Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : Hausa Book Store
karan hawayen idonta kasa ‘daukewa suka yi, ta sake su suna zuba kamar famfo, ita kanta ta San ta bu’de bayan haihuwar Aisha, rashin ku’di y’a hanata zuyartar babban asibitin birni duk kuma wani magani na gargajiya da tayi ya kasa karb’arta. Ya fice ya na ayyana tabbas rabuwarsu ta matso kusa don daman gaban nata yake yiwa to da alama gaban nata ya tashi daga aiki. Ya fice daga ‘dakin daga shi sai gajeran wando yana sake Jin tsanar Talatun a cikin zuciyarsa yaushe akayi auren? Yaushe ma har ya gama cin sadakinsa da za’a ce har ya gama ‘debe ni’imar Talatu? Har ya fito daga wanka tunanin sakinta kawai yake don ba zai iya cigaba da zama da ita babu mamora ba. Yana da ku’din da zai auri ko y’ar mai gari ce a garin don haka zai yi amfani da ku’dinsa ya auro duk matar da yake so, idan yaso ya jinginar da Talatu don kada ya saketa idanun duniya su dawo kansa a ce ya ci amanarta don ya ga ba inda zata je, duk da shi surutun mutane bai fiya damunsa ba.
Sai da ya fita ya sake dawowa, sannan ya lura da y’ar jaririyar da Talatun take shayarwa Akan cinyarta. Tun daga bakin k’ofa ya fara k’unduma zagi. “Kan Uban can, wata haihuwar kika yi Talatu, ke dai wato kin zama kaza nan da nan kin saka k’wai. Ko da yake jiki magayi ai, wannan karan kuma me kika Haifa?” Jabiru da yake gefe ya dinga auna masa harara ta bayansa yana jin kamar ya shak’eshi ya Mutu. Talatu kuwa muk’ut ta ha’diye wani Abu a wuyanta tana kallonsa, ya birkito y’ar yana masifa “Na ce me kika haifa? Allah yasa dai namiji ne wannan karan kiga yarda zan Miki gata don burina na ga an haifa min namiji ba mata gayyar matsala, Allah yasa magaji….” Cak yawun bakinsa ya k’afe ya tura jaririyar jikinta “Ungo tsiyarki Talatu, Allah dai ya tsinewa haihuwa irin taki ace duk sanda zaki haihu mace zaki haifa don masifa..” Wannan karan ba Talatu ba Har Jabiru sai da ya saki hawayen bak’in ciki musamman jin yarda A’isha ta tsanyara kuka saboda bugeta da yayi da hannunsa garin turata. Suna kallo ya shige ‘daki yana fa’din “Komawa zan yi ba zan zauna bak’in ciki ya kashe ni ba, Amma kafin na koma sai na samu dalleliyar yarinya na aura na huce takaici, ke kuwa wallahil azeem sai dai ki yi wahala da y’ay’anki ina tsiya ina haihwuar yara mata.” Tana kallo Ya saka kai ya fice daga gidan bayan ya fallawa Majeeda yarinya y’ar shekara hu’du mari ya fice yana “Shegun ‘yay’annaki idanunsu kamar na mayu.”
Ya fice ya bar Talatu da tafasar zuciya ta rasa wa zata rarrasa tsakanin Majeedah Aisha da Jabiru da shi ma yake kukan kamar mace.
Kabiru gidan mahaifinsa kai tsaye ya wuce akan sabon machine ‘dinsa, sanye da shaddarsa da aka yiwa bugun k’yalli. Tun a tsakargida ya fara musu yayyafin Naira. Da’di kamar ya kashe Innarsa ‘danta Kabiru ya ku’dance bata damu da inda ya shiga ya fita ya samo ku’din ba.
