Chapter 36 Reading TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt Arewa Novels

TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Hausa Book Store

Chapter   36 / 45

105K to 108K   out of 132.1K words

y’ay’ana daga yau na zare sunan sa daga matsayin mahaifinsu, bana buk’atar ya sake kusanto inda nake ko ya kira kansa Uban y’ay’ana, Allah ya isa tsakanina da shi kuma In sha Allahu sai Allah ya saka min.” Daga haka ta ja y’ay’anta ta mik’e don ko garin Shagogon bata son gani, ranta a b’ace ya ke sosai. Haka nan suka bar garin Shagogon bayan ta masa kallon da ta kira na k’arshe don bata jin ko ita ko ahalinta wani zai k’ara ziyartar garin. Kabiru ma a ranar mutanen garin suka masa tofin Allah tsine suka raka shi har da masu jifansa shima ya bar garin zuciyarsa cike da dana sani da tarin nadama. Daga lokacin kuma komai ya caku’de masa, duk abinda ya tab’a madadin riba in dai da sunan kasuwanci ne sai dai ya tafka gagarumar asara. Har ya dawo matalauci na bugawa a jarida ‘daya matar ta zube masa yara uku maza ta bar gidan sai Uwar gidansa da take zaune da shi da da’di ba da’di don ita ta zama mijin shi kuma yake mata biyayya kamar mata. Yaransa maza kuwa gaba ‘d’aya ba na gari a cikinsu, ba kuma sa tausaya masa, daga mai shaye-shaye sai tantirin b’arawo da ‘dan daba.


Talatu kuwa kafin ta samu ta nutsu an ‘d’au lokaci Ayra kanta sai da ta dinga kaita ganin likita sabida yarda kanta yake nema ya tab’u kullum a cikin razana da firgita take, ta kuma sakawa kanta tsanar Maza gaba ‘daya. Ta zama mara sukuni mara magana daga ita har Majeeda da sauran y’ay’an sai da Amman ta saka aka dinga musu addu’oin da saukar alkur’ani sannan suka samu zuciyarsu ta daidaita. Suka koma makaranta Ka’in da na’in. Don su Majeedah har sun fara jami’a ita da Zainab. Companynsu na k’ara hab’aka da arziki. A lokacin ne suka samu mazajen aure masu son su da gaske kuma duka masu hali ne, duk da an sha hak’ilo kafin dangin mijin su yarda a cewarsu y’a’yan mata ne, Kamilu ne ya kai su har garin Shagogo suka ga asalin su sannan suka amince. Ita kuwa Majeeda mijinta bai da uwa bai da Uba sun rasu sai y’an uwa don haka ba wata matsala da aka samu a danginsa aka yi komai cikin kwanciyar hankali, duk da Amma bata yarda ba sai da ta kirasa ta gaya masa k’addarar da ta fa’dawa Majeeda. Bai ce komai ba don ya san k’addara Kuma shi soyayyar Majeeda a jininsa take ba don budurci yake son ta ba, ya ce ya ji ya gani yana sonta a haka zai aureta. Amma ranar sai da ta raba dare tana sallah don farin ciki. Haka aka aurar da su cikin farin ciki kuma suke zaune k’alau a gidajensu. Bayan shekara guda kuma Aysha ma ta samu miji shima mai hali da wadata itama aka aura mata Justice Abdul Kareem Har’do. Ya rage daga Jidda sai Ayra. Ayra har mamaki suke bata idan ta ga sun yi aure, don ita bata ji a duniya akwai mijin da takewa kallon salama ta tsani maza sosai.

Tana Ss 3, JIDDA na level 1 aka yi auren Jidda da wani ‘dan majalisa da ya mutu a kanta yana da ku’din gaske. Amma har tsoron aurensa take ji, amma Jidda ta kafe sai shi, haka Amma ta hak’ura ta aurar da ita bayan ta tabbatar da nagartuwar halayensa. Ya rage daga ita sai autarta. Bayan shekara guda ne suka gina gidan su da yake railway gidan da ya lamushe mak’udan ku’dade don ma Mazajensu sun taimka musu. Ayra kuma ta fara running business ‘din tun tana level one a Sky line don ta k’i yarda ta fita waje karatu, sannan ta toshe duk wata kafa da zai zama tana tarayya da ‘da namiji. Wannan shine tarihin su Ayra Gaya da duk wasu k’addarori da suka same su a rayuwa.


