KAMAR DA WASA HAUSA NOVELS COMPLETE PDF.doc

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 36

21K to 24K   out of 106.8K words

ginin nashi ke bukata, kamar koda yaushe nan suka baje atsakar gida suka sha hirarsu har 9 nadare sannan yashiga daki bayan yarufe kofar gida. Wanka yafara yi sannan ya dauki sakon da bilkisu tabiyoshi dashi, farfesun kayan cikine yasha kayan kamshi da lemon kankana mai dankaren sanyi sai ruwa, duk da yasan zaiyi wuya ace itace ta girka amma yana fatan hakan shiyasa ma yazage ya cinye tas, saida ya dan zazzage cikinsa sannan ya kwanta, wayarshi yadauka yakunna recording din da yayi na programs dinta nan muryarta radau ta bayyana, haka yarinka bi daya bayan daya yana saurara.....




*_Ummi Shatu_*

? *HASKE WRITERS ASSO.*


*KAMAR DA WASA...!*



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


*15*

*Kamar da wasa na siyarwa ne duk mai ra'ayin karantawa ta biya saita karanta, masu fitar min da book kuma kusani Allah yana ji kuma yana gani sannan yana jiran kowa a madakata*


****Akwana atashi alamari sai kara matsowa yake bilkisu ji take kamar tayi hauka domin har yau bata samu hamood ba amma tasawa ranta ko ranar dauren aure ne hamood yadawo mata tilas tafasa auren fahad ya aureshi, duk wasu shirye shirye tuni anfara su domin fita kunyar jama'a musamman ma bakin da za agayyata, su Hindu kuwa kusan kullum suna hanyar gidan abin nema yasamu, amaryar dai kawai tana binsu ne amma har cikin zuciyarta bata son wannan auren kawai dan dai ta gujewa jarabar iyallo da auren ya mudan ne.

Ango fahad kam abangarensa komai yana tafiya daidai yanzu hakama adaren jiya salim ya rakashi yaje kasuwa suka siyo akwatunan da za azuba lefen aciki, saida yaduba mai tsada ajin farko w???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?anda baza araina ba sannan yabiya kudin danma yasamu ragi kasancewar shagon baffa ne yayan salim,akwatuna guda biyar yasiyo har dan kit na shida kalarshi pink mai haske sosai sai walwali da kyalli yake, dakin mamuh yakai domin acan ake tara kayan wanda kusan yanzu komai yagama haduwa sai dan abinda ba arasa ba, kowa saida ya yaba da wadannan akwatunan domin sunyi mutukar kyau, shifa yanzu wani girma yake jin yazo masa saboda zaiyi aure. Daren ranar baiyi bacci da wuriba sai wurin 2 nadare, washe gari bai fita shagoba sai yamma dan har saida yayanshi Abba yadawo ya iske shi agida,yana dakin yana baje akatifa amma ba bacci yakeyi ba idonshi biyu,

"Kaga ango... Saura wata nawane?"

"Saura yan satittika fa, saura sati nawa zakace ba wata nawa ba?"

Dariya Abba yayi yanemi wuri ya zauna bayan ya cire rigar jikinshi,

"To Allah yanuna mana ashe abin yazo"

"Yazo gaskiya domin saura kiris"

Dariya Abba yayi saboda shi gaba daya kallon abin yake kamar a mafarki wai fahad ne zaiyi aure. Da yamma yana shago yayiwa bilkisu text ya sanar da ita za akawo lefe nanda kwana biyu domin ayiyah tace yakamata akai kayan haka nan tunda yan uwa da abokan arziki sun gama gani, dawo mishi da reply tayi tace Allah yakaimu, wani text din yasake tura mata wai wanne colour din fenti zai yiwa gidan nanma tadawo da reply tace light purple. Bayan faruwar haka da kwana biyu aka shirya kai lefe tun ana igobe za akawo lefen iyallo aka sauka itada yafendo domin akarbi komai dasu, yan uwan ammah kuwa sai ranar da za akawo lefen sukazo da safe, anyi hidima iya hidima sannan annuna bajinta domin anyiwa baki tanadi na musamman, mamuh da anty Fauziyya da Anty asabe ne suka kawo lefen sai maman su salim da matan yayun su fahad guda biyu juwairiyya da kubra,