Sai da suka gaisa ta ce “Oh Kabiru shikkenan kuma sai muka nemeka b’at muka rasa.” Ya ‘dan shafa sajen da ya tara yana fa’din “Neman ku’di Inna, birni na wuce don na lura idan ka zauna a k’auyen nan ba zaka tab’a arziki ba.” “Tabbas kuwa Kabiru yanzu da ka tsallaka ga ka nan shar da kai.” Ya na dariya ya ce “Wallahi kuwa Inna ai bana Insha Allah zaki sauke farali.” Innan ta ‘d’an ja ajiyar zuciya “Wace ni da zuwa Makka bayan matarka tana ta haihuwar yara mata akai akai kamar wacce aka cewa jeki kya gani, ai tarin aurensu ya kamata ka fara.” Ta fa’da da gatsali don itama haihuwar Talatun tana ci mata tuwo a k’warya, kuma hakan da tayi so tayi ta bugu cikinsa ta ji ko ya damu da Talatun da yaran da take haifa masa. Sai ta ji Ya ce “Wa? ni? Allah ya kiyaye ai sai dai ta nemi uban da zai wa yaranta kayan ‘daki don masifa a ce shekara hu’du y’ay’an mace uku, kuma duk mata, ni wannan ta k’arshen ma ban san da cikin ba sai haihuwar na ji, ni fa Inna zama na da Talatu ya isheni tana can ta yamushe kamar tsohuwar mota, don haka sakinta zan yi..” “Kada ka fara, so kake mak’iya su saka ni a wak’a, ka barta da halinta ka samu wata kai kuma ka aura abinka ita kuma ta ci kanta ita da yaranta.” Kabiru ya ji da’din maganar mahaifiyarsa don haka ya gyara zama yana fa’din “Hakan ma za’a yi Inna, yanzu wace yarinya zaki samo min a garin nan y’ar manyan mutane.” Inna ta yi dariya sosai kafin ta ce “Haba dai Kabiru garin nan kuma? Ai birnin zaka koma ka samo y’ar manyan mutane ka aura tunda dai yanzu arziki ya zauna maka kamar yarda nake so.” Ya yi tsam da ransa yana tunanin anya matan birni za su so shi? Sai dai kamar yarda Innarsa ta ce arzikinsa shi zai siya masa aure don haka Ya ja ‘damarar auren matar birni. Tabbas Innarsa ta yi gaskiya da ta ce yafi k’arfin matan da
Suke k’auyen Shagogo. Ya kissima kalar matar da yake so ya aura y’ar manyan mutane mai ilimi matar da zai shiga da ita duk inda yake so. Haka ya tashi Ya bar Innan bayan ta da’da kambamashi da sanar da shi ko y’ar sarkin kano ya ce yana so Babu mai hana shi in dai da uwar ku’dinsa.
Yana fitowa ya yi kicib’us da Hadi abokinsa Hadi Har da tsallensa yana fa’din “A’a lallai Inye sai ga Kabiru. Ko da yake yanzu ka zama Alhaji Kabiru, wai don Allah menene sirrin ne? Ko nima dai birnin nan zan zo na bika.” Nan da nan fara’ar da take fuskar Kabiru ta ‘dauke ya girgizawa Hadi kai “Ba zaka iya harkar da nake ba Hadi, don haka kawai ka tsaya a inda kake.” Hadin ya kalleshi Galala kafin ya ce “Bak’in ciki kake min Kabiru?” Ya girgiza kai “Ba wani bak’in ciki ni gaskiya kawai na gaya maka Amma idan ka ga sai ka je sai ka bari na gane kan harkar sosai tukun na sai nazo na ja ka.” Hadi ya amince da haka suka k’arasa daga majalissar abokansu inda suke zama.
Tsaf ta gyara gidan ta kuma yi masa tuwon masara mai kyau miyar kub’ewa har wake ta watsa saboda miyar ta sake ‘dan’dano. Ta wanke yaranta tas duk don kada ta sake laifi a wajensa. Sannan ita ma ta yi wankan ta saka Jabiru ya amso mata bashin turare mai sauk’in ku’di Wanda ake ‘durawa a
K’walabe k’anana. Jabiru ba don ya so ba yaje siyan turaren nan yana tafe yana tsinewa Kabiru. Atamfarta da take sonta sosai duk da ta sha jiki sai dai itace sabuwa a cikin kayan ta ita ta saka ta ‘d’an yi kyau da ita Har da wanke kai da taje shi ya yi baya, sai ga kai yana k’yalli abinka da gashin fulani, kuma da yake mace ce mai tsafta tana kulawa da jikinta sosai.
