Author : Nazeefa Sabo Nashe Category : Hausa Book Store
rabuwa?” “Sai alheri Anty, komai ma ya faru Amma dai bayan bari na gida ban wani wahala ba na samu scholarship ‘din da aka da’de ana gayyata ta ina kaucewa, bari na gida sai na nufi Kano gidan su wani amini na a can muka nemi scholarship da shi muka dace aka tura mu k’asar Egypt zamu koyi karatun likitanci. Shikkenan tunda na saka k’afa na bar Nigeria ban sake waiwayarta ba sai yanzu da k’addarar ha’duwa ta da ku ya sa na zo Nigeria a kan Health Minister yana son ganin mu, likitocin Nigeria da suke aiki a wata k’asa. Last month na zo aka kuma rik’e mu a k’asar mu a kan cewa Nigeria ta fi buk’atarmu fiye da k’asashen da mukewa bauta. Ina nan zaune a Abuja a Maitama.” Amma ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Barinka gida Alheri ya zame maka Jabiru, Allah ya sake yiwa rayuwarka albarka.” Ya amsa da ameen yana cewa “Amma saura ku ya labarin taku rayuwar?” Amma ta saki murmushi ta ce “Ta mu rayuwar sab’anin taka ce Jabiru mun fuskanci k’alubale iri iri kafin Allah ya warware mana komai. Karo na farko da Amma ta fara bada labarinsu ba tare da kuka ko hawaye ba ba kuma nauyin zuciya ko ka’dan duk wannan tarin bak’in cikin da take ji ya kau sai wanda ba za’a rasa ba. Kafin ta gama Jabiru ya jik’e handkerchief d’insa da hawaye gaba ‘d’aya ji yake da ace zai ga Kabiru ba abinda zai hana sa sumar da shi idan ma bai zama ajalinsa ba. Ummeey ce ta yi k’ok’arin ba shi hak’uri kawai don kowa a ‘dakin kukan da Jabeer yake ya kashe musu jiki. “Ka yi hak’uri Jabeer, komai ya wuce shi kuma Kabiru Allah ya shirye shi ko da yake tun a yanzu ya fara ganin hukuncin Ubangiji a kansa. Ku gode wa Allah da ni’imomin da ya yi muku, ba mamaki da Kabirun bai cutar da ku ba da baku samu wa’dannan tarin alhairan da suka bibiyeku a rayuwa ba, da tuni kuna nan a can k’auyen ba tare da kun kai matsayin da kuke kai yanzu ba. Allah ya kiyaye mu daga halayya irinta Kabiru, ba zan ce ku yafe masa ba, amma zai kyautu ku ba shi hak’kinsa na Mahaifi kada hakan ya zama Hujjar da gobe alk’iyama Allah zai yi fushi da ku. Kada ku zama d’aya ku da shi, shi ya tauye muku hak’kinku kuma kun tauye masa shikkenan ranar alk’iyama duk za ku tashi a tutar babu! Ku kula da hakkinsa da yake kanku ko da ba ku yi mu’amala mai kyau da shi ba.” Amma ta saki ajiyar zuciya tana jin sauk’in zuciyarta sosai kuma ta yarda abinda Hameeda ta fa’da yana kan hanya, tabbas Kabiru yana da ha’k’ki akan y’ay’ansa ba zata hanasu kula da Babansu ba idan sun yi niyya sai dai da bakinta ba zata saka su su yi ‘din ba, kamar yarda take ganin su ma ba za su saki jiki su kyautata masan ba. “Hakan ni’ima ce babba idan kuka yi masa, ya zama kun tura masa aniyarsa kenan, ku ‘din da yake gudu kune dai kuka zame masa majingina a rayuwa, amma fa ku yi tunani shawara ce na baku, da kuma tunawa da girman Ayar nan da ta bayyana girman iyaye.” Hameeda ta sake fa’di jikinta a sanyaye. Duka ‘dakin tsit aka yi musamman Majeedah da take jin da ku’dinta dai ba zata iya taimakawa mahaifinta ba. Ta rufe idonta kawai ruf tana jin tsohon mikinta yana taso mata, don ma tata zuciyara akwai juriya sab’anin Ayra kuma ta samu Miji mai share mata hawaye wanda baya son ganin b’acin ranta ko ka’dan. Hameeda ta saki ajiyar zuciya don tabbas ta san daga ganin yanayinsu shawararta da nasiharta bata karb’u ba, ba kuma ta jin zata karb’u nan kusa sai dai za tai ta nusar da su har su gane inda ta dosa. Sai bayan isha duk suka tafi gidajensu suka bar Ummeey Hameedah da Aysha da za su kwana da Amma. Jabiru kuwa har past 11:00 Yana tare da su kafin ya tafi gida zuciyarsa cike da tunanin irin rashin mutuncin da zai wa Kabiru da ma Hadi d’an kanzaginsa gaba ‘daya ya saka a ransa da zarar an sallami Amma k’afarsa k’afarsu zai je har Kano ba don komai ba sai don ya ga Kabiru ya sauke masa kwandon rashin mutuncin da ya tanadar masa.
