Author : Miss Hajo Category : Romantic Hausa Novels
kusa”
Wani irin faɗuwa gaban mom ya yi ta ce “innalillahi Hajiya me ya sameta”
daidai likita na ƙarasowa wajen fuskarsa kawai za ka kalla ka san akwai damuwa ya ce”muna buƙatar mutum biyu makusanta *IBTIHAL ADAM* ya na gama faɗar haka ya koma office ɗinsa daidai Abba ya bisa da sauri tare da Aunty salma,
Damuwa ƙarara a fuskar Dr Najib bayan sun zauna ya ce “Alhaji magana ce ta gaggawa muna buƙatar jini a gaggauce domin yarinyar na buƙatar jini kuma mun gwada jininta O Negative ne wanda cikin kashi ɗari masu irinsa basu da yawa idan akwai mai irinsa a dangi a bincika da gaggawa”
“Innalillahi wa inna ilaihiraji’un Aunty salma ta faɗa hawaye na siraro mata saboda dukkaninsu sun san Kaf Babu mai irin jininta a Family Ɗinsu dukkaninsu mafi yawaici O Possitive ne “
Abba ya ce”Dr Babu yanda za ayi kaf family ɗinmu ita kaɗai ce mai irin jinin nan ko nawa ne zan kashe tunda nasan kuna ɗaukar number masu irin jinin saboda irin haka ta kama don Allah a taimaka a ceci ran Ƴata”
Dr ya ce “innalillahi wa inna ilaihiraji’un Wallahi Alhaji Mutum biyu ne idan irin haka ta kama suke bayarwa ko ba a nema ba suna zuwa da ansha watanni a Ɗauka na farko *SANATA MARZOUQ MALEK* sai Alhaji Bukar to shi Alhaji bukar ya na ma garinsu yanxu haka Allah yayiwa mahaifinsa. Rasuwa shi sanin da nayi Alhaji Marzouq ba ya Ƙasar sauran waɗanda kuma muke da su mutum ukku ne kuma duk mata kaga bazaiyu ba”
Hawaye na xuba idanun Aunty salma ta ce “Shikenan yanzu Dr zamu rasa ƴarmu babu wata mafita”
Dr na shirin Magana Wata Nurse ta shigo fuskarta washe cike da girmamawa ta ce “Dr Munyi babban Baƙo Sanata Marzouq ne ya zo duba marasa lafiya kamar yanda ya saba zuwa lokaci zuwa lokaci”
Dr ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya ya na miƙewa da zallar farinciki ya fice Abba da Aunty Salma suka bi bayansa suma cikin sauri”
Lokacin ne wani kyakyawan matashi ke shigowa cikin taku irin na Hamshaƙan maza Fari ne ba Kal ba kyakyawa ajin farko wanda ko ɗan uwansa namiji ya kallesa dole ya ƙara kalla ballantana ƴan matan wannan zamani,
Dukda kasancewar sanye ya ke cikin manyan kaya farar tsadaddar shaddar da tayi masifar yimasa kyau Sajen nan nasa kallo ɗaya zaka masa kasan na musamman ne masu irinsa ƙalilan ne kodan ya danganta da gyaran da suke samu ,
idanunsa sanye cikin wani farin tsadadden glass da ya ƙara ƙawata baiwar kyawunsa kansa sanye da hula da ta dace da kayansa takalman ƙafafunsa kaɗai ya isa kayi ƙauyanci sam yanda gayu da tsabta gami da kyan jiki ya ratsa sa baka taɓa ɗaukar ya kai shekaru Arba’in zaka ɗauka bazai wuce 35yrs ba ya yi wuta,
Gaba Ɗaya wajen karaɗewa ya yi da daddaɗan ƙamshin turarensa mai matuƙar daɗi da sanyin shaƙa,
“Ranka ya daɗe barka da zuwa”
Dr ya faɗa cike da girgimamawa har ya na haɗawa da russunawa bayan ya basa hannu sukayi musabaha Cikin daddaɗan muryarsa mai cike da miskilanci da rashin son magana ya ce”ya masu jiki”
Muryar sam ba ta ma fita,
Dr ya ce “masu jiki alhamdulillahi ranka ya daɗe ya fama da jama’a “ya faɗa suna yin gaba don masa jagora kamar ko yaushe idan yazo duba marasa lafiya.