Tun da ya doso gidan ya ji zuciyarsa ta fara tsananta da b’acin rai, sam baya son tafiya gidan don ya san kwashi kwaraf zai tarar a gidan sunan da ya saka mata kenan. Gaba ‘d’aya yanzu gani yake ya fi k’arfin a kirashi da mijin Talatu saboda yarda yake ji da tashen naira, ku’din da ba a San inda ya samo su ba..
Kamar yarda ya saba haka ya danna kai cikin gidan ba sallama bakomai sai gyaran muryar da shi yake nuna musu ya dawo.
Majeeda a tsorace ita da Zainab suka rungume Jabiru suna k’ikkifta ido, ba don komai ba sai don tsoron mahaifinsu da ya zame musu tamkar dodo jikinsu Har rawa yake, hakan ya ankarar da Kabiru Ya watsa musu wani kallo, mai nuni da zallar takaici shi suke gani su razana haka kamar wani Dodo ai kuwa yau zai yi maganinsu. Ya shige ‘daki Ya cire babbar rigarsa Ya wurgar don daman sabonsa ne duk abinda zai cire wurgar da shi zai yi sai dai Talatu ta ‘dauka ta adana na wankewa ta wanke. Wata igiya ya hango mai kauri igiyar da Jabiru yake k’ullo itace idan ya yiyo. Ya zaro igiyar ya fito tsakar gidan da sauri. Majeeda ya fara ja daga jikin Jabiru duk da k’ok’arin Jabirun na son cetonsa sai dai da yake Kabirun jibgege ne tuni ya wancakalar da Jabirun a gefe ya fara zabga musu igiyar. Zaniya sosai ya musu tun suna ihu har suka kasa ihun sai mayar da numfashi suke. Sai da hannayensa suka gaji sannan ya yar da bulalar yana zubawa Talatu ido “Ko zaku rama musu ne don na ga kuna hararata.” Talatu ta mayar da k’wallar bak’in cikin data gangaro kwarmin idonta tana girgiza masa kai cike da takaicin halayensa, ya shige ‘d’aki yana fa’din “Gobe ma don Uban yarinya ta sake gani na ta gudu. Y’an jakar Uba idanu kamar na mayu.”
Ya ci karo da kwanukan tuwon da ta jera masa, ya ‘dan bu’de da sauri kafin ya saki tsaki ya mayar da kwanon ya rufe ji ta yi yana k’wala mata kira da wani sabon suna da ya ra’da mata “Ke Uwar y’ay’a Ballagaza zo nan..” Ta mik’e ta saka k’afa zata je Jabiru ya ce “Don Allah Yaya kada ki je.” Ta juyo tana masa alamar ya yi shiru ta shiga cikin ‘dakin. Durk’usa wa ta yi sosai murya a raunane ta ce “Ga ni.” “Na ganki Ai, uban wa kika ajiye da zai ci miki bak’in abin nan? Na miki kala da mutumin da zai ci irin wannan abincin?” Ta yi saurin girgiza kai “To maza ‘debe shirginki kafin na miki facali da su a fuskarki shashasha kawai.
Takaicin Uba..
