IBTIHAL HAUSA NOVELS PDF COMPLETE BY MISS HAJO.docx

Author :  Miss Hajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 36.4K words

jaririnta a hannun Zainab Shine wasiyarta na ƙarshe zainab ta matuƙar jin mutuwar Aisha,

Wanda lokacin ta so shayar da shi amma hakan bai yiwu ba sakamakon tsohon ciki da take ɗauke dashi dole sai haƙura tayi wata ƴar uwarsu ta shayar dashi amma anan gidanta saboda daman zawarace ,

sosai zainab ke Ƙaunar Adam Tamkar ɗan da ta haifa a cikinta yanda take bamu labari bata taɓajin banbanci tsakaninsa da ƴaƴan da ta haifa ba Lokacin Allah ya sauketa lafiya ta haifi Aisha watau Momyn Sajida daga nan kuma sai bayan shekara huɗu ta sake haihuwar wata ƴa macen ta ci suna Nafisa Kafin ta haifi Salma Momy na kenan Bayan ita ta haifi ɗanta namiji Allah yayi masa rasuwa,bayan shekaru biyu da haihuwarsu,

Ƴaƴanta sun taso cikin soyayya da ƙaunar juna gami da tarbiya haɗe da ilimin boko da na zamani domin Alhaji dikko mutum ne mai Tsananin Aƙida da Ƙaunar boko hakan ya sa duk ƴaƴansa suka taso cikin boko ba kowa yasan Da Adam ba uwa ɗaya uba ɗaya suke ba a cikin ƴaƴansa sai daga baya da mahaifinsa ya ke zuwa ganinsa kafin ya na da shekaru goma Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa a hanyarsa ta komaqa chan katsina da ya zo ganin Ɗansa daman shi kaɗai ya haifa a nan katsina akayi suturarsa,

A lokacin mutum ne mai arziƙin Gaske Ɗan kasuwa ne daman a harkar kasuwancinsa ya kaisa har Bama ya ga aisha ya aura gona ɗari Ya bari banda filaye da shanaye da gidaje tare da zunzurutun kuɗi masu yawa a lokacin ,

Wanda dukkan wannan dukiya ɗansa Adam kaɗai ya gada domin bashi da uwa bashi da uba wannan haushin ya sa Tun lokacin danginsa suka Tsani Adam Da uwar riƙonsa domin sun so su handame dukiyar Adam da mahaifinsa ya bar masa ,

Alhaji dikko ya tsaya tsayin daka wajen ganin Ya ƙwatowa adam haƙƙinsa sanin ba Allah a ransu ya sanya duka dukiyar Adam da ke garin ya sayar ya haɗa kuɗaɗen waje Guda ya saya Masa Manyan gonaki da filaye dukansu a maiduguri wanda hakan ya ƙara musu ƙiyayyarsu a ransu hakan ya sa tunda aka tafi da Adam ba su ƙara waiwayarsa ba Matsayinsu na Dangin Mahaifinsa,

To fa lokacin ne Adam da su Momynmu suka fahimci Alaƙarsu da adam,

Lokacin momy na na ƙarama momyn ibtihal ma na shekaru ukku shaƙuwa ce da soyayya ta musamman tun a lokacin tsakaninta da Adam ba wanda ya isa ya taɓa Nafisa ko laifi tayi ko Hajiya da ya ke haka suka taso suke ce mata ba ta isa ta yi mata faɗa ba bare duka inko aka taɓa ta ya dinga fushe-Fushe ko a makaranta a ba taɓa ta ita kuma ta na da jan baki kullum ya na tare mata faɗa har Allah ya kawo girmansu lokacin ne kowa ya fahimci soyayyar da ke tsakaninsu,

lokacin har anyi Auren Abba Bashir da Matarsa Lubna ƴar Niger state ce lokacin har ta haifa masa yara biyu yaronsa na farko ya ci sunan kakansu yusuf tsakanin yusuf da Marwan kwanika ne shekara biyu ta sake haihuwarta ɗanta namiji ya ci sunan Kakansa Dikko akayi masa inkiya da Marwan wanda daga nan haihuwar ta tsaya mata cik,

Anyi Auren Aunty Aisha Da mijinta Babban likita ne tun lokacin kafin daga baya ya samu babban cigaban aiki ya koma Canada da aiki wanda suka koma baki ɗaya lokacin ta haifi ƴarta mace Zainab lokacin ne akayi Bikin Nafisa da Adam bayan nan Aunty aisha suka wuce Canada Tare da mijinta da ƴarsu ɗaya ana ce mata Mahmah