Acan gidansu bilkisu kuwa gida cike yake da mata ita kam tana daki ita da khulsum bayan sun dawo daga aiki, su maama kuwa ba zama ana can ana raping din soye soyen da za abaiwa baki tun safe suke aiki itada su Hindu ammah bata saka musu ko hannu ba sai dai tazo taga me ake ta komawarta daki wurin baki. Misalin karfe biyar na yamma baki suka karaso hajiya iyallo da guda da shewa ta taresu nan aka soma shiga da akwatina falon ammah inda yan karbar kayan suke, sosai lamarin ya kayatar domin kowa sun girmama kowa, gwaggo badiya kanwar ammah me bimata itace takawo tukwicin dubu talatin ta basu,basu bar gidanba sai jikin magriba dauke da garar arziki nan kowa ya raja'a wurin kallon kayan banda su meenah dake can dakin bilkisu suna tasu shaftar ita kuma Hindu na kwance tunda suka gama wadannan soye soyen kanta ke juyawa,

"Amarya kodai da bayani ne?" Inji khulsum, dariya maama tayi tace,

"Ai ba ita kadai ba har dayar itama dazu tagama amanta yanzune ta warware..."

Caraf meenah tayi tace,
"Kai Anty mama kiji tsoron Allah.... Maine fa yahau min kai"

Ita dai bilkisu na zaune tana jinsu tana bin kowa da ido bata uhm bare um um, tasan da ace hamood ne yakawo mata lefe yau ai da farin cikin da zata tsinci kanta aciki Allah kadai yasani amma bata fitar da ran hakanba agaba tunda idan da rai to da rabo.

Sai dare suka samu zarafin kallon kayan bayan mutane sun baje domin hatta yan uwan ammah adaren suka tafi yanzu sai su iyallo, bilkisu na saman kujera sukuma su khulsum suna gaban akwatunan suna kallon kayan daya bayan daya, saida suka gama tsaf sannan ta raka khulsum tatafi da tadawo dakinta tawuce bata koma wurinsu maama ba domin ita kadai tasan abinda take ji.

Ango dai abangarenshi yagama komai duk da har wata yar rama yayi kadan saboda stress danma yanada mataimaka, ko shago yanzu ba sosai yake zuwa ba, shiyasa lokacin da salim yakai musu labarin wai fahad zaiyi aure abin yabasu mamaki duk sai suka fara zargin to ko husnah zai aura amma sai salim yace musu a'a wannan watace daban basu ma santa ba. Saida biki yarage saura sati daya yana shago yana dinka farar shaddar da zai saka ranar daurin aure saiga husna, daga cefane take tabiyo ta shagon dama arana takan zo shagon nan sau biyu ko sau uku,

Su biyune ashagon daga shi sai kanin hamza dake koyon dinki, sauri yake yagama yatafi gida domin ayiyah na nemansa,

Zama husna tayi gefenshi dayake akan benci yake,

"Prince... Yakake"

"Lafiya husna, ya karatu?"

Kayan dayake dinkawa ta kalla sai kuma ta kalli bakar ledar dake gefen keken da tarin invitation card aciki, babu bata lokaci takai hannu ta dauko kafin ya fauce har ta matsa tana karantawa tiryan tiryan, idanuwanta ne suka cika da kwalla ganin sunanshi baro baro ajiki domin harda saka Prince in bracket, ai cefanen da tashigo dashi shagon nan tatafi tabarshi tana kuka fahad yanata kiranta amma taki ta ko waiwayo, duk kuma yau sai yaji tausayinta ya kamashi ganin akanshi take wannan kukan, duk da yana saurin yaje gida amma hakura yayi yakira Salim dan ya rakashi school of nursing wurin husnah, kayanta da tabari yadaukar mata yatafi mata dashi, yakirata yafi sau biyar amma bata dauka ba tana kwance tanata kuka yan dakinsu kawayenta sai rarrashinta sukeyi amma taki yin shiru fiyeda mintuna talatin kenan take kukan nan, ganin taki daga wayarshi sai yatura mata text akan tayi hakuri tazo yana son ganinta, wannan shine karo nafarko da yazo wurinta har cikin makarantarsu amma ita kullum sai taje wurinshi kaf kawayenta babu wanda bai san prince ba yan dakinsu kuwa da sunanshi suke kiranta saboda kowanne bango dake jikin dakin sunanshi ne rubuce da marker, idanuwanta sunyi jajur tafito tazo wurinshi suna tsaye shida salim amma shi yana kan roba roba din Salim da alama shine ya tukosu yakawosu,

Wani sabon hawayene yazubo mata lokacin da sukayi ido hudu dashi,

"Husnah menene abin kukane? Meye zaki tada hankalinki?"