Na Nazeefah Nashe
Pg 18
💔💔💔💔💔💔
Ta runtse idanunta tana Jin takaici da zafin zuciya yana k’ok’arin buga mata zuciya, Ya Ilahi ya Kabiru yake so ta yi ne? Wannan wulak’anci tabbas ya fara mata yawa sai dai rashin takamaimai inda zata je ne yake durk’usar da ita a gidan Kabiru, tabbas da ta San inda zata ga dangin mahaifiyarta da bata zauna gidan wannan bak’in azzalumin ba, da bak’in cikinsa yake shirin aikata lahira. Ta sauke idanunta kan abincin da ta sha wahalar girka masa shi, har sai da ta surfa Masarar ta wanke ta tas, sannan da daketa a turmi Amma duk da wannan wahalar Kabiru yake kiran tuwon ta da bak’in tuwo alhali ko Mara gani sosai ya dubi tuwon nan ya san fari ne tas da shi, tuwon da babu ficikarsa a ciki ta yi ne kawai don ta kyautata masa a matsayinsa na Wanda ya bar gida wata da watanni. “Ba zaki kwashe ba? Sai na kifa Miki mari?” Ta juyo muryarsa a sama cikin daka tsawa, a razane ta hau tattare kwanukan ta fice da su da sauri hawaye na bin fuskarta, ta zauna a tsakar gida hannayenta zube a k’unci tana kallon yaranta da Jabiru yake ta hidima da su, tunani ta zurfafa a cikin sa na yarda ta taso a rayuwarta cikin wahala ga shi har zuwa yanzu bata huta ba, ba mamaki ma yaranta su tashi suma a wahalar.. Kuka ne sosai a kufce mata ta shiga furta “Ya Allah kada ka k’addarawa yara na koda makamanciyar wannan wahalar balle irinta.” Tana zaune ta dinga jan Hasbunallah kafin ta ji zuciyarta ta yi sauk’i. Daga ‘dakin ya dinga k’wala mata kira hakan ya sa ta farka daga tunanin da take ciki a razane, da sauri ta amsa tana shiga k’uryar ‘dakin. Sai da ta bita da kallon sama da k’asa sannan ya saki tsaki “Mace duk a koma’de, ni dahalla samu mifici ki yi min fifita na kasa barci. Wallahi na tsani na bu’di ido na ganki wai a matsayin matata, na rantse da Allah da na San haka zaki koma’de ba ta yarda za’a yi na biya sadaki na aureki, ga shi yanzu kin zame min k’arfen k’afa na sake ki ace ban Miki adalci ba don na ga ba inda zaki idan banda haka wallahi sakinki zan yi ki tafi gidan Ubale.” Bata masa magana ba haka ta dinga masa fifitar yana antaya mata bak’ak’en maganganu ga Kukan A’isha tana ji Amma ya hanata zuwa ta ‘dauketa.
___________________
Haka rayuwar ta cigaba da gangara musu cikin matuk’ar wahala da rashin matallafi sai Allah, Kabiru idan yasa k’afa ya tafi birni bata sake Jin ‘duriyarsa sai ya yi wata shida, ga shi baya ajiye musu komai ita takewa kanta da y’ay’anta komai, a hakan har makarantar boko ta gwamnati ta cilla Majeeda da Zainabu, suke tafiya da Jabiru da yake secondary. Har fargabar zuwan Kabiru take saboda da yazo tijara iri-iri yake mata, kuma ba yarda ba tayi da shi ya bata ku’di a mata aikin bu’dewar da gabanta ya yi Amma Kabiru ya hana ya ce ba shi da shi, ita kuma ku’din Sun mata yawan da ba zata iya biya ba, don haka ta yi zamanta a haka tunda shi yake mora ai ba ita ba. Ta wani fannin ma ita hakan ya fiye mata, tunda ko bakomai ta samu hutun haihuwa da gurzar da yake mata ba dare ba rana tunda yana daga cikin irin Harijan mazan nan.
Kwatsam wata tafiya da Kabirun ya yi da ya tashi zuwa gida sai suka gan shi ya dawo da dalleliyar mace babbar mace sosai kuma Wanda a haife ta haifi Talatu tare suka zo a cikin mota yana janta.
Tunda zauren gidan suka fara jiyo k’amshin matar don haka Talatu ta hau zuba ido tana son ganin mai shigowa. Tsaye turus ta yi sanda ta ga Kabiru y’a shigo da matar suna tafe suna wasan banza a tsakaninsu yana dukan mazaunar matar da k’afafunsa alamar a cikin nisha’di yake. Talatu ta tsaya tana kallonsu yarda suke lamura ko kunyar k’ananan yaran ba sa ji. Ya wani kama matar ya rungumeta yana shafar jikinta, da sauri Talatu ta kalli Jabiru da yake tsaye yana anta yawa Kabirun mugun kallo ta ce “Jabiru maza ku tafi ka raka su makarantar allo kafin ka wuce gonar.” Jabiru ya janye yaran suka fice yana Jin kamar ya mangare Kabiru da yake shirin tub’ewa matar riga, to yarda ya zura kansa yana laluben matar kamar mayunwacin zaki, dama kuma shiryota ya yi, yazo ne don ya ba’kantawa Talatu ko ta gaji ta hak’ura da aurensa su gudu da yaranta idan ta ga matar da ya aura, ya sha alwashin sai ya koreta don a gabanta zai dinga saduwa da matar idan ma bata gudu ba, yafi so zuciyarta ta buga ta Mutu ya huta ta yarda babu mai zarginsa.
