KAMAR DA WASA HAUSA NOVELS COMPLETE PDF.doc

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   28 / 36

81K to 84K   out of 106.8K words

da su maama suka yi jere agidan ya kwana adakin Bilkisu kuma akan gadonta, kawai tunani yayita yi acikin ransa yana sake jinjina girman ubangiji saboda gashi cikin iyawarsa da hikimarsa yasake dawo masa da Bilkisu akaro na biyu,

"Hmmmm ko yanzu wanne irin zama kuma zamuyi oho... M" haka yaketa maimaitawa acikin ranshi. Ranar laraba da daddare aka raka Bilkisu gidanta tun amota iyallo take zuba ruwan fada tana cewa wannan amarya akwai shashasha shine ko dan sunkuben lallen nan bata kunsa ba bare tayi kitso? Ita dai Bilkisu najinta batayi ko da tariba har suka karasa gidan inda su anty kubra dasu anty asabe ke zaune suna zaman jiransu, babu Wanda yakara koda mintuna goma acikin gidan duk tafiya sukayi lokaci guda kamar ana korarsu,yaye mayafinta tayi bayan tafiyarsu tana kallon dakinta wannan karon komai blue ne amma furnitures dinta farine tass kirar royal, bata bukatar sake fita koda falo saboda bacci take son tayi tahuta amma kuma bata son wannan dan rainin wayon yazo ya isketa tana bacci saboda jikinta na bata komai na iya faruwa.

Sai dai abinda bata saniba shine fahad yashirya zamansu yanda zai kasance, sam bazasu yi zama irin nada ba yanzu yanaji aranshi lokacin shine yazo shima, awanccan zaman Bilkisu tayi yadda takeso to yanzu shima shine zaiyi yadda yakeso shiyasa lokacin da yadawo ma bai ko shiga dakinta ba yawuce daya dakin wanda kayansa naciki dama wanka yayi yashirya cikin kayan bacci masu taushi yayi kwanciyarsa babu jimawa bacci yayi gaba dashi,Bilkisu nata jiran shigowarsa shiru shiru har tagaji da saurare tayi bacci ba ita tatashi ba sai asubah, tana kan gadon tana niyyar saukowa taji yana yimata knocking,

"Kitashi lokacin salla yayi..."

Daga haka taji shiru alamar yabar wurin, sake kwanciyarta tayi bayan tayi salla ba ita tasake tashiba sai 10 saura wannan dinma karar wayarta ne yatada ta,tsaki tayi sakamakon ganin khulsum ce me kiran nata,

"Labour har yanzu ba awartsake bane? Ko dai sai nazo ne?"

"Uwar me zakizo kiyi min? Wallahi khulsum zan ramane..."

"Shikenan sai nazo din to"

Katse wayar tayi tana hamma saboda yunwa da kuma sauran bacci baccin dake kanta, wanka tashiga tayi tafito ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atamfa coffee colour sai dison yellow yellow ajiki, batayi kwalliya ba dan kawai powder tashafa sai kwalli ta fita falo, dama kayan abinci tasan babu matsala domin wannan karonma kamar waccan abba ya ajiye musu komai cikin store, afalo taganshi kwance daga shi sai three quarter da yar t shirt, yana kwance kan three sitter yana lallatsa waya, kanta ta dauke kamar bata ganshiba shima haka domin yasan awannan shegen son girman nata bazata yimasa magana ba saboda jira take ya gaidata tukun, harda wani dan bata rai yayi sai kace shine babba koda yake shima yanzun jin kansa yake a babba tunda shi yake aurenta ba itace take aurenshi ba dan haka yazama tilas tayi respecting dinshi a matsayinshi na mijinta, maganar hakkinshi kuwa dama shi yanzu ba ta wannan yakeyi ba saboda aduk lokacin da yatuna cewar ta auri wani yayi tarayya da ita sai yaji baya sha'awar abun, gaba daya abun yafice masa akai saboda yatsani hamood dinnan tsana mai tsanani. Kitchen tawuce domin taga kayan tea akan table,tana neman cattle tajiyo buga gida, duk haushi yabi yakamata sakamakon rashin gaishetan da fahad baiyiba,

Fitowa tayi daga kitchen din dan ganin suwaye, daidai lokacin da su mariya suka shigo dauke da kuloli akansu fahad yana biye dasu, nunata yayi yana cewa,

"Maza ku kai mata gata can"

