KAMAR DA WASA HAUSA NOVELS COMPLETE PDF.doc

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 36

48K to 51K   out of 106.8K words

mutum aciki,ahaka yakwana yawuni har dare yayi sai dai idan lokacin sallah yayi yatashi yayi yakoma ya kwanta,har dare atakaice dai acikin wannan halin fahad ya kwana agidan babu Wanda yasani har saida safiya tayi lokacin da baba zai fita yazo saitin kofar dakin yajiyo fahad yana yin tari cikin mawuyacin hali, buga kofar baba yashiga yi wanda har karar bugun ta janyo hankalinsu ayiyah suka fito domin ganin meke faruwa, cikin mawuyacin hali yataso yazo ya bude kofar yana jin kamar zai fadi saboda rashin karfin da jikinsa ke fama dashi,wuri yasamu yazauna ya jingina da bango yana kallon su baba dake kokarin shigowa cikin dakin,

"Muhammadu... Ya akayi? Tun yaushe ka shigo cikin dakin nan?" Baba yafara tambayarsa cikin mamaki,

"Tun jiya ne baba..."

"Ikon Allah, to ya zakazo kashiga daki karufe kanka kai daya, ina matar taka?" Mamuh tafada cikeda mamaki,

"Na saketa...."

Ai gaba dayansu jin maganar tasa sukayi tamkar saukar aradu acikin kunnuwansu.

"Saki.....?"

Su ayiyah suka fada cikin razani har bakinsu na haduwa wurin tambayarsa,

"Muhammadu meyasa kayi haka? Meyasa ka yanke hukunci da kanka batare da ka tuntubemu ba?" Baba yafada cikin kwantar da murya,

"Baba kuyi hakuri dan Allah....."

Dukansu samun wuri sukayi suka zauna cikeda jimami, sunfi mintuna goma ahaka babu wanda ya iya yin magana zuwa can baba yaja gwauron numfashi cikeda damuwa yace,

"Fahad meyasa ka saki yarinyar nan yar mutunci yar gidan mutunci? Laifin me tayi maka haka...?"

Kasancewar dan jiri na daukarshi yasashi zamewa ya kwanta idanuwanshi taf da hawaye,

"Baba ni bata yimin laifin komai ba..... Kawai..... Kawai dai.... Kawai bazan cigaba da zama da ita bane...."

"Me? Fahad acikin hankalinka kake kuwa? Wannan wanne irin shashanci ne? Ina kataba ganin anyi haka? Kowa da yake zaune da abokin zamansa ba hakuri yakeyi ba?" Mamuh tafada cikin fada,

"A'ah yimasa ahankali.... Ai ba tatashi zamu biyaba, ni yanzu haka ta gidansu yarinyar zanbi inbaiwa mahaifinta hakuri sannan innemi bikonta adawo da ita dakinta tun abu baiyi nisa ba.... Saki nawa kayi mata?" Baba yakarashe maganar yana kallon fahad wanda idanuwanshi ke rufe,

"Baba babu aure atsakaninmu fa yanzu saboda saki.... Saki ukun...."

Ai tun kafin yarufe bakinsa su ayiyah suka rufeshi da fada ta inda suke shiga ba tanan suke fitaba shi baba sai shiru ma yayi yana saurarensu daga karshe ayiyah tatashi tafita cikin fushi, saida itama mamuh tafita sannan baba yadora da nasa fadan amma shi nasa cike yakeda nasiha, sun jima baba yana yimasa fada sannan yatashi yafita bayan yasanar dashi cewa gobe zaije gidansu bilkisu su gana da mahaifinta, agaba baba yasashi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? suka shiga cikin gida har dakin ayiyah yakaishi sannan yafita shikuma fahad ya kwanta nan saman daddumar dake shimfide a falon, sam ayiyah bata saurareshi ba bare ta kulashi sai can wurin azahar sannan tashigo wurinsa dauke da kwanon kunu wanda ta dama masa domin ta fahimci baici komai ba kuma yana tare da yunwa domin gashi nan duk yafige ya fita kamanninsa, yako ji dadin kunun nan domin da zafinsa haka ya zauna yasha da yawa sannan yakoma ya kwanta yana jin irin sarawar da kansa keyi masa.

A bangaren bilkisu kuwa tana fita daga gidan fahad sai kuma hawaye suka fara gudana daga idanuwanta, dama mata haka suke wani lokacin sune zasu nemi sakin da Kansu amma ana sakinsu kuma sai sufara kuka karasa dalilinsu, napep ta tare tahau tana kuka har sukaje kofar gidansu, da yake safiya ce Abba yana gida ko fita baiyi ba, ammah tana kitchen itada Rabi mai aikinta suna hadawa Abba abincin karyawa.

