na langaɓe kai ta ce”to faɗamun laifin sai na baki haƙuri kinji princess ɗina”

Ta na gyara zama kamar wata babba ta re da fara nuna yatsa da hannu irin lissafin nan ta ce”First You haven't called me in four days And Second You said you would come and see me but You haven't come”

Ibtihal ta yi kalar tausayi tare da cewa

“Kiyi hakuri to”

Ta na sanya hawaye ta ce “I will not”

Safa na dariya ta amsa wayar tare da cewa “hy mummy’s princess “

Lokaci guda ta saki fuska ta na dariya ganin Safa ta bayyana a screen din wayar saboda kullum sai sunyi video call akwai shaƙuwa me ƙarfi tattare da su Ibtihal miƙewa tayi tare da nufar pridge ta na ɗaukar gorar ruwa me sanyi ta na kafa kai ta ce “kin fansheni rigimar Afren ina zan iya “

Safa na harararta ta gefe ƙasa-ƙasa yanda Afren bazataji ba ta ce”Kin saɓa mata alƙawari ba dole ta tuhumeki ba”

Sun kusan 50minutes suna wayar cikin harshen turanci kafin momy ta zo suyi sallama ta ce lokacin baccinsu ya yi sukayi sallama Ibtihal na kallon Safa ta ce ,

kun nace sai kun mayar da yarinya baturiya sarai tanajin hausar fa ta iya take ƙin yi wai ita yaren baya mata daɗi kiji fa wani rainin hankalin shiyasa ba na biyeta nake mata hausa kuma da kuna mata da dole zata so yaren ni ina mamakin mom da ta ƙyale ta “

Safa tayi ƴar dariya tare da cewa “mu abunda take so shi muke so yarinya ce idan ta girma zata daina in banda wayau ma da Allah ya bata wasu kamar ita bakowace magana suka iya ba shekara biyu da wata tara “

Ibtihal ta taɓe baki ta ce “kudai kuka sani ni dai amma dai ba two days ɗin da kika saba kiyi ki tafi ba zakiyi “

Safa na amsa wayar boy friend ɗinta ta ce “da kika samu ma zanyi two days ɗin ke ko kwana ɗaya daƙyal kike”

Ta ƙyaleta batare da ta amsa mata ba sai ma kwanciya da tayi tare da fara karanto adduo’in bacci.

Kwanan safa Biyu ta tafi ba a son ran Ibti ba don ta na matuƙar jin daɗin idan suna tare da safa ko ba komai za ta sata magana don safa ba dai son zance ba da kawo labari”

Washegari kasancewar ta na son yin safko kasancewar friday kuma ta na son ta yi sauko domin ziyartar gidan marayu kamar yanda tun wancen lokacin ɗan zaman da tayi a abuja ta sabarwa kanta xuwa duk friday sosai tayi missing yaran da tayi mugun sabo da su a wajen”

Washegari 8:30 ta gama shirinta sosai tayi kyau cikin shigar Doguwar riga Abaya mai matuƙar tsada ta amsheta tayi mata masifar kyau musamman yanda ta yi roalling gyalen kasan ƙwararriya ce a fanni saka irin kayan”

A gaggauce ta yi sallama da hajiya tare da fita ta na shiga motarta wanda mai gadi na hango hakan ya gaggauta buɗe mata get daidai motar Yusuf na fitowa ga alamun shikuma office zaije horn yayi mata da ƙarfi wanda tasan idan yayi mata haka alamun ta tsaya ne ya zo ya ɓata mata lokaci a cewarta hakan yasa ta murza motar da masifar gudu ,

hakan ba ƙaramin baƙanta ran yusuf ya yi ƙwafa ya yi tare da cize yatsa ya ce “zanyi maganinki marar kunya “

shima ya figi motar a mugun guje fiye da yanda ta yi.