Nufarta sukayi suna fara'a babu shiri itama tasaki fuskarta tana yimusu murmushi gamida karbar kayan dake kansu, maryam tariko kular wainar shinkafa ita kuma maryama tariko kular miyar agushi, anty Fauziyya ce tashiryo musu wannan wainar ta musamman domin ta hutar da amarya girkin safe, fahad baiko kalleta ba yawuce dayan bedroom din wanda ke gefen nata amma akwai dan tazara kadan,

Tare ta hada musu tea din dasu Maryam suka karya, ba karamin dadi taji wainar nan tayi mata ba wannan dalilinne ma yasata zagewa taci wainar sosai tana korawa da ruwan tea, daga nan falo suka tarkata suka koma ta kunna musu kallo har lokacin fahad bai fitoba ko breakfast dinma shi bai fito yayiba har 12 saura. Misalin karfe daya saura mintuna biyar ya Abba yakawo musu abincin rana, su maryama ne suka shigo da abincin amma shi ko shigowa baiyiba yadai ce agaidata, yanzunma tare suka ci abincin ranan shinkafa da miya da salad, bayan sun gama tawuce dakinta domin lokacin salla yayi, wanka tayi tai alwala tafito tashirya tana ta mitar shine babu wanda yazo mata yau wato har khulsum dinma da take cewa zatazo shine itama tayi zamanta ko leke, da abin sallarta tafita ahannu da hijabinta wurinsu maryama, tunda tashiga falon kamshi yacika kofofin hancinta wanda ko ba afada mata ba tasan na dan mulkinne saboda da alama yau da mulki yatashi da nuna isa,

"Anty ya fahad yanzu yafita yace lallai lallai muna yin salla mutafi gida saboda zamuje islamiyyar yamma..."

"Ba yau alhamis ba, har yau kunayin islamiyyar ne?" Tafada tana kokarin shimfida rug din sallar,

"Ehh munayi ranar juma'a ne kawai ba azuwa yanzu..." Maryama tabata amsa,

"Ok, fahad din yaci abincine?" Tayi tambayar da ita kanta bata san daliliba,

"A'a baiciba" suka hada baki wurin amsawa,

Sallarta ta tayar batare da ta kara magana ba, bayan ta idar tatashi tawuce daki tana ninke hijabinta tabarsu maryama afalo suma suna yin sallar, rasa abinda zata bawa yaran tayi daga karshe ta dauko wata atamfarta wadda matar abokin abba ta aiko mata da kyautarta lokacin da tana gida amma bata dinkaba,saida ta wahala kafin tanemo ledar da zata saka musu aciki, da atamfar da dari biyar tabasu sukayi mata sallama suka tafi, wayarta ta dauka tana latsawa amma kuma can kasan ranta tunani takeyi, wato wannan yaron dan rainin wayo ya karo wulakanci shine harda wani ficewa baiko fada mataba? Ohh sai yanzu tagano dalilin dayasa jiya baiko shiga dakinta ba, wato irin zaman da ya zaba musu kenan ahalin yanzu? To azuba agani zataga tsakaninsu wanda zai sauko yabi daya........


*_Ummi Shatu_*
*Littafina na siyarwa ne me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*



48***Kawai tana zaune ne amma bawai dan tana jin dadin zaman ba, tunani ne fal ranta wanda mafi yawa na wulakancin fahad ne atoh wulakanci mana ita aganinta ai wannan wulakancine wato ahaka yake son yakawo wata gidan ya ajiye alhali ita baya girmamata?

"Wanne girma zai baki tunda yace ke matar sadaka ce...." Zuciyarta tabata amsa a sirrance,

Tabbas ko tantama batayi wannan shine dalilin da yasa yanzu baya rawar kafa akanta tunda ita matar sadaka ce ba matar so ba, kamar zatayi kuka takeji sauki daya tasamu shine su elmustapha sun kirata awaya sun shafe dogon lokaci suna hira cikin barkwanci. Tana nan zaune har daf da magriba lokacin ne fahad yadawo yana rikeda bakar leda wadda yasiyo fruits aciki dayake yau yana azumi itama husnah tanayi kawai bayaso yasawa husnah zargi ko mummunan tunani akan Bilkisu shiyasa baije wurinta sunsha ruwa tareba kamar yadda suka saba, yasan muddin yaje yasha ruwa awurinta yau to zata raina Bilkisu ko kuma taki ganinta da kima shikuma bazai so hakanba.