________________
Cikin dare Ayra tana barci ta dinga jin bugun k’ofa a hankali kamar za’a b’alla. A tsorace ta mik’e tana kunna switch ‘din fitilar da yake gefen gadonta. Kafin ta mayar da gashinta da ya bar baje ta saka band ta k’ulle sa ta mik’e tana ‘daura igiyar rigar barcinta. “Waye?” Ta furta a hankali bayan ta isa bakin k’ofar “Please Ayra ki bud’e ba ni da lafiya, wallahi kamar zan mutu.” Ayra ta ‘dan waro idonta sai dai jin muryarsa ya bayyana mata tsananin ciwon nasa don haka bata kawo komai ba ta bu’de k’ofar. Tana bu’dewa ya k’ank’ameta jikinsa na wani irin shivering kamar mai jin sanyi. Ayra gaba ‘d’aya hankalinta ya tashi jin jikinsa kamar ana hura masa wuta. Ta rintse idonta tana k’ok’arin janye jikinta. “Kada ki janye zan fa’di.” Ya fa’da cikin muryar wahala. Ayra cikin d’an tashin hankali ta ce “Kan bed zan mayar da kai.” Sannan ya ‘dan raba jikinsa da nata ta samu ta ja hannunsa kan gadon ta. Kwanciya ya yi ruf da ciki hannayensa a damk’e da k’asan cikinsa ya ce “Ayra mutuwa zan yi.” Ayra hankali ta ce “Me ya sameka?” Sai ji ta yi kawai ya yi yana kishi sama-sama. A razane Ayra ta ce “Ina wayarka na kira Doctor.” “Tana bedroom.” Ta juya da sauri zata nufi waje don ‘dauko wayar ta ji kawai ya fisgota “Ke ce maganin Ayra, don girman Allah ki yi hak’uri ki yafe min laifina Wallahi idan baki amince da ni anything can happen cikin daren nan.” Ayra ta zaro ido kafin ta ce “Oho! Shine sanadin ciwon naka kenan, ai kuwa ba zaku samu sauk’i ba wancan ‘din ma da kaga na yarda na gaya maka dalili don haka gwara ma ka je ka nemi maganin ka ba Ayra ba.” Ya sake kamata yana ‘dora k’irjinsa a bayanta ya rungumota ta baya “Ki yarda Ayra ba maganin da zai iya yi min aiki a daren nan, na sha Wallahi ba su yi min ba sun ga ji da yi min aiki.” Ayra ta cije leb’enta tana jin wani abu mai kama da tausayinsa yana son lullub’eta kafin ta runtse idonta tana jin yarda hannunsa yake shawagi a jikinta yana tab’a duk inda yake so. Kawai sai ta dinga jiyo amsa kuwwar maganarsa yana ce mata duk ranar da na kusanceki ki k’addara kamar kin amshi takardar sakin ki ne a hannunki me Zan Yi da karuwa! Da k’arfin gaske Ayra ta tureshi daga jikinta duk da ganin ya kai wani yanayi da ba zai amsa kira ba, so yake kawai ya kai ga harawa ya ga ta angajeshi sam ba shi da k’arfin rik’eta yana ji yana gani ta fice parlour duk da kiranta da yake yana fa’din “Please sweety ki cike ladanki” amma ta fice ta na rufo k’ofar da k’arfi. Bedroom d’insa ta wuce ta shige tana mayar da numfashi bayan