Ƙarfe 9:30 ya yi mata a bakin gate ƙatoton gidan marayu da ya haɗu matuƙar haɗuwa don bazaka taɓa Ɗauka ma gidan marayu ba ne lura da yanayin tsarin ginin da yayi matuƙar haɗuwa ,

Tun a get ɗin farko securityn da ke gadin wajen suka shaida ta suka gaisa cikin mutunci kafin ta nufi gate na gaba ta na parking tare da fito da ƙatuwar ledar da ta biya shopping ta yo hakan ne ma ya sa har ta yi 1hour a hanya,

yara ne a farfajiya mafi yawaici duk uniform na makaranta jikinsu masu kyau da tsada cikin tsabta domin dukkaninsu kayansu ma har da guga bayan wanki,

sai wasa suke alamun kamar break suka fito tsayawa tayi ta na kallonsu cike da jin daɗin ganin yanda suke walwala da kulawa tamkar yaran da suke da gatan uwa da uwa tabbas ko wasu masu gatan bazasu sami gatan da yaran nan suke samu ba,

kafin ma ta ƙarasa wata yarinya da gudu ta rugo tare da rungumeta wanda hakan yasa sauran yaran hankalinsu dawowa gareta wanda kusan yara goma sha suka rugo da gudu har rigen-rigen rungumarta da zallar murnarsu na ganinta wacce ta fara rungumarta ce ta sanya kuka tare da ƙara rungumeta ta ce ,

“ina kika je tsawon shekaru Aunty kika daina xuwa ganinmu duk friday sai munyi kukan rashin ganinki idan Abbey ya zo sai munce ya nemo mana ke don Allah aunty karki ƙara tafiya ki daina zuwa ganinmu muna sonki muna so ki zama mamanmu Muna matuƙar ƙaunarki”

ta ƙarasa faɗa cikin kuka suma sauran Yaran sai suka hau kuka suna cewa”karki ƙara tafiya ki barmu Aunty Muna so ki zama mamamu”

Sosai Suka Karyar da zuciyar Ibtihal har bata san sanda Hawaye suka zobo ba ta maza ta goge tare da shafa kan Ikhlas ta ce”insha Allah bazan ƙara tafiya na barku ba har Abada ku share hawayenku Yaran aunty oya……………✍🏽

*SHARE SHARE SHARE PLX YAN AMANA*

https://chat.whatsapp.com/JYPWPtF78zlIr2kJcbp6ms?mode=gi_t

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~

*HAJARA L SADEQ*

(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼

Auren wata tara

Ni da yaya arman

Matar uncle

Najmat abiy

Komai mukaddari ne

Khadijatul Sabren

Ribar so

Mata ta ce

*And now*

*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*04*

Lokaci guda duk suka bar kukan tare da fara tsalle ta goge ƙwallan da suka cika mata idanu tare da sakar musu murmushi ta na kama hannun Ikhlas da farida saboda daman chan sunfi shaƙuwa suka nufi wajen da suke zama duk lokacin da ta zo,

Ɗaya daga cikin mai kula da su dattijuwa ta nufo ta da murmushi tare da cewa”jikata Hajiya Ibtihal wata sabon gani”

“ta ɗanyi ɗan murmushi tare da cewa”

Alhamdulillahi mama salame mun sameku lafiya”

Ta na zama gefenta ta ce “lfyqlau sai kewa shekaru da yawa Allah ya sa dai lafiya”

Ta ce “lafiya qlau na yi tafiya ne ban dawo ba sai satin nan “

Ta ce”Allasarki fatan andawo lfy”

Ta ce”Alhamdulillahi ya ƙoƙari”

Ta ce “ƙoƙari na wajenku hajiya mu da aikin biyanmu ake ladan ai na wajenku masu ƙoƙarin”

Ibtihal ta ce”da kinsan ɗubbin ladan da kuke samu a aikin nan mama salame da baki faɗa haka ba kula da yaro ba ƙaramun lada ba ne musamman kuma akace Maraya “

Ta ce “Hakane amma ai hajiya kina Ƙoƙari duk sati fa sai an aiko saƙo wanda na tabbatar daga wajenki ya ke zuwa dukda bakya nan sannan mai kawo saƙon ya ƙi ba da koda numberki yara duk sati suyi ta tsammanin zuwanki “