Daidai lokacin Abba na ƙarasa zowa wajen da murmushin nuna sanayya ya nufi wajensu tare da cewa”Sanata Marzouq”
Cike da ladabi marzouq ya miƙawa Abba hannu ya ce “ranka ya daɗe barka da yamma”
Ya ce “A ah saidai muce ranmu ya daɗe tare “duk sukayi murmushi Abba ya ce”Ya majalissar kwana biyu ba a ganinka”
Ya ce “Na yi tafiya ne Ɗazu ba jimawa dawowata Ƙasar”
Abba ya ce”Allah ya taimaka “
Duk suka ɗunguma har Abba Bayan securityn Marzouq ya dakatar da su .
Ɗaya bayan ɗaya duk gadon da yaje ya musu ya jiki sai ya aje musu bandir kudaɗe masu yawan gaske suna gaba ya na tambayar Dr akwai issue na Aiki waɗanda ba su da hali”
Dr ya ce”Eh akwai na mutane huɗu mararsa ƙarfi yanzu dai akwai issue mai girma ranka ya daɗe na irin taimakon da kakeyi Yarinyar Sanata Bashir Dikko ce ke buƙatar jini kuma jinin irin naka ne an bincika kaf ba a samu ba har ma mun cire rai da rayuwar yarinyar sai gashi Allah ya kawo mana kai”
Cikin sauri ya kalli Dr ya ce “Subhanallah ai abunda ya dace ayi tun farko meyasa ba ka faɗa da wuri ba ayi sauri muje a ɗauka”
Cikin ƙalilan mimtuna akayi masa text ɗin duk da ya dace aka tabbatar ba matsala tattare dashi kafin a ɗeba jinin leda Ɗaya da gaggauwa akaje aka maƙala mata Abba harda hawayen farinciki ya kama hannun Marzouq ya ce.
“Bani da bakin da zan gode maka bisa ceton rayuwar ƴata da kayi Sanata nagode Allah ya biya maka dukkanin buƙatun ka na Alkhairi ya ƙara maka nasara da ci gaba a dukkan al’amuranka kamar yanda na saba faɗa yau zan maomaita a gabanka *MARZOUQ MALEK* kai ɗin na musamman ne a cikin Al’umma ririnka basu da yawa a duniya”
Sam nauyin godiyar da Abba keyi masa yakeji don bai ɗauki hakan a wani babban abu ba “
Bayan ya huta Ya tashi ya na kallon Abba ya ce “ mu je na duba ƴar taka sai mu wuce”
Bisa jagorancin Dr tare da Abba suka nufa Ɗakin da Ibtihal ta ke kwance hannu ɗaya maƙale da ruwa ɗayan kuma maƙale da jinin da ya fara shiga jikinta”
Samun kansa ya yi da zuba mata ido fuskarta ta yi fayau kyawunta ya ƙara bayyana dukda kasantuwar idanunta na a rufe numfashinta ne kawai zai tabbatar maka da ta na raye wani irin tausayin halin da take ciki ne lokaci guda ya shige shi don duk wanda yasan marzouq ya san mutum ne mai tsananin tausayi minti ukku cikakke baiyi ba ya miƙawa Abba hannu sukayi musabaha ya ce “Allah ya bata lafiya yallaɓai “
Abba ya ce “Ameen ranka ya daɗe ina ƙara matuƙar godiya Allah y saka da mafificin alkhairi”
Suka fito tare momy da ke kuka jikin hajiya da ke ta lallashinta Abba ya kalla ya ce”ki kwantar da hankalinki Nafisa Allah ya kawo mana agajin gaggawar da bamu taɓa tsammani nan kusa ba yanzu haka An saka mata jinin insha Allah zata samu lafiya nan kusa sannan ciwon zuciya ma muna fatan zata rabu dashi gaba ɗaya da yardar Allah”
Da sauri ta ɗago ta ce “Yaya da gaske a ina aka samun jinin bayan an tabbatar da baza’a samesa nan kusa ba “
Ya nuna mata Marzouq da ya duƙa ya gaishe da hajiya cikin sauri momy na hawaye ta ce “mungode Allah ya saka da alkhairi ya biya maka buƙatunka na alkhairi”
Ya amsa da Amen ya na mai jin daɗin Addu’ar na ta Hajiya ma Albarka ta sanya masa da adduo’i kala-kala kafin ta kalli yarinyar da tunda suka zo tare lokacin afren ta tashi a bacci shikenan suka hau wasa ta ce “Jikata zo ki tafi kar babanki ya tafi ya barki”
Lokaci guda ta sanya kuka ta na maƙale kafaɗa “
Duk sukayi murmushi Aunty salma ta ce “bazaki bi baban naki ba”?