Fuskarta sharkaf hawaye tashiga cikin gidan shiyasa kallo daya ammah tayi mata tagane cewa ba kalau ba musamman ma da taganta da sanyin safiya irin wannan, barin abinda takeyi tayi suka shiga cikin falonta har lokacin bilkisu kuka take wanda ita kanta bata san dalili ba,

"Mai gado duk yanda akayi ba lafiya ba saboda idan lafiyace takawo ki bazaki taba zuwa da safiya irin hakana sannan bazaki shigo kina kuka ba...."

Hawayen fuskarta ta goge yayinda wasu ke kara zubowa,

"Ammah ya sakeni......"

Salati ammah tashiga yi tana karawa cikeda tashin hankali,

"Saki mai gado? Saki fa kikace? Meya hadaku? Wani abun kikayi masa?"

Girgiza kanta tayi tana hawaye,

"Babu abinda nayi masa..."

"To Allah yarufa asiri... Zauna nan zan kawo miki abin karyawa"

Tashi ammah tayi takoma kitchen suka karasa hada kayan karin kumallo ta dauki na bilkisu takai mata sannan ta dauki na abba tanufi wurinsa cikeda karfin hali take gudanar da komai, cikin farin ciki da annashuwa suka karya tareda Abba saida suka kammala sannan tayi kokarin sanar masa,

"Ga mai gado can fa tazo dazun nan babu jimawa...."

Shiru abba yayi yana kallonta,

"Lafiya kuwa?"

"Ba najin lafiya ce takawo ta gaskiya"

"Kira min ita naji"

Tashi ammah tayi takwashe kayan da suka gama amfani dasu tafita, yanda tabar bilkisu haka takoma ta sameta tana zaune sai faman goge hawaye take,

"Zo abbanku yana kiranki...."

Wata mummunar faduwar gabace ta ziyarceta, tunda aka fara rigimar sakin nan bataji ko darr ba sai yanzu saboda bata tanadi amsar da zata baiwa abba ba, gabanta na faduwa har suka shiga falon Abba,

"Uwata lafiya? Meke faruwa?"

Zama tayi gaban Abba,

"Abba sakina yayi..."

"Saki.... To laifin me kikayi masa?"

"Babu abinda nayi masa"

"Babu abinda kikayi masa?" Inji ammah, daga kai bilkisu tayi alamun ehh,


"To shikenan zan kira mahaifinsa dashi kansa yaron suzo aji mai yafaru saboda shi aure gyarashi akeyi akoda yaushe saboda yafi rabuwar tunda ba asan abinda Allah ya boyeba..."

"Abba saki ukune fa...."

"What...? Yana shaye shaye ne?"

"A'a baya shan komai"

"Amma har saki uku? Yanzu abinda yaron nan zaiyi mana kenan ina yimasa kallon mai hankali? Shikenan tashi kije, Allah yazaba miki abinda yafi zama alkhairi arayuwarki.... Kiyi hakuri kinji uwatah, wannan jarrabawa ce babu komai insha Allah zaki samu wanda yafishi"

Tashi tayi tafita har lokacin bata daina kukaba yayinda shikuma Abba da ammah ke can sunata jajanta abin gaba dayansu zukatansu babu dadi.Tana nan zaune falon ammah ta kifa kanta jikin kujera ammah tashigo cikeda damuwa ta zauna sannan daga bisani ta daga kai ta kalleta,

"Mai gado wannan kukan da damuwar babu abinda zai tsinana miki sai ko ma yakara miki damuwa dan haka ki tattara komai ki mikawa Allah lamarinsa sannan kibaiwa zuciyarki hakuri amma wannan kukan ba mafita bace.... Ga abinci nan dauki kici..."

Batayi musuba ta share hawayenta taja abincin da Ammah takawo mata soyayyiyar agada da kwai sai farfesun hanta da ruwan zafi, kadan ta dan tsakura tahada tea tasha ta mayar ta rufe kwanukan, kafin wani lokaci har ammah tasa angyara mata tsohon dakinta nada wanda yanzu yake arufe babu kowa aciki domin mai aikinta ba kwana takeba da safe take zuwa tatafi da daddare, komai da take bukata akwaishi acikin dakin gashi Rabi ta shirya mata kayanta cikin drewar, bata yarda sunyi waya da hamood ba domin suna tare da ammah duk tsawon yinin ranar sai dai wani lokacin idan tayi shiru sai tarinka tambayar kanta anya kuwa tayiwa fahad adalci? Anya kuwa tayi abinda yadace? Haka take ta yawaita yiwa kanta wadannan tambayoyin amma daga karshe tayi fatali dasu tana ji aranta abinda ta aikata daidai ne domin ita hamood takeso ba fahad ba. Tun aranar dukkan yan uwanta suka samu labarin abinda yafaru marar dadi wai auren bilkisu da fahad ya mutu, duk waya suka bugo mata suna tayata jaje da jimami kafin suzo gidan gobe, duk da yinin ranar tayishi sukuku ne amma da daddare tasamu kuzari domin sunyi waya da hamood ta zayyane masa dukkan abinda yafaru yayinda shikuma yace da zarar ta kammala iddah zai fito sai maganar aure.