Da sauri Talatu ta shige ‘daki tana Jin zuciyarta na shirin bugawa kamar wuta, ta jingina da bango hannayenta a k’irji sai mayar da numfashi take na zallar takaicin Kabiru da bak’in cikin rashin wajen zuwa da tabbas bata k’ara koda awa guda a gidansa ba zata tsere kafin Kabiru yasa bak’in cikin sa ya kasheta.
Tana runtse da ido hawaye na malala ta ji Sun danno kai cikin ‘dakin suna sakin wata irin dariya. Yanayin da ta gansu ba kaya a jikinsu ya sata saurin saka k’afa zata bar ‘dakin sai dai me? Sai Jin muryar Kabirun ta yi yana fa’din “Kina fita daga ‘dakin nan, a bakacin aurenki ki tsaya ki ga yarda ake saduwar aure mai da’di da cikakkun mata masu cikakken Gaba ba naki fafaroma ba..” ta tsaya
Cak bata jiyo ba, Amma Kabiru yana kan matar yana wani irin nishi ya ce rashin juyowarki da kallonmu kamar kin tsinke igiyar aurenki ne..” Jin haka ya sa ta juyo jikinta na rawa ganin wasu irin abubuwa da suke ta runtse idonta Kabiru ya sake daka mata tsawa ya ce “Bu’de ki ga yarda macen da ta San abinda take, take kula da mijinta…. Wayyo sahiba cigaba da’di da’di…….” Wani irin duhu Talatu ta dinga gani kafin su ji kif ta kifa da alama zuciyarta ta buga kamar yarda Kabiru yake so….
Kabiru bai bi ta kanta ba sai da suka samu gamsuwa sannan ya isa inda take yana fatan Allah yasa ta Mutu ya huta, sai dai burinsa bai cika ba domin da alama akwai sauran kwana tare da ita don jijiyar hannunta tana motsawa, ya saki tsaki ha’de da janta gefe ya fice daga ‘dakin. Wanka suka yi tare da karuwar matarsa da take jurewa Harijancinsa, don itama Harija ce mabu’kaciya ta masifa kuma ta da’de tana Neman miji kamar Kabirun bata samu ba dalili kenan da aurenta yake ta mutuwa sai dai gamuwarsu da Kabiru a gidan wata magajiyar Karuwai ta ji shi a jikinta a matsayin irin mijin da ta da’de tana nema shikkenan ta ce ta samu mijin aure don duk maitar sha’awarta tsaf Kabirun yake ‘dauke mata har ma ya buk’aci k’ari hakan dama take so shi ya sa zamansu ya zo ‘daya take lallab’a Kabirun kamar k’wai don bai k’i su kwana suna Abu ‘daya ba ba ya gajiya Sam, style kala-kala na kwanciya ba Wanda shi da matar ba su k’ware a kansa ba.
Suka yi wanka suka saka k’afa suka fice daga gidan, yana fatan Allah yasa kafin su dawo daga gidan su Talatu ta k’arasa cikawa shikkenan ba shi da wata sauran matsala…
Takaicin Uba…
Pg 19
Nazeefah Nashe.
💔💔💔💔💔
Shigowar su Jabiru da yarda suka tarar da ita ne yasa hankalin Jabiru a tashe ya yi kanta da sauri yana girgiza ta, sai dai shiru babu alamun numfashi a tattare da ita, da sauri Jabiru ya kandamo ruwa ya zuba mata, sai sannan ta saki ajiyar zuciya tana kallon su Jabirun da k’yar ta mik’e zaune tana Jin yarda k’irjinta ya mata nauyi. Abubuwan da suka farun suka dinga dawo mata daki-daki ta runtse idonta tana fatan duk abinda ya wakanan ya zama mafarki… zata so hakan, zata so ace mafarki take don lamarin yafi kada da mafarki ba gaskiya ba… Maganar da Majeedah ta yi ne ya sata ta bu’de idonta da k’yar tana kallonsu ganin yarda suka