Ta gyaɗa kai ta na hawaye cike da muryar sangarta ta ce “Wajen Ƙawata Afren zan zauna”
Sosai mamaki ya kama Marzouq Tasnem mai masifar rashin son mutane da ƙiyiwa idan ba gidansu ba ko gidan kakanninta ba ta yarda ta zauna itace yau za ta ce zata zauna wajen mutanen da bata sonsu ba”
Ranƙwafowa yayi ya na rage tsawo tare da dafa kanta ya ce”a hanya zan saya miki chochulate sannan gobe da kaina zan kawoki wajen ƙawartaki kinji”
Ta sanya kuka ta ce “a a Daddy a nan zan zauna”……………✍🏽
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
🪅*IBTIHAL*🪅
~MALLAKAR~
*HAJARA L SADEQ*
(miss Hajo)
MARUBUCIYAR👇🏼
Auren wata tara
Ni da yaya arman
Matar uncle
Najmat abiy
Komai mukaddari ne
Khadijatul Sabren
Ribar so
Mata ta ce
*And now*
*IBTIHAL*
*Shafin nan naku ne Hindu Bulama Uwar Lena Tare da Matar Mijinta Allah ƙara muku basirar sabarbaɗo sharhi mai tashin kai Alkhairin Allah yakai muku har gadon baccinku*😘😘
*DEDICATED TO MY HUSBAND*
🅿️…………………………..*10*
Afren ma na ganin ƙawarta za ta tafi ta sanya kuka ,
Kowa ya dinga mamaki wanda daƙyal Safa ta ɗauke afren da ke Haure Haure ita kuma Tasnem Ahmad da ya tsaya tare da security ya na ta game a tab ɗinsa ya ɗauketa wanda kamar zata kada shi don bori Suka yi sallama suna barin wajen wanda har suka tada motocinsu kuka da ihu Tasnem ta ke itama kuma Afren.
*ASOKORO*
Hmmmm Lallai Arziƙi na inda ya ke na faɗa ina ƙarewa wani tsadadden tsararren katafaren wani mentions da ya yi fice a arear kallo,
Tundaga yanayin tsarin gidan kasan turawa suka gina irin gidajen nan ne da idan a hoto ka gani za ka rantse Zane ne Gida har gida tamkar ba a ƙasa nigeria ba,
Ashe banyi kallo ba saida na ƙarasa shiga Cikin compound bayan wuce gate na farko da ya ke shaƙe da security tamkar gidan shugaban ƙasa,
Duk yanda na so irin kwatanta muku yanda Mentions ɗinnan ya ke mai karatu ɓata lokaci ne na ga daular da bantaɓaga irinta ba wanda har saida na yi hawaye da Fatan Allah ya bamu Aljanna,
Ƙaton mention ne da idan ka na son nufar wani ɓangaren na gidan ma idan ba mai jurar doguwar tafiya ba ne to fa to ka na buƙatar Mota amma sauran Ɓangarorin ba shi da tazara sosai,
Ɓangare ne a ƙalla Biyar Wanda kowannensu ya tsaru iya tsaruwa sai Sauran filin gidan da aƙalla za a iya ƙara irin ginin wannan goma a ciki,
Gidan ya tsaru da shuke-shuken zamani tare da decoration masu matuƙar ƙayatarwa.
A wani Ƙaton falo na tsinci Kaina Ashe kalllon waje daban da na ciki,
nidai tsaf da ba da kaina na shigo ba tsintar kaina nayi kawai a wajen to fa zan rantse Ba Ƙasa Nigeria nake ba Dukiya ta yi kuka a palourm Ƙasaitattun Kujeru ne na Alfarma kaiii a iya falon kaɗai na ce zan zauna kwatanta muku yanda yake sai muyi rabin littafin bamuje inda muke so ba ku ƙiyasta da kanku ya wannan Daula za ta Kasance.