Tana kaiwa nan ta saki ajiyar zuciya tana gyara kwanciyarta. A hankali ta ce “Tabbas sai na rama Turaki.”



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖋𝖆𝖍 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊👌
Takaicin Uba.

53.



______


Turaki kasa runtsawa ya yi a daren, ya yi dakacen bai kusanci Ayra ba balle ya jangalo wa kansa, yanzu ji yake duk duniyar ta masa zafi. Da k’yar ya mik’e ya nufi parlour don gwara ya je ko barci ya samu ya yi a jikinta ya samu sukuni. Sai dai yana isa parlourn ya mur’da k’ofar bedroom ‘din da ya zama mallakinta sai ya ji sa a kulle gam. Tsayawa ya yi a bakin k’ofar cikin tashin hankali kafin ya ja k’afarsa da k’yar ya koma parlour ya yi zaune a kan kujera yana murza goshinsa da ya ya dameshi da ciwo. Tunani yake wani abu zai ma Ayra ya samu ta huce daga fushin da take yi da shi, ta kuma yafe masa ta amshesa a matsayin Mijinta kamar yarda zuciyarsa ta cika da tsananin son sa shima ya samu ya cilla nasa son ko da kaso ‘d’aya ne a cikin ‘dari cikin tata zuciyar. Wai ma me yasa tun a fari daga jin jita-jita ya amincewa kansa Ayran tana bin maza tun bai tabbatar da hakan ba. Ya runtse idonsa yana jan numfashi da k’yar kafin ya sake tashi ya ja jikinsa ya koma bedroom. Alwala ya yi ya tada sallah ya da’de a sujjada yana rok’on Allah ya sassauta zuciyar Ayra ta so shi koda a ce ka’dan ne.


Da asuba da ta mik’e ta ji jiknta wasai ba wannan ciwon da yake mata. Sai da ta yi sallah sannan ta shiga wanka. Ta fita parlourn gidan don tsaftacewa don sam bata son k’azanta ko ka’dan. Kan kace me? Wani irin sihirtaccen k’amshin turarukan wutan data kunna a burner ya kara’de lungu da sak’on gidan. K’amshin da ya kai har hancin Turaki da yake barcin wahala.

Tana gamawa ta sake shiga kitchen ta musu omelette da Chips sai ruwan tea mai kayan k’amshi da ta dafa. Ta tsaftace kitchen ‘din ta fito. Haka kawai sai ta samu kanta da tsananin annashuwa a zuciyarta. Wanka ta sake yi ta saka wani white skin tight d’inta da body hug red ta kama kanta ta k’ulle da red band. Lipsticks ta shafa nude colour ta bi kuma lungu da sak’o na jikinta ta ba’de da turaruka sannan ta koma saman gado ta kwanta tana danna wayarta har a lokacin layin Amma take nema amma still not reachable yake saka mata. Ta ‘dan ja tsaki ka’dan tana lalubar numberr wayar Yaya Deejah. Deejah da take zaune gefen Amman da aka samu ta farka da kyar daga dogon suman da ta yi ta mayar da kallonta kan wayar tana sakin murmushi don ta tabbata Ayra ce. Da fara’a ta ‘d’aga wayar “Ayrateey Ayran Amma, ya gida ya amarci hope dai an kashe boss ‘don yanzu an daina k’in maza.” Ayra ta ja tsaki a hankali kafin ta furta “Allah ya shiryeki Ya Deejah, k’in maza a jinina yake ba zan daina kin su ba. Ina Amma na yi kiranta severally bana samunta.” “Amma na lafiya ta ‘dan yi fever ne amma da sauk’i.” Cikin fargaba Ayra ta ce “Allah sarki Ammata mai ya sameta?” “Missing autarta, so ya Moscow ya honeymoon?” Tsaki Ayra ta saka ta ce “Yana garinku. Don Allah bani Amma ta.” Deejah ta ce “Idan muka gan ki da baby za mu ji labarin in da kika samo shi, ga Amman taki.” Ta fa’da tana kara wayar a kunnen Amma. Cikin k’arfin hali da son danne ciwon da take ji ta ce “Ayraty ya gida? Ya bak’unta kin tafi kin bar mu da kewa, don Allah Ayra ki kula ki bi Mijinki sau da k’afa kada ki yi abinda zai zo yana jin haushin ki, kin ji? Ba duka maza ne suka taru suka zama ‘d’aya ba irin Babanku.” Ayra ta share k’wallar idonta tana fa’din “Zan bi sa Amma ko don ke zan masa biyayya.” Amma ta ji da’di sosai ta ce “Allah miki albarka, ki kira Ummeey ku gaisa.” Ayra ta ce “To Amma, Zan kirata.” Sun da’de suna waya kafin Ayran ta sake tana sakin ajiyar zuciya. Ita bata ma da numberr Ummeey ‘din kuma ya kamata kam kamar yarda Amma ta ce ta kirata su gaisa don haka ta mik’e ba tare da ta ‘d’au mayafi ba, ta fice a haka zuwa parlour don ta ga idan ya fito ta amshi numberr Ummeey ‘din.