Harara ta watsa masa batare da tayi magana ba, murmushi Salim yayi yasa baki cikin sigar lallashi yace,

"Kiyi hakuri husnah, kedai prince kikeso to ko yayi aure karki duba aurensa kawai kidubi soyayyar da kike yimasa saboda rayuwa tsarice daga ubangiji tayuyu ke ata biyu zakizo, wannan ba matsala bace, ki kwantar da hankalinki dan Allah..."

Kalaman Salim sunyi nasarar dan rage mata radadin da takejin zuciyarta nayi amma har lokacin taki koda kallon fahad, har Salim yagama tsarata tasauko bata kalli fahad ba, da zai bata ledar ta wacce ta baro ashago bata kalleshi ba ta karba, tura babur din yayi yamatsa kusa da ita kamar zai takata ai kuwa babu shiri takai masa duka duk da idan tayi masa irin wannan hade fuska yake yau murmushi yayi yace,

"To ki dan kalleni mana husnah tah..."

Ai kuwa kalmar tayi mata dadi shiyasa babu bata lokaci ta dan warware harda su kyalkyala dariya ganin haka yadauki Salim suka tafi, shidai yasan baya son husnah amma yau yana tausaya mata domin tanuna masa iyakar soyayya tun ranar da tafara zuwa shagonsu taganshi tafara sonshi duk da fada yafi yawa cikin mu'amular tasu saboda ita bata kunyar tabashi agaban kowaye ko yanzu kafin su baro wurinta saida ta dafashi ta hanyar dora hannunta kan nashi,

"Gaskiya akwai matsala fa, dan wallahi yarinyar nan dagaske take sonka"

"To ya zatayi sai dai tayi hakuri tunda nidai aure zanyi"

"Sai ka kara da ita"

Dariya fahad yayi,

"So kake bilkisu ta korene daga gidan kenan"

"Kaida gidanka taya zata koreka"

"Allah saita koreni ai gida yazama nata, ko kuma daga daki kasa akoroni falo"

Dariya sukayi gaba daya, har gida salim yakaishi sannan yatafi shikuma yashiga wurinsu ayiyah domin jin ba'asin kiran da ake yimasa, gyadar yatarar da mamuh na tacewa akwando ta dahu ligif kanfata yayi a cup yawuce falon ayiyah yana ci,

"Ayiyah wannan gyadar badai dadiba ta dahu wallahi"

"To santi kake kenan, yawwa dama maganar sati dayan da amarya zatayi ananne shine nace ai gara kafara tuntubarta tun yanzu dan tasani ko"

Dan jimm yayi, tabbas yasan kam haka al'adarsu ayiyah take yayinsu ma duk da sukayi aure saida matansu sukayi kwanaki bakwai bakwai agidan,

"Idan kuma kana ganin wani za atura babba to sai atura yaje yasanar dasu..."


"A'a ayiyah bari zanje anjima infada mata"

"Yawwa ka kokarta dama shine kiran da nake yimaka"

Saida ya cinye gyadar nan tsaf sannan yatashi yafita, yaci sa'a salim na gida dan haka Babur dinsa yaje yakarba yanufi gidansu bilkisu duk da baida tabbacin ko tana nan, dawowarsu kenan daga kasuwa sun siyo furnitures tana kokarin rage kayan jikinta yakirata yace yana waje, ita wallahi bataso wannan zuwan nashi ba haka dai ta daure ta zura doguwar riga da hijabi tafita....


*_Ummi Shatu_*

? *HASKE WRITERS ASSO.*


*KAMAR DA WASA...!*


_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



*16*


*Littafin kamar da wasa na kudi ne yar uwa idan kinada bukata kibiya ki karanta.*


***Ba dan tanasoba haka ta fito ta sameshi yana compound din gidan tsaye jikin wata bishiya,

"Baby..."

Batare da ta kalleshi tace,

"Yakake?"

"Lafiya lau ranki yadade, ya mutanen gida?"

Atakaice ta amsa da,

"Lafiya"

"Am dama namanta ne ban fada miki wani abuba shine yanzu nazo sanar dake, mu a family dinmu idan anyi aure sai ankai amarya gidansu ango acan za aware mata daki har sai tayi tsawon kwanki bakwai ko wani abu mai kamada haka..."

"Wannan al'adar wanne garine kenan?" Ta tambaya batare data kalleshi ba,

"Fulanin kura..."

"So yanzu dai kana nufin gidanku za akaini acan zan zauna har na tsawon 1 week?"