ta murza key ‘din k’ofar. Ta saki ajiyar zuciya tana k’arewa ‘dakin nasa kallo da abinda yake fitarwa sai zallar k’amshin turarukan da yake amfani da su, sun kama d’akin ra’dam. Ayra ta gyara y’ar k’aramar rigar barcinta don ta yarda top ‘din a can. Ta koma kan gadonsa ta kwanta tana jan abin rufarsa k’amshin turaren ne yasa itama ta dinga jin wani feeling da bata tab’a ji ba a rayuwarta. Ta dinga juyi cikin tashin hankali kafin ta dam’ki pillow tana jin kamar ta tashi ta kai kanta wajensa. Tsawon daren Ayra ta kasa runtsawa kamar wacce ta sha wani abu saboda yarda Turaki ya bi ya tayar da duk wata sha’a wa da take jikinta. Tsam ta mik’e ta nufi k’ofa ba abinda zuciyarta take gaya mata irin “Tafi Ayra ki samu ladan kan ki da na mijinki kada ki halaka!” Ta saka hannu ta murza key ‘din kafin ta runtse ido tana fa’din “Anya na je kuwa? Me Zan ce masa idan na je.”
Da alama Turaki zai ci wasan nan,,, tunda ga Ayra tafe zata kai kanta 😂
Takaicin Uba..
55.
Mayar da k’ofar ta yi da sauri, tana k’ara murza key ‘dinta jin kamar takun da Sawayen Turaki. Ta jingina da k’ofar tana mayar da idonta ta runtse ha’de da sakin ajiyar zuciya. Tana jinsa ya mur’da handle ‘din key ‘din alamar zai bu’de sai ya ji ta a kulle. Ya ‘dan yi knocking nan ma bata bu’de ba tana juyowa ya saki ajiyar zuciya kafin ya sake jan k’afafunsa ya bar wajen. Ayra ta runtse idanunta tana jin tausayinsa na tsirga mata sai dai da sauri ta wancakalar da tausayin da tunanin shi ne ya hanashi tausaya mata a lokacin da yake tunanin ta rasa budurcinta. Kuka ne ya kufce mata tana jin k’unar abin a cikin ranta, kamar yanzu komai ya faru. Ta shige toilet tana sakarwa kanta shower da sauri kafin ta ‘dauro alwala ta fito. Sallah kawai ta tayar. Kafin ta zaro wayarta ta fara booking ‘din flight da zai ta shi jibi wanda zai isar da ita Nigeria.
Da k’yar ta tashi k’arfe goma na k’asar can saboda rashin barci da bata samu ta yi ba. Ta gyara gidan kamar yarda ta saba da sauri ta kuma yi musu break fast sannan ta shiga wanka. Mai kawai ta mutstsika ta kawo y’ar rigarta wacce da ka’dan ta wuce mata gwiwa. Rigar ba ‘dan ka’dan ba ta yi mata kyau sai dai duk ta bayyana duk wata sura ta jikinta. Cikin zuciyarta ta ce “Allah ya isa Deejah. Don ita ta cuceta da ya fitar mata irin wa’dannan kayan. Ta kama gashin kanta da sauri kafin ta murza sihirtacciyar Humra a jikinta. Ta fice falo tana ‘dan ji music a hankali cikin wayarta. Barci ne yake son sake fisgarta ita kuma bata son yi don haka ta ‘debi oat ka’dan ta zauna tana sha.