Ta yi shiru dai batare da tace komai ba sai ɗan murmushi,

Chochulate,Biscuits,Halawa,Mayukan shafawa masu tsada,sabulai,Maclean,Takalma ,Kayan shan iska kasantuwar zafi,da turaruka tare da kayan wasar da tayo musu shopping duk ta basu suka dinga tsalle suna murna tare da mata adduo’i da fatan alkhairi tamkar ba yara ba a ƙarshe duk suka ce Allah ya bata miji na gari don sun San auntyn na su budurwace a ganinsu ,

ba ƙaramun sanyi da daɗi Ibtihal take ji ba duk ranar da yaran nan suna mata addua ta na matuƙar jin daɗin addu’in na su Sannan ta na ƙarajin ƙarfin gwuiwar taimaka musu.

lokacin break na yi duk suka koma class Mama Hauwa ma ɗayar mai kula da su da suka ɗanyi sabo ta zo suka gaisa cike da girmamawa ta koma bakin aikinta,

Zaune suke ita da mama salame samar ƙatuwar tanarma ƙarƙashin wata bishiyar zaitun,

Dafo ta kaɗan mama salame tayi ganin yanda kamar ta zurmiya a duniyar tunani ta ce ,

jikata ko dai akwai abunda ke damunki na kula ko wancen lokacin kina yawan tafiya tunani wanda ke kanki bakya sanin lokacin da kike shiga wannan yanayin a dinga godewa Allah duk wani rufin asiri na duniya Allah yayi muku saidai kawai kuyi fatan samun lahira itama kuma insha Allah ke da mai gidan nan kun sameta don a masu kuɗi irinku ƙalilan ne”

Ibtihal ta yi wani murmushin yaƙe tare da cewa “hmmm Mama wasu mutanen a ganinsu kuɗi kawai sune jin daɗin rayuwa indai ka na da kuɗi ba ka da wata matsala wanda basusan ƙalubalen rayuwa da jarabawar rayuwa ba a kuɗi take ba talaka da mai kuɗi dukkaninsu halittar Allah ne kuma kowannensu bai fi ƙarfin jarabta ba wasu ga kuɗin amma ba ya jin daɗin su ko kaɗan wasu ga kuɗin Allah ya rarabcesu da ciwo,wasu marasa jin Ƴaƴa,wani jarabtar mata,wata jarabtar miji,wani jarabtar ƴan uwa ,wani jarabtar iyaye,wani jarabtar kishiya,wata uwar miji,wani Aboki Amini ,wani rashin haihuwa,Gasu nan dayawa ita jarabtar rayuwa ba a kuɗi take ba”

Mama salame ta katse ta da cewa”ke kuwa ƴata a wannan ƙarancin shekarun naki me zai haɗaki da damuwa haka?

Cike da gajiya da sanyata surutu da mama salame ke yi ta ce”Mu bar maganar mama salame”

Ta ce “Hmmm to shikenan jikata Allah yaye miki abunda ke damunki ya cika rayuwarku da farinciki har Abada Ke da Alhaji *Marzouq Malek*

“ta amsa da Ameen “ta na maimaita *Alhaji Marzouq a cikin ranta kamar ta san sunan”

Mama salame ta ce “Wlh jikata Sai yanzu na kula maganarki Hakane kam jarabawar rayuwa mu gashinan ma a gabanmu muna gani Alhaji Marzouq mai gidan nan ne da nake baki labari tunda yake shekara sha biyu da Aure amma Allah bai basa haihuwa ba kuma bawai haihuwarce bayayi ba da farko a a tuggu da sharrin mace ya gamu dashi wanda ta zalunce sa ta cutar masa da rayuwa domin halin yanzu likitoci sun tabbatar masa ba zai sake haihuwa ba har abada gashi mutum ne mai tsananin kyauta da kirki ga karrama ɗan Adam bai ɗauki dukiyar da mulkin da Allah ya ba sa a bakin komai ba ki duba kiga yaran nan da yake kula da su ko iyayensu sai haka yayi masu gata iya gata ilimin arabi da na zamani sutura me kyau ci da sha me kyau yaran nan kaji ma sai sun ture mu kanmu da muke kula da su wani gata ne baiyi mana ba dukkanin meturorin da ke kula da wajen nan babu wacce ba a sayawa gida aka kaita makka ba Albashin ko da yake biyanmu wlh ko wani malamin asibitin gwamnati bazai gwada mana albashi ba samun ɗan siyasa a ƙasar nan irin bawan Allahn nan sai antona ke ƴata sai ma ince miki wlh babu mu har yqnzu fatanmu da burinmu bai wuce Allah ya cikawa Bawan Allahn nan burinsa ba a duniya ya basa haihuwa tare da mata tagari “