Fahad haka yawuni kwance yana ciwon kai sai daf da magrib yasamu yayi wanka bayan ayiyah ta dafa masa ruwan zafi gashi throughout baici komai ba sai ruwan kunu da yaketa sha sama sama, gaba daya yayunshi fada suka rinka yayyafawa lokacin da labarin abinda yafaru yaje musu shi dai yaki magana domin shi kadai yasan abinda yake ji. Yana fitowa daga wanka yadauki t shirt acikin kayan abba yasaka da wando yayi salla ya kwanta har saida baba yashigo sannan yaga ayiyah tashigo rikeda maganin ciwon kai da balangu wanda baba yakawo, agaba tasaka shi har saida yaci naman yasha magani sannan tafita tabarshi babu jimawa bacci ya daukeshi ko sallar ishah bai samu damar yi ba. Washe gari ma da ciwon kan yawayi gari ga rashin iya cin abinci dake damunsa aranar da salim yazo yasan komai na daga abinda yafaru amma fahad bai sanar dashi gaskiyar abinda yafaru ba kawai dai yafada masa cewa sun rabu da bilkisu rabuwa ta har abada. Atakaice dai saida fahad yayi kwana uku akwance ganin haka yasa su ayiyah matsanta masa akan yaje koda chemist ne idan bazaije asibiti ba, wanka yayi ya shirya cikin kayanshi wanda salim yaje ya debo masa jiya, riga kalar ruwan toka mai botira sai wando rouser baki, ahaka ya daure yafita zuwa chemist din daga can kuma yawuce shago iya tj da customers dinsa guda biyu wadanda ke jiran yagama yimusu dinkinsu yabasu kadai yasamu acikin shagon, zama yayi kan keken hamza bayan sunyi musabaha da tj, yana nan zaune yana hango mutane daketa kaiwa da kawowa awaje ya hango husnah wacce tafito yin cefane direct shagon tashigo ko cefanen bata kai ga yiba, fuskarta da alamun damuwa ta karaso gabansa ta zauna,

"Haba ya fahad.... Ina kashiga kwana biyu dan Allah? Gaskiya ka sani acikin damuwa wallahi...."

Tagumi ya rafka yana kallonta,

"Husna banida lafiya ne...."

"Ayyah my prince sorry.... Tun yaushe? Meke damunka? Kaje asibiti?" Tajero masa wadannan tambayoyin cikin damuwa,

"Yanzu ma haka daga chemist nake nabiyo ta nan...kinga magungunan da nakarbo nan....."

"Ayya sannu... Muji... Da zazzabi?"

Tafada cikin sanyin murya tana kai hannu goshinsa zuwa wuyansa, baiyi yunkurin hanata ba har tagama tattabashi domin jikinsa akwai alamun fever kawai dai bai gama sauka ajikinsa bane,

"Sorry bari naje kasa nasamo allura nayi maka saboda bana so zazzabin yarufeka...."

Baiyi magana ba sai kai da yadaga mata kawai nan tayi maza ta sauka kasan plaza din tashiga wani pharmacy tayi amfani da kudin hannunta tasiyo alluran da take bukata guda uku takoma wurin fahad lokacin tj yafita masallaci sallar azahar customers dinsa kuma sun tafi, zama tayi gabansa tana hada allurar sai faman girgiza kai takeyi alamun tausayawa,

"Ya fahad kayita zama da ciwo ajikinka tun tuni baka nemi magani ba...."

Hannunshi daya ta kama ta yimasa allurar a damtsensa sannan takara yimasa wata daga bisani takoma daya hannun tayi masa guda daya.Jiri yaji yafara daukarsa nan yayi gaggawar riketa gudun kada ya fadi ai kuwa ta riku a hannun maza domin ji tayi kamar zai ballata, saida tajira allurar ta dan fara sakinsa sannan ta fita takira mai napep yazo har gaban plaza din ya tsaya, cikin shagon takoma ta kamo fahad suka fito dai dai lokacin da tj yadawo daga masallaci shine ya rike fahad din yataimaka masa yakaishi cikin napep, tare da husnah suka tafi gidansu yayinda shikuma tj yakoma shago, har gida husnah ta rakashi amma bata shiga cikiba daga waje ta tsaya bayan taga shigarshi gida itama tajuya tatafi.