Kusan 12:00 ya fito black jeans ne a jikinsa da farar Riga. Yau ko gashinsa bai taje ba sabida ba shi da nutsuwa sam a tare da shi. Jikinsa a sanyaye kamar mara lafiya ya isa cikin jeren kujerun falon ya zauna ba tare da ya sake yiwa Ayra second look ba. Itama ba bata kulashi ba tana ta shan oat ‘dinta. Da peppe soup da ya gama cika wajen da k’amshi. Tana gani ya saka hannu a aljihu ya zaro wayarsa ya shiga daddannawa kafin ya saka a kunne bata ji me ya ce ba ta dai ji ya ambaci Shaheeda cikin k’asa da murya sosai. Haka kawai sai ta ji ranta ya b’aci ta fara kallonsa ta gefen ido shi ma a sace yake kallonta suka ha’da ido sai ta ga ya ‘dan kawar da kai yana tsaki. Ba a fi 10 minutes ta fara jin knocking k’asa-k’asa. Ba shi da courage na tashi don haka cikin k’asa da murya ya ce “Please Open the door.” Ayra ta zuba masa ido kafin ta mik’e don kawai sai jikinta ya bata Shaheedan tasa ya kira. Don haka ta mik’e daga ita sai b’ingilar rigar da take jikinta ta nufi bu’de k’ofar. Turaki ya runtse idonsa yana jin wani irin bugun zuciya ya lura so yarinyar nan take ta kashe sa. Ya sake shak’ar Humrar yana jin kamar ya janyota ta k’arfin gaske sai dai ya yi alk’awarin ba zai sake kusantarta ba har sai ya dasa mata soyayyarsa mai girma a zuciyarta.
Ta saka hannu ta bu’de k’ofar Budurwa ta gani tsaye cikin shigar black jeans da red shirt. Sai mayafi da ta yi rolling jikinta ka’dan. Shaheedah ganin Ayra ya saka gabanta fa’duwa ta fara matsa yatsunta tana kallon Ayran k’asa k’asa tana jin gwiwarta na sanyi. Ayran ma naga gaban fa’duwa ya yi kafin ta finciki leb’enta tana lumshe idanunta da ta ji suna neman bayyana damuwarsu k’arara. “Menene?” Ta fa’da tana ware idonta a kan Shaheedan. “Matsa” ta jiyo Turakin da yake gefenta bata san da isowarsa wajen ba ya fa’da. Cikin mamaki ta juyo tana kallonsa ba tare da ta matsa ‘din ba. Ya cafki hannunta ya matsar gefe yana kallon Shaheedah ya ce “Shigo” ta ‘dan saki murmushi tana bi ta gefen Ayra ta shige cikin takun da yake nuna isa da iko. Ta isa falon ta zauna kan kujera. Ayra tsoro ne yasa ta ware idonta kan Turaki da yake damk’e da hannunta. Ya watsa mata wani kallo kafin ya saki hannun ya juya yana zama daf da kujerar da Shaheedan take. Ayra ta tsaya cak tana kallonsu suna magana k’asa-k’asa sai kuma suka saki dariya suna Kallon Ayran. “Shaheeda ta maza ki samar min something special a kitchen you know i like your special cooking.” Shaheedan ta mik’e cike da yauk’i tana fa’din “Your wish is my command Habibeey.” Ta ‘dan kalli Ayran da take tsaye ta yi folding hannayenta kawai tana kallonsu. Kafin ta tab’e baki ta shige kitchen wani bak’in ciki ya dugunzuma zuciyar Ayran a fisge ta kalli Turaki tana jin wani irin hucin b’acin rai ta ce “You mean wannan ka kawo gidanka ta maye gurbina?” Sai kuma ta saki murmushi ta ce “Ashe kai ne ‘dan iskan shi yasa baka son ka auri y’ar iska… so let me tell you nima ba zan zauna da ‘dan iska mai kule-kulen ko wasu tarkacen mata ba, yarda ka tabbatar ni nutsatsstiya ce haka zan auri kind husband wanda ya fika.” Sam bata san sanda ya iso gabanta ba sai ganinsa ta yi a gabanta ya saka hab’a ya ‘dago fuskarta ta runtse ido tana jiran ta ji saukar hannayensa a fuskarta. Ya k’arewa fuskar kallo kafin ya saki murmushin takaicin “Idan ban kulata ba ya kike so na yi? Kina son na kai kaina wajen turawa ne? Tunda ke kin kasa ba ni abinda nake so, ki rik’e kayanki ki jik’a a ruwa ki sha, ga mata nan da yawa a gari…” Ayra ta runtse ido tana fa’din “Matan ma suna suka tara.” Ta fincike jikinta tana kallonsa “Kada ka sake tab’a k’azamin jikinka da ya Riga ya gama gogayya da y’an matan bariki da nawa.” “Ni kike gayawa haka?” Bata san sanda ta ce “Na fa’da ‘din ko k’arya na yi.” Ya ciji leb’ensa kafin ya ce “Ba kiyi k’arya ba.” Ya juya ya barta nan a tsaye yana komawa kitchen ‘din. Ayra ta runtse idanunta da sauri ta shiga bedroom ta mayar da k’ofa ta rufe har da murza key sannan ta ji wani irin kuka ya zo mata. A hakan ta shiga tattara kaf kayanta ta ha’de su waje ‘d’aya a akwati. Tana jin tafasar zuciyarta na k’aruwa ji take dama ta bu’de idonta ta ganta a gaban Amma right now. Da ta sani flight ‘din ranar ta nema ba na next day ba. Ta kwanta lamo a kan gado haka kawai sai idanunta yake gano mata Turaki rungume da Shaheeda suna wasu al’amura masu girma. Takaici da haushi wanda kai tsaye za’a iya kira kishi suka rufe ta duk da ita bata yarda kishin take ba.