D'an bata rai tayi lokacin da yashigo cikin falon ganin haka yasa shima ya dan tsare gida kadan yawuce can saman dining yana sanye da shadda kalar ruwan shanshanbale, amma babu hula akanshi, ganin bai kulata ba yasata mikewa cikeda takaici tawuce bedroom dinta nan yabi bayanta da kallo yana girgiza kai,

"Hajjaju kenan.... Kina wahalar da zuciyata fa.... Kina azabtar dani" yafada acikin zuciyarsa, saida yasha ruwan tea da fruits sannan yaje yayi salla, tsintar kansa yayi da yin addu'ar Allah yasaka sonshi azuciyar Bilkisu kamar yadda shima yake sonta. Tunda tashiga daki tsabar takaici bata sake fitowa ba kawai mamakin fahad takeyi, to meyake nufi? Wannan tambayar tayiwa kanta tafi sau goma amma bata da amsarta, fahad kam har yasha ruwansa yagama yafita sallar ishah baiga Bilkisu tasake fitowa ba, shima ana idar da salla yadawo gida, daki yawuce ya dan kishingida yana kallo a laptop dinshi gefe daya kuma yana dan taba chat da friends, shi kadai yaketa dariya sakamakon hirar da sukeyi da su mukhty, sun sakashi agaba sai tsokanarshi suke suna cewa sai yafada musu yadda al'amarin ya kasance dariya kawai yaketa tura musu da gwalo yaki yayi magana shine bash yake cewa kai ku rabu dashi ai dama mijin hajiya ne kila ta gwabeshi akan yayi shiru kar yafada mana,wannan maganarce tabashi dariya wai mijin hajiya,har lokacin bacci yayi Bilkisu ta kwanta bata kara ganin keyarshi ba yauma haka tayita raba ido ko zai shigo amma shiru. Washe gari ita da kanta ta hada breakfast mai sauki tana falo tana karyawa yafito yanata shan kamshi kamar bai iya dariya ba,

Wuceta yayi zuwa kan table yazauna shima yafara karyawa abunda yasake kona ranta kenan yasata mikewa takoma bedroom tabar masa falon gaba daya, tana zaune gefen gado da system akan cinyarta saboda nanda kwana biyu zata koma aiki dama sati daya aka bata kawai taji yana knocking abakin kofa,

"Yes..." Yafada atakaice, bude kofar yayi ya dan leko kansa ciki batare da yashigo ba yace,

"Ki duba store koda akwai abunda babu wanda kike bukata saiki rubuta fita zanyi...."

Batare da ta kalleshi ba tace,

"Kayan miya zaka siyo kadai...."

Baice komai ba yakoma yaja mata kofar, wanka yaje yayi yafita bai wani jimaba yakawo kayan miyar yasake komawa kai tsaye gidan anty asabe yawuce ta can suka tafi kasuwa tare da ita, kayan lefen husnah suka hado sannan suka sabunto lefen Bilkisu nada suka sassauyo kayan ciki da akwatunan saboda kafin yakoma makaranta za akai lefen husnah sannan za ayanke rana, wuni cur sukayi akasuwa shida anty dan sai yamma liss suka koma gida duk da tana ta cewa yazauna yaci abinci yace a'a girkin amarya zaije yaci,

"Babu ko kara ko fahad?" Ta fada tana dariya, baiyi magana ba yasaka sau cikinsa yanufi gida.

Kamar yadda jiya bata san fitarsa ba haka yauma batare da ta saniba yayi tafiyarsa shiyasa abun ya tsaye mata arai, tana kitchen tana girkin abincin rana khulsum tazo dauke da danta khalifa,tare suka karasa wuni da yamma tatafi, khulsum na tafiya bayan takoma ciki tayi wanka tana shiryawa fahad yadawo, yunwa yakeji sosai sannan gashi yagaji lilis, rigar shaddar dake jikinsa yacire ya zamana daga shi sai yar farar singileti da dogon wando, zama yayi kan table yafara bude abincin dake wurin, jallop din shinkafa ne sai hadin vegetables salad mai dauke da dafaffen kwai aciki. Yana tsaka da cin abincin yajiyo karar wayarshi amma bai iya tashiba saboda yana jin dadin abincin sosai ba kadan ba, yayi missing girkinta da ita kanta gaba daya, saida ya koshi dam sannan yataso yana rikeda tissue yana goge bakinsa, dai dai lokacin itama tafito daga cikin daki, kallon juna sukayi tazo tawuce shi tanufi dining area ta bude fridge ta dauko banana milk shake ta zuba acikin glass cup tazo tawuce daki, ganin abinda ta debo yasashi shima komawa dining area din yazuba cikin cup ya shanye yana lumshe ido saboda gardi da dadi gashi yadau sanyi ba karya, rigarshi da ya cire yaje ya dauka tareda wayarshi yashiga daki, zama yayi saman katifa yana kokarin kiran husnah saboda itace ta kirashi dazu, tana dagawa yace,