A lokacin shi kuma Abba Bashir babban ɗan hajiya ya gama Degree ɗinsa inda ya samu babban aiki a Abuja,

Lokacin mahaifinsu Yayi ritaya Tsayayyen tsohon Soja jajirtacce tsoho mai ran ƙarfe da suka bautawa ƙasa suka sha Gwagwarmawar rayuwa Tsakani da Allah batare da cin haƙƙin kowa ba,

Nafisa Da Adam amarcin sati biyu sukayi a Bama suka wuce Kano Tare da amaryarsa domin a chan ya fara bautar ƙasa saura watanni shidda ya dawo gida wanda iyayen sun so ma ya bar Nafisa a gida amma fir ya ƙiya itama kuma sun lura tafi son ta bi mijinta suka ƙyale su suka tafi tare,

Cikin ikon Alkah daga Bautar ƙasa Adam ya na leƙawa Kasuwa Wasa-wasa a hankali ya fara ƙananun kasuwanci lokaci guda ya ji ba abunda ya ke ƙauna kamar kasuwanci abun ya shiga ransa sosai gefe guda suna shan soyayyarsa kamar su cinye juna da amaryarsa wata shidda na yi lokacin za su dawo gida Adam ya ce “shi fa ya ga guri”

Alhaji dikko da kansa ya zo ya ga irin hulɗar kasuwancin da Adam ya fara Hakan ya sa ya saida wasu daga cikin gonakinsa wanda lokacin suka ninka kuɗinsu sau goma ya basa domin ya jaraba fara kasuwar Lokacin ta na da Ƙaramun ciki ta na ta fama da Laulayi Hajiya da suka zo tare taso tafiya da ita har cikin yayi ƙwari amma fir ba kunya adam ya ƙi dole ta haƙura suka koma ita da Mijinta Watan cikin Ukku ya Ɓare bayan ta sha ƴar wahala wanda sunji baƙincikin ɓarewar cikin har sun fara sayayya domin ba ƙaramun guri suka ci akan cikin ba musamman Adam,Allah bai nufa ba,bayan nan ta samu samun wani cikin watansa biyu shima ya zube,

Aunty Aisha ta sake haihuwar ƴarta Sajida a chan Canada ta haihu hakan ya sa ba kowa ya samu zuwa ba,

Sajida na da wata Biyu suka zo Nigeria Bikin Momyna da tayi karatu nan abuja ta zauna gidan Abba bashir ta auri wani abokin aikin sa anan Bama aka sha Biki lokacin momyn Ibtihal na ta fama da wani cikin daman tare suka zo da Adam Domin nan da nan baya bari nafisa ta taka ba tare dashi ba dukda hidimar biki amma yaƙi bari ko kwana tayi cikin ƴan uwanta haka duk bayan isha’i zaizo ya ɗauke ta su tafi su aunty Aisha su dinga zolayansa da yazama mijin tace kamar ba namiji ba shima ya mayar mata don abuyar wasansa ce sosai,

An kai momyna Abuja wanda yanayin jikin Momyn Ibtihal don kowa ya kalleta yasan laulayi take ta fama dashi hakan ya sa ba aje da ita ba bayan biki da kwana biyu Adam ya zo musu sallama za su koma Hajiya ta ce ya koma amma ya bar Nafisa a gida har cikinta ya yi ƙwari,Sam Adam ya nuna a a da matarsa zai tafi Hajiya ta yi mirsisi ta ce “ba inda zaitafi da ita sai cikinta ya yi wata Huɗu ya yi ƙwari don ta fahimci dalilin zubewar cikin gwara ta zauna a wajenta ,

Adam ha da Kukansa kamar ba Namiji ba Hajiya ta ce “ko kukan jini zaiyi ba inda zaitafi da ita”