Shaheedah na gama yi masa abincin suka fice tare ya sauke ta a school kafin ya nufi office ‘dinsu.
Ayra kuwa ta da’de kwance a d’akin tana jin wani irin tafasar zuciya a ranta, kafin ta sake duba Internet ta ga ta samu flight da zai tashi 6:30 na safe. Ta saki ajiyar zuciya gwara ta tafi ta je ta gaya ma Uwars ba aure a tsakaninsu yanzu ta sahalawa kanta auren idan yaso idan ya shirya neman aurenta ya faro daga farko ba mamaki ya san mahimmancinta lokacin. Ta sake lumshe idonta tana tunanin yarda zata ja masa aji, tunda ba zata rabu da shi ya yi mata a yanzu ita da kanta ta amince tana son sa, amma ya kamata ta nuna masa Ayra Gaya ba karabitin matan da ya saba kulawa a titi ba ce, Ayra Gaya mai quality ce ajin farko. Kuma sai ta kafa masa shara’din daga ita ba zai sake kula kowace mace ba da sunan yi mata kishiya.
Sai dare ya dawo gidan, bai kuma nemeta ba don haushinta yake ji sosai. Ya isa kan dinning yana bu’de warmers d’in har a lokacin abincin safe ne a ciki alamar bata sake wani girkin ba, idan ma ta yi to iya cikinta ta yi wa. Ya ‘dan tab’e baki yana sakin ajiyar zuciya, ji yake kamar ya je ya kai kanta inda take Amma yana tsoron abinda zai biyo baya, don baya son yana kusanta kansa da ita shi ka’dai ya san azabar da take ba shi. Ya shige bedroom ‘dinsa kawai ya kulle.
Tana idar da sallah ta ja k’aramar trolley ‘dinta don ba duka kayan ta ‘diba ba ta fice da sauri bayan cab d’in da ta yi order ya gaya mata ya iso. Tana fita ta ja masa gidan ta kulle don ta tabbatar zuwa lokacin ya koma barci.
Ba su da’de da isa airport ‘din ba jirginsu ya tashi. Ayra ta saki ajiyar zuciya tana jin wata salama a zuciyarta da tunanin zata ‘d’aga hankalin Turaki. Kuma direct wajen Ummeey zata fara zuwa kafin ta isa wajen Amma.
Sai 9:00 ya fito daga ‘dakin sai zabga k’amshi yake a gaggauce ya isa dinning sai dai yana bu’de warmers ‘din ya ga still abincin jiya ne a ciki. Da sauri ya juya yana k’arewa falon kallo ba abinda ta gyara a cikinsa bai san sanda ya isa bakin k’ofar ‘dakinta ba yana fatan Allah yasa lfiya. Yana murza handle ‘din ya ji shi a bu’de mamaki ya kama shi yarda ya ga yanayin ‘dakin komai a hargitse ga k’ofar toilet a bu’de alamar bata ciki. Hanjin cikinsa ne ya juya cikin tashin hankali ya isa kan gadon inda ya hango takarda a ajiye. Hannunsa