Sosai bilkisu ta ware ta sake bata saka damuwar komai aranta ba dan kamarma harsu maama sun fita damuwa amma ita ko ajikinta saboda sunata shirya yanda al'amuransu zasu kasance itada hamood sannan kullum sai yabita office sunsha hirarsu ta soyayya shiyasa basuda matsalar komai, bayan sati biyu da faruwar lamarin suka shirya zuwa kwaso kayanta agidan fahad itada su maama dama shi fahad rabonsa da gidan tun ranar da bilkisu tasa kafa tabar gidan dan hatta kayan sawarshi ma da sauran kayan bukatunsa na yau da kullum sai salim ne yaje ya debo masa shiyasa ranar da zasu kwashe kayanma sai salim dinne yaje yabude musu gidan tunda gidansu fahad din suna da masaniyar za azo adebi kayan saboda baba har gidansu bilkisu yaje suka tattauna da Abba akan maganar tareda baiwa juna hakuri akan abinda yafaru, wuni su bilkisu sukayi suna aikin tattare kayan zuwa karfe uku na yamma sun kwashe komai babu abinda suka bari sai akwatunan lefen fahad kamar yadda ta sanar dashi tun farko, salim bai bar kayanba ya kwashesu zuwa gidan anty fauziyya can yabarsu sannan yakoma wurin fahad wanda ke kwance ciwon kirji da ciwon kai na addabarshi,

"Salim ta kwashe komai nata ko? Dama nasani..."

Kallonsa salim yayi cikin tausayawa,

"Wai abokina ya akayi hakan tafaru? Meyasa ka saketa? Yanzu baku saniba ko kilama tanada juna biyu kuma katashi ka saketa...."

Girgiza kai fahad yayi,

"Bata da wani ciki saboda babu...."

Sai kuma yayi shiru bai karasa ba,

"To ai laifinka ne, danme zaka zuba mata ido kazauna kana kallonta? Da ace kayi abinda yadace da tuni yanzu wallahi kuna tare tunda ko bata zauna dan kaiba dole ta zauna dan cikin jikinta...."

"Salim mubar wannan maganar kar zuciyata tafashe..."

"Allah ya sawwake yabaka lafiya, amma yakamata kayi gaggawar cireta aranka kamar yadda itama tayi..."

Shiru fahad yayi masa domin shi kadai yasan abinda yakeji, haka yayita murkususu har zuwa dare danma tare da salim din yanzu suke kwana, karfe 9 nadare a asibiti tayi musu saboda tsananin da jikin fahad yayi wani zazzafan zazzabine ya mamayeshi inbanda karkarwa babu abinda jikinsa keyi ga ciwon kirji dake barazanar tarwatsa mata hakarkari wannan dalilinne yasa su baba kaishi asibiti shida salim, babu bata lokaci aka bashi gado nan aka shiga kara masa ruwa babu ji bare gani saboda jikinsa yagama galabaita sosai.......