Ta ƙarasa maganar ta na shafce hawaye”

Shiru Ibtihal ta yi ta na kallon mama Salame da ke kuka afujajan hakanan ta ji ta na son sanin waye bawan Allahn nan ta tabbata maganganun mama salame babu ƙarya a ciki domin ita sheda ce jin cewa ɗan siyasa ne abun yayi matuƙar bata mamaki daman muna da irin ƴan siyasa masu irin wannan halayar a ƙasar nan?”

ta tambayi kanta har a ranta ta ji ta na son jin labarinsa kallon mama salame tayi tare da miƙa mata handkitchiep ta ce “ki bar kukan mama salame da ga labari kuma sai kuka”

Ta na shafce majina ta ce “

“Bazaki gane ba ƴar nan domin duk wanda yasan Alhaji Marzouq yasan Ƙaunar sa da yara da chutarwar da akayi masa akan hakan dole ya koka masa”

Ibtihal ta ce”ai kukan bazaiyi magani ba mama Allah ya basa haihuwar me Albarka zakuyi masa fata”

Ta ce “ƴata munayi mu yanzu fatanmu ma ya yi auren da addu’armu kenan domin yayi alƙawarin ya gama aure har abada”

Ibtihal a ranta ta ce “daman akwai mai ra’ayi irin nawa na gama aure har abada “

A zahiri ta zuba mata idanu ta ce “Mama ba kince ya yi aure shekara Sha Biyu baya ba”

Mama salame ta jinjina kai ta ce “hmmm ke dai bari ƴata har bana son tuna labarin bawan Allahn nan mace tayi masa Giɓin da bazai taɓa mantawa ba a rayuwa ya ga tuggu da sharrin mata”

Cike da zaƙuwa da son jin labarinsa ta ce “me macen tayi masa mama daman har akwai chutarwa da mace mai rauni zata iya yiwa ɗa namiji da bai ɗauki mace a bakin komai ba face ƙasƙantacciyar marar galihun da take ƙarƙashinsa a tunani na maza ke zaluntar mata ba wai mace ta zalinci namiji ba”

Mama salamatu ta ce”waya faɗa maki haka ƴata to ai wani sheɗancin da mace zatayi wlh rabinsa namiji bazai iya ba matan kala-kala ne kamar yanda mazan suma suke haka duk ɗan adam ɗin da kika gani da halinsa wani shi mutumin kirki ne mumuni mai tsoron Alkah da tsoron lahiransa wani ko kwata-kwata ma babu Allah a ransa yo sheɗancin da wani musulmin zaiyi ai kafiri ma arne bazai yisa ba donma dai wasu musuluncin na su a baki ne amma sun jima da barinsa yanzu kamar Hajiya Mariya tsohuwar matar Alhaji a gaskiya ban yarda da musulucinta ba”

Cike da zaƙuwa Ibtihal ta ce “ita kuwa mama salamatu me ta aikata haka”

Ta na tauna goro ta ce “zan baki labarin Alhaji Marzouq Kamar yanda kika buƙata ƴata kafin ta gyara zama ta ce Asalin Mahaifinsa da mahaifiyar sa haifaffun………………..✍🏽

