Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : Hausa Book Store
gani da dukiyar fulaninta da suke tsaye cokar cokar kamar torch light. Da sauri ya ware idonsa yana kallonsu ta mudubi ta ganshi don haka itama cikin tashin hankali ta ja towel tana rufe jikinta da shi, muryarta na rawa ta runtse idanunta tana fa’din “Out Malam! Ta ya zaka shigo min ‘d’aki without any notice.” Kamar mara motsi haka ya tsaya da yaji tsayuwar na neman gagararsa sai ya koma jikin bango ya jingina yana kokawa da magana’disun da ke k’ok’arin jansa zuwa gareta. Komai ma ya kunce masa a yanzu kawai ita yake buk’ata da duk wasu halittu na jikinta, da gaske yarda yake zaton samunta haka take koma ya ce ta wuce haka ta ko ina itace kalar macen da yake so ya runtse idanunsa madadin ya daina ganin abubuwan sai ya ga still su idanunsa suke hasko masa hannunsa ya tusa cikin sumar kansa da yake jin kamar ana fisgar gashin nasa. Ita kuwa Ayra tana can k’udundune da mitsitsin towel ‘din da idan ta yi sama da shi k’asanta ne zai fito idan ta barshi a k’asan kuma dukiyar fulaninta zai cigaba da gani, abinda wani mahaluk’i bai tab’a ganar mata ba. Murya na rawa tace “Please Turaki hakan bai dace ba, ba kyau ganin tsiraicin wani don Allah ka fita.” Maganartata da yarda muryarta take shaking sai ya zame masa kamar fami daga abinda yake ji har bai san sanda ya iso wajenta ba cikin wani irin taku, sai dai kawai jin k’amshin turarensa ta yi ya k’ara yawaita a hancinta. Murya a dashe ya sunkuya daidai wuyanta yana sauke hucin numfashi a dokin wuyanta ya furta “Menene bai dacen ba? Abubuwan da mutane bila adadin suka gani without dowry shine bai dace ni da na biya sadaki na kalla ba, halak ‘dina ne fa, kuma ya halatta na ga duk inda naga dama a jikinki don haka cire min wannan towel ‘din Sadakina zan mora…” da sauri Ayra ta damk’i towel ‘din ganin fuskarsa ba annuri da gaske yake son rabata da towel ‘din “Ki bari na cire ta limana, ko na fisge da k’arfin iko, tunda dai gaba ‘dayanki ni nake iko da ke.” Ya fincike towel da k’arfin gaske ya wulla shi can gefe, da sauri Ayra ta damk’i k’irjinta da tafukan hannayenta. Turaki kuwa numfashinsa ne yake neman ‘daukewa da kyar ya sake k’arfin halin watsa mata magana “Abin mamaki kika bar wasu banza ye ma suka gani sai nine marainin wayanki.” Shammatar sa Ayra ta yi ta shige toilet da mugun speed ta datso k’ofar. Ba shi da k’arfin binta don duk jikinsa a sanyaye yake da k’yar ya zame ya fice daga ‘dakin Yana jin yarda halittunsa suke ‘daurewa tamau agaji kawai suke nema.
Ayra kuwa kuka ta saka a toilet tana tunanin k’arshen tozarci da wulak’anci yau Turaki ya yi mata shi. Ta dinga hango mayatattun idanunsa da suke bu’dewa Suna lumshewa a
Kan halittunta. Da k’yar ta fito jin ya fita daga ‘d’akin ta datse k’ofarta ta zura Riga ha’de da kwanciya tana mayar da numfashi.
__________
Da k’yar ya mik’e da safe don yana son zuwa karb’o musu boarding pass. A falo ya tarar da ita tana ta aikin babbaka turare jikinta sunk’ufe da hijabi kallo ‘d’aya ya mata ya ‘dauke kai ita kuwa mamakin yarda ya fito da wani bak’in glass ya maka take, har ya gifta ta ya juyo murya a shak’e ya ce “Ki zama ready Flight ‘din mu zai tashi 4:00 sharp. Ki buga waya ki sallami kowa.” Bai jirata ba ya fice da sauri ya barta tsaye tana jin wata razananjiyar fa’duwar gaba, da tunanin shikkenan tata ta k’are idan ta sake ta bi shi k’asar da ba tasu ba yanzu menene mafita? Ta fa’da tana cizon leb’enta na k’asa abinda ya zame mata jiki…….