Tsit kakejin falon ba motsin komai sai na Ac da kuma TV da ke evening Azhkar an rage volume kaɗan Daddaɗan ƙamshi kawai ke tashi a wajen,
Wata matashiya ce ta shigo ɗakin da gudu kamar wacce aka tunkuɗo cikin tsananin kuke ta ke ƙwala kiran,
“Ummy Ummy”
Ba ta kai ga tsakiyar falon ba wata Kyakyawar farar dattijuwa ta fito sanye cikin wani tsadadden yadin material Ɗinkin bubu da yayi matuƙar mata kyau doguwa ce mai ƙiba irin mutanen nan ne da ƙiba tayi musu bala’in kyau dukda ƙibar na ta ba na tashin Hankali ba ne amma ta na da jiki kallo ɗaya za ka mata kasan hutu sun zauna a wajen Ka na ganinta ka ga tsohuwar ƴar boko domin ilimi ya gama ratsa ta tundaga suffarta,
Hankali tashe ta ƙaraso tsakiyar palon cikin tafiyar kamala ta na kama hannun Matashiyar ta ce”Me ya ke Faruwa Saudat meye kike kuka har haka”
Cikin kuka ta rungumeta ta ce “Ummy Abban Ahmad ne”
“Subhanallah me ya samu Ashraf ɗin ɗazunnan fa yabar nan”
Ta faɗa damuwa ƙarara fuskarta,
Cikin kuka da sangarta ta ce”Ummy haka yace wai sai na tafi gidanmu nace zan tafi da yarana ya amshe su sun tafi wani waje wai ba da su nazo ba wlh ummy bazan iya rayuwa ba yarana ba kuma ya ce ce kar yadawo ya iskeni a gidan “
Hankali tashe Ummy ta ce “Innalillahi wa inna ilaihiraji’un na rasa me ya ke kan Ashraf Mutum sai zafin zuciya na hanasa ba sau ɗaya ba sau biyu ba Akan an samu saɓani kace mace ta tafi gida to babu inda zaki zauna bar kukan bari na kirasa”
Ta na gama faɗa ta zaunar da saudat ta na nufar ɗakin da ta fito minti kaɗan ta fito kunnanta kare da waya ƙirar Iphone 17promax kafin ta katse ta dawo ta zauna idanunta akan Saudat da ke sharar kuka ta ce “Kema bakyajin magana Saudat yanzu haka wani laifin kika masa shi kuma da zafin zuciyar masifa me kika masa“
Batace komai ba sai cigaba da kuka da tayi Ummy ta girgiza kai ta ce “to Allah kyauta ya shiryeku girma kuke amma bakwasanin kun girma kuna da yaron shekara goma amma bakusan me kuke ba kullum kuna rigima yaranku na kallonku”
Minti talatin sai ga Shi ya Iso kallo ɗaya ya yi mata kamar zai bugeta ya ce”ubanme ya kawoki nan gidanku na ce ki tafi ba gidanmu ba “
Ummy na haɗe fuska ta ce “Ohh watau gabana ma zaka maimaita ko Ashraf to babu inda zata ta na da gidan da ya wuce nan marar mutunci sau nawa zan hanaka korar matarka wani irin mutum ne kai Ashraf ka dubi Sadeq da matarsa Ƙaninka ne ya ma rigaka aure amma shekara sha ukku matarsa ko yaji bata taɓa ba amma kai da saudat bazan iya Ƙirga adadin yajinta da faɗanku a gidan nan ba in banda ma yarinyar ta yi hankali yanzu ba ta tafiya ta na zuwa ta sameni me kake tunanin zai faru wallahi da tuni Aurenku ko bai lalace ba ya na gab “
Ya yi shiru ya na huci Ummy ta ce “Me ya Haɗaku yanzu kuma”
Saudat ta sa kuka ta ce “Ummy don Allah ba sai an maimaita ba “
Ya ce “kingani ummy tun a nan ta kama kanta ba ta da gaskiya idan ina faɗa maki rashin mutuncin yarinyar nan bakya yarda “
Ummy ta yi shiru ta na kallonsu har ga Allah Faɗan Saudat da Ashraf abun ya fara damunta ta ma rasa wani irin mataki za ta Ɗauka,
“Assalamu alaikum”