*_Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~

*HAJARA L SADEQ*

(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼

Auren wata tara

Ni da yaya arman

Matar uncle

Najmat abiy

Komai mukaddari ne

Khadijatul Sabren

Ribar so

Mata ta ce

*And now*

*IBTIHAL*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*05*

Asalin Mahaifinsa da Mahaifiyarsa Haifaffun Garin Haɗeja ne da ke Jahar Jigawa mahaifiyarsa Hajara ita kaɗai Mahaifiyarta ta haifa ta koma ga Allah a wajen haihuwar ɗanta na biyu da har an cire rai da sake haihuwarta tare da cikin suka koma ga Allah wanda lokacin shekarun Hajara goma sha ɗaya a duniya ,

ta taso cikin maraicin uwa tare da gallazawar matan uba da ƴan uba goma sha takwas wanda dukkaninsu iyayensu sun chusa musu tsanarta ba don komai ba sai don soyayyar da mahaifinsu ya ke nuna mata daman akwai kishi mai zafi da jin haushin mahaifiyarta da mijinsu Malam Mutari ya fifita a kansu domin Rabi’atu macece da duk wanda yayi mu’amula da ita sai ya so ta mace ce mai tsananin kyakyawar zuciya ga haƙuri da kawaici ga kirki da ibada gami da tsananin tsoron Allah wannan shine babban makamin da ta kama Allah ya ɗorata akan kishiyoyinta da ba abunda suka iya sai bin bokaye ƴan tsubbu da malaman boge masu ci da addini bokaye mushirikai,

ba irin asirin da basa mata amma ko kaɗan Allah bai basu ikon cin galaba akanta ba da mijinsu wanda har ta koma ga Allah bai bar ƙaunarta ba.

mutuwarta ta gigiza masoyanta da dama saɓanin maƙiyanta da hakan yayi musu matuƙar daɗi (Allahsarki murnar mutuwa murnar banza).

wanda tundaga mutuwarta malam mutari ya haɗu da hawan jini to daman a wajenta kawai yake samun sauƙi ita ce mai kwantar masa da hankali domin shima mutum ne mai tsananin haƙuri da kamala muddin kaga faɗan sa to ba ƙaramun kai sa bango akayi ba .

Haule ita ce uwar gidansa yaranta goma sai matarsa ta biyu Marariya mai ƴaƴa takwas sannan Rabi’atu itace matarsa ta ukku kuma ta ƙarshe,

ta haifa masa ƴa Ɗaya Hajara yaransa goma sha tara a duniya maza huɗu sauran duk mata ne wanda dukkaninsu a ƴaƴan nasa basa son hajara sai ƙwara biyu kachal Ibrahim da Shafa’atu,wanda ibrahim yayantane itakuma shafa’atu ƙanwartace domin itace Autar gidan dukkaninsu yaran Marariya ne.

Malam mutari mutum ne da ya tara arziƙi a noma tsohon manomi ne da yayi suna a garin,da kewayen kusa da su.

Hajara ta ta so da farinjinin samari kasancewarta jinin asalin fulani gami da rumawa domin mahaifiyarta haifaffiyar Raɗɗa da ke ƙarƙashin wata local govermemt da ke jihar katsina ne,

mahaifinsu kuma malam mutari fulanin haɗeja ne kinga ko jinin rumawa ya haɗu da fulani dole ya haifar da kyakyawa,

hajara kyakyawace tun a zamanin ga hasken fata kuma mahaifinta ya tsaye mata ilimin boko da arabi wanda a ƴaƴansa duk suka gagara yi domin lokacin gani suke rashin galihu ne ya sanya ta ke karatu su ko ƴaƴansu da suke da gata karatun me zasuyi.

A kaf ƴaƴan malam mutari babu wanda yayi ko da makarantar firamari islamiyar ma ba zuwan kirki suke ba hakan ya sa suka ta so cikin jahilci saɓanin Hajara da ta yi zarra a cikinsu domin Allah ya yi mata baiwar ƙoƙari.

Bayan gama karatun sakandire ɗinta malam mutari aure ya so ya yi mata a masoyanta da ke biɗarta amma sam ta nuna ita karatu ta ke son ƙarawa wanda yarda da ita da son

3 / 13