JikarNashe.✍🏽✍🏽
Takaicin uba….
Nazeefah Nashe
37.
💔💔💔💔
Saukar hawayen da ta ji a saman kuncinta ya tabbatar mata da ta kai k’ololuwar b’acin rai. Me Turaki yake son mayar da ita ne? Abar ikonsa da zai dinga juyawa kamar sitiyarin mota a duk sanda ya so, shi bai san sam ba sonsa take ba, ba kuma ya gabanta kamar yarda ta tabbatar ita ‘din ma ba a gabansa take ba. Ta ha’diye abinda ya tsaye mata a mak’oshi kafin ta raruma wayarta da sauri ta shiga danna kiran layin Amma gwara ta sanar mata ita ba zata bi Turaki ba, to idan ma ta bi shi wa zai cigaba da kula musu da dukiyarsu. Bugu biyu Amma ta ‘dauka don dama zancenta suke da Dijah tana bata sak’o zata kai mata na kazar ta da aka kawo daga zuru, da sauran tarkacen kayan matan da ya jaddadawa Dijah a kan ta shanyesu tas a gabanta. Ta ‘d’aga wayar tana murmushi kafin ta ce “Y’ar gidan Amma ya aka yi?” Madadin ta amsa mata sai ta saki kuka, kuka sosai take yi kukan da ya razanar da zuciyar Amma, da sauri ta hau fa’din “Ke tsaya, me yake faruwa Ayra?” “Amma na gaji da k’arfin ikon da mutumin nan yake nuna min, juya ni yake kamar wadda ya saka ku’di ya siya.” “Haka auren ya gada Ayra sai hak’uri. Yanzu me ya faru?” Ayra ta sake sakin sautin kukanta da take son lallai sai ta siye zuciyar Amma da shi ta amince da buk’atar da zata zo mata da shi. “Wai sai na bi shi,
Ni kuma in yi yaya da nawa aikin idan na bi shi.” “Ki ajiyeshi ki bi umarnin aure shi ne abinda zai rabauce ki duniya da lahira, ina za ki bi shi?” “Can inda yake aiki.” Amma ta saki murmushi ta ce “Ma sha Allah haka ake so.” Da sauri Ayra ta zaro ido jin abinda Amman tace “Me kika ce Amma?” Da sauri Amman ta k’unshe baki don dariya ce take son kufce mata “Cewa nayi Allah sarki zan yi kewar autata, ki yi hak’uri kin ji ki bi shi Allah ya miki albarka.” Kuka ta saka sosai tana jan hanci ta ce “To Amma kuma ya hana nazo na muku sallama ke kizo don Allah.” Amma ta waro ido “In
Zo ina? Rufa min asiri da zuwa gidan suriki, ga dai Deejah nan dama ina shirin aikota gidan naki kiranki ya shigo, ki tabbatar duk abinda ta kawo miki kuma kin yi amfani da shi tas kin ji y’ar albarka bana son ki min musu sai ‘dan gata ne yake samun irin wannan kayan kada ki min wasa da su in dai kina son farin ciki na.” Ta saki ajiyar zuciya murya na rawa ta ce “To Amma.” Amma ta zare wayar a kunnenta tana fa’din “Ayra Danger! To idan baki bi mijinki ba me zaki zauna ki yi anan ni nagode masa ma Ai daga ganinsa ba zai ‘d’au shirgin shiriritar ta ba.” Deejah na dariya ta ce “Yau da kanki Amma kike kiran Ayra mashiririyace.” Itama dariyar ta yi kafin ta ce “Ai sunan nata kenan, kullum madadin girma k’ara zama yarinya take, ta shi maza kije ki titsiyeta sai ta cinye komai na jikin kazarnan ta kuma shanye roman sannan ta shanye tsumin nan tas kada ta saka ni asarar mak’udan ku’di kazar nan ka’dai ta isheta komai ta b’arin aurattayya koda zata shekara bata sha komai ba dangane da magungunan mata.” Deejah ta mik’e ‘dauke da ledar a gabanta tana fa’din “Mu Amma wannan karan baki mana kazar ba.” Ta harareta kafin ta ce “Ta autata nake yi kowa ta fitar da ku’dinta ta siya.” Deejah ta ‘dan turo baki tana fa’din “Ai shikkenan zan samu Anty Surayya marubuciyar Halin yau na siya a wajenta don itama tana kawo su masu kyau.” “Ya dai fi miki.” Amma ta fa’da tana gyara kwanciyarta a saman 3 seater don da gaske sosai take gyara y’ay’anta bata son su yi rayuwar boranci a gidan aurensu kamar yarda ita ta yi a nata gidan auren saboda rashin gata.