"Ba lallai yakai hakaba dama kawai al'adace amma yana yuyuwa ma bazaifi 3 days ba ko 2"

Jijjiga kai tayi ta jingina jikin bishiyar flower tana kallon gefe,

"Babu damuwa..., ya maganar dinkuna ne wai? Naji shiru kuma tun ranar fa nayi maka maganar"

"Bani intafi dasu adaren nan zan yanka, abubuwane suka yimin yawa wallahi baby ko bakiga har nayi baki ba na fada...?"

"Bafa na son sunan nan nafada maka, so kadaina"

Murmushi yayi shi wlhi drama din da zasuyi da bilkisu kawai yake hangowa,

"Am sorry bazan sakeba amma seriously na dan rame fa"

"To ya za ayi ai situation ne"

Daga haka tawuce ciki ta dauko masa kayan da zai dinka mata takoma wurinsa,yana tsaye a inda tabarshi yana yin waya ganin tana jiranshi yakatse wayar yamaida hankalinsa gareta,

"Gashi duk riga da skirt zaka yimin..."

"Banda doguwar riga?"

"To Kaduba dai kagani idan akwai wanda zaiyi kyau da doguwar rigar sai kayi min"

"Shikenan to, kigaida su ammah"

"Zasuji"

Fita yayi yatafi ita kuma takoma ciki wurin khulsum wacce ke jiranta tayi wanka su fita gidan da za ayi mata gyaran jiki saboda yau za afara.

Cikin kwana biyu yagama dinkunan bilkisu kala takwas ne shadda guda biyu leshi guda biyu sai material da atamfa suma duk kala bibbiyu amma abinda yabashi mamaki duk cikin kayan babu na cikin lefenshi wanda yasaka amma bai kawo komai aranshi ba tunda watakila wannan din agidansu aka yimata, bai samu damar Kai mata kayan da kansa ba sai salim ne yakai saboda shi ranar yana can gidanshi ana saka masa tile da sauran abubuwan da ba akarasa ba, washe gari aka karasa komai na gidan akayi fenti gida yafito rangadau dama unguwar shiru take babu gidaje da yawa ma domin sabuwar unguwace bata fara yawaba, agajiye yakoma gida bayan sallar ishah wanka kawai yayi ya kwanta ko abinci bai nema ba babu bata lokaci baccin gajiya yace muje zuwa, koda Abba yashigo yaganshi baje yana bacci dariya yayi yace,

"Dole kayi bacci ango, irin wannan commitment Haka?"

Dasafe garau yatashi sakamakon baccin da yasha sosai adaren jiya, miss called din bilkisu yagani har guda uku hakan yabashi tabbacin akwai dalili shiyasa yayi gaggawar calling dinta back,

"Fahad dakuna nawane agidan, kofofi nawane sannan windows nawane? Muna wurin masu dinka cuttens ne"

"To hajjaju bari naturo miki gaba daya pics din gidan ki ganshi"

"Yawwa dan Allah hanzarta"

Katse wayar tayi nan yashiga whatsapp yatura mata aranshi yana cewa,

"Akwai rikici nasani"

Bai kara jin duriyarta ba sai text tamishi akan yabasu keys din gidan saboda masu zuwa jeren kaya gobe nanma aiken yayi mata aka kai musu, sai ana igobe kamu ta kirashi tana yimishi maganar itafa baza suje wata dinner ba walima kadai zatayi da friends dinta dan haka shima ya hada reception da friends dinshi kawai ya isa, tayi hakane saboda kunyar yaje dinner mutane su ganshi take,bai musa ba yace to.

Tana zaune tayi uban tagumi bayan mai kunshi tagama yarfa mata jan lalle da baki, khulsum tashigo agajiye itama daga kunshin take, zama tayi kusa da bilkisu wacce ke kallon masu shigowa da masu fita tayi tagumi,

"Wallahi fahad dinnan yayi yaro da yawa, Allah mai yadda yaso..."

Dariya khulsum tayi,

"Baiwar Allah ki rungumi kaddara kiyi hakuri, haka Allah yashirya ko jinjirine dai shine mijinki uban yayanki..."

"Tab.... Allah ya kiyaye, nifa wallahi baki ma san wani abuba, kunyar nunashi nake a matsayin mijina"

"Sai kiyi kuma malama, wai inasu maama?"