*Idan har kin san baki biya ba kiyiwa kanki adalci nima kiyi min karki karanta.*



*_Ummi Shatu_*

? *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*KAMAR DA WASA...!*



_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



*29*



***Tunda aka kai fahad asibiti yake cikin mawuyacin hali gaba daya bai san a inda yakeba bare yasan wanda ke kansa, babban likitan da yake dubashi sai faman fada yake tayiwa su baba yana cewa ya za ayi abar karamin yaro kamar fahad yakamu da ciwon hawan jini wanda ke barazanar taba kwakwalwarsa da lafiyar jikinsa? Domin acewar likitan Allah ne kadai ya takaita abun aka kawoshi asibiti dawuri amma da ace ba akawoshi tun wuriba to irin wannan ne kesawa mutum yana tsaka da tafiya ya yanke jiki yafadi shikenan yahadu da babbar lalura dan haka yazama dole asan yanda za ayi yanisanta kansa da damuwa da yawan tunani domin jininsa yayi masifar hawa hawan da ba aso dan haka yanzu dole akan magani zasu dorashi domin lalurar ta rigada ta kamashi. Daga ayiyah har mamuh kuka suke yi jin wai dan karamin dansu yahadu da cutar zamani ta hawan jini tunda ko su da suke tsoffi basu gamu da irin wannan ciwonba lallai wannan jarraba ce daga Allah, kullum a asibitin suke wuni suna kula da fahad, salim da ya Abba wanda yazo gida saboda dan break din da suka samu na good friday Easter monday, suke kwana awurin fahad sannan suna kula dashi, husnah ma kusan kullum sai tazo asibitin ta dubashi wani lokacin ma har girki take iyo masa, shi dai fahad tunda yafara bude ido dishi dishi yake kallon kowa baya ganin mutane clearly sai ahankali sannan ganinsa yasoma washewa har yadawo daidai acewar Dr Allah ne yarufa asiri abun bai shafi ganinsa ba, tunda yafara gane mutane bai furta koda kalma daya ba har yaji dan sauki, karin ruwannan da aketa yimasa har yagaji dashi gashi duk jikinsa ciwo yake yimasa saboda alluran da aka huhhuda jikinsa dasu, satinsa biyu a asibiti aka sallameshi bayan andorashi akan magani sannan duk karshen wata zai rinka zuwa yana ganin likita, da yamma aka sallamesu suka tattara suka koma gida. Wanka yashiga yasamu yayi yafito Abba da salim na zaune saman katifa salim na karanta labaran da BBC suka saki akan Facebook,yarfe hannu fahad yayi domin har lokacin hannunsa na dama akwai cannular ajiki wadda har hannun ya dan kumbura kadan musamman ma wurin da aka saka cannular din, zama yayi gefen katifar yana duba kayan da zai saka yana ji aransa dole yabar garin kano domin yayi masa zafi bazai taba iya cigaba da zama agarinba,

"Yazama dole ma inbar garin nan wallahi....."


Dagowa Abba yayi ya kalleshi sannan yagyara kishingidar da yayi agefen katifar,

"Kamar ya?"

"Ya Abba wallahi bazan iya cigaba da zaman garin nan ba.... Gaba daya garin yafita akaina"

"To ina zaka tafi?" Salim ya bukara yana kokarin tashi zaune,

"Salim karatu zan koma...., kuma ba arewa ba, kudu zan tafi idanma son samune inbar kasar gaba daya ko Niger ne intafi"

"Fahad kenan sai hakuri fa rayuwar nan, kayi hakuri kadauki abinda yafaru dakai a matsayin jarrabawa...."

Jin abinda yaya Abba yafada yasashi yin murmushin dole shi kansa ajikinsa yana jin irin ramar da yayi duk yadawo wani shafal shafal dan har yakasa da akiba, bai sake magana ba yadauki bakar round neck t shirt mai gajeren hannu yasaka sannan yasa blue din wando yamike yana laluben turarensa yana jin zuciyarsa na suya,

"Bilkisu wallahi kin yiwa zuciyata tabon da bazai taba gogewa ba har abada......" Yafada acikin zuciyarsa yana kokarin feshe jikinsa da turare, yana gamawa yanufi kofa zai fita domin so yake ya dan fita ya zagaya ko zai ji karfin jikinsa saboda yanzu kam baida wani karfi na azo agani,maganar salim ta dakatar dashi daga yunkurin fitar da yayi niyya,

"Lover boy ga husnah fa na magana a whatsapp....."

Komawa yayi da baya yakarbi wayar yana duba sakon nata kamar haka,

_My prince ya jikin? Kasamu kayi wankan kaci abinci....? Dan Allah karka zauna da yunwa_

Murmushin karfin hali yayi yana kallon salim da ido salim yayi masa alamar tambaya, daga girarsa guda daya yayi ya tsuke baki har lokacin fuskarsa dauke da murmushi, dariya salim yayi,

"Abokina kenan.....,husnah fa kullum idan taje dubaka sai tayi kuka"

Kafin fahad yayi magana Abba yatashi yafita yabar musu dakin gaba daya dan suji dadin tattaunawa dakyau, su dinma basu wani jima acikin dakinba suka fita, da kafa suka dan bi lungunsu fahad har zuwa bakin titi domin fahad ya ware kafarsa sai magrib sannan suka koma gida. Cikin kwana biyu jikinsa ya dan warware yaji dama dama amma kuma har lokacin raunin dake cikin zuciyarsa bai warkeba kawai yana daurewa ne sannan yaji dadin cewa baba saki uku yayiwa bilkisu domin da yace saki dayane yasan dole atursasasu sake zama da juna koda kuwa bata so shikuma bazai so hakanba.

***

A bangaren bilkisu kuwa tana kammala idda abba yace hamood dinta yafito saboda kowa agidan yasan hamood hatta iyallo mutanen

17 / 36