Da sallama Deejah ta shiga chalet ‘din gidan sai dai tsit da alama Ayran tana can ciki, don haka ta zaro wayarta ta fara kiranta tana ‘d’agawa ta ce “Malama ina k’ofa ki bu’de min.” Ayra da sauri ta yayimi gyale ta fito daga kitchen ‘din don bu’de mata k’ofar kana ganin yanayinta ka ga mara walwala sam zuciyarta bata mata da’di.
Sosai ta rungume Deejah cike da tsananin farincikin ganinta Deejah tana murmushi ta ce “Malama kada ki yar da ni, yau ke ce kike murnar gani na?” Ayra bata yarda ta saketa ba sai da ta saki kukanta sosai a jikinta sannan suka shiga ciki Deejah tana fa’din “Kukan da’di kike Ayra, Allah ya kashe ya baki dandatsetsen Mijin kerewa sa’a madadin ki gode masa sai kike son butulce masa dubi fa ni’imar da ubangiji ya miki ta ko ina, kuma daga ganin Turaki irin mazan nan ne masu kashe Matansu da soyayya mai nutsar da zuk’ata, kulawa da riritawa har sai kin gaji da shi.” Ayra ta zaro ido tana fa’din “Mhnm! Yaya Deejah baki san halin wannna mutumin ba kenan, wallahi wahala kawai yake ba ni kin san kallon da yake min kuwa? Wai karuwa! Ko uban wa ya gaya masa na tab’a karuwanci?” Deejah ta waro ido a tsorace ta ce “Ban gane ba ya kusanceki ya ji akasin budurci a tare da ke ne?” Ayra ta ‘dauke k’wallar da take zuba k’asan idonta tana girgiza kai “Allah ya kiyaye wannan mutumin ya kusanceni, shima ya yiwa kansa togaciya ya ce duk ranar da ya kusanceni na k’addara kamar na karb’i takardar Sakina a hannuna ne, shi ba zai kusanci fasik’a ba da ta Riga ta gama rabawa maza jikinta a waje ba,
Wannan maganar Ya Deejah tana min k’una a rai, kuma wallahi bana tunanin zan yafe masa wannan k’azafin, koma me ya faru Ai k’addarar bawa baya wuceta.” Deeejah kanta jikinta tsuma yake da b’acin ran abinda Ayran ta gaya mata take, sam sai ta ji ta fara jin haushin Ameen duk da ta tabbatar da wata a k’asa ba mamaki wani ne ya zo ya bashi labarin akasin labarin su. Jikinta a sanyaye ta dafa Ayran murya da laushi ta ce “Tabbas! Bawa baya shige k’addararsa, Auren Turaki shine ta ki k’addarar Amma kuwa zai yi nadama a duk sanda ya samu labarin ainahin abinda ya faru, kada ki kula shi a wannan gab’ar duk abinda zai miki ki zama tamkar doluwa ki k’ask’antar da kanki ina tabbatar miki wata rana da bakinsa zai furta Kaico na ni Turaki, yanzu ki cigaba da amfani da duk wasu magunguna da za’a baki, za su miki amfani wata rana, ga kaza nan Amma ta ce ki cinye tas a tattaro mata k’ashin na kai mata ki shanye tsumin nan, ita kuma wannan zumar da garin maganin ki tafi da su da fresh milk za ki dinga sha ko yoghurt k’arfe nawa ya ce za ku tafi?” Ta nuna mata yatsunta hu’du alamar k’arfe 4:00 za su tafi. Deejah ta duba agogo ta ce kin ga ba lokaci yanzu har 1:00 ki zauna ki ci kazar ni bari na shirya miki akwatin da za ki tafi da shi, shawarata ki jajirce wajen kwalliya da dadda’dan girki har sai kin janye hankalinsa tsaf sannan wasan zai fara. Sai yazo ya yi regretting kalamansa.” Ayra murmushi kawai ta saki tana tunanin idan ta samu ta b’alle daga gidan Turaki bata tunanin akwai wani mahaluk’in da zai mayar da ita. Tsaf ta gyara zama ta fara cin kazar nan, don dama bata ci wani abincin kirki ba, ga kazar ta yi mata da’di a bakinta tsumin ma kamar Lemo haka take kurb’arsa ba canjin taste sosai.