Ta kusan 30 minutes a parlourn Turaki bai fito ba, har ta gaji ta yi joining vidmate tana kallon wani film. Azababben k’amshin turarensa na companyn Rasasi ya ba’de parlourn. Tsaf yake cikin shigar English wears da suka sake fito da kyawu da cikar kamalarsa. Fuskarsa ta ‘dan tasa ka’dan ya isa kusa da inda take zaune ya zauna idanunsa cikin nata da yake lumshe su kamar mai jin barci. Kallon ne ya saka ta a wani yanayi ta yi saurin ‘dauke kanta murya a cunkushe ta ce Ina kwana? Madadin amsa mata, sai kawai ya bu’de mata hannunsa yana sakin tattausan murmushi “Zo nan mana na ji d’uminki Hayateey.” Ta ‘dauke kanta tana cuno bakinta kafin ta ce “ka manta alk’awarin da kai min kenan?” Ya ‘dan shafi gefen fuskarsa kafin ya ce “A yi hak’uri a min afuwa banda na gaisuwar safe, just hug and kisses pls.” Ayra ta ‘dauke kanta ya taso a hankali ya zo kusa da ita ya saka hannu ya mik’ar da ita “Ki min wannan favor ‘din daga shi ba zan k’ara ba.” Ayra ta runtse ido kawai tana jin yarda ya jata jikinsa ya rungume yana sakin ajiyar zuciya a hankali. Kafin ya kai mata sumbata a k’asan wuyanta kiss ‘din da yasa jikinta ya fara shaking. Turaki ya saka hannunsa a gefen wuyanta yana fa’din “Just a minutes Ayra pls.” Ya sake hugging ‘dinta sosai kafin ya saketa yana sakin murmushi. Shiru Ayra ta yi ta ja jikinta ta zauna a kujera. Turaki yana kallonta k’asa-k’asa a zuciyarsa ya ce “a hankali za ki kawo kan ki Ayra, wannan abin ba a iya ‘dauke masa kai.” A fili kuwa shafa gefen fuskarta ya yi a kunne ya ra’da mata “That’s my Angel. Oya zo mu je mu yi break fast, ko na ‘dauke ki.” Da sauri ta girgiza kai “No I will go by myself.” Ta fa’da cikin kakkarwa murya. Turaki ya saki smilling kawai ya wuce Dinning. Ayra kuwa ta da’de zaune kafin ta samu nutsuwa ta bi shi Dinning ‘din. Idanunsa a kanta har ta zauna yana ha’da tea yana kallon ta Jefi-jefi kafin ya ce “Kun yi waya da gida?” Ta ‘d’aga masa kai “Kin zama kurma ne?” Ta ‘dago kai tana kallonsa. Ya shigar da idonsa cikin nata yana sake narkar da duk wani saran k’arfin da take da shi. “Ki min magana.” Da sauri ta kawar da kanta murya ciki-ciki ta ce “Mun yi, ka bani numberr Ummeey ina son kiranta.” Hannunta da ta ke k’ok’arin zuba sugar ya rik’e yana dubansa “Me yasa ba ki yi lallen biki ba?” Ta janye hannun tana jin shock ‘din da ya biyo bayan hannun “Bana ra’ayi.” “Ko kuma saboda za ki auri mak’iyinki ba.” Ta ‘dago da sauri tana kallonsa. Ya ‘dan saki murmushi “Hakane mana, Right?” Samun kanta ta yi da saurin mik’ewa ta bar wajen don ba zata jurewa wannan sabuwar ‘dabi’ar ba. Turaki ya bita da kallo yana sakin murmushi a hankali kafin ya fisgota da k’arfi ta fa’da jikinsa ya saka hannu ‘d’aya ya yi hugging ‘dinta ‘Dayan kuma yana d’iban omelette ya kai bakinta idanunta a runtse ta tauna abinda ya saka mata kafin ta yi saurin mik’ewa ta ce “Naga alama ba zaka iya cika alk’awarin mu kawai zan tafi kada ka saka na fara abinda ban shirya ba.” Ya mik’e da sauri ya sha gabanta “Zan iya mana, waye ya ce miki ba zan iya ba? Wannan Ai ba komai bane ba dai zan yi having sex da ke ba sai dai idan kin amince da kan ki. Wannan shine alk’awarin da na miki.” Ta janye jikinta da yake k’ok’arin rik’ewa. “Ni dai na gaya maka bana so” murmushi ya yi ya cikata yana fa’din “Shikkenan to zan yi aure dama Shaheedah ta matsa min, anan neighbor suke, so zan nemi aurenta kawai don ba zan iya sake rik’e kaina ina ganin ki kusa da ni ba, da na aikata haramci kuwa gwara na yi auren.” Ya fa’da yana shafa gashin idanunta da suke kulle “Na amince ka yi auren in dai ba zaka kusanceni ba.” Turaki ya saki ajiyar zuciya yana mik’ewa ha’de da kai wa lips ‘dinga peck “Okey thanks, zan samu Shaheedah mu yi magana, bari na je office sai na dawo.” Sai da ya juya Ayra ta bu’de idanunta tana kallon bayansa, yana juyowa suka ha’da ido ta yi saurin ‘dauke kanta. Shi kuma ya fita kafin ya shiga mota ya tafi office sai da ya kira numberr Shaheedan ya ce mata za su yi magana idan ya dawo. Sannan ya shiga mota ya tafi office.