Nan fa Alhaji dikko ya sa Baki ya ce “ta bashi matarsa su tafi “lokacin momyn Ibtihal ta sanya kuka ta ce “ita a barta wajen mamanta”wanda hakan ya ƙular da Adam ya tafi da fushinta wanda hakan yawa hajiya daɗi daga baya Kuma sai nafisa ta ji Babu daɗi ta dingawa Hajiya Kuka ta mayar da ita Kawai ,

ta mata fata-fata Ashe fushin baije ko ina ba satin sa Ɗaya a kano ya dawo ya ce saidai ayi rainon cikin tare da shi ba irin faɗan da Hajiya basuyi masa ba akan ya koma ya baro hulɗoɗinsa da shagunansa ya ce babu inda zaije Dole suka haƙura suka ƙyalesa wanda shima nan gidan ya tare da zama cikin na yin wata huɗu hajiya ta karkatasu ta ce su koma gidansu Allah raba lfy wanda a ranar suka koma kano,

Sunci gaba da rainon cikinnsu cikin kulawa da tsantar soyayya Har ranar wata Alhamis Allah ya sauki Nafisa Lafiya bayan gwagwarmayar wahalar da ta sha ta haifi kyakyawar yarinyarta mai tsananin kamanni da ita Fara saidai bata kaita haske ba ko dan kasancewar babanta na da duhun fata Allah masani Amma yarinya so cute kyakyawa son kowa ƙin wanda ya rasa ,

lokacin duk yanda ake santin kyan ƴaƴan Aunty Aisha Mahmah da Sajida sai ibtihal ta shanyesu ga yarinyar ta zo da farinjinin mutane bayan kwana biyu da haihuwar suka koma Bama wanda a chan akayi suna yarinya ta ci suna Ibtihal ba sunan kowa ba me kawai hakanan mahaifinta ke son sunan tun suna Soyayyya daman yake cewa shi dai idan aka haifa masa mace Ibtihal zai sanya mata ya na son sunan wanda ita kuma ta ce a a Aisha za a sanya mata sunan mamansa sai ya ce sai ta ƙara haihuwar wata amma ƴarsa ta farko ibtihal ce sai gashi Allah ya cika masa burinsa ranar Adam hada kukan farinciki,Wata irin ƙaunar yarinyar ya ke tamkar ya cinyeta ba ya kara ko a gaban kowa Aunty aisha su dinga zolayansa Ya na ramawa wasa-wasa sai gashi yaƙi komawa kano wannan karin ma ya jingine kasuwancinsa har akayi arba’in shi ne har wankan Ibtihal domin lokacin Aunty Nafisa haka takecewa ba ta iya ba ita tsoro take ta shaƙa mata sabulu shiko adam ya tsorata tsaf ya iya wankan yarinyarsa hakan ya sa koda suka koma kano duk safiya shi ke mata wanka kafin ya tafi kasuwa bini bini ya hayo mashin ya dawo gida ya koma rabin hankalinsa na gurin ƴarsa,

Watan Ibtihal biyar aka haife ni Anan Abuja akayi suna sakamakon Dadyna Iyayensa mazauna Abuja ne amma asalinsu ƴan Jos ne Lokacin da akazo da ibtihal ta ƙara wayau kyanta na ƙara fitowa,

Sajida ta ba ibtihal Wata Bakwa nikuma Ibtihal ta bani Wata Biyar a haife nikuma sajida ta bani shekara guda hakan zaisa kiga duk mun taso kusan sa’anni,

Rayuwa na ci gaba da tafiya ta kowani ɓangare kowa na samun cigaba Abba Bashir ya faɗa harkar Siyasa Shi kuma Abban Ibtihal ya fara zama hamshaƙin ɗan Kasuwa,

Ƙaunar ƴarsa kullum ƙara ƙaruwa take a ransa wani irin gata yake mata wanda kowa tsoronsa kar ya sangartata matsayinta na mace ba ta bacci sai a saman cikinsa idan ba ta da lafiya har kuka ya ke domin shi mutum ne mai karyayyar zuciya da rauni akan abunda yake so ,

Arziƙinsa na ta gaba wanda lokacin Ibtihal na da shekaru Huɗu ya gina wani katafaren Gida a Anguwar Bompai G.R.A Miyangu Road,

Gida ne da ya haɗu ya kashe dukiya a ciki sunfara rayuwarsu cikin gidan ita daman chan mom Ibtihal ko a waccen tsohuwar anguwarsu ba ta shige shige bare wannan da kowa na gidansa sai ka gama rayuwarka ma bakasan makocinka ba,

A Lokacin ne daƙyal Abban Ibtihal ya yarda ta jona B U K karatu domin duka ƴan uwanta daga masu degree sai masters itace masifar kishi ya sanya ya hanata ta jona sai daƙyal dai yanzu ta yi sa’a ya barta ta jona wanda ita kuma Ibtihal aka sanyata a wata Tsadaddiyar makaranta,