Deejah wasu irin futinannun kaya ta dinga zubawa Ayran a babban akwatin da za ta tafi da shi, Nightwears masu masifar bayyana surar jiki da English wears sai kayan mu na gargajiya ka’dan. Ta saka mata wasu sexy turaruka masu masifar janye hankalin namiji duk a kayan da ta taho mata da su. Ta gama gyara wa ta kulle akwatin tana ‘dan sakin murmushi don ta tabbbata idan Ayran ta san tsiyar da ta k’ulla mata sai sun kwashi y’an kallo.
Tana komawa falo bugun k’ofar su Ummeey yana ratsa falon Ayran na dubanta ta ce “Ya Deejah har kin yi me?” “Har na ha’da kwashe tarkacen Ki ki shiga ciki ga bak’i nan kin bararraje.” Ta fa’da tana sakin labulan windown ganin su Ummeey ne. Tsam Ayra ta mik’e da sauri ta shige ‘d’aki da shirginta. Ummeey tana murmushi tace “A’a Yaya Deejah ana nan kenan.” Deejah ta mata sannu da zuwa tana amsa gaisuwar su Tayseer da suke gaisheta ta ce “Ban da’de da zuwa ba na zo mata sallama.” Ummeey ta girgiza kai hakan Yayi kyau mu ma sallamar muka zo mata don shak’iyanci sai yau Turakin yake gaya min wai yau za su tafi.” Deeja ta yi dariya kawai ta basu hanya suka shiga ciki ita kuma ta shiga kitchen don kawo musu abin tarar bak’i.
Hijabinta ta zumbula ta fita falon, fuskarta washe da murmushi ta isa kusa da Ummeeyn tana shirin Zubewa Ummeey ta jata gefenta “Zo ki zauna kusa da ni kin ji daughter, nifa bana son wannan y’ar kunyar ki saki jikinki ni Mamanki ce ba wani surika.” Ayran ta ‘dan shiga jikin ta ka’dan tana gaisheta. Ummeey ta amsa cike da kulawa “Ya shirin tafiya? Mijinki Ai bai kyauta min ba
Da sai yau yake sanar da ni za ku tafi, Allah yaso na yi miki tanadin tafiyar.” Su Tayseer suka gaisheta ta amsa musu cike da kulawa tana tsokanarsu da “Shine ko ziyara? Ai shikkenan nagode.” Tayseer ta yi dariya “Wallahi mun so zuwa Ummeey ce ta hana mu wai ba a zuwa gidan amarya.” “K’warai ni na hana ina dalili kuzo ku dameta, Aman ma hana shi zuwa na yi yanzu ma ni na hana uban su tafi da shi na ce ya yi zamansa a nan, idan an kwana biyu suka zo hutu sa tafi da shi ko su barshi ma gaba ‘d’aya.” Ta bu’de jakarta ta mik’awa Ayra wata shopping bag mai kyau “Kada ki yi wasa da su turaruka ne masu kyau da nagarta ko Wanne da gab’ar da ake gogashi akwai bayanansu a jiki. Wannan Kuma yaji ne ki tabbata kina yawan cin sa a abinci shima akwai nasa sirrin daban sauran kayan kuma duk akwai yarda zaki yi amfani da su, ki min alk’awarin ba zaki yi wasa da su ba Mu daughter.” Ayra tana murmushi ta ‘d’aga mata kai tana mamakin hali irin na Uwar mijinta mai sauk’in hali ta Kuma ‘dauketa kamar y’arta ba surika ba.