"Am sorry my love.... Dazu kin kirani time din ina tare da antynki ne ina cin girkinta mai dadi...."

Duk da taji haushin maganarsa amma saita waske tanuna kamar bataji zafin hakan ba tace,

"Babu komai my prince dama zan fitane zamuje kasuwa nida Fa'iza...."

"Adawo lafiya my love.... Allah yatsare"

Daga haka sukayi sallama yakatse wayar dama tun lokacin da suka jone da husnah ko ba ya gari idan zata fita saita tambayeshi shiyasa har sun dade da sabawa da wannan tsarin sam basa kallonsa asabon abu. Irin zaman da su Bilkisu suka faro shi suka cigaba da yi na ba ruwan kowa da kowa, gaisuwa kuwa tab rabon da taji fahad ya gaisheta har ta manta gashi yanzu wani sabon salon wulakanci da ya koya shine sai yarinka kiranta da Bilkisu, idan zaiyi mata magana sai dai yakira sunanta, yauma da zai fada mata sakon su ayiyah tana daki tana ware kayan sawarta tana karasa shiryawa cikin drewar, zama yayi gefen gadonta yace,

"Am Bilkisu ayiyah tabani sako.... Tace wai gobe za akai lefen ya Abba gidansu salim idan kinada lokaci kije akai dake...."

"Naji...." Tafada atakaice saboda tasoma kosawa da wannan rashin kirkin nashi akan me zai rinka kiran sunanta kai tsaye? Duk da bawai yau yafara ba amma yau kamar hakan yafi kona mata rai. Washe gari da yamma bayan tadawo daga aiki ta shirya tatafi gidansu fahad sai kaffa kaffa ayiyah takeyi da ita, dama tasan bata da matsalar uwar miji dan ayiyah na mutukar sonta hakama sauran yan uwan mijinta kawai dai abinda ta lura shine matar ya sunusi wato anty juwairiyya bata faran faran da ita tun wancan lokacin har yanzu dan tun aurensu nafarko taketa kukkushe Bilkisu tana cewa ai fahad tsohuwar yayarshi ya auro dan wannan a haihuwar kajima ai ta haifeshi, ko yauma da ta shigo gidan kowa yanata murna da lale marhabun da ita amma banda Anty juwairiyya shiyasa itama takama class dinta daga gaisuwa bata kara cewa komai ba,tarba ta girmamawa aka yimusu agidansu salim akwatuna shida masu kyau suka kaiwa nusaiba bayan an karbi kayan da babu jimawa suka koma gidansu fahad lokacin magriba tayi, Bilkisu tafito tsakar gida tana alwala sai ga fahad yashigo daga masallaci yake anty juwairiyya na ganinshi tafara cewa,

"Kaga sabon ango....kaima nanda wani satin zamuje Kaduna mukai maka naka...."

Baiyi magana ba sai murmushi kawai duka hannayenshi na cikin aljihun rigar farar shaddar da take jikinsa,gun Bilkisu yakarasa ya tsaya kusa da ita tana alwala,

"Zaki tafi yanzune injiraki ko sai anjima sai indawo in daukeki?"

Jin abinda yace ba karamin dadi yayiwa Bilkisu ba saboda tasan dai ko babu komai anty juwairiyya zata gane fahad na yinta kuma tanada wani matsayi na musamman agareshi,rausayar da kai tayi ta kalleshi sannan tace,

"Da sallah nake son nayi... Ko sauri kakeyi?"