A nan ne fa aka fahimci baiwar Ƙoƙarin ibtihal wata irin ƙwalwa gareta wacce cikin mutum dubu ya yi wuta a samu mutum biyar ma su irinta Karatu ɗaya takewa abu ta hardaceta gam a kanta hakan yasa Malamai ke matuƙar sonta ga yarinyar bata da hayaniya so silent saidai shegen shagwaɓa da kuka bata son abunda zai taɓa lafiyar jikinta shiyasa take da tsoro ba ta ko laifin da za a daketa kodan kasancewar ba a taɓa dukanta ba a gida,hakan ya sa ba abunda ta ke tsoro a rayuwa kamar duka har ta gama sch ba ta taɓa laifin da za a dake ta ba hakan ya sa ko tayi laifin malaman ke yi mata uzuri ba sa dukanta,

Dady kamar yanda take kiransa shi ke kaita school ya ɗauko ta kullum sosai mom tayi busy sakamakon zaryar karatu da take,

Lokacin ne yarinyar Maƙotansu wata mai suna Hauwa’u ta taɓa kawo mata takalman sayarwa kara ya sanya mom saya ba don tayi niyya ba lokacin ne hauwa’u ta ga Ibtihal ta nuna ta shiga ranta ta so ta jata gidansu su yi wasa taƙi binta daman momynta ba bari zatayi ba,ta ce mata Akwai Ƙanwata Jamila Sa’arki ce kina so ta dinga zuwa kuna wasa”

Da sauri Ibtihal ta gyaɗa mata kai saboda Ibtihal na son mutane kodan kaɗaicin da ta taso cikinsa ita kaɗai wajen iyayenta ga su basu da kowa a kano ba inda suke zuwa ita da mom ɗinta,

Aiko washegari sai ga Hauwa’u ta kawowa Ibtihal Ƙanwarta a ƙalla zatayi shekarun sa’annin Ibtihal ko ta girmeta baifi da shekaru biyu ba,

Daga ranar Ibtihal Ta yi ƙawa suka fara wasa suka zama tamkar ƴan uwa kullum jamila na gidan wanda lokacin Ibtihal ba ta taɓa zuwa gidansu ba don Dadynta ba ya barin ta fita ko bakin get tsoronma fitan take bazata iya ba ,gani take idan ta fita ita kaɗai saceta za ayi don ibtihal ba dai tsoro ba,

kullum Jamila na gidan don ita lokacin ba ta zuwa makaranta amma ta san lokacin da Ibtihal ke dawowa daga school ta na dawowa ta ke zuwa a nan take cin abinci ana magrib mom ta ke sanyawa mai gadi ya rakata gidansu kullum haka sai yazama har su mom sunyi sabo da Jamila kusan wata guda jamila ba ta fashin zuwa wata rana mom ta ce yau dai zataje taga gidan su jamila ta faɗawa Dad da yamma ya amince mata da kashedin karta jima aiko ta shirya sosai sukayi kyau ita da ƴarta kallo ɗaya zaka musu kasan dukiya ta zauna don dad ya tsaye musu ba abunda suka nema suka rasa sutura ko saidai su ba wani don sana’arsa ce manyan shagunsa Ukku a kwari duk na sutura wanda ba wanda baisan da zamansu ba a kasuwar yanda ya shahara,

Mom ta kama hannunsu su biyun suka fito gida ukku suka Wuce Jamila ta nuna musu gidansu Tsayawa mom tayi kallon gidan Safa ta numfasa ta ce “

Hmmm Wlh Lena Baƙinciki da takaicin Ƙarasa miki labarin nan nake domin daga nan ne ba na Ƙaunar Ko tunawa jin baƙinciki da tsananin takaici nake ji bana son ko tunawa da tsinannun la’anannun mutanen nan da sukayi silar rugujewar Rayuwar ma’auratan da samun masu Ƙaunar junansu kamar su sai an tona”

Da sauri Lena ta ce “Haba Besty meyasa kiyi haƙuri ki ƙarasamun saida aka zo inda na matsu na ƙarasa jin labarin zaki nemu ki tsaida mu “

saida suka sha juice me sanyi kafin Safa ta sauke Ajiyar zuciya ta ce”