Ba su da’de a gidan ba, Turaki ya dawo da ‘dan hanzari don har 2:45 ta yi kuma kamata ya yi a ce 3:00 suna airpot. Turus ya yi ganinsu zube a falon sai kuma ya ‘dan zauna Kusa da Ummeey yana gaisheta ta amsa tana nuna masa Deejah jin bata ji gaisheta ba “Baka ga Yaya Deejah bane?” Ya mayar da kallonsa inda take nuna masa ba tare da ya ganeta ba ya ce “Ina yini?” Ta amsa masa da sakakkiyar murya Ummeey ta ce “Na san dai baka shaidata ba, to surikarka ce Yayar Ayra ce ita Ayran take bi.” Ya ‘dan saki fuska ha’de da sabunta gaisuwar sannan ya mik’e da sauri yana duban Ayra “Ki wuce ki shirya da sauri mun kusa makara kuma ba mamaki kina da kaya ke za ki yi delaying ‘dina.” Mamaki ya kusa kashe Ayran a zaune ganin yarda yake mata magana murya a nutse cike da kulawa. “Ai kuwa mace ba za’a rabata da shirgi ba, Maza Ayra ki je ki shirya sai mu sauke ku a airport ‘din mu wuce.” Ta mik’e ta shige ‘dakinta tana sake jaddada mamakin makircin Turakin.
Tsaf ta shirya cikin wata doguwar Riga mara nauyi sosai light blue ta yane kanta da mayafin rigar ba k’aramin kyau ta yi ba duk da bata shafa komai a fuskar ba sai powder da lip balm. Tattausan k’amshi ne a jikinta wanda in dai ba ka matso kusa da ita ba bai zama lallai ka ji shi ba. Ta saka Blue shade ‘dinta a jaka sannan ta watsa chewingum da sweet a jakar. Takalmi rufaffe ta saka duk da yana da ‘dan tudu ka’dan.
Tunda ya fito yake duban agogo yana tsaki k’asa-k’asa yarda ba za’a ji shi ba. Gaba ‘d’aya falon suka zuba mata ido ganin yarda ta fito kamar a saceta a gudu, shi ‘din ma ta k’asan ido yake kallonta yana fa’din ’Me Kyan ‘dan miciji.” Babban akwatin ya kalla sai ya ji Ummeey ta ce “Ke Tayseer za ki iya jan akwatin ne, ga mijin ta Ai da kin bari ya taimka mata ya yi koyi da sunnar Manzon Allah.” Da sauri ya ja Trolley ‘din don da gaske sun kusa makara. Su Ummeey suka bi bayansa bayan Deejah ta kashe duka switch ‘din gidan tana jin kamar ta saka kuka haka kawai take kewar rabuwa da Ayran.
Har Airport suka rakasu suna tafe Ummeey tana sake jaddada musu muhimmancin aure da zaman lafiya a cikinsa. Turaki ji kawai yake don duk abinda ta fa’da ya san sa kawai dai akan wannan yarinyar ne ba zai gwada ba, haushi yake ji sosai idan ya tuna yarda ta sarayar da mutuncin ta a kan titi, shi kuma irin jararabawarsa kenan bai tab’a zina ba amma ayi ta aura masa mazinata. Suka yi sallama kowanne da guntun hawayensa a idonsa Deejah dai kasa daurewa ta yi sai da ta saki kukanta sosai.
Sun shiga jirgi Ayra ta dinga duban jama’ar kowa zata gani sai ta ganshi a kan trolleyn sa da jibgegiyar rigar sanyi da hula a saman trolleyn, shima kuma Turakin haka ta gansa da su. Bata dai yi magana ba ta shige ta bi bayansa tana kallon yarda yake wani ha’de rai yana mazewa kamar wanda aka gayawa bak’ar magana. Suna zama yana sakin tsaki musamman ganin yarda wani ya zubo mata ido kamar zai lasheta murya k’asa-k’asa cike da Takaici ya ce “Matsalar ka auri yarinyar da ta tab’a yawon duniya kenan, duk inda ka je da ita sai ka