“Wa alaikumussalam Alhamdulillahi gwara da Allah ya kawoka Don gaskiya lamarin nan nema ya ke ya fara fin ƙarfi na gwada maza ku fara shiga”
Ummy ta faɗa idanunta akan Baƙin kamilallen dattijon da ke shigowa tsakiyar palon ya na zama gefen kusa da ita ya ce “To fa irin wannan Hamdala Haka Ummynsu me ya faru”
Ta ce”Ashraf ne bansan me ya haɗasu ba da saudat ya ce ta tafi gidansu na hanasa kalaman nan amma baiji ba”
Abba na cire glass ɗin saman fuskarsa ya mayar da hankalinsa gurin Ashraf ya ce “Ba na buƙatar jin Me ya haɗaku wannan kalamin kaɗai da kayi ya sanya duk gaskiyarka na baka rashin gaskiya lusarin namiji kawai “
Kafin ya maida kallonsa ga Saudat da ke sharar ƙwalla har lokacin ya ce”Kiyi haƙuri ƴata karki sanar da iyayenki ki fara shiri Zanyi muku booking Flight Ki je ki kawomun Passport Ɗinki daman Ranar Friday ni da ummynku zamu wuce umrah ki fara shiri tare zamu wuce sai ki bar masa ƙasar ma baki ɗaya ba ma gida ba”
Lokaci guda saudat ta bar kuka tare da sakin mirmushi ta ce”Nagode Abbanmu passport ɗin ya na part ɗinmu please Abba ya tsaya a nan naje na Ɗauko kar ya biyoni”
Abba ya ce “jeki ɗauko maza sannan ki harhaɗo da kayayyakinki na sakawa”
Cikin sauri ta Miƙe da zata wuce ta faki ido su Abba ya yiwa Ashraf gwalo wanda ya ƙara ƙuluwa akan haushin da Abba ya chusa masa Saudat na barin Wajen ya ce ,
“Haba Abba bakaji me ya faru ba ka Goya mata baya sanadin ta cigaba da Abubuwan da takemun Tsaki fa tayi mun Daga ina mata faɗa ta na latse-latsen wayarta ta bar tasnem na wasan ruwa alhalin Tasan laruranta na Lamonia kunsan ai bata da kunya na faɗa ta faɗa har ta tunzari ni na ce ta tafi gidansu tunda ban isa da ita ba sannan planning take na mata magana ba sau Ɗaya ba sau biyu ba ina buƙatar ƴaƴa tayi burus da ni shine yanzu ta zo angoya mata baya kenan ta cigaba da duk abunda takemun Shikenan nasan maganinta Aure zan ƙara daga chan ma ta tafi bangon duniya”
Abba ya ce “Ashraf to nima ko rashin kunyar zaka mana”
Ya ce “Allah ya huci zuciyarka Abba amma ni gaskiyata na faɗa“
Ummy ta ce “in dai haka ne gaskiya ba ta kyauta ba ƴaƴan da wasu ke nema ruwa jallu shine ita ke gudu wallahi ni duk a zatona Jinkiri ne kawai daga Allah to me yasa tun farko ba ka faɗa mana ba sai ka hau ta kuyi faɗa ina amfanin haka Saudat ba ta da wayau cikin hikima da ruwan sanyi wlh kace tayi abu bari ta ke amma ka hau ta da faɗa wataƙila ma maganganu masu ciwo ka dinga faɗa mata har itama ta biyeka tayi maka tsakin.
Abba ya ce “Ashe kin fahimta wannan masifar da ƴaccewa in banda raini a wajen mace me zata haifar maka “?
Ummy ta ce “Ayi Haƙuri yallaɓai a barsa haka “
Kafin ta maida kallonta ga Ashraf ta ce “ina yaran”
Ransa kamar an aiko masa da saƙon mutuwa ya ce”Su na tare da Dadynsu sun rakasa Asibiti Ziyara”
Ummy ta ce “to daga dawowa ƙasar ko hutawa baiyi ba Allah ya dawo da su lafiya na so tare ma zamuyi tafiyar da yaran to makaranta ita kuma Zenat ta na fama da laulayi saidai gaba idan Cikin nata ya yi ƙwari itama suntafi kartaga wannan karin an tafi da ƴar uwarta kaɗai nayi mata bayani anjima ta shigo insha Allah”