“zuwan Hauwa’u gidan tare da Farawar Abokantakar Ibtihal da Jamila da wannan rana ta zuwansu gidan su shine mafarin silar Ƙaddarorin momyn Ibtihal Tare da ita kanta Ibtihal ɗin da ahalin gidan baki Ɗaya da ka na da ikon dawo da rayuwarka baya da ka dawo ka gyara wasu abubuwan da dama Da ba ma mom zatayi sha’awar rayuwarsu a kano ba bare komawarsu Bombai bare har su haɗu da waɗannan Mazanbata kuma azzalumai macuta ,Mayaudara,waɗanda babu Allah a ransu,

Kamar yanda mom ta ke Labarta mana saida ta Ƙarewa gidan Kallo ɗan gida ne madaidaici mai Ɗauke da ƙaramun ƙofa milk a duk arear ma shi kaɗai ne za a kira da gidan talakawa domin dukkan gidajen anguwar mafi yawaici Hamshaƙan gidaje ne”

Mom haka kawai ta ji faɗuwar gaba ta Daure dai ta shiga hannunta riƙe da na Ibtihal Da Jamila Da sallama a bakinta…………✍🏽

*PAGE UKKU YA RAGE MU KAMMALA FREE PAGE NA IBTIHAL KUNA DA DAMAR FARA PAYMENT TUN YANZU AKAN 500 KACHAL TA ASUSUN BANKIN NAN 7026166536 OPAY HAJARA ABUBAKAR LAWAL TARE DA SHAIDAR BIYA TA WANNNAN NO 07026166536*



_*Miss Hajo ce*_🤙🏿

🪅*IBTIHAL*🪅

~MALLAKAR~

*HAJARA L SADEQ*

(miss Hajo)

MARUBUCIYAR👇🏼

Auren wata tara

Ni da yaya arman

Matar uncle

Najmat abiy

Komai mukaddari ne

Khadijatul Sabren

Ribar so

Mata ta ce

*And now*

*IBTIHAL*

*ZAMU KAMMALA FREE PAGES NA WANNAN LITTAFIN A PAGE 15 KUNA DA DAMAR FARA BIYAN KUƊINSA TUN YANZU 500 TA WANNAN ASUSUN BANKIN 7026166536 OPAY HAJARA ABUBAKAR LAWAL TARE DA SHAIDAR BIYA TA 07026166536*

*DEDICATED TO MY HUSBAND*

🅿️…………………………..*14

Ta shiga da sallama bakinta wata dattijuwa ta amsa mata tare da sakin fuska ta tarbesu mom na kallon gidan Ɗaki huɗu sai kitchen da banɗaki tsaf-tsaf sai suka burgeta don mom akwai son tsaf ta zauna kan tabarmar da aka shimfida ta gaishe da matar cike da girmamawa dukda mom na ɗan satar kallonta ganin yanda take zubi kamar wacce ta taɓa bariki Lokaci guda saida ta ja mom sukayi sabo ta ɗauko mata wannan hirar ta ɗauko wacce itakuma jamila da ibtihal suna game a tab ɗin ibtihal”

A lokacin ne hauwa’u ta dawo ta gaishe da mom ta na ɗaukar kayan sana’arta na Awara ta na fita ta na lodawa a napep ta na dawowa mom ba ta jima ba ta fice bayan an cika ta da ɗanyar awara mom ta amsa ta fice tare da ƴarta ranar da Dare ta soya awarar kamar bazataci ba saikuma ta tuna tsabtar gidan hakan ya sanya ta ci wanda sosai taji daɗinta zatace bata taɓa cin awara me daɗin ta ba Ta ba Ibtihal amma taƙi amsa domin bata taɓa ganinta ba ma bata ci,

mom ta cinye kayanta tas,

Tundaga ranar wasa-wasa alaƙa mai ƙarfi ta fara shiga tsakanin mom da Gidan Turai Suka fara shaƙuwa Hauwa’u na zuwa na taya mom aiki ita dama jamila kusan kullum suna tare da Ibtihal a gidan,

kusan kullum sai Mama turai ta aikowa mom Awara soyayya da yaji me daɗi mom idan ta bada kuɗin aƙi amsa Cikin ƙanƙanin lokaci Turai ta zamewa mom uwar Ɗaki Abokiyar shawara Ta nunawa mom ƙauna tamkar ita ta haife ta da farko Dad

11 / 13