"A'a kiyi mana... Kiyi sai mutafi"

"Yawwa nagode" tafada tana kokarin shiga falon ayiyah inda anty juwairiyya ke tsaye tana kallonsu sai jan fahad take da maganar bikinsa shida husnah amma yaki biye mata suyi saboda shi yanada wani abu guda daya akan Bilkisu, idan daga shi sai itane baya raga mata ahalin yanzu amma idan agaban mutane ne ko wani to yana nuna har gobe yana sonta yana martabata, shiyasa abun bai cika damun Bilkisu ba saboda sai idan iya shi da itane yake nuna shine oga dole ta girmamashi. Har ta idar da salla bai bar kofar falonba yana tsaye da wayarshi a hannu yana dannawa, lokacin da take yiwa ayiyah sallama tana jiyo anty juwairiyya nace masa,

"Ko da amaryar ake soyewa ne dan kanina...."

"Kai anty nifa gaskiya kin saka min ido da yawa..." Yafada yana dariya, sosai Bilkisu taji dadin amsar da yabata, fitowa tayi rikeda irin kayan snacks din da aka basu agidansu salim wanda anty asabe ta zubo mata, karba yayi daga hannunta yawuce gaba tana biye dashi abaya har waje, su ya Abba na zaune akofar gida shida salim sai taji duk kunya ta kamata musamman ma lokacin da zata hau bayan babur din nashi dole saida ta dafa kafadunshi duka guda biyun, har sukaje gida babu wanda yace da wani ci kanka sai dai idan sun dan shiga kwari ko gargada yaji ta rikeshi da haka suka je gida. Cikin yan kwanakin aka kammala komai na zuwa kd domin kai lefenshi komai iri daya yayi ma husnah da Bilkisu bai banbanta ba ita Bilkisu ma bata san wacce wainar ake toyawa ba, ita dai kawai abinda tasani shine bazata taba daukar raini ba nashi ko na matarshi, ranar da aka tafi kai lefen ma bai fada mata ba saboda har gobe irin zaman da ya zabar musu sukeyi, ita anata ganin ai ba ita yadace ta rinka shan kanshi ba ko kuma ta nemi shiri dashi, shiyasa gaba dayansu ba wani dadin zaman sukeji ba saboda kowa baya sakarwa kowa, har aka kai lefen aka saka rana wata biyu babu wanda ya gaya mata batama saniba gaba daya, shi kam fahad shirin komawarsa makaranta yasaka gaba yana kammalawa ya tafi bayan yabar mata duk abinda yasan zata bukata. Wani lokacin Mariya ko maryama ayiyah ke turo mata su tayata kwana amma ba kullum ba, tunda yatafi kuma bai kirata ba sai bayan kwana hudu da tafiyarsa nan dinma iyakarta gaisuwace daga nan ya tambayeta ko da akwai abinda take bukata tace babu shikenan yace mata sai anjima, hakace take faruwa har yayi sati uku da tafiya a lokacin ne yazo gida weekend, tun ranar Thursday yazo yana son komawa Monday ko Tuesday,lissafin bikinsu kuwa saura sati hudu babu yan kwanaki, a wannan zuwan da yayi yai niyyar fadawa Bilkisu maganar aurenshi da husnah, ranar ya fada mata da safe tana karyawa zata tafi aiki saboda Monday ce shikuma yana kwance kan three sitter yana kallo, a laptop dinshi,

"Bilkisu aure zanyi fa...., yau saura sati uku da kwana biyu..."

Saida ta dan ja numfashi sannan cikin halin ko inkula tace,

"Allah yabada sa'a... Ko akwai wani abu da zanyi baya ga haka?"

Girgiza kai yayi yana murmushin takaici bai san sai yaushe Allah zai karbi addu'arshi yasa Bilkisu ta soshi kamar yadda yake sonta ba, ita kuwa tsabar takaici da bacin rai ko gama cin abincin ba tayiba tabarshi ta tashi ta dauki wayarta da handbag dinta tafita dama tun dazu mai napep din dake kaita aiki yazo. Fahad kwanciyarsa yaci gaba dayi har saida husnah ta kirashi tace yataimaka yazo ya dinka mata atamfarta domin da ita take son tatafi gida jibi, jibi zata gama exams dinta kuma idan tatafi bazata dawoba sai bayan bikinsu saboda hutun session ne, tashi yayi duk jikinsa babu karfi yayi wanka yashirya cikin kananan kaya, bakar riga da milk colour din trouser, zama yayi ya karya sannan yafita yasamu husnah a shagonsu salim tana jiransa, tsokanarsu salim yafara yi yana waka yana cewa ga amarya ga ango, tare suka haura saman shagonsu fahad inda zaiyi mata dinkin.

Bilkisu kam tana can office tarasa

28 / 36