_________\

Jikin Amma ne ya yi tsanani sosai, har abin yafi k’arfin likitan da yake kula da ita. Don haka ya dubi Ummeey bayan sun shiga office ya ce “Hajiya na son kamu wa da ciwon zuciya, don jininta ya hau sosai tun kafin abin ya yi nisa akwai wani special Doctor da ya dawo daga germany last week yana aiki a national hospital why not na samar muku appointment ku kaita can.” Ummeey da sauri ta ce “Bakomai Doctor ka samar mana idan yaso ko gobe sai mu yi booking flight mu wuce, dama da yaranta mazauna Abujan duk muna nan tare da su, to zaman can ‘din ba zai mana wuya ba.” Doctor ya girgiza kai kafin ya ‘daga waya ya kira Doctorn da ya kasance amininsa. Bai sha wani wahalar samar musu appointment ba za su je su gan shi gobe..


Flight ‘din 7:00 suka bi zuwa Abuja da Amma da yaranta gaba ‘d’aya sai Ummeey da Tasleem.

Private room suka amsa don su samu sakewa sosai. K’arfe hu’du da Rabi likitan ya nufi ‘dakin Amman don ya dubata.

Cikin takunsa na nutsuwa yake tafiya kana ganinsa ka ga kammalallen mata shin Dattijo mai ji da ilimi ya tura k’ofar bayan ya yi nocking ya shiga. Amma da idonta biyu a lokacin ta sauke ganinta akan mutumin da yake tsaye wanda ake kira Doctor J. Cikin muryar ru’dani Amma ta ce “Jabiru?” Shima idanunsa bu’de ya ce “Anty Talatu…..”



𝕹𝖆𝖟𝖊𝖊𝖋𝖆𝖍 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊✍️
Takaicin Uba….

54.


Tsananin mamaki yasa Talatu mik’ewa da ‘dan hanzari duk da nauyin da k’irjinta ya mata. Da sauri Hameeda ta dafata tana fa’din “Be careful Amma.” Shi Kansa Jabirun an hanzarce ya ‘daga k’afarsa ya Isa Inda Talatun take cikin tsananin farin ciki.
Su Majeedah kuwa binsa suke da ido saboda ita da Zainab ba zasu mance kamanninsa ba, don da wayansu sanda ya bar gida. Yana nan yarda yake a farin bafulataninsa sai da ya ‘dan manyanta ka’dan hakan ma sai ka lura da kyau zaka ga y’ar furfura tsilla-tsilla a gemunsa. Ya yi kyau jikinsa ya murje kana ganinsa ka san yana cikin kwanciyar hankali da rufin asirin rayuwa. Amma har a lokacin kallon mamaki take masa da jinjina girman Ubangiji Sarkin da ba ya barci kullum ta yi Sallah sai ta rok’i ubangiji ya bayyana mata Jabiru yasa yana raye cikin k’oshin lafiya. Murmushi ya k’i ‘daukewa daga fuskokinsu duka, a hankali Jabiru yake bin manyan yaran Amma da kallo ya ganesu tsaf musamman Majeeda, Zainab da Aysha. Deejah ce ma sai da ya waro ido yana kallon Majeedah ya ce “Auta ce ko?” Majeedah ta girgiza kai ta ce “Ba Auta ba ce Abba Jabiru, Auta na Moscow sunanta Ayra.” Ya ‘dan lumshe ido yana ‘dan durk’usawa ya gaida Amma. Amma ta shafa kansa tana fa’din “Alhamdulillah da wannan rana yau ga babban yaro na Jabiru a gabana Allah nagode maka.” Ya juya yana gaida Ummeey kafin ya sauke idonsa a kan Tasleem da take gaishe sa cikin siririyar muryarta haka kawai sai ya ji gabansa ya fa’di ya ‘dan maze yana dafa Hannun Amma. “Bari na duba ki Anty, kafin labari ya biyo baya, don na k’agu na ji bayan rabuwa da irin yarda rayuwa ta sauya muku na ganku cikin jin da’di da walwala fiye da yarda na dinga rok’a muku ubangiji. Wallahi kullum kuna raina ko lastweek sai da na yi niyyar zuwa Shagogo to ina tuna abinda aka min sai na ji sam bana sha’awar komawa garin.” Amma ta lumshe ido haka kawai sai ta samun kanta da jin sanyi a zuciyarta, wani dunk’ulallen abu da ya da’de da taruwa a k’irjinta ta ji ya fara raguwa a hankali, tun lokacin da wancan sharri da aka musu da Jabiru abin ya tsaya mata sai yau ya kau da ta ga Jabirunta fes cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali. Nauyin da zuciyarta ta yi ya ragu sosai da kaso Sittin cikin ‘dari bata da wata sauran damuwa yanzu a rayuwarta Ayranta ta yi aure kamar yarda take buk’ata kuma alamu sun nuna tana zaune lafiya a gidan Mijinta, ga Jabirunta yau Allah ya ha’data da shi. Me ye sauran burinta ganin dangin mahaifiyarta, ta ji zuciyarta ta bata amsa. A hankali ta lumshe ido tana fa’din “Shima zai cika In sha Allah.” Ta mayar da kallonta kan Jabiru da ta k’agu ta ji bayan rabuwarsa da gida ya yi da rayuwarsa har yanzu da yake durk’ushe a gabanta. “Jabiru Amma dai ka yi aure ko?” Jabiru ya saki murmushi yana murza gemunsa da ya masa kyau a fuskarsa “Ban yi ba Anty.” Ta waro ido tana fa’din “Me yasa Jabiru?” Ya girgiza kai “A duk sanda na je neman aure sai an buk’aci ganin danginsa da sanin asalina abinda ni kuma har abada na shafesu a tarihin rayuwata su kuma iyayen yarinya idan suka ji ba ni dangi sai su hana ni auren y’arsu. Wannan dalilin ya hana ni aure.” Amma ta saki ajiyar zuciya a ranta tana cewa Ina ma ba duka yaranta ta aurar ba tabbas da ta bawa Jabiru Mata. “Allah ya kawo ta gari tunda yanzu ga ka ga danginka. Ya labarin bayan

36 / 45