"Suna can gidanshi karasa jere"

"Gidanki dai, kyace wani gidanshi"

"Kinga malama ni idan kina tashi kitashi mutafi kitson nan idan kuma baki zuwa ki sanar dani"

"Ahh kinga karki fada min bak'a, shirya muje amma wallahi da retouching kikayi zaifi kitson nan, kinga kanki yanzu fa kullum sai yaji ruwa"

"Kanki akeji, ni tashi mutafi dan bamuda lokaci"

Hijabinta tasaka har kasa suka tafi bayan tayiwa ammah sallama iyallo sai jaraba take wai yakamata ta daina fita hakanan amma tunda tazo gidannan bataga ta yini agida batare da ta fita ba, batace komai ba tabi khulsum suka tafi,

"Shagon ma da babu wani nisa nan bayane fa amma shine iyallo sai tayiwa mutane ihu aka, kai Allah yakyauta"

"Ai keda iyallon nan taku kuna sani nishadi wallahi, gaskiya i have been missing my grandma"

Dariya bilkisu tayi,

"Uhm ai iyallo bata haduba sam wallahi, hajjaye kakarmu ta wurin uwa tafi kirki"

"Kya hadu da Abba wallahi"

"Bawani nahadu da abba ai gaskiyace"

Har sukaje shagon hirar iyallo suke yi. Kitso hadadde aka yarfawa bilkisu dan har la'asar lis suna shagon ita kuma khulsum akayi mata retouching, tun suna hanya taga su meenah nata kiranta, koda tashigo gida suma suna gidan ana yimusu kunshi har angama musu yanzu hindu ake yiwa itama ankusa gamawa,

"Wai wai wai... Gaskiya yakamata yaya fahad yaga wannan kitson da lallen" inji Hindu bayan bilkisu tacire hijab din kanta,

"To ke gaggawar me kike ko kin mantane nanda jibi suna jone ana..." Maama tafada cikin shakiyanci, tun kafin tarufe bakinta bilkisu takai mata duka ta gudu,

"Allah adda labour idan ya fahad yaga kunshin nan da kitson nan zaucewa kawaine bazai yiba" meenah itama ta karbi zancen,

"Wai dama haka kuke bakuda kunya?" Khulsum tafada tana rike haba,

"A'a wallahi Anty khulsum ai kin san Adda labour kakarmu ce fa dole mu rinka janta" inji meenah,

"Adda mai gado ki fada masa angama komai yatura wadanda zasu jire gidan saboda anjima suma su yafendon zasu taho"

Bata tanka ba takarasa shiga cikin daki wanda yanzu kayan ciki suka zama sai saura domin duk su maama sun shirge mata kayanta sunyi mata gaba dashi sai wanda zata nema kawai aka bari, zama tayi gefen gadonta tana kallon tv domin wani Indian film ake haskawa atashar MBC Bollywood mai suna a gentleman, wayar fahad takira ringing biyu yadauka,

"Ranki yadade..."

"Am yawwa kaga angama jeren nanne shine zan fada maka katura wasu sai su kwana agidan"

"Angama ranki yadade"

Katse wayar tayi tamike tafita waje wurinsu khulsum. Kamar yadda yafada da daddare su salim da Abba ya tura domin su kwana agidan,lokacin da zasu tafi jan salim yayi yace masa,

"Allah karku kwanta mana agado kasan dai babu kyau..."

Dariya salim yayi yakai masa duka,

"Allah ko fitsararre? To ai ya Abba yadace ka fadawa tunda shine babba amma baniba"

"Shi ai nasan bazaiyi hakaba sai kai...."

"To kuwa kwana bisa gadonku daram..."

"Wallahi karka kuskura..."

"Sai kayi kuma...."

Daga haka yayi gaba abinshi, fahad kam neman wuri yayi ya zauna nan kofar gida domin cikin gidan cike yake da mata yan uwa da abokan arziki, saida yakira bilkisu yasanar da ita yatura wadanda zasu yi gadin gidan sannan hankalinta ya kwanta.

Washe gari da shirye shirye aka tashi kasancewar ranar za ayi kamu, kuma anan compound din gidan za ayi kamun domin ita bata da ra'ayin zuwa hall, kowa kagani acikin hidima yake fuskarsa dauke da farin ciki ba ma kamar ya mahaifiyarta ammah wacce ke jin kamar ancire mata k'aya, yanzu kam tasan zasu huta da wadannan maganganun da habaice habaicen da ake yimusu acikin dangi, mutane sukan manta da cewa Allah shine gwani wurin iya tsara komai na rayuwar bayinsa kuma duk yanda ya tsara to hakance zata faru ko anaso ko ba aso, ko anshirya ko ba ashirya ba. Su meenah dai ana can wurin masu decoration ana nuna musu